Zaria da Kewaye

Zaria da Kewaye Ameer Shehu Idris Foundation

17/02/2023

Muna Cikin Matsananci Bukatar Cash.
Allah Yasa Cikin Mutanenmu.
Da wanda zai taimaka.
NB: Andaina Amsar Old Note👌

TARIHIN SABON SARKIN DUTSEAn haife shi a ranar 26/2/1979. Kuma shi ne babban ɗa ga marigayi sarkin Dutse Nuhu Muhammadu ...
12/02/2023

TARIHIN SABON SARKIN DUTSE
An haife shi a ranar 26/2/1979. Kuma shi ne babban ɗa ga marigayi sarkin Dutse Nuhu Muhammadu sunusi.

Ya yi makarantar firamare a makarantar 'ya'yan sojojin sama da ke Kano. Daga nan ya fara karatun sakandare a Crescent International School amma bayan shekara biyu ya koma kwalejin gwamnatin tarayya ta Kano (FGC Kano) a inda ya kammala karatun sakandaren.

Ya yi karatunsa na digiri a fannin kwamfuta a Jami’ar Monash ta ƙasar Australia reshen Malaysia.

Bayan nan ne kuma ya yi digiri na biyu a fannin kasuwanci, wato MBA, a Jami’ar Nottingham Trent, a Malaysian.

GOGEWAR AIKI
Ya yi aiki na shekara ɗaya a kamfanin Marcus Evans Consulting na Malaysia a matsayin jami’in kasuwanci

Sannan kuma ya koma aiki a Bilyak Consulting a matsayin mai kula da sashen haɓaka kasuwancin kamfanin daga 2007 zuwa 2011.

daga baya kuma ya koma kamfanin SMD Consulting daga 2011 zuwa 2016 inda ya zama jami’in kula da yankin Arewacin Nigeria na kamfanin.

Ya zama Babban Darakta na kamfanin MHS Energy Limited daga shekara ta 2016 har lokacin da ya zama Sarkin Dutse.

MUƘAMAN DA YA RIƘE
Kafin naɗin nasa a matsayin sabon sarkin Dutse, Hameem Nuhu Muhammad Sunusi ya riƙe sarautar Sarkin Dawakin Tsakar-Gida da kuma Ɗan Iyan Dutse.

Kuma sabon sarkin shi ne shugaban kamfanin gine-gine na MHS Engineering.

IYALANSA
Sabon sarkin Hameem Nuhu Muhammad Sunusi na da mata ɗaya da 'ya'ya biyu.

Emiratesm

SABON SARKIN DUTSE ✊🏼Sabon sarkin Dutse kenan, Hamim Muhammad Sanusi. Allah Yasa yayi koyi da mahaifinsa wajen kishin ad...
05/02/2023

SABON SARKIN DUTSE ✊🏼

Sabon sarkin Dutse kenan, Hamim Muhammad Sanusi.
Allah Yasa yayi koyi da mahaifinsa wajen kishin addinin musulunci.

TURAKIN ZAZZAU AMINU SHEHU IDRISMaigirma Turakin Zazzau Alh Aminu Shehu Idris Lokacin da ya isa Fadar Zazzau don daurin ...
03/02/2023

TURAKIN ZAZZAU AMINU SHEHU IDRIS

Maigirma Turakin Zazzau Alh Aminu Shehu Idris Lokacin da ya isa Fadar Zazzau don daurin auran 'yar sa Fatima Ahmed Nuhu Bamalli .

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN Marigayi Mai Martaba Sarki Zazzau Alh Dr Shehu Idris CFR Marigayi Alh Danjuma Bawa M...
02/02/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN

Marigayi Mai Martaba Sarki Zazzau Alh Dr Shehu Idris CFR Marigayi Alh Danjuma Bawa Marigayi Alh Bello Aliyu. Duk Yau Babu Sun Koma Ga Allah. Aminai Juna Sun So Juna Saboda Sunyi Zumunci Saboda Allah. Muna Adu'an Allah Yayi Musu Rahama Yasa Suna Kyakyawan Matsayi Ya Jikan Magabatan Mu Bakidaya.

~Kasar Zazzau A Jiya Da Yau

Innalillahi wa Inna illaihin Rajiun..Allah ya yima Alh Danjuma Bawa.Rasuwa
02/02/2023

Innalillahi wa Inna illaihin Rajiun..
Allah ya yima
Alh Danjuma Bawa.
Rasuwa

ALLAHÚ AKBAR: Yaú Sheíkh Albaniy Zaría Ké Cíka Shékaru Tara Da Rasúwa A yau ne fitaccen Malamin Addinin Musulunci Muhd A...
01/02/2023

ALLAHÚ AKBAR: Yaú Sheíkh Albaniy Zaría Ké Cíka Shékaru Tara Da Rasúwa

A yau ne fitaccen Malamin Addinin Musulunci Muhd Auwal Albani Zaria ya cika shekaru tara da rasuwa.

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne, sun kashe malamin a ranar ɗaya ga watan Fabrairu na shekarar 2014.

Muna afdu'ar Allah ya gafartawa Malam.

DÁGA Abubakar Shehu Dokoki

YANZU YANZU, An kammala gina Asalin tambarin Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, bayan rushe wancan tsohon tambarin.”
01/02/2023

YANZU YANZU, An kammala gina Asalin tambarin Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, bayan rushe wancan tsohon tambarin.”

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN !!!Allah ya yiwa mai martaba Sarkin Dutse.Alhaji Dr. Nuhu Muhammad Sunusi CON, rasuw...
31/01/2023

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN !!!

Allah ya yiwa mai martaba Sarkin Dutse.
Alhaji Dr. Nuhu Muhammad Sunusi CON, rasuwa a Abuja.

Allah ya gafarta maka yayi maka rahama yasa ka a aljannah ma ɗaukakiya.
Amin ya Allah.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un 😭Allah yayi masa rasuwa akan nemar hakkin sa, yayinda jak ya goce motar ta danne shi,...
31/01/2023

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un 😭
Allah yayi masa rasuwa akan nemar hakkin sa, yayinda jak ya goce motar ta danne shi, muna roqon Allah yakai haske qabarin sa kuma Yayi masa rahma Ameen-we need your prayers to him and soul rest in perfect peace in the grave Ameen.

Allah ya jikanshi da rahma.

*TARIHIN SARAUTAR DAN MAJE*```sarautar DANA MAJE itama tana cikin sarautu da s**a samo Asali daga Kano akwai maganganu m...
29/01/2023

*TARIHIN SARAUTAR DAN MAJE*

```sarautar DANA MAJE itama tana cikin sarautu da s**a samo Asali daga Kano akwai maganganu mabambanta akan Asalin wannan sarauta Ance a Zamanin sarkin Kano kisoki aka Fara yin ta Wanda yayi mulki daga 1509 zuwa 1565 shi DANMAJE sunan wani ne daga cikin manyan baraden yakin sarkin Kano kisoki kenan daga shi wannan Barde sunan DANMAJE ya samo Asali wasu Kuma sunce Kalmar MAJE tana nufin sarki to Dan sarki Ana kiransa DANMAJE wasu Kuma sunce Kalmar MAJE Sunan wani ice ne Mai suna maje akwai wani sarki daga cikin sarakunan kano dayake zuwa Gurin wannan ice ya zauna tare da wani dansa karami shine ake Kiran Dan nasa da suna DANMAJE wato Dan sarkin da Sarki ke zuwa da shi wajen itacen maje to daga Nan Aka samo sunan danmaje daga nan aka samu sarautar Dan maje```

```Tin Bayan wucwar zamanin sarakunan Habe ba a Fara nada wannan sarauta a Kano ba Sai zamanin Sarkin Kano Usman na biyu wato zamanin fulani kenan Bayan zuwan turawa itama wannan sarauta ta yadu kwarai sauran masarautu Kuma An fi yinta ga yayan sarki```

```Inama wannan sarauta Masartan fada suna Yi Mata kirari da cewa MAJEN KANO MAI KAMSHI BA MAJE BANE SANDAL MAI KOGIN MADARA MAI KOGIN NONO```

SARAUTAR DAN MAJE A KASAR ZAZZAU.

An Fara Nada Sarautar Dan Maje A Kasar A Lokacin Marigayi Mai Martaba Sarki Zazzau Alh Dr Shehu Idris. Wanda Ya Fara Nadawa Shi Ne Marigayi Alh Balarabe Husaini, Daga Shi Kuma Sai Dan Maje Zazzau Prince Nasiru Shehu Idris, Kuma Duk 'Ya'yan Sarki Ne.

*✍🏻 DAGA ZAUREN DAGA MASARAUTUNMU*

DAGA TASKAR KARATUKAN MAL ALBANIY ZARIA (RAHIMAHUL-LAH): KARATUN RANA TA ƘARSHE A RAYUWAR MALAMA ranar Asabar ɗaya ga wa...
28/01/2023

DAGA TASKAR KARATUKAN MAL ALBANIY ZARIA (RAHIMAHUL-LAH): KARATUN RANA TA ƘARSHE A RAYUWAR MALAM

A ranar Asabar ɗaya ga wata Fabrairu na shekarar miladiyya ta 2014 (1/Rabi'ul Akhir/1435), Mal. Albaniy Zaria ya yi darussa guda uku
1. Da safe ya gabatar da karatun Littafin Tariqus Saliheen Darasi na 1
2. Da la'asar ya gabatar da karatun Littafin Saheehu Muslim Darasi na 172
3. Bayan Sallar Isha'i, Mal. Albaniy Zaria ya je Markazul Salafiyyah dake Tudun Wada Zaria-Nigeria ya gabatar da karatun Littafin Saheehul Bukhari Darasi na 308.

Bayan an tashi karatun Bukhari ya kamo hanyarsa ta komawa gida, watau anguwar Gaskiya Layout. Akan hanyarsa ne ƴan ta'adda s**a tare matarsa, s**a buɗe masa wuta s**a kashe shi, shi da matarsa Ummu-Abdilbarr da ɗansa Abdullahi.

Muna roƙon Allah Ubangiji ya gafarta masa. Allah ya sa mutuwa ta zame masa hutu shi da iyalinsa da ɗansa. Allah Ubangiji ya ba su darajar shahidai.

https://t.me/sheikh_auwal_albani_zaria_audios

Copied from the wall of Dr Kabir Asgar

INNALILAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN 😭😭ALLAH Yayima Kakata (HAJIYA HABIBA LADAN) Rasuwa Mata Marigayi ALH Ladan Usman Mai Dut...
28/01/2023

INNALILAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN 😭😭

ALLAH Yayima Kakata (HAJIYA HABIBA LADAN) Rasuwa Mata Marigayi ALH Ladan Usman Mai Dutse Rasuwa Yanzu Haka A Garin, Allahu Akbar.
Rayuwa Kenan Akwaii Ta Da Zumunci Sossii Kuwa.

Allah Yemiki Sakayya Da Gidan Aljannah Firdausi 🙏

Mai girma Turakin Zazzau Alh Aminu Shehu Idris tare da dan uwansa maigirma Danmajen  Zazzau Alh Nasiru Shehu IdrisUmar L...
27/01/2023

Mai girma Turakin Zazzau Alh Aminu Shehu Idris tare da dan uwansa maigirma Danmajen Zazzau Alh Nasiru Shehu Idris

Umar Ladan

NIGERIA TA ƊAUKI ZAFIMatasa kar wani ya zuga ku, ku fito zanga-zanga ko bore ga shugabanni ko jami'an tsaro domin haka b...
26/01/2023

NIGERIA TA ƊAUKI ZAFI

Matasa kar wani ya zuga ku, ku fito zanga-zanga ko bore ga shugabanni ko jami'an tsaro domin haka ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Sannan shugabanninmu yana da kyau su sani akwai rayuwa bayan mutuwa sannan ba koda yaushe ake amfani da karfi a mulki ba, lallashi ma salo ne mai kyau na shugabanci idan bukata ta k**a.

Allah ka bamu shugabanni nagari zaɓi daga gare ka ba zaɓi daga gare mu ba.

Haza wa salam.

✍️ UMAR SHEHU ZARIA
03 Rajab, 1444
(25/01/2023).

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'unn. Mun Sami Labarin wasu Bata gari, Marasa imani, sun sace wani yaro Mai Suna Abdulka...
23/01/2023

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'unn.

Mun Sami Labarin wasu Bata gari, Marasa imani, sun sace wani yaro Mai Suna Abdulkadir mai kimanin Shekara Goma Sha biyu, da Haihuwa sun kasheshi a bayan dutsen Madarkachi Cikin Birnin Zariya. Sun ciccire wasu abuba a jikinsa.

Allah Ka tunana asirinsu duk Wanda yake da hannu a irin wannan mummunan da'bi'a. Allah ka bamu zaman lafiya.

Innalillahi wa inailaihi raju’un...!!! ya Allah mu na rokon ka da ka jikan bawan ka Kamal Aboki, ka mishi rahama. Lalle ...
16/01/2023

Innalillahi wa inailaihi raju’un...!!!
ya Allah mu na rokon ka da ka jikan bawan ka Kamal Aboki, ka mishi rahama. Lalle mun yi rashi babba, jama’a mu na roko da ku sa shi cikin adu’a ku. Allah ya sa ya huta Amin. 💔💔😭😭

A yau ne Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ya cika shekara 57 da rasuwa. 😭An kashe shi ne a ranar 15 ga watan Janairun ...
15/01/2023

A yau ne Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ya cika shekara 57 da rasuwa. 😭
An kashe shi ne a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966 a Kaduna.
Wane darasi ne kuke ganin shugabannin zamanin nan ya k**ata su koya daga marigayin?

Shugaban Kungiyar Jama'atul izalatul bidi'a Wa'ik**atul sunnah.(JIBWIS) Na Karaman Hukumar Zariya. Sheik Muhammad Sani Y...
14/01/2023

Shugaban Kungiyar Jama'atul izalatul bidi'a Wa'ik**atul sunnah.(JIBWIS) Na Karaman Hukumar Zariya. Sheik Muhammad Sani Yakubu. Maddibon Zazzau. Yana Fama da Rashin Lafiya. Wanda yanzu Haka Yana kwance a Asibiti.

Yana Bukatan Addu'arku. Allah ya Bashi lafiya yasa Kafface ce. Tare da Dukkan marasa lafiya.

Zage-Zagi A Zage-Zagi A Yau.Zage-Zagi A Yau.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJUNYanzu Muke Samun Labarin Rasuwar Malama Khadija Dije (Amarya) Daga Gidan Marigayi Iya A...
13/01/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJUN

Yanzu Muke Samun Labarin Rasuwar Malama Khadija Dije (Amarya) Daga Gidan Marigayi Iya Abdullahi. Dake lemun cikin Birnin Zariya. In Allah ya yarda za'a Sanar da Lokacin Jana'iza.

Allah ya Gafarta Mata yasa Aljannar Firdausi ce Makomanta. Amin

ALLAHU AKBAR.The whole family engulfed by fire Outbreak last night.@ Kofar Gayan Lowcost Zaria.  Allah Ya karbi Shahadar...
13/01/2023

ALLAHU AKBAR.
The whole family engulfed by fire Outbreak last night.
@ Kofar Gayan Lowcost Zaria.

Allah Ya karbi Shahadar ku🤲😥

MALLAMAIFitilla ne ga Al'umma, Don haka ku haɗa kawunan ku, Kada siyasa ta raba ku.Yã Allah ka yi mana zaɓi na alkhairi....
12/01/2023

MALLAMAI
Fitilla ne ga Al'umma, Don haka ku haɗa kawunan ku, Kada siyasa ta raba ku.
Yã Allah ka yi mana zaɓi na alkhairi.

Mal. Usman Abubakar Magaji Zaria

Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un😥😥😥I regret to announce the death of Engr. Muhammad Sani Bello May Almighty Allah grant...
10/01/2023

Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un😥😥😥

I regret to announce the death of Engr. Muhammad Sani Bello May Almighty Allah grant him jannatul firdausi. Jana'iza will take place tomorrow 11am at Sultan Bello Mosque Kaduna. My condolences to the entire family. Allah Yakara hakuri yasa ya huta Amin.

Source: Dr. Auwal Abubakar PhD.
#10/01/2023

KADUNA STATE HIGHER INSTITUTIONS.1. Ahmadu Bello University, Zaria2. Kaduna State University 3. Greenfield University,Ka...
07/01/2023

KADUNA STATE HIGHER INSTITUTIONS.

1. Ahmadu Bello University, Zaria
2. Kaduna State University
3. Greenfield University,Kaduna
4. Kaduna Polytechnic, Kaduna
5. National Open University of Nigeria, Kaduna Study Center
6. Nigerian College of Aviation Technology, Palladan Zaria
7. Nigerian Defence Academy (NDA), Kaduna
8. Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria
9. Air Force Institute of Technology,mando Kaduna
10. Ameer Shehu Idris College of Advanced Studies, Zaria
11. College of Education Gidan Waya-Kafanchan
12. Federal College of Education, Zaria
13. Federal Training Centre, Malali, Kaduna
14. National Institute For Hospitality and Tourism, Kaduna
15. National Teachers Institute (NTI), Kaduna
16. Nigerian Institute for Trypanosomiasis Research (1951) Kaduna
17. Nigerian Institute of Transport Technology, Palladan Zaria
18. School of Midwifery, Kafanchan
19. Shehu Idris College of Health Sciences And Technology, Makarfi
20. School of Midwifery, Kaduna
21. Federal College of Forestry Mechanization, Kaduna
22. Division of Agricultural Colleges (DAC) Zaria
23. Institute of Agricultural Research (IAR) Zaria
24. College of Agric and Animal Science, Kaduna
25. National Research Institute for Chemical Technology, Basawa, Zaria
26. Nigerian Institute of Leather and Science Technology, Samaru Zaria
27. Nigerian Army School of Military Police, Basawa Zaria
28. Nigerian Military School, Zaria
29. Military Training Center Parade Ground, Mando Kaduna
30. Armed Forces Command and Staff College, Jaji
31. Nigerian Military Training School, Kaduna
32. Federal Cooperative College, Kaduna
33. Federal School of Statistics, Kaduna
34. Institute of Certified Geographers of Nigeria, Kaduna
35. Nigeria Army School of Legal Services, Basawa Zaria
36. City College of Health Science and Technology, Zaria
37. Elite International School of Health Science, Zaria
38. Northern International Health Academy, Zaria
39. St. Francis of Assisi Theological Colleges, Zaria
40. Beijing college of health science

Tuna baya shine roko kowa ya wayi gari a birnin Zaria yasan wannan bawan Allah. Allah ya jikan hon. Mustapha bawa🙏
06/01/2023

Tuna baya shine roko kowa ya wayi gari a birnin Zaria yasan wannan bawan Allah.
Allah ya jikan hon. Mustapha bawa🙏

Wani gida a Zariya ne cikin shekarar 1923. Shekaru dari (100) a ke magana ke nan fa.Mu ma cikin wani kundi mu ka ga hoto...
05/01/2023

Wani gida a Zariya ne cikin shekarar 1923. Shekaru dari (100) a ke magana ke nan fa.
Mu ma cikin wani kundi mu ka ga hoton. Wadannan mutanen babu mamakin duk sun bar gari fa.
📷 Lugude

ALLAH SARKI RAYUWA: Ni Salisu Hussaini Kano Matashi Mai Shekaru 23 Nahadu Da Babbar Jarabawar Rayuwa 😭😭Ina sana’ar dinki...
05/01/2023

ALLAH SARKI RAYUWA: Ni Salisu Hussaini Kano Matashi Mai Shekaru 23 Nahadu Da Babbar Jarabawar Rayuwa 😭😭

Ina sana’ar dinki, na tashi tunda sassafe ina ta farinciki, ba abunda kemin ciwo a rayuwa. sai naje kasuwa wurin sana’a ta domin cigaba da aiki.

Awannan ranar har dare nakai ina aiki misalin karfe tara 9:00pm sai na rufe shago mukaje dani da maigidana domin mukai kayan da mukagama dasu.

Ina zaune sai naji hayaniyar mutane awaje

Bayan nafita sai natarar da mutum biyu suna fada, nan take nashiga tsakiyarsu domin rabon fadan.

Kawai sai dayan ya zaro wuka 🔪 ya caka mun a hannu 😭 ganin yanda jini 🩸 ke zuba sosai, sai s**a gudu.

Aka kaini assibitin Dala domin ayimin aiki, likitan yace sai ancire hannun domin kuwa jijiyar jinin hannun ta tsinke.

😭😭😭😭😭😭

Ahaka ne Allah ya jarrabani da rashin hannu daya, daga wurin aikin alkhairi (Rabon Fada) tsakanin mutum biyu domin sulhuntasu.

Ina neman addu’a da taimakon ku yan uwana maza da mata, ina fatan Allah ya kare mu daga dukkan mummunar kaddara. 😭 Ameen.

Innalillahi Wainna Ilaihi Rajiun 😭Yanzu samun labarin rasuwar Hon Shagarin Dambo Innalillahi Wainna Ilaihi Rajiun 😭 ya A...
04/01/2023

Innalillahi Wainna Ilaihi Rajiun 😭

Yanzu samun labarin rasuwar Hon Shagarin Dambo Innalillahi Wainna Ilaihi Rajiun 😭 ya ALLAH ka Jikanshi da Rahma.
Kayi mishi gafara ya ubangiji idan mutuwar mu tazo kasa mu cika da imani ka bamu Ikon tashi da imani.

Allah YaJikanshi da Gafara Ameen🙏

📷 Hon. Suleiman Ibrahim Dabo

Address

No. 1, Emir's Palace
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zaria da Kewaye posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zaria da Kewaye:

Videos

Share

Nearby media companies


Other News & Media Websites in Zaria

Show All