Newsroom Radio Jigawa

Newsroom Radio Jigawa Keeping you updated

18/06/2024

18-06-2024 STOWA
Hukumar samar da ruwansha a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa STOWA ta ce ta kashe kudi fiye da naira miliyan dari biyar da hamsin da tara wajen inganta samar da ruwansha a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na 2024
Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na cikar gwamnati shekara daya akan karagar mulki
Yace sun yi amfani da kudaden ne wajen gyaran gidajen ruwa 156 da kuma mayar da injiniya samarda ruwansha masu amfani da man gas zuwa hasken rana guda 19
Injiniya Adamu Garba ya kara da cewar daga watan shida na 2023 zuwa watan shida na 2024 , hukumar ta kashe kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari bakwai da ashirin da hudu
Manajan Daraktan yana mai cewar a shekara guda ta mulkin Umar Namadi sun gyara gidajen ruwa guda 314 akan kudi naira miliyan dari shida da tamanin, sun kuma mayar da gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa hasken rana guda 53 kan kudi naira miliyan dari shida da sabain
Haka kuma sun gina gidajen ruwa masu amfani da hasken rana kan kudi naira miliyan dari uku da sittin
Injiniya Adamu Garba kuma shugaban kungiyar Injiniyoyi ta jihar Jigawa, ya ce suna alfahari da cewar jihar Jigawa ce ta daya a samarda ruwansha mai tsafta a arewacin Nigeria kuma ta biyu a kasa baki daya

18/06/2024

18-06-2024 TAAZIYYA
Gwamna Mallam Umar Namadi ya bayyana rasuwar marigayi Alhaji Ibrahim Umar Dawakiji a matsayin babban rashi ga alummar musulmi
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokaci da ya kai ziyarar taaziyya gidan marigayi dake garin Makole dake karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano
Ya yi adduar allah ya ji kansa ya kuma baiwa iyalai da yan uwa hakurin jure babban rashi
Daga bisani kwamishinan ilmi matakin farko na jiha Dr Lawan Yunusa Danzomo ya jagoranci adduoi na musamman ga marigayi
Kafin rasuwarsa , marigayi Ibrahim Dawakiji na daga cikin na hannun damar tsohan gwamnan jihar Jigawa kuma ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar

18/06/2024

18-06-2024 COMMITTEE
Kwamitin aiki da cikawa na malamai da kuma maaikata na manyan makarantun jihar nan ya yaba da kokarin gwamnatin jiha na nadin shugabannin manyan makarantun jihar nan
Hakan na kunshe ne a cikin takardar bayan taron kwamitin da ya gudanar a kwalejin fasaha ta jihar Jigawa dake Dutse
Kwamitin ya bukaci maaikatar Ilmi mai zurfi ta jiha da ta hanzarta daidaita dokar kwalejojin fasaha da ta kwalejojin ilmi kan batun abin da ya shafi daukar aiki da jin dadin maaikata
Takardar bayan taron kwamitin mai dauke da sa hannun sakataren kwamitin Buhari Habu ta kuma bada shawarar sake rubutawa gwamna Umar Namadi bukatar biyan Karin albashi na kaso 25 da kuma 35 na malamai da maaikatan kwalejin Ilmi ta Gumel da kuma Kwalejojin Fasaha dake jihar nan k**ar yadda gwamnatin tarayya ta amince kuma take aiwatar a manyan makarantun tarayya
Haka kuma kwamitin ya nuna damuwarsa kan rashin sakin kudaden yan kungiya na watan Afirilu da gwamnati ta yi, wanda hakan ya kawo tseiko ga alamurran kungiyoyin manyan makarantun jihar nan
Daga nan kwamitin ya jaddada cikakken goyan bayansa ga kyawawan manufofi da kuma tsare tsaren gwamnatin jiha na bunkasa harkokin ilmi

18/06/2024

18-06-2024 condolence
Governor Mallam Umar Namadi has described the death of Alhaji Ibrahim Umar Dawakiji as a great lost to the entire muslim Ummah
Mallam Umar Namadi who visited the deceased residence at Makole town in Dawakin Tofa local government area prayed for the Almighty Allah to grant him eternal rest and the family to bear the loss.
Special prayers was offered for the deceased by the state commissioner for Basic Education Dr Lawan Yunusa Danzomo Alhaji Lawan Yunusa Danzomo
Until his death, Alhaji Ibrahim Dawakiji was close political associate of the former Governor Muhammad Badaru Abubakar
SMG/MAG

17/06/2024

17-06-2024 GWAMNA
Gwamnatin jihar Jigawa ta kwace dazukan gwamnati kuma za a bada aransu ga jama-a domin su yi noma
Gwamna Umar Namadi ya sanar da hakan a lokacin hawan bariki da mai martaba sarkin Dutse ya kai masa
Ya ce gwamnati ta kwace duk wani daji da aka bayar ba bisa kaida, kuma gwamnati ta kwace Makiyayu da burtalai na gwamnati kuma an haramta yin noma a cikinsu
Gwamnan ya cigaba da cewar an kafa kwamiti domin duba wannan lamari kuma tuni kwamitin ya bada rahotan wucin gadi
Gwamnan ya bayyana cewar shugabannin kananan hukumomi da Hakimai da Dagatai da masu unguwanni sune babbar matsalar da ke tattare da matsalar dazuka a jihar Jigawa
Mallam Umar Namadi yana mai cewar duk shugaban karamar hukuma ko Hakimi ko Dagaci ko mai unguwa da aka samu ya bada daji ba bisa kaida ba za a hukunta shi
Ya ce gwamnati zata kai doka majalissar dokokin jiha domin hana saran itatuwa a jihar jigawa
Gwamnan ya kuma ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada takin zamani tirela 80 domin rabawa alummar jihar Jigawa kyauta, yayinda ita gwamnatin jihar Jigawa ta sayo takin zamani domin sayarwa manoma a farashi mai sauki
Ya ce an kafa kwamiti domin sa ido wajen rabon takin zamanin na shugaban kasa da kuma wanda gwamnati zata sayarwa manoma

17/06/2024

17-06-2024 FAGAM
Kansilan mazabar Fagam kuma kakakin majalissar kansilolin karamar Hukumar Gwaram Alhaji Isa Usaini ya yi kira ga gwamnatin jaha da ta gyara kwalbatin dake tsakanin Kwarko cikin gari da Bagiya domin kawo karshen barazanar sa ga alumma.
Ya ce kwalbatin yana daf da karyewa wadda karyewar sa zai datse alaka da al'ummomin dake yankin.
Alhaji Isa Usaini Kwarko ya kuma jajantawa manoman da rairayi ya binne musu amfanin gona wadda hakan tasa manoman shinkafa a yankin suke sake shuka.
Kansilan na mazabar ta Fagam ya kuma jajantawa wadanda s**a gamu da iftila'in ruwan sama da ya yi sanadiya rushewar dakuna da kuma katangu
Alhaji Isa Usaini Kwarko ya yi ad du'ar Allah ya mayar musu da abin da su ka yi hasara da alherinsa.

17/06/2024

17-06-2024 FULATA
Wakilin mazabar Guri da Kirikasamma da kuma Birniwa a majalissar wakilai ta kasa Dr Abubakar Hassan Fulata , ya raba kudi naira miliyan talatin da bakwai a matsayin kudaden sayen raguna da kuma cefanan babban salla ga alummar mazabarsa
Daya daga cikin Hadiman dan majalissar, Abubakar Isyaku IMAC ya tabbatar da hakan ga wakilinmu ta wayar hannu
Yace an raba kudaden ragunan da cefanan sallar ne ga malamai da sarakuna da jamian tsaro shugabannin jamiyya da kungiyoyin siyasa dana addinai dana Fulani dana matasa dana mata dana media dana
Abubakar Isyaku IMAC yace daga cikin adadin kudaden an raba naira dubu ashirin da kuma talatin a matsayin kudaden cefanan salla, yayin da aka raba naira dubu hamsin hamsin da kuma dubu dari dari a matsayin kudaden sayen raguna
Hadimin na dan majalissar tarayyar, yace shi da kansa ya raba na kananan hukumomin Guri da kuma Kirikasamma, yayinda wakilin dan majalissar a karamar hukumar Birniwa Musa Muhammad Isyaku Birniwa ya raba naira miliyan goma sha biyu da dubu dari biyara matsayin kudaden sayen raguna da kuma na cefanan salla a karamar hukumar Birniwa a madadin Dr Abubakar Hassan Fulata
Ya kara da cewar an baiwa rabawa exco na jamiyyar APC na kananan hukumomin uku da shugabannin mazabu naira dubu ashirin ashirin domin yin cefana sai hukumomin tsaro da aka baiwa kowannensu naira dubu hamsin hamsin yayinda kungiyoyin addinin musulunci s**a sayi raguna

17/06/2024

17-06-2024 BKD
Kungiyar amintattu mai kula da marayu reshen karama Hukuma Birnin kudu ta kaddamar da rabon Naman layya ga marayu 350 mata da maza a karamar Hukumar Birnin kudu
A jawabin daya gabatar Shugaban kungiyar Alhaji Aliyu Abdullahi Mai-kwai. yace kungiyar ta zabo marayun da zasu amfana da naman layyar ne ta hanun Dagatai da kuma masu unguwanni domin samun saukin rabon da kuma samun cancantar wadanda ya k**ata a baiwa
Ya ce kungiyar tana tallafawa marayu da kayan abinci a lokacin azumi tare da daukar nauyin rashin lafiyarsu da kuma kaisu makaranta da sauransu
Daga nan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da masu hali dasu rinka bada gudunmawarsu ga kungiyar domin tallafawa marayu
Alhaji Ali Abdullahi ya ce kungiyar ta yanka shanu shida ga marayun
Ita kuwa wakiliya a kungiyar Hajiya Hadiza Abdulkadir Fanini ta yi kira ga masu hali dasu rinka taimakawa kungiyar dan tallafawa marayu
Shi kuwa Hakimin Birnin Kudu , Sarkin kudu Alhaji Garba Hassan Jibrin ya yabawa kungiyar bisa yadda ta ke gudanar da aiyukanta yadda ya k**ata

16/06/2024

16/07/2024 GOVERNOR SALLAH
Gwamnatin jihar Jigawa ta shawarci manoma dasu hanzarta yin shuka da wuri domin sak**akon hasashen daukewar ruwan damina da wuri
Gwamna Umar Namadi ya bada wannan shawara a sakonsa na barka da salla ga alummar jihar nan
Ya ce gwamnatocin jihohi dana tarayya a shirye suke su taimakawa manoma ta hanyar shawarwarin malaman gona da kuma sauran kwararru domin bunkasa noman abinchi
Malam Umar Namadi ya shawarci alumma dasu cigaba da yin adduoi domin kara samun zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a jiha da kuma kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma taya alummar musulmi murnar bukukuwan salla babba tare da bukatar yin koyi da halayen manzon tsira

16/06/2024

16/06/2024 IMAM DUTSE
Majalissar masarautar Dutse ta bi sahun takwarorinta na kasar nan wajen gabatar da sallar Idin layya
A hudubar da ya gabatar , Babban Limamin masallacin jumaa na Dutse Dr Musa Bala ya tunatar da gwamnati bukatar daukar kwararan matakai domin ganin ana dasa bishiyoyi domin kare kwararowar Hamada.
Ya ce sare bishiyoyi yana kawowa gurbacewar muhalli da dumamar yanayi da kuma hana bahaya a bainar jama’, inda ya ce hakan ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.
Haka kuma Dakta Musa Bala ya shawarci jama’a da su cigaba da yiwa shugabanni biyayya domin su sauke nauyin da ya rataya a kan su.
Sallar Idin ta masarautar Dutse ta samu halartar Gwamna Mallam Umar Namadi da wakilan majalissar zartarwa da shugabannin kananan hukumomi da sauran alummar musulmi

16/06/2024

16/06/2024 D/GWAMNA
Gwamnatin jihar Jigawa tace tana shigo da managartan tsare-tsare domin tallafawa Al’umma wajen inganta samar da abinci.
Mataimakin gwamnan jiha Injiniya Aminu Usman Gumel ne ya bayyana haka a sakon sa na barka da Sallah a masarautar Hadejia.
Ya ce samar da abinchi da kuma inganta tsaro na daga cikin kudurorin gwamna Malam Umar Namadi 12 na inganta rayuwar al’umma , dan haka ya kara da cewa gwamnati tana aikin jinga domin magance ambaliyar ruwa a garin na Hadejia.
A jawabin sa Mai Martaba Sarkin Hadeji Alhaji Adamu Abubakar Maje ta hannun Galadiman Hadejia Alhaji Usman Abdulaziz ya yi kira ga gwamnati data tallafawa alumma wajen inganta harkar noma da tsaro da samar da ayyukan yi da kuma magance matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa tare da yabawa gwamnati bisa aiwatar da ayyukan alkhairi a masarautar.
Tun farko a jawabin sa shugaban karamar hukumar Hadejia Alhaji Abdulkadir Bala T.O ya godewa gwamnati bisa ayyukan alkhair a masarautar.
Mataimakin gwamnan na tare da kwamishinonin yada labarai da na kasa da safiyo da kuma sauran jami’an gwamnati.

16/06/2024

16/06/2024 EMIR
Mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Hamim Nuhu Sanusi ya hori alummar masarautar sa da su guji toshe magudanan ruwa domin kaucewa afkuwar ambaliyar ruwa.
Sarkin ya bada wannan shawar ce a sakon sa na barka da Sallah ga alummar masarautar sa a fadar sa dake Garu.
Alhaji Muhamadu Hamim Nuhu ya kuma gargadi manoma da makiyaya da su zauna lafiya da junan su kuma kowa ya tsaya a muhallin sa domin kara samun wanzuwar zaman lafiya.
Daga nan sai sarkin ya taya zabbabu k**a daga kan shugaban kasa zuwa Gwamnoni da yan majalisun tarayya dana jiha da shugabannin kanannan hukumomi da kansiloli murnan sallah babba tare da adduar Allah ya cigaba dafa musu.

16/06/2024

16/07/2024 GOVERNOR SALLAH
Jigawa state government has advised farmers to commence early preparations for raining season farming activities as reports indicates that the rain fall would not last long.
Governor Umar Namadi gave the advice in his sallah message to the people of the state.
He said both the state and federal government are ready to assist the farmers with extension services and other technical support to boost agricultural production for food security and wealth creation.
Malam Umar Namadi therefore called on the people to continue praying for peace, unity and progress of state and the nation at large.
The governor also congratulates Muslims ummah for observing the Eid El Mubarak and urged them to reflect the teachings of prophet Muhammad S A W.
Governor Umar Namadi and members of the state Executive council were among thousands of muslims ummah who attended the Dutse Eid prayer ground.
COV/SMG/MAG

16/06/2024

16-06-2024 KIRIKASAMMA
Kirikasamma local Government council has paid three point seven million naira as monthly allowances to its 182 casual staff.
Head of water and sanitation Department Alhaji Muhammad Maisamari made this known to newsmen
He said one point two million naira was paid to 60 non technical staff working under the department
On his part the Coordinator primary health care development agency in the area, Musa Abdullahi Diladige said 65 technical casual staff and 57 Non technical staff were employed to work at various health facilities across the area .
He said the 65 certified technical staff are receiving 20,000 Naira as monthly allowances while the 117 Non technical staff received 10,000 respectively.
In his remarks the council chairman, Alhaji Isah Adamu Matara said the gesture was part of the council commitments to reduce unemployment.
PR/IO/MAG

16/06/2024

16-06-2024 MINISTRY
Jigawa state ministry of women affairs and social development, has spent over one million naira for the supply of two bulls and a ram to the inmates of Jahun VVF Center, Kafin Hausa Reformatory School and Dutse Orphanage Home to celebrate Eid el Kabir.
The Commissioner of the ministry, Hajiya Hadiza Tamuri AbdulWahab disclosed this when she visited the centers.
The Commissioner said in addition to the slaughtering of animals, foodstuffs and a token of ten thousand naira were also given to each of the centers.
She added that, the gesture was aimed at putting smiles at the faces of VVF patients, Reformatory children and the orphans during the festive period.
The Commissioner also inspected the renovation work at Reformatory School, Kafin Hausa, where she expressed satisfaction on the work done.
PR/SN/MAG

16/06/2024

16-06-2024 GUMEL
The Emir of Gumel Alhaji Ahmad Mohammad Sani has directed District,Ward and Village heads to prevent illegal cutting of trees in their domain to avoid desert encroachment.
He disclosed this in his Sallah massage.
Alhaji Ahmad Mohammad Sani then calls on Farmers and headsmen to respect each other’s right for peace to continue reigning in the State.
The Emir urged parents to enroll their children into Islamiya and Western education schools.
Alhaji Ahmad Mohammad Sani thanked Governor Malam Umar Namadi led administration for the provision of infrastructure in the Emirate and the State at large.
In his address, Governor Malam Umar Namadi represented by the secretary to the State Government Malam Bala Ibrahim said the State Government has employed over six thousand Youth as permanent and pensionable staff as J-teach,J-health and J-agric.
He said this is was in line with Governor's 12 points agenda and solicit for the continue support and cooperation of the Emir and the people of the Emirate to make the 12 agender a reality.
Earlier in his welcome address, the acting chairman of the area Haladu Musa Mele said the local Government has recorded achievements during his seven months stewardship.

KID/MAG

15/06/2024

15-06-2024 DUTSE
Majalissar masarautar Dutse ta fitar da jaddawalin bukukuwan babbar salla
Babban dan majalissa kuma Galadiman Dutse Alhaji Basiru Muhammad Sanusi ya sanar da hakan ga masu dauko labarai na fadar sarki
Yace za a gabatar da sallar Idi da misalin karfe takwas da kwata na gobe lahadi , sannan tawagar mai martaba sarki zata wuce zuwa Garu domin gabatar da jawabin barka da salla
Alhaji Basiru Muhammad Sanusi ya kara da cewar idan an tashi da ruwan sama za a gabatar da sallar Idin a babban masalaci
Galadiman na Dutse ya cigaba da cewar a ranar Litinin mai martaba sarki zai gabatar da hawan bariki inda za a gabatar da jawabai a dandalin taro na Muhammad Sanusi Bello dake daura da gidan gwamnati
Haka kuma idan an tashi da ruwan sama za a gabatar da hawan na bariki ta cikin motoci
Sannan kuma za a gudanar da hawan daushe a ranar talata, wanda inda an samu ruwan sama za a dage hawan zuwa washegari laraba
Galadiman na Dutse ya taya alummar musulmi murnar bikin babbar salla

15/06/2024

15-06-2024 BIRNIN KUDU
Wakilin mazabar Birnin Kudu a majalissar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim ya raba ragunan layya da kuma kudaden cefanan babban salla na kimanin kudi naira miliyan bakwai ga limamai masalatai da kuma masu ruwa da tsaki na jamiyyar PDP na mazabarsa.
Dan majalissar ya sanar da hakan ne a lokacin ganawa da wakilinmu ta wayar hannu.
Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim ya ce an raba ragunan sallar layyar ne ga limamai da Na-Iban masalatan juma=a dake mazabarsa
Haka kuma suma shugabannin jamiyyar PDP na mazabu dana karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki sun amfana da rabon ragunan
Ya kara da cewar ya baiwa matasa kudaden cefanan sallar layya, domin gudanar da bikin sallar cikin annashuwa
Dan majalissar ya ce hakan na daga cikin kudirinsa na tallafawa alumma a lokacin bukukuwan salla babba da kuma karama
Inda kuma ya bukaci alummar musulmi da su yi amfani da bukukuwan sallar Idin ta layya wajen yin adduoi domin kara samun zaman lafiya da kuma bunkasar tattalin arziki

15/06/2024

15-06-2024 HIGH COURT
Babbar kotun jiha mai lamba ta shida dake zamanta a garin Birnin kudu ta zartar da hukuncin kisa akan wasu matasa uku masu suna Ahmad Abubakar da Dan Ladi Buba da kuma Yakubu Usman dake Maiduguri bisa hadin baki wajen kashe marigayi Yakubu Ibrahim
Alkalin kotun mai sharia, Musa Ubale, yace lefi na biyu da matasan s**a aikata sun hadar da yiwa marigayi fashin wayar hannu da kudade da kuma sace masa mota da dauri da kuma yi masa duka
Matasan sun gudanar da aika aikar ne a ranar 30 ga watan Agusta na 2021 a kan hanyar Kantoga zuwa Birnin-kudu.
Kotun bayan ta saurari shedu hudu da gabatar da hujjoji, ta zartar musu da hukuncin daurin rai da rai da kuma daurin shekaru 21 kowannesu a gidan gyaran hali ba bu tara na hukuncin aikata fashi da kuma zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya
Kotun ta basu waadin watanni uku domin daukaka kara idan basu gamsu da hukuncin ba

15/06/2024

15-06-2024 STOWA
Hukumar samarda ruwansha a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa STOWA tace ta kashe kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari da sittin da hudu wajen gudanar da aiyukan samar da ruwan sha a tsakanin watan shida zuwa watan Disamba na 2023
Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na musamman na cikar gwamnati shekara guda akan karagar mulki
Yace aiyukan samarda ruwan sha da s**a gudanar da kudaden sun hadar da gyaran gidajen ruwa 157 da sauya gidajen ruwa masu amfani da Injina zuwa masu amfani da hasken rana guda 34 da samar da sabbin tashoshin bada ruwansha guda talatin karkashin aiyukan mazabu
Injiniya Adamu Garba ya ce hukumar tana da gidajen ruwa masu amfani da man gas 527 , inda daga ciki tuni ta mayar da guda 287 zuwa masu amfani da hasken rana
Ya bayyana kudirin hukumar na cigaba da samar da ingantaceen ruwan sha ga matsakaitan garuruwan jihar nan
Manajan Daraktan ya kuma yabawa kwamishinan albarkatun ruwa na jiha bisa hadin kai da goyan bayan da yake baiwa aiyukan hukumar a kowane lokaci

15/06/2024

15-06-2024 JNI
Reshen Jihar Jigawa na kungiyar jama’atu Nasril Islam ya aike da sakon barka da salla ga alummar musulmi bisa murnar zagayowar ranar Babbar Salla
Sakon barka da sallar mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Ahmed Muhammad Babangida ta bayyana sallar layya a matsayin lokacin ibadu da s**a hadar da aiyukan Hajji, da sallar Idi da kuma yanka layya
Ya bayyana cewar sallar layya ta bana tazo cikin matsin rayuwa da ake fata Mahajjata da sauran al’umma Muslmi za su yi amfani da damar wajen rokon Allah dan samun sauki
Kungiyar ta bukaci musulmi su kara kusan tuwa ga Allah da kuma yin adduoi domin shawo kan halin matsin da ake ciki
Sanarwar ta bada sgawarar cewar wani bangare da za a kara inganta rayuwar jama’ar kasar nan shine wayar da kai da cusawa jama’a kishin Kasa da yin aiki tukuru da baiwa muhukunta goyon baya da shawarwari kan yadda za’a shawo kan matsalolin tattalin arziki da na tsaro da na muhalli, da na zamantakewa
Kungiyar ta bukaci masu hali dasu rinka taimakawa mabukata musanman ta fuskar ciyarwa da tufatarwa a wadannan raneku uku masu albarka ta yadda masu karamin karfi za su yi salla cikin walwala da jin dadi

15/06/2024

15-06-2024 BKD
Kungiyar Matasa masu Rajin Kawo Cigaba ta karamar hukumar Birnin Kudu ta shirya taron fadakarwa kan matsalolin da ke biyo bayan ritaya daga aikin gwamnati a tsakanin ma'aikata.
A jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Isyaku, ya ce sun shirya bitar ne domin fadakar da ma'aikatan da su ke kusa da ritaya daga aikin gwamnati da kuma wadanda ba su dade da yin ritaya ba domin su gane matakan da su ka k**ata su dauka dan samun kwanciyar hankali bayan kammala aikin gwamnati.
Da ya ke gabatar da makala a lokacin taron, Farfesa Gambo Babandi Gumel na Jami'ar Tarayya da ke Dutse, ya yi bayani kan yadda yak**ata ma'aikaci ya dauki matakin koyon sana'a ko kasuwanci tare da zuba jari domin rayuwarsa ta cigaba da gudana bayan ritaya daga aikin gwamnati.
A sakon sa ga taron, Farfesa Usman Da'u Aliyu ta hannun Limamin Ahalussunah Ustazu Mahmoud Hassan, ya bayyana irin matakai nagari da mutum ya bi a lokacin kuruciyarsa a matsayin matakin samun nasara a lokacin tsufa.
A nasa jawabin, Hakimin Birnin Kudu Sarkin Kudu Alhaji Garba Hassan Jibrin, ya godewa kungiyar bisa hangen nesanta na shirya wannan taron lakca bisa la'akari da dinbin ma'aikata da ke kusa da ritaya da ma wadanda su ka yi ritaya a fadin karamar hukumar.
Taron ya samu halartar Hakimin Zareko Magawatan Dutse Alhaji Salihi Sulieman da Shugaban Muryar Birnin Kudu Jarman Birnin Kudu Alhaji Balarabe Sa'id da ma'aikata da ke bakin aiki da wadanda su ka yi ritaya daga sassan karamar hukumar.

15/06/2024

15-06-2024 BUJI
Kimanin magoya bayan jamiyar APC 130 ne s**a amfana da tallafin Dogaro da kai Na shugaban karamar Hukumar Buji Alhaji Abdullahi Suleiman Yayari wada ya raba a sakatariya karamar Hukumar
Tallafin dogaro da kan ya hadar da Babura 10 da keken dinki 10 da 10 Injinunan Markade 10 da bandiran kwano 37 da kuma siminti buhu Dari.
An dauki mutane dai dai daga kowacce mazaba domin karbar babur
Tunda farko a jawabinsa na maraba shugaban jamiyar APC Na karamar Hukumar Buji Malam Inuwa Gwadayi ya yabawa shugaban karamar Hukumar bisa yadda yake tallawa yam jamiyya.
A nasa jawabin Dan majalisa jihar jigawa mai wakiltar karamar hukumar Buji , Sale Baba Buji yace Gwamna Umar Namadi da shugaban karamar Hukumr suna gudanar da salon mulki dake tafiya kai tsaye ga yan dangwale.
Da suke jawabin godiya a madadin wadanda s**a sami tallafin Hajiya Jamila sabo Gambasha da Auwalu BBC sun yabawa shugaban karamar Hukumar bisa wannan tago mashi da yayi musu na Dogaro da kai.

14/06/2024

4-06-2024 FATU
Kwamitin tattara fatun layya karkashin kungiyar Izala reshen jihar Jigawa ya ware cibiyoyin tattara fatun layya fiye da dubu biyar da dari biyu a jihar Jigawa
Shugaban kwamitin Dr Zaharadeen Haruna ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na musamman
Dr Zaharadeen Haruna yace an ware manyan cibiyoyi 260 da kuma kananan cibiyoyin fiye da dubu biyar na tattara fatu a fadin jihar nan
Dr Zaharadeen Haruna yu ce a bara kungiyar ta yi kokari wajen tara fatun layya duk da hujewar da fatun s**a yi, inda ya kara da cewar inda ta tara ta fiye da miliyan uku yayinda s**a tara ta fiye da naira miliyan dari da bakwai a kasa baki daya
Dr Zaharadeen ya kuma yi bayani akan yadda ake amfani da kudaden a sabuwar jamiar Izala da ake ginawa a garin Hadejia
Ya kuma bukaci alumma musulmi dasu bada tasu gudunmawa domin samun lada anan duniya da kuma gobe kiyawa

14/06/2024

14-06-2024 WOFAN
An yabawa kungiyar mata ta WOFAN ta jihar Jigawa da kuma dakin gwajin jinni na Mys diagonistic dake Ringim bisa bikin da s**a gudanar na ranar bada tallafin jini kyauta ga mata masu juna 2 da kuma kananan yara tare da masu hadarin mota domin ceto rayuwarsu.
Mataimakin gwamna na musamman kan kula da lafiyar jama'a Dr Atiku Hafiz ne yayi yabon yayin bikin ranar bada tallafin jini ga jama'a wanda kungiyar WOFAN ta jiha tare da dakin gwajin jini na mys diagnostic s**a shirya.
A jawabansu daban daban Daraktocin kula da dakunan gwaje gwaje da na harkokin lafiya Aliyu Usman Turaki sun bayyana muhimmancin ranar bada tallafin jinni ga rayuwar jamaa tare da bada shawarwari kan harkar kula da lafiya
A jawabinta shugabar kungiyar WOFAN ta jiha Hajia Bilkisu Aujara ta ce sun shirya bikin ne bisa muhimmancin ranar da take dashi domin tallafawa masu rangwamen gata tare da godewa shugabanni da sauran alumma da s**a halarci bikin

14/06/2024

14-06-2024 STOWA
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar samar da gidan ruwa a garin Gwari dake karamar Hukumar Dutse
Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa STOWA Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ta cikin shirin Radio Jigawa na musamman na cikar gwamnati shekara guda akan karagar mulki
Yace gwamna Umar Namad ya amince da bada aikin akan kudi naira miliyan casein
Injiniya Adamu Garba yana mai cewar a yanzu hakan dan kwangilar da aka baiwa aikin ya fara aikin haka rijiya a garin na Gwarin
A cewarsa hakan na daga cikin kudirin gwamna Umar Namadi na wa

14/06/2024

14/06/2024 HISBA/JG
Rundinar Hisba ta Jihar Jigawa za ta tura dakarunta guda dari da ashirin zuwa wuraren ibada da sauran muhimman wurare a fadin Jihar nan domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan babbar Sallah.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamandan rundinar, Ustaz Dahiru Ibrahim Garki ya rabawa manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundinar Muhammad Sale Korau.
Sanarwar ta gargadi masu wasa da abubuwan fashewa na Nok-out dasu guji tsorata mutane a lokacin bukukuwan Sallah, tare da yin kira ga iyaye su rika kula da zurga-zurgar ‘ya’yansu domin ganin an yi bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

14/06/2024

14/06/2024 FOUNDATION
Fiye da mata zawarawa da masu karamin karfi da kuma marayu dari takwas ne da aka zabo daga kananan hukumomi hudu na masarautar Gumel s**a amfana da tallafin naira dubu ashirin-ashirin karkashin shirin tallafawa masu karamin karfi na Gidauniyar Nazifi Sani Danmajalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin masarautar Gumel.
A jawabin data gabatar a wurin bikin raba kudaden Uwar Gidan Danmajalisar, Hajiya Khadija Nazifi Sani, ta ce tallafin zai bunkasa rayuwa da na tattalin arzikin wadanda s**a amfana da tallfin.
Hajiya Khadija Nazifi Sani ta bayyana damuwa ganin yadda mata da masu karamin karfi ke fuskantar matsalolin rayuwa, inda ta bukaci wadanda s**a amfana da rabon kudaden su yi cikakken amfani da su wajen kafa kananan sana’oi domin su kasance masu dogaro da kan su.
Uwar gidan Danmajalisar ta ce da yardar Allah Gidauniyar zata cigaba da tallafawa mata da masu karamin karfi da kuma marayu.
A jawabansu na godiya wasu daga cikin wadanda s**a sami tallafin sun godewa Gidauniyar bisa karamcin data yi musu, tare da alkawarin sarrafa kudaden ta hanyar data da ce.

Address

Kiyawa Road Dutse
Dutse

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Newsroom Radio Jigawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Newsroom Radio Jigawa:

Share