11/09/2022
Wallahi akwai wani bakin zalunci dana taba aikatawa wanda har yau nake nadamarsa, lokuta da yawa nakan zauna inyita istighfari kan haka, kuma bansan ta wacce hanya ubangiji zai yafemin ba (domin baya yafe hakkin wani).
Kimanin shekaru 8 baya lokacin ina shekarata ta karshe kuma semestar karshe a makarantar koyon malanta N.C.E Gumel, gabannin fara jarrabawa lokacin Malamai sunata Revision, na gamu da wani ibtila'i wani ya sacemin kayan abincina gabadayansa wanda nayi terming zai isheni har zuwa karshen zangon karatun.
Nashiga damuwa sosai don daman banyi niyyar zuwa gida ba saina kammala.
A lokacin sai Allah ya had'ani da wani mutum wanda ya bani wani abu da ake cewa SHASHATAU, ba Guru bane ba Laya bane sannan kuma ba Daga bace, wasu d'alasiman kalmomi ne da mutum zai karanta a lokacin daya tunkari wanda yake nufin ya cuta ko ya shashantar.
Tun daga lokacin kusan kullum cikin gari nake fita anan nake cin kayan dadi da duk wani nau'in abinci da nakeso kuma batare da kowa ya tambayeni ina kudi ba, wasu ma suna gani zan tahowa ta.
Akwai wani babban Shago a masarautar Gumel da ake cewa DAN WASHA, gaban shagon akwai masu kaji da tsire, wallahi tun daga ranar har zuwa karshen semester kullum sai naci kaza ko tsire, haka na dinga bushasha ta har na kammala karatuna da wannan siddabaru.
Nayi nadama sosai akan haka domin bazan iya tattaro ko tuna mutanen da naci abinci a wurinsu ba, iya abinci ne da kayan dadi kawai, bayan wannan ban cutar da kowa ta bangaren kudi ko kayan sakawa ba.
don Allah .t. kubani shawara mezanyi 🙏
✍️Muntari Gezawa