Zamani TV

Zamani TV Zamani TV kamfani ne dake kawo sahihan labaran da suke faruwa a Najeriya harma da ƙasashen ƙetare.

18/02/2025

Shirin Tsangayar Kura tare da Muhammadu Jinaidu

18/02/2025

Shirin Tsangayar Kura tare da Hon. Usman Matori

SO GAMON JINI: Mawaki Grand P ya canja shawari inda ya raba gari da manyan mata ya koma yan dai dai dashi.Mawakin Ɗan Ka...
18/02/2025

SO GAMON JINI: Mawaki Grand P ya canja shawari inda ya raba gari da manyan mata ya koma yan dai dai dashi.

Mawakin Ɗan Kasar Guinea me shekaru 34 ya chanja alakar sa da Auren manyan mata yayin da yayi sabuwar masoyiya kuma mata

Hukumar kwalejin fasahar lafiya na Malikiyya College of Nursing Sciences Bauchi na sanar da fara sayar da takardan neman...
18/02/2025

Hukumar kwalejin fasahar lafiya na Malikiyya College of Nursing Sciences Bauchi na sanar da fara sayar da takardan neman gurbin karatu (Application Form) na shekarar 2024/2025 a fannin karatun ingozoma (Midwifery Programme).

Masu sha'awar wannan karatu zasu iya ziyartan;

https://www.applicant.safapply.com/malikiyanursing/personal-area

domin neman gurbi.

Koh kuma a kira waɗannan lambobin domin neman karin bayani.

08034762802
08063555763
08065868790
08035799217

18/02/2025

Shirin Tsangayar Kura tare da Comr. Hamza Abdulmuminu

Sarki Sanusi ya halarci bikin cikar Gambia shekaru 60 da samun ƴancin kaiA jiya Litinin ne mai martaba Sarkin Kano, Muha...
18/02/2025

Sarki Sanusi ya halarci bikin cikar Gambia shekaru 60 da samun ƴancin kai

A jiya Litinin ne mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya isa birnin Banjul, babban birnin kasar Gambia, a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

A wata sanarwa da ta fito daga masarautar Kano, ta ce ziyarar ta biyo bayan gayyatar shugaban kasar Gambia, Adama Barrow.

Sanarwar ta ce, an gayyaci Sanusi ne a matsayin babban bako na musamman a wajen bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai na jamhuriyar Gambia.

Ministoci da wasu jiga-jigan gwamnati da s**a karbi bakuncinsa sun tarbe shi a lokacin da ya isa filin jirgin sama na birnin Banjul.

Daga bisani kuma da yammacin ranar, Sarkin ya bi sahun shugaba Barrow da uwargidan sa, Fatumatou Bah Barrow a wata liyafa da aka gudanar a wani bangare na bikin cika shekaru 60 na Gambiya.

Babban bikin ya ci gaba da gudana a yau Talata tare da fareti na musamman da sojojin kasar Gambia su ka yi a dandalin Banjul Grande.

Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran Sarki Sanusi zai dawo gida a yau.

18/02/2025

Shirin Tsangayar Kura
Martani ga Martani wa Adamu Aro Gori

Wani dattijo mai shekaru 94, Adedapo Idowu, ya yi rajistar zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, UTME, ta ...
18/02/2025

Wani dattijo mai shekaru 94, Adedapo Idowu, ya yi rajistar zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, UTME, ta 2025.

Labarin Idowu ya fito ne a cikin mujallar shirya jarrabawar, inda ya bayyana jin dadinsa wajen samun damar yin karatu a jami'a.

"Yanzu zan iya cimma burina na karatun jami'a amma a cikin tsufa," in ji shi.

Ya bayyana tsarin yin rajistar ta UTME a matsayin mai inganci da sauki, inda ya yaba wa JAMB bisa yadda ta sanya lambar shaidar zama ta kasa, wanda a tunaninsa ya kawar da wariya ga tsofaffi, marasa galihu, da nakasassu.

Ya kuma shawarci sauran ɗalibai da su riki kwarewa da kwazo a harkar neman ilimi.

Majalisar Wakilai za ta gudanar da taron jin ra’ayi na jama’a kan kudirorin gyaran haraji a ranar 26 ga Fabrairu.Kakakin...
18/02/2025

Majalisar Wakilai za ta gudanar da taron jin ra’ayi na jama’a kan kudirorin gyaran haraji a ranar 26 ga Fabrairu.

Kakakin majalisa, Tajudeen Abbas, ya sanar hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata inda ya ce za a shirya taron jin ra’ayi don tattara ra’ayoyi daga al’umma.

Domin cimma wannan buri, majalisar ta kafa kwamitin musamman mai mambobi 36 da ke da alhakin tsara zaman. Wannan kwamiti zai hada da kwararru a fannin gudanar da haraji, inda za a mayar da hankali kan fa’idodin da gyaran harajin zai kawo.

A cewar Kakakin Majalisa Abbas, Abiodun Faleke zai shugabanci kwamitin, yayin da Seidu Abdullahi, mataimakin shugaban kwamitin kudi na majalisa, zai zama mataimakinsa.

Sauran mambobi sun hada da Alhassan Ado-Doguwa, Nicholas Mutu, Fred Agedi, da Idu Igariwey, tare da wasu 'yan majalisar.

HOTUNA: Sabbin tituna da gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sen. Bala Mohammed Abdulkadir ta kammala a ƙaramar ...
18/02/2025

HOTUNA: Sabbin tituna da gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sen. Bala Mohammed Abdulkadir ta kammala a ƙaramar hukumar Jama'are.

Waɗannan tituna anyi su ne da nufin samar da sauƙaƙa hada-hada tare da bunƙasa kasuwanci, noma da cigaban al'umma a yankin

-Zamani TV

18/02/2025

Tattaunawa ta musamman daga Sashin Zakka da waqafi na hukumar Shari'ar Musulunci ta Jihar Bauchi tare Dr. Hamza Abubakar Hussaini, Mal. Musa Dahiru, Mal. Muhammad Yakubu Daraktan Zakka da waqafi na jihar Bauchi

Azumi saura kwanaki 11 Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya.
18/02/2025

Azumi saura kwanaki 11 Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya.

17/02/2025

Shirin Tsangayar Kura tare da Bala Abi Doka
Jan hankali ga Dan Majalisa Mai Wakiltar Sade District, Karamar Hukumar Darazo

17/02/2025

Shirin Tsangayar Kura
Kiranye wa Bala Wunti domin tsayawa takarar Gomnan Jahar Bauchi

17/02/2025

Shiri na Musamman tare da Barr. Abba Hikima daya daga cikin Jagororin Tafiyar Matasa

Gwamnatin Tarayya na neman sauƙaƙa tsarin ba da biza don ƙarfafa kasuwancin ‘yan Nijeriya a duniyaMinistan Yaɗa Labarai ...
17/02/2025

Gwamnatin Tarayya na neman sauƙaƙa tsarin ba da biza don ƙarfafa kasuwancin ‘yan Nijeriya a duniya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ƙasashen duniya da su sauƙaƙa tsarin ba da biza ga kamfanonin Nijeriya da ke ƙoƙarin kafa masana’antu da kasuwanci a ƙetare.

Ministan ya yi wannan kira ne a Addis Ababa, babban birnin Habasha, a ranar Lahadi yayin da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Afirka karo na 38 da Majalisar Tarayyar Afirka (AU) ta shirya.

A yayin wata ganawa da shugabannin al’ummar Nijeriya da ke Habasha, Idris ya jaddada cewa Nijeriya na samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanonin ƙasashen waje don su zuba jari a cikin ƙasar, don haka ya dace a samar da irin wannan dama ga ‘yan kasuwar Nijeriya a ƙasashen waje.

Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya.

"Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar da muke da ita na sayen kayayyakin su da ayyukan su, to ya kamata a samar da tsarin da zai ba da dama ga kamfanonin Nijeriya su ma. Matsalar ba da biza ga ‘yan Nijeriya na nan a Indonesiya da Habasha."

Dangane da matsalar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta bayan da gwamnatin Habasha ta soke tsarin nan na 'e-visa' da 'Visa-on-Arrival' ga matafiya daga Nijeriya, Idris ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin diflomasiyya ta hannun Ministan Harkokin Waje don magance matsalar.

Ministan ya bayyana cewa manufofin ba da biza a tsakanin ƙasashe na tafiya ne bisa tsarin da ke bai wa kowanne ɓangare dama daidai.

Ya ce ya zama dole ƙasashe su kasance masu adalci wajen aiwatar da manufofin da za su amfanar da ‘yan ƙasar su da na ƙasashen da suke hulɗa da su.

Ya ce: “Duk wata dangantaka da ƙasashen waje tana tafiya ne bisa tsarin amfanin juna. Idan muna ba su 'Visa-on-Arrival', babu dalilin da zai sa su hana mu 'Visa-on-Arrival'."

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje da su kasance jakadu nagari, su nuna halaye nagari domin inganta sunan ƙasar.

“Ba ma yarda da mutanen da za su ɓata mana suna. Kuna da rawar da za ku taka, saboda ku ne ke zaune a nan. Idan ba ku wakilce mu da kyau ba, ba za a girmama mu ba. Ba wai ziyarar Shugaba Tinubu ko wani minista ce za ta gyara abin ba, amma ‘yan Nijeriya da ke zaune a nan ne za su iya gyara yadda duniya ke kallon ƙasar mu,” inji shi.

Idris ya kuma yi bayani kan sababbin manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, inda ya ce an samu cigaba mai kyau a fannin farfaɗo da tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa, yaƙi da rashin tsaro, da kuma dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari a Nijeriya.

Ya ce Nijeriya ta samu jarin ƙetare na kusan dala biliyan 1.07 don kafa masana’antu da za su ƙera magunguna, matakin da zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar magunguna a ƙasar, samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa ɓangaren kiwon lafiya.

Haka nan, Ministan ya bayyana cewa a cikin kwanaki ƙasa da 250, an raba sama da naira biliyan 32 ga ɗalibai ƙarƙashin Shirin Lamunin Ɗalibai, domin tabbatar da cewa kowa na samun damar karatun boko ba tare da matsalar rashin kuɗi ba.

Dangane da ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro, Idris ya ce a shekarar 2024 kaɗai, jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan fashi 8,000, sun ceto mutane 8,000 da aka yi garkuwa da su, tare da cafke mutane 11,600 da ake zargi da aikata laifuka.

Har ila yau, ya tabbatar da cewa an kawar da ‘yan ta’adda daga hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda a da wurin aikata miyagun laifuka ce, lamarin da ya kawo sauƙi ga matafiya.

Da yake jawabi, Shugaban Al’ummar Nijeriya da ke Habasha, Muideen Alimi, ya ce suna shirin yin haɗin gwiwa da Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare (NIDCOM) don shirya taron tattaunawa kan bunƙasa tattalin arziki ta hanyar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka.

Ya buƙaci Nijeriya da ta goyi bayan shirin samar da Babban Bankin Afirka, tare da tabbatar da cewa Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa a Hukumar Harhaɗa Kuɗaɗen Afirka (African Remittance Agency).

Taron ya samu halartar Darakta Janar ta Hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, da wasu manyan jami’an gwamnati.

DA DUMI-DUMI:Mustapha Nabraska ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar APC.Wani fata kuke masa?
17/02/2025

DA DUMI-DUMI:Mustapha Nabraska ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar APC.

Wani fata kuke masa?

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir, ya samar da hanyoyi a cikin Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Bauchi domin sauka...
17/02/2025

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir, ya samar da hanyoyi a cikin Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Bauchi domin saukaka ayyukan karatu a cikin harabar jami’ar.

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamani TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zamani TV:

Videos

Share