Duniyar Mu A Yau

  • Home
  • Duniyar Mu A Yau

Duniyar  Mu A Yau Don samun ingantattun labarai aiki da wajen kasarmu da tallata hajojinku cikin sauki da rahusa, Makarantu, 'Yan siyasa da Malaman Addini

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Darasi Ga 'Yan MataDaga Amina Amisco Adamu'Yan mata wannan rubutun nawa yau akan ku...
17/02/2025

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Darasi Ga 'Yan Mata

Daga Amina Amisco Adamu

'Yan mata wannan rubutun nawa yau akan ku ne. Ku kiyaye bin mutumin da kuke tunanin kamar ba zai cútąr daku ba. Dan Adam sai Allàh.

Wannan matashin ba za ka taba cewa zai iya ķìșa ba. Aŝhe makãșhi ne halinsa kenan, ya fake da addini yana kíŝa.

Dubunsa ta cika ne akan wata yarinya, inda ya ķãșhe ta ashe da dan rakiya ta zo bai sani ba. Aka yi ta jira shuru karshe lamba ta daina shiga. Ba ta fita a gidan ba bincike ya yi bincike har aka gano komai.

Dan Allah mata ku yi kokarin kare mutuncin ku namiji idan yana sonki dan Allah ba sai kin je gidansu ba.

Allah Ya kyauta.

DAARUL-HADEETHIS SALAFIYYA ZARIA Wannan wakafi ne da Malam Albaniy Zaria Rahimahullaah yayi domin gina Da'awa da fahimta...
04/02/2025

DAARUL-HADEETHIS SALAFIYYA ZARIA

Wannan wakafi ne da Malam Albaniy Zaria Rahimahullaah yayi domin gina Da'awa da fahimtar Musulunci bisa koyarwan Salafussaliheen.

Duk mai son ganin dalilai dake DAARUL-HADEETHIS SALAFIYYA na Sadaqatul Jariya ne, Malam Albaniy Rahimahullaah ya bayar kuma har ranar Alkiyama babu mai ita sai Allaah, sai dai wakilai wanda Malam ya ayyana Ɗaliban, inda yake fadi cewa koda dan shi ne, baya fahimta irin nashi ko bazai iya da'awa irin nashi ba, ko ma bai cancanta ba, bashi da bukatar shi.

Wani gurin kuma yace wannan wakafi da yayi, yace ko dan shi kar ayi shawara dasu wajen yadda gudanar da Wannan makaranta zai kasance.

Wannan kadan ne daga cikin rubutun hannun shi ke nuna DAARUL-HADEETHIS SALAFIYYA ZARIA Bama mallakin Malam Albaniy Rahimahullaah bane duk da shine ya ginata.

Mu daunga bincike kafin yanke hukunci koda akan makiyin ne

MENENE GASKIYAR ABINDA KE FARUWA DA IYALAN MALAM ALBANIYIdan ka kalli videon guda biyu dake yawo karka yanke hukunci kai...
02/02/2025

MENENE GASKIYAR ABINDA KE FARUWA DA IYALAN MALAM ALBANIY

Idan ka kalli videon guda biyu dake yawo karka yanke hukunci kai tsaye ba tare da bincike ba, domin Maman su Abdul Rahman Malam Albaniy ya rasu basa tare dashi, ma'ana bata yi ma Malam takaba ba b***e taci gadon Malam ba.
Ita kuma A'isha 'yar Malam tace tana kasuwanci tace an cuce ta, amma fa dan uwanta yace bata da wannan kudi da take ikirarin an cuce ta, kuma in an cuce ta, ta nuna sheda, sannan ina maigidanta dake aurenta?

'Yan social media dake yada maganganun nan, tare da makiya Malam Albaniy da kuma waɗanda suna tafiyan amma an samu matsala dasu, sune ke rura wutan fitinar.

Wanda ya yada videon hirar tsohuwar Matan Malam Albaniy Zaria Rahimahullaah bai bayyana cewa ita ce tsohuwar Matan Malam ba, b***e jama'a su fahimta.
Babu wanda yayi bincika Jagororin Wannan makaranta b***e yaji daga bakin su.

Malam Albaniy Zaria Rahimahullaah ya kafa DAARUL-HADEETHIS SALAFIYYA ZARIA ne. Don yada Addinin musulunci.

Ya sha fadi a lokuta mabanbanta cewa babu gado, sannan duk dan shi daya ce yana da gado bai yafe mishi ba, duniya da lahira

Yace yana da Kamfanin Safwa shine na iyalan shi, da zasu rayu akai.

Cigaba..........

Wata sabuwar gobarar daji ta fara ci ganga-ganga a birnin Los Angeles da tsakar dare inda ta ƙone kusan Eka dubu 10 kwat...
23/01/2025

Wata sabuwar gobarar daji ta fara ci ganga-ganga a birnin Los Angeles da tsakar dare inda ta ƙone kusan Eka dubu 10 kwatankwacin murabba’in kilomita 38

Wutar mai ɗauke da iska mai ƙarfi na rurawa ta tursasa kwashe mutum dubu 31 saboda irin barazanar da ta ke yi a yankin.

Me kuke ganin yasa wannan wuta 🔥 taki mutuwa har yanzu ?
Ku sanya mana Comments

Tawagar Mabiya Shi'a almajiran Sheikh Zakzaky, sun halarci babbar Cocin Sabon Gari da ke Zaria, domin taya kiristoci mur...
25/12/2024

Tawagar Mabiya Shi'a almajiran Sheikh Zakzaky, sun halarci babbar Cocin Sabon Gari da ke Zaria, domin taya kiristoci murna da ranar Kirsimeti.

Ko wani fata zakuyi musu

Hotunan Yanda 'Yan Damfara Sunka Tsiyata Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa, Mansura Isah, Inda S**a Yi Kutse A Asusun Ban...
11/12/2024

Hotunan Yanda 'Yan Damfara Sunka Tsiyata Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa, Mansura Isah, Inda S**a Yi Kutse A Asusun Bankinta S**a Kwashe Kudin Dake Ciki Baki Daya

Allah Ya kiyaye gaba.

DA ƊUMI-ƊUMI: Tsohon Dan Majalisa Daga Jihar Kano Ya Shaƙi Iskar 'Yanci Bayan Kammala Zaman Gidan YariTsohon ɗan majalis...
22/10/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Tsohon Dan Majalisa Daga Jihar Kano Ya Shaƙi Iskar 'Yanci Bayan Kammala Zaman Gidan Yari

Tsohon ɗan majalisar tarayya da ya wakilci ƙaramar hukumar Ɓagwai da Shanono Faruk Lawan ya shaƙi iskar 'yanci bayan kammala zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar sabòda bądaƙálar cin haɲciɲ Dala 500,000

Wane fata zaku yi masa?

An cire babban mai tsaron Tinubu, Adeboyega FasasiBabban Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta SSS, Tosin Ajayi, ya ts...
20/10/2024

An cire babban mai tsaron Tinubu, Adeboyega Fasasi

Babban Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta SSS, Tosin Ajayi, ya tsige Adeboyega Fasasi a matsayin babban jami’in tsaro, CSO ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Majiyoyin tsaro masu sahihanci, wadanda s**a tabbatar da tsige Fasasi a karshen mako sun ce an maye gurbinsa da Rasheed Atanda Lawal, mataimakin darakta wanda halin yanzu ya ke ɗaukar wani horo a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Kasa.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Tinubu ya amince da tsige Fasasi bisa buƙatar shugaban DSS ta ya tura shi ƙarin daukar horo, wanda wannan zancen jami'an tsaro su ka saba yi a matsayin dalilin da ya sa a ka cire jami'i daga mukami.

K**ar yadda jaridar samu bayanai daga majiyoyi, Lawal ya kamata a kara masa girma zuwa mukamin darakta tun watan Yulin 2023 a lokacin tsohon shugaban DSS da ya sauka, amma sai ya ƙi yi masa saboda ba sa ga maciji.

GWAMNA BALA MUHAMMAD YA KARƁI BAƘUNCIN TSOHON SHUGABAN ƘASA OBASANJO A BAUCHIGwamna Bala Abdulƙadir Muhammad na Jihar Ba...
20/10/2024

GWAMNA BALA MUHAMMAD YA KARƁI BAƘUNCIN TSOHON SHUGABAN ƘASA OBASANJO A BAUCHI

Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad na Jihar Bauchi, ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban Najeriya, Janar Olusegun Obasanjo domin ƙaddamar da wasu ayyukan tituna da gwamnan ya aiwatar a Jihar.

A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu daga mai taimakawa gwamnan kan sabbin kafafen sadarwa na zamani, Lawal Mu'azu Bauchi, gwamna Bala Muhammad da tawagarsa sun tarbi tsohon shugaban ƙasar ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Jihar, "Sir, Abubakar Tafawa Balewa International Airport" tare da sanya mishi kayan Fulani don nuna cewa garin Fulani yazo. a wannan rana ta Lahadi, 20 ga watan Oktoba, 2024.

TIRƘASHI: An jiyo mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ambaci sunan Alhaji Aminu Ado ...
04/10/2024

TIRƘASHI: An jiyo mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ambaci sunan Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a wajen taro a Abuja

Me kuke fahimta?

YANZU-YANZU: Matar Seaman Abbas ta fashe da kuka bayan mijinta ya shaki iskar ƴanci, Bayan shafe shekaru 6 a ɗaure.Kuma ...
27/09/2024

YANZU-YANZU: Matar Seaman Abbas ta fashe da kuka bayan mijinta ya shaki iskar ƴanci, Bayan shafe shekaru 6 a ɗaure.

Kuma daga ƙarshe aka sake shi tare da korar shi daga aikin sojan, Yayin da s**a bayyana a gidan Radio Berekete family bayan shakar iskar ƴancin, A safiyar yau Juma'a 27 ga watan Satumbar 2024.

Shin wane wani jinjina matar ya kamata ayi mata?

Daga Garin Wudil...An K**a Barawon Babur Mutane Sun Kone Shi.Kuna ganin wannan mataki yayi dai-dai ko akwai kuskure acik...
18/09/2024

Daga Garin Wudil...

An K**a Barawon Babur Mutane Sun Kone Shi.

Kuna ganin wannan mataki yayi dai-dai ko akwai kuskure aciki, muna son jin ra'ayoyin ku.

SUBHANALLAH: An wayi gari da ambaliyar ruwa da ba'a taba ganin irinsa ba a cikin garin Maiduguri. Ruwa ya shafe gidajen ...
10/09/2024

SUBHANALLAH:

An wayi gari da ambaliyar ruwa da ba'a taba ganin irinsa ba a cikin garin Maiduguri. Ruwa ya shafe gidajen mutane a halin da ake ciki yanzu haka

Ubangiji Allah ka basu mafita na alheri.

KALLI HOTUNA: Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilci Shugaban ƙasa a wajen jana'izar Hajiya Dada Sauran jig...
03/09/2024

KALLI HOTUNA: Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilci Shugaban ƙasa a wajen jana'izar Hajiya Dada

Sauran jiga-jigan Najeriya da s**a halarci jana'izar sun haɗa da jagoran yan adawa Atiku Abubakar da Peter Obi da sauran su

Margayiyar mai shekara 100 kafin rasuwar ta ita ce mahaifiyar tsohon shugaban kasa Malam Umaru Musa Yar'Adua

DA DUMI-DUMI: Innalillahi wa'innalaihi raji'un mun samu labarin rasuwar Hajiya Dada mahaifiyar marigayi Umaru Musa Yar'a...
02/09/2024

DA DUMI-DUMI: Innalillahi wa'innalaihi raji'un mun samu labarin rasuwar Hajiya Dada mahaifiyar marigayi Umaru Musa Yar'adua

Rayuwa kenan Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi Umar Musa 'Yar'AduaLitar Fetur = N65 Gas = N112Shinkafa = 3,500Simi...
01/09/2024

Rayuwa kenan

Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi Umar Musa 'Yar'Adua

Litar Fetur = N65
Gas = N112
Shinkafa = 3,500
Siminti = N750
Taki = N2500.
Buhun Siga= 7,000.
Buhun Fulawa = N6050

Da Sauran farashin kaya, duk babu tsada a lokacin sa, kuma ya dauko hanyoyin gyara kasa, Allah ya dauki ransa.

Gaskiya Najeriya mun yi rashin Adalin Shugaban Kasa, Ya Allah Ka haskaka Kabarin Umar Musa Yar'Adua, Ka sa shi a Aljannar Firdausi makoma, Allaah swt yajiqan magabatan mu baki daya.

A cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya 'yan bindigar kudin fansa...
21/08/2024

A cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya 'yan bindigar kudin fansa da s**a buƙata, inda ya ce idan wa'adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.

Allaah swt ya kawo mana maganin fitintunun nan

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnoni Jahohi Sun Dakatar Da 'Yancin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi Na Tsawon Wata UkuDaga Muhammad Kwairi ...
13/08/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnoni Jahohi Sun Dakatar Da 'Yancin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi Na Tsawon Wata Uku

Daga Muhammad Kwairi Waziri

A ranar litinin ɗin da ta gabata ne gwamnonin Najeriya s**a bayyana buƙatar su na dakatar da biyan ƙananan hukumomi kai tsaye daga gomnatin tarayya.

Gwamnonin sun bayyana cewa biyan k
Ƙananan hukumomi zaisa jihohi su gagara biyan albashi da kuma yin ayyuka masu muhimmanci, kamar yadda jarida Punch ta ruwaito a jiya litinin.

Dan haka ya kamata ƙananan hukumomi su jira zuwa watan Oktoba kafin aiwatar da doka a cikin biyan kuɗi kai tsaye a cikin asusun su.

Idan mai karatu bai mance ba, a ranar 11 ga Yuli, 2024, kotun ƙoli ta yanke hukunci da ke tabbatar da cin gashin kai na harkokin kuɗi na ƙananan hukumomi 774 dake faɗin Najeriya, kotun ta ƙara da cewa gwamnonin ba za su iya amfani da kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi ba.

Kotun ƙolin ta kuma umurci Akanta-Janar na Tarayya da ya biya LG kason su kai tsaye zuwa asusunsu.

Address


Telephone

+2348067317021

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar Mu A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Duniyar Mu A Yau:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share