21/10/2023
(๐๐๐๐๐ฅ๐๐ ๐๐๐๐๐ก ๐ฃ๐๐ข๐ง๐จ๐ก๐)
Gwamnan jihar Kano
Abba Kabir Yusuf ya tura Ya'yan Talakawan jihar Kano 101 zuwa kasar India
Domin karo ilimi mai zurfi yaran da aka zabo bisa kokari da cancantan su
SHIRIN INGANTA ILMI A KANO: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida ta bi gida-gida ta kwashi ษalibai 1001 zuwa karatu ฦasashen waje
Gwamnatin Jihar Kano ta zaษi ษalibai 1001 da ta fara ษaukar nauyin karatun na digiri na biyu a ฦasashen waje.
Yayin da wasu za su yi na su karatun a Indiya, wasu kuma a Uganda za su yi na su kwasa-kwasan daban-daban.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ฦaddamar da Shirin Bada Tallafin Karatu ฦasashen Waje, wanda aka fara ranar Alhamis da jigilar ษalibai 550 daga Kano.
Gwamna Kabir ya ce ya ษora wannan gagarimin aikin alheri ne daga inda tsohon Gwamnan Kano, kuma madugun Kwankwasiyya, Rabiโu Kwankwaso ya tsaya, a lokacin mulkin sa.
Ya ce ayyukan alherin da gwamnatin Kwankwaso ta yi wa alโummar Kano a baya, su na da muhimmancin da ba za a iya daina ci gaba da su ba.
Kabir ya ce ga shi nan ฦarara ana ta cin moriya da amfanar waษanda s**a je waje karatu a ฦarฦashin gwamnatin Kwankwaso, inda wasu na riฦe da muฦamai sosai a gwamnati da sauran fannonin ayyukan yau da kullum.
Ya lissafa wasu da s**a haษa da Kwamishinan Ilmi Mai Zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim, Shugaban Sashen ฦididdigar Alฦaluma na Jihar Kano, Farfesa Aliyu Isa Aliyu da Mashawarci na Musamman a Fannin ฦirฦire-ฦirฦire, Dakta Bashir Muzakkir da sauran su.
Gwamnan ya ce, โBari na bayyana cewa shi wannan shirin tallafin gurbin karatu waje, madugun mu Sanata Rabiโu Kwankwaso ne ya ฦirฦiro shi.โ
Ya ce Kwankwaso sai da ya ษauki nauyin rukuni-rukunin ษalibai har rukuni uku zuwa ฦasashe 16 daban-daban.
โWannan ฦoฦari ya sa an samu nasarar samar da daktoci, masu digiri na biyu da dubban ฦwararrun likitoci, injiniyoyi, matuฦa jirgin sama da gwanayen ayyukan harkokin jiragen ruwa da sauran su.
A jawabin sa tun da farko, Kwankwaso ya gode wa wannan gwamnati ta Abba Kabir, ganin yadda ta ci gaba da ayyukan alherin da ta fara a lokacin ya n