News update hausa

News update hausa Wannan shafin munbideshine don kawomuku ingantattun labarai news update hausa

Babbar kotun da ke jihar Kano ta haramtawa hukumomin yaki da cin hanci ci gaba da binciken Muhuyi Rimingado.Hukumomin EF...
29/08/2023

Babbar kotun da ke jihar Kano ta haramtawa hukumomin yaki da cin hanci ci gaba da binciken Muhuyi Rimingado.

Hukumomin EFCC da ICPC da kuma CCB na tuhumar shugaban yaki da cin hanci a Kano kan badakalar kudade a hukumar.

Yayin yanke hukuncin, Alkalin kotun ya ba da umarnin dakatar da ko wane irin shiri a kan Rimingado zuwa wani lokaci.

Rahotanni na nuni da cewa an dakatar da Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar NNPP.Kwamitin amintattun jam'iyyar na jihar Kano ...
29/08/2023

Rahotanni na nuni da cewa an dakatar da Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar NNPP.

Kwamitin amintattun jam'iyyar na jihar Kano ne s**a bayyana batun dakatarwar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon sauraron hukuncin kotu kan ƙarar zaɓen gwamnan jihar.

Ko da ba ka da labari:Siyasa ta dau zafi a Kano yayin da ake jiran sakamakon kotun zaben gwamna.Jam'iyyar APC ta yi kira...
29/08/2023

Ko da ba ka da labari:

Siyasa ta dau zafi a Kano yayin da ake jiran sakamakon kotun zaben gwamna.

Jam'iyyar APC ta yi kira ga mambobinta su dauki azumi da cigaba da rokon Allah don samun nasara.

A bangarensu, NNPP suma sun yi sallah na neman nasara a kotun.

29/08/2023
Mune Mukaci Zabe Da Kuria Sama Da Dubu 30,000 Kuma Hujjojinmu Bazasu Tashi Hakanan ba In Sha Allah Sai Allah Ya Bamu Kuj...
29/08/2023

Mune Mukaci Zabe Da Kuria Sama Da Dubu 30,000 Kuma Hujjojinmu Bazasu Tashi Hakanan ba In Sha Allah Sai Allah Ya Bamu Kujerarmu.Gawuna Is Coming!!

Daga Hassan Cikinza Rano

Fulani sun yi watsi da barazanar Wike, “inda s**a kai shanu kiwo kusa da “Aso Villa” fadar shugaban ƙasa da kuma harabar...
29/08/2023

Fulani sun yi watsi da barazanar Wike, “inda s**a kai shanu kiwo kusa da “Aso Villa” fadar shugaban ƙasa da kuma harabar babban bankin kasa na (CBN) dake birnin Abuja.”

29/08/2023

Irin Wannan Abubwa dake Faruwa Sam Babu dadi
Amma Fa Hassada itace Mafari,
Allah yawanke Zukatan mu Daga Cutar Hassada 🤲

Gwamnatin Tinubu ta gama shirin ɗaukar mutum 7,000 aiki a kowace jiha da Abuja.Idan aka haɗa a jumlace, za a ɗauki mutan...
28/08/2023

Gwamnatin Tinubu ta gama shirin ɗaukar mutum 7,000 aiki a kowace jiha da Abuja.

Idan aka haɗa a jumlace, za a ɗauki mutane 300,000 a faɗin Najeriya.

Ma'aikatan zasu yi aiki ne a sabuwar hukumar da aka kafa NATCOM, mun tattara muku cikakkun bayanai.

Wannan batu ya soma ɗaukar hankali ne tun lokacin da wasu kafofin yaɗa labarai na Najeriya s**a kwarmata cewa Hannatu Mu...
28/08/2023

Wannan batu ya soma ɗaukar hankali ne tun lokacin da wasu kafofin yaɗa labarai na Najeriya s**a kwarmata cewa Hannatu Musawa ta karɓi muƙamin minista ba tare da kammala aikin hidimar ƙasa ba.

28/08/2023

Har yanzun wasu na ganin Peter Obi zai kwace mulki daga hannun Tinubu a Kotun zaɓe.

Shugaban LP na ƙasa ya ce yana da tabbacin Kotu zata ayyana Obi a matsayin shugaban ƙasa.

Ya ce daga nan zuwa watan Satumba za a yanke hukunci, ya ce hankalin wasu ya tashi, ba su iya bacci.

28/08/2023

An bukaci 'yan Najeriya su koma amfani da naira a kasuwanci tsakaninsu da ƙasar China.

Babban lauya Femi Falana ne ya bayyana hakan a ranar Litinin ɗin da muke ciki.

Ya ce har yanzu yarjejeniyar amfani da naira a tsakanin ƙasashen biyu tana nan daram.

28/08/2023

Ana zargin gwamnan Ogun da turmushe kason tarayya na ƙananan hukumomin jiharsa.

Ciyaman din Ijebu ta gabas ya rubuta doguwar wasiƙar ƙorafi zuwa ga tsohon gwamnan Ogun.

Ya ce tunda s**a hau mulki a 2021, gwamna bai taɓa barin kason ya iso aljihun kananan hukumomi ba.

28/08/2023

Mali ta juya baya ga dakarun wanzar da zaman lafiya, tare da dogaro a kan mayaƙan Wagner domin samar da tsaro. Amma yanzu, shugaban sojojin hayar na Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a hatsarin jirgin sama.

Kadan Daga Cikin Sunayen Kanurai Da Ma'anoninsuNGARI = USMANB3RA = IBRAHIMGARWA = ABUBAKARKALLA = MUSATAR = MUKTARARI/GA...
28/08/2023

Kadan Daga Cikin Sunayen Kanurai Da Ma'anoninsu

NGARI = USMAN

B3RA = IBRAHIM

GARWA = ABUBAKAR

KALLA = MUSA

TAR = MUKTAR

ARI/GARGA = ALI

DALA = ABDALLAH

KONTO = ADAM

BUNAMI = BILYAM

BUNU = UMAR

BUTARI = ABU TALIB

MODU/MOMMODU = MUHAMMAD

AJI = ALHAJI

MELE = IDRIS

FOJI/KUURA/MANGU = HADIZA

MADARI = HAUWA

TUKULE/KARU/FANDI/FANDAU/FALTA/FALMATA/YAALTA/KOLO = FATIMA

KODO = HALIMA

NGWARI/YABURRA = ZAINAB

AMSA/SHETU/YAMARA = HAFSAT

BUDU = MARYAM

BALU = BILKISU

YARUWAIYA = RUKAYYA

MAIDA/AISA = AISHA

SATO = AMINA

Daga JIBRIN MUHAMMED KH, SHUWARI MADINATU

Sama Da Shekara Hamsin Kenan Ban Leka Gida Kano Ba, Ina Zaune A Garin Makurdi, Ina Rokon 'Yan Uwana Su Zo Su Dauke Ni Do...
28/08/2023

Sama Da Shekara Hamsin Kenan Ban Leka Gida Kano Ba, Ina Zaune A Garin Makurdi, Ina Rokon 'Yan Uwana Su Zo Su Dauke Ni Domin Na Samu Damar Yin Ibada Yadda Ya Kamata, Cewar Wannan Dattijo

Bawan Allah Shu'aibu mutumin Kano ne, dan arin Tudun Wadan Dankade. Gidan Mai Unguwa Tanko.

Wannan bawan Allah yana son 'yan uwansa su taimaka su yi hanyar da za su zo su maida shi gida ya samu ya yi Ibada yadda ya kamata.

Yanzu haka yana garin Makurdi dake jihar Binuwe cikin wani kauye Lower Benue gabata da unguwar Wadata.

Jama'a don Allah a yada (sharing) har ya kai ga 'yan uwansa.

Za a iya tuntunbar wadannan lambobi don karin bayani;
08034983021
09020512419

Tsohon hadimin Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya hasaso kwanakin da s**a ragewa Tinubu a kan kujera.Ya bayyana cewa watan...
28/08/2023

Tsohon hadimin Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya hasaso kwanakin da s**a ragewa Tinubu a kan kujera.

Ya bayyana cewa watanni biyu ne kacal s**a ragewa Tinubu kafin ya bar karagar mulki.

Ya shawarci Tinubu da ya naɗa ƙarin mutum ɗaya cikin ministocinsa kafin lokacin.

28/08/2023

Shehu Sani ya caccaki ministan ayyuka, David Nweze Umahi.

Tsohon sanatan ya zargi Umahi da riƙe muƙamin sanata da na minista a lokaci guda.

Shehu Sani ya ce tsohon gwamnan yana tsoron reshe ya juye da mujiya ne ya rasa muƙaman biyu idan a ka ƙwace kujerar Tinubu.

Malamin Addini ya ankarar da Kanawa a kan kokarin maido jam’iyyar APC kan mulkin Jihar KanoSaboda a samu nasara a kotu z...
28/08/2023

Malamin Addini ya ankarar da Kanawa a kan kokarin maido jam’iyyar APC kan mulkin Jihar Kano

Saboda a samu nasara a kotu zabe, mukarraban Gwamnati da Rabi’u Musa Kwankwaso su ka fito sallah

Idan NNPP ta yi rashin sa’a, za a iya yin waje da Gwamna Abba Kabir Yusuf da bayan watanni 3 a ofis

Ya Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Magance Tashin Farashin Kayan Abinci Ko Kuma Ta Dawo Da Tallafin Man FeturDaga Audu Bulama...
28/08/2023

Ya Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Magance Tashin Farashin Kayan Abinci Ko Kuma Ta Dawo Da Tallafin Man Fetur

Daga Audu Bulama Bukarti

Ya zama lalle Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki na gaggawa a kan bala'in yunwar da ta jefa mutane a ciki. Yanzu fa masu ci su koshi sau biyu a rana sune kadan a Nijeriya. Kasa fa ba ta zama lafiya cikin tsananin yunwa. Wannan fa ba matsalar da za a dauki wasu 'yan kudade a tallafawa wasu 'yan tsiraru da shi bane. Kowa yana ji a cikinsa.

Idan gwamnati ta gaza samo wata hanyar magance tashin farashin abinci, to kawai ta dawo da tallafin mai. Ai dama man namu ne kuma me amfanin abinka da ba zai iya kashe maka yunwa ba? Ya zama tilas gwamnati ta dau mataki kafin tura ta kai bango. Idan kuma ba haka ba, wanda ya ƙi bari...

TALLAFI: Wannan Kason Al'ummar Unguwa Guda Ce Da Za Su Raba A Matsayin Tallafin Gwamnati A Jihar Nasarawa, Inda Za A Kar...
28/08/2023

TALLAFI: Wannan Kason Al'ummar Unguwa Guda Ce Da Za Su Raba A Matsayin Tallafin Gwamnati A Jihar Nasarawa, Inda Za A Karkasa Kowa Ya Samu Rabonsa

Rahotanni sun nuna cewa kason al'ummar Angwan Tofa ne dake garin Keffi a jihar Nasarawa.

28/08/2023

Asslaualaikum jama an wannan
Gidan Mai albarka kuna tare da
Daya daga cikin admin ne
Mai suna lawal abubakar

Don Allah 🙏 muna neman afuwan
DUK Wanda muka batama rai
A Wannan gidan

Sa Anan Idan kukaga kuskure
Ku sanar damu

Allah yabamu zaman lfy

A kasar mu ta Nigeria

Allah Ya Bada Sa'aDaya daga cikin matasan da s**a wakilci Najeriya a gasar musabakar Al-Qur'ani ta Duniya a karo na 43, ...
28/08/2023

Allah Ya Bada Sa'a

Daya daga cikin matasan da s**a wakilci Najeriya a gasar musabakar Al-Qur'ani ta Duniya a karo na 43, Alaramma Abdullahi yau Yahau mimbari, ya rera karatun Al-Qur'ani mai Girma, mai dadin ji da dadin sauraro.

A gobe Talata, shima Alaramma Sadiq zai hau mimbari. Duka matasan guda biyu 'yan asalin jihar Zamfara ne. Muna musu fatan Alkhairi.

Daga Comr Abba Sani Pantami

YANZU-YANZU: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bada Umurnin Rufe Dukkannin Gidajen Gala Na Raye-Raye Da Kide-Kide Dake Fadin Jihar ...
28/08/2023

YANZU-YANZU: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bada Umurnin Rufe Dukkannin Gidajen Gala Na Raye-Raye Da Kide-Kide Dake Fadin Jihar Gombe

Daga Comr Abba Sani Pantami

Sakataren Gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya sanar da wannan umarnin ta hannun babban daraktan yada labarai na Gwamnatin jihar Ismaila Uba Misilli.

Sakataren Gwamnatin ya ce matakin ya biyo bayan jerin korafe-korafe da jama’a ke yi kan ayyukan lal*ata da ayyukan ta’a*ddanci da kuma matsalar ts*aro da ake tafkawa a irin wadannan gidajen da dare.

Don haka Gwamnan ya umarci ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya da kuma Operation Hattara da su tattara jami’ansu domin aiwatar da wannan umarni, tare da tabbatar da bin doka da oda.

Duk Ministan Da Ya Gaza Taka Rawar Gani, Zan Yi Waje-Rod Da Shi, Cewar Shugaba Tinubu
28/08/2023

Duk Ministan Da Ya Gaza Taka Rawar Gani, Zan Yi Waje-Rod Da Shi, Cewar Shugaba Tinubu

Sojoji Sun Ceto Mutane 35 Dake Tsare A Hannun 'Yan Boko Haram A Jihar Borno
28/08/2023

Sojoji Sun Ceto Mutane 35 Dake Tsare A Hannun 'Yan Boko Haram A Jihar Borno

28/08/2023

An kai batun kafa kwamitin da zai binciki asusun NUPRC zuwa ga Ministan shari’a na tarayya (HAGF)

Sabon Ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN zai duba dokar kasa kafin a bar kwamitin ya fara yin aiki

Femi Gbajabiamila ya ce ana umartar kwamitin ma’aikatar man fetur ya dakatar da binciken kudi a NUPRC

"Kwankwaso ba Dakta ba ne, idan ya isa ni da shi mu buga Satifiket din mu a jarida gobe. ~ Dr. Abdullahi Umar Ganduje,"
28/08/2023

"Kwankwaso ba Dakta ba ne, idan ya isa ni da shi mu buga Satifiket din mu a jarida gobe. ~ Dr. Abdullahi Umar Ganduje,"

28/08/2023

Jarumar fina-finan Yarbawa, Lizzy Anjorin ta ce ta hakura da Musulunci bayan ta koka kan yadda Musulmai su ka mata.

Anjorin ta ce a lokacin da ake yakarta a kafafen sadarwa, babu wani Musulmi ko wata kungiyar Musulunci da ta tsaya mata.

Ta kuma gargadi mutane a wani faifan bidiyo inda ta ce kada su sake kiranta da sunan Musulunci.

28/08/2023

Gwamnatin tarayya ta umurci a ba dakataccen shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, damar ganin lauyoyi da yan uwansa.

An rahoto cewa babban kalubale da ake fuskanta kan lamarin Bawa shine ya ki ba masu bincike hadin kai.

Haka kuma, mahaifinsa ya hana lauyoyinsa shigar da kara kotu don neman a sako shi.

DA DUMI-DUMI : Jami'an Tsaro Sun  Cafke Wani Matukin Jirgin Sama Mai Saukar Angulu, Mai Suna Juan Remy, Wanda Yake Kaiwa...
28/08/2023

DA DUMI-DUMI : Jami'an Tsaro Sun Cafke Wani Matukin Jirgin Sama Mai Saukar Angulu, Mai Suna Juan Remy, Wanda Yake Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai Domin Kai Hari Ga Bayin Allah A Jihar Neja.

CNN Hausa Nigeria

Address

New
Minna

Telephone

+2347025439493

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when News update hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to News update hausa:

Videos

Share

Nearby media companies



You may also like