DMA Hausa News

  • Home
  • DMA Hausa News

DMA Hausa News Muna Maka Barka Da Zuwa Shafin
DMA Hausa News mai Inganttatun Labarai Daga Tushe Ingantattce

Sabuwar Littafi kenan Mai Suna Mafita Cikin A Lamarin Aure wanga Littafi Dai Ankaddamar Dashi ne A Jiya  Lahadi  inda Ma...
29/04/2024

Sabuwar Littafi kenan Mai Suna Mafita Cikin A Lamarin Aure wanga Littafi Dai Ankaddamar Dashi ne A Jiya Lahadi inda Mai Littafi Sayyadi Abubakar Sadiq Umar Sanda Abi-Huraira ya Rubuta .

Littafin Mafita A Cikin Lamarin Aure Dai Ya Kunshi Abubuwan Da Dama karsu Yadda Bawa zai Nima Matan Nagari Domin Samu Ingantarciyar Zuriya Da Kuma Wasu Abubuwan Da Budurwa zata Kaucewa A Yayin da Namiji Yake Nimanta Akan Aure Da Yadda Namiji Zai Zauna Da Mace A Yayin da Yazo zance Da Ita A Tafarkin Addinin Musulunci Da Yadda Iyaye Zasu Bi Wajan Aurar Da Yaransu Acikin Sauki A Cikin Tafarkin Data Dace Da Sauransu Ana Sayar Da wanga Littafi A Garin Minna Cikin Anguwanmu Chanchaga A islamiyar Madarasatul Abi-Huraira Dake Garin Minna Akan Farashin #500 Mai Niman Karin Bayani Yana iya Kiran Wanga Number 07068257853

Yabon Kasida kenan A Taron Walimar Saukar Karatun Al-qurani  Daga Daliban Makarantar Abi - Huraira Dake Anguwan Chanchag...
28/04/2024

Yabon Kasida kenan A Taron Walimar Saukar Karatun Al-qurani Daga Daliban Makarantar Abi - Huraira Dake Anguwan Chanchaga Garin Minna Jahar Neija

Anyi Jan Hankali Zuwa ga  Matasa Maza Da Mata Da Su Kasance Masu Riko Da Al-qurani Mai Girma A Kowani Lokaci  Sheikh Moh...
28/04/2024

Anyi Jan Hankali Zuwa ga Matasa Maza Da Mata Da Su Kasance Masu Riko Da Al-qurani Mai Girma A Kowani Lokaci Sheikh Mohammad Mohammad Sidi Saba Shine Yayi wanga Magana A Taron Walimar yaye Yara Talatin Da Uku Na Karatun Al-qurani Karo Na Bakwai Wanda Makaratar islamiyar Madarasatul Abi-Huraira Ta A Gudanar A Makarantar Firamariy Dake Anguwan Chanchaga Dake Garin Minna A Jahar Neija Ayau Lahadi

Mal Sidi Saba Wanda Yace Roko da Al-qurani Mai Girma Wata Babbar Azikine Ga Rayiwar Al-umma Musulmi Daga Nan Duniya Har Kiyama inda yakara da Cewa Daliban Su Kasance Masu Jajircewa wajan Ganin Sun sauke Dukan Hakkin Da Yarataya A wuyarsu A wanan Lokaci Da Ubangiji Yabasu Kyautar Saukan Karatun Al-qurani Akarshe Yayi Fatan Alhairi Zuwa ga Daliban awajan Rokon Ubangiji Ya Albarkaci Saukar karatunsu

DMA Hausa

Ana cigaba da shagalin bikin daya daga cikin yayan Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP Prince Sunus...
28/04/2024

Ana cigaba da shagalin bikin daya daga cikin yayan Mai martaba sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP Prince Sunusi Aminu Ado Bayero (Halifa) inda ayammacin jiya juma'a aka gudanar da zaman AJO a kofar kudu fadar masarautar kano. Ango yana tare da dan uwansa Prince Kabiru Aminu Ado Bayero (Badde)

gwamnan jihar Rivers Similanayi Fubara ya kai ziyara inda tankar mai ta k**a da wuta a birnin Fatakwal. Rahotanni sun ce...
28/04/2024

gwamnan jihar Rivers Similanayi Fubara ya kai ziyara inda tankar mai ta k**a da wuta a birnin Fatakwal. Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu.

SANARWAN GAGGAWA: Ga Wanda Yasan Wanan Baiwar Allah Yayi Gaggwar Zuwa Royal Hospital  Dake Garin Busu Ta Karamar Hukumar...
27/04/2024

SANARWAN GAGGAWA: Ga Wanda Yasan Wanan Baiwar Allah Yayi Gaggwar Zuwa Royal Hospital Dake Garin Busu Ta Karamar Hukumar Jahar neija

YANZU-YANZU: Yadda Jama'ar Garin Rigasa S**a Hana A Binne Gawa Biyu.....Wani Mummunan Al'amari Ya faru A Garin Kaduna! W...
27/04/2024

YANZU-YANZU: Yadda Jama'ar Garin Rigasa S**a Hana A Binne Gawa Biyu.....

Wani Mummunan Al'amari Ya faru A Garin Kaduna! Wasu Mutane Da Ba'a san Ko Su waye Ba Sun Shiga Maƙabartar Layin Bola Dake Unguwar Rigasa Da Wata Motar Asibiti (Ambulance Car), Inda S**a yi Yunƙurin Birne Wasu Gawarwaki Guda Biyu Ba tare Da Sanin Hukumar Maƙabartar Ba😥.

Bayan Jama'ar Gari Sun Sami Labari Shi ne S**a je S**a yo Waje Da Gawarwakin Da Ba'a san Ko na Su Waye ba, Da kuma Dalilin Da yasa Aka Kashesu Ba, Sannan S**a Cinnawa Motar Asibitin Wuta Kamar Dai Yanda Kuke Gani a Hotunan dake Kasa.

Zuwa Yanzu Dai Ba'a san Dalilin Da yasa Aka yi Yunƙurin Birne Gawarwakin a Sirrance ba, kuma ba a san ko Gawarwakin Waye Ba, A Taƙaice Dai Jama'ar Gari Sun Ɗauki Doka A Hanunsu,Wanda Wannan Yunƙurin Ɗaukar Dokar Ne Yasa Aka Rasa Wadanda S**a zo Da Gawar, Domin sun bi ta cikin Hayaniya Sun Sulale sun gudu.

Allah ya kyauta.

Najeriya za ta zama ta farko a Afrika wajen ƙarfin tattalin arziƙi, in ji shugaba Tinubu.Ko Mai Zakuce ?
27/04/2024

Najeriya za ta zama ta farko a Afrika wajen ƙarfin tattalin arziƙi, in ji shugaba Tinubu.

Ko Mai Zakuce ?

Yanbindiga Sun Harbe Kwamandan Sojoji Har Lahira A Kastina’Yan bindiga sun kashe kwamandan sojoji da ake aikin samar da ...
27/04/2024

Yanbindiga Sun Harbe Kwamandan Sojoji Har Lahira A Kastina

’Yan bindiga sun kashe kwamandan sojoji da ake aikin samar da tsaro a wani harin kwanton bauna a yankin Sabon Garin Dan’Ali da ke Jihar Katsina.

Shaidu sun ce a ranar Alhamis ne kwamandan sojojin mai muƙamin Manjo ya gamu da ajalinsa, kuma an kai gawarsa asibiti.

Wata majiya mai tushe ta ce an kai wa sojojin harin ne a kauyen Malali da ke Karamar Hukumar Kankara, inda kwamandan da ya jagoranci kai musu agaji domin kurkushe harin da aka kai wa kauyen.

“Malali yana kan hanyar Zangon Pawwa kuma ka san ’yan bindiga sun mamaye yankin.

“Duk lokacin da aka kai hari jami’an tsaro s**an nemi abokan aikinsu daga sansanin da ke Maraban Dan’Ali su taimaka musu, kuma shi wannan kwamandan yakan amsa ba tare da bata lokaci ba.

“To a wannan karon ma sun nemi hakan, amma sai ya zo a cikin Hilux ba a mota mai sulke ba, watakila ba ta kusa ne a lokacin.

“Sai kuma aka yi rashin sa’a maharan sun bi sawunsa, inda s**a harbe shi a kai.”

Wani mazaunin yankin ya ce an yi kazamin fada tsakanin ’yan bindiga da sojojin kafin su dauki gawar kwamandan.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin sojoji a Jihar Katsina, Oiza Ehinlaidlye, amma hakan bai yiwu ba, saboda jami’in bai amsa kiran ko sakon da wakilin namu ya aika masa ba, har zuwa lokacin da ya aiko rahoton.

Allah Ya Jiƙansa Da Rahama!

Majiya: Aminiya

Kano Ce Kan Gaba Wajen Zuƙar Taba Sigari A NajeriyaJihohin Kano da Jigawa su ne a sama a cikin jerin jahohin da aka fi s...
27/04/2024

Kano Ce Kan Gaba Wajen Zuƙar Taba Sigari A Najeriya

Jihohin Kano da Jigawa su ne a sama a cikin jerin jahohin da aka fi shan taba sigari a Najeriya, k**ar yadda wani bincike ya tabbatar.

Wataƙila A Samawa Katsinawa Lafiya A Maganar Shan Taba Sigari.

'Yan ta'adda sun kashe kwamandan sojin Najeriya a wani harin kwanton bauna a jihar Katsina. Lamarin dai ya faru ne a san...
26/04/2024

'Yan ta'adda sun kashe kwamandan sojin Najeriya a wani harin kwanton bauna a jihar Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a sansanin sojin da ke Sabon Garin Dan'ali na karamar hukumar Danmusa.

EFCC ta bukaci makarantar American International School Abuja da ta dawo $845,000, kudin da Yahaya Bello ya biyawa dansa...
26/04/2024

EFCC ta bukaci makarantar American International School Abuja da ta dawo $845,000, kudin da Yahaya Bello ya biyawa dansa dake karatu a makarantar.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta bukaci makarantar American International School, Abuja, da ta mayar da makudan kudi dala 845,000 da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya biya dansa wanda dalibin babbar makaranta ne.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ola Olukoyede, a wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, ya bayyana yadda tsohon gwamnan da ke cikin rikici ya cire $720,000 daga asusun jihar domin biyan kudin makarantar yaronsa.

Ana zargin Bello ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da makarantar na biyan dala 845,000 har zuwa 2034 ga babban dansa mai suna Ali Bello.

Amma da aka gano laifin kudi da ake zargin tsohon gwamnan ya aikata tare da tsananta binciken hukumar EFCC, hukumar ta bukaci makarantar da ta dawo da kudaden nan take.

A martanin da makarantar ta mayar, ta amince da cewa Bello ya biya kudin ne a watan Satumbar 2021 kuma ya amince ta maido da kudaden da ya kai £760,000 bayan ta cire ayyukanta na ilimi da ake bawa dan tsohon gwamnan tun 2021.

Har ila yau makarantar ta makala rasiti da takardun yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kan gudanarwar ta dan Bello.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan yarjejeniyoyi ita ce:

“Yarjejeniya tsakanin Malam Ali Bello da AISA na kudin makaranta kafin kammala karatu. Sharuɗɗa sun haɗa da biyan kuɗi, yuwuwar haɓaka kuɗi, da manufofin dawo da kuɗi. Mista Greg Hughes ne ya sanya hannu na AISA da Mista Ali Bello. Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da hakan.”

Gwamnatin Tarayya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 3.8 daga CBN a cikin watanni 6.Gwamnatin tarayyar Najeriya ta samu kari...
26/04/2024

Gwamnatin Tarayya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 3.8 daga CBN a cikin watanni 6.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta samu karin Naira Tiriliyan 3.8 a wani sabon salo da hanyoyin karbar bashi a cikin watanni shida na karshen shekarar 2023.

Wannan bisa ga bayanan wucin gadi da aka buga a cikin sabuwar sanarwar kididdiga ta kwata na hudu na 2023 da babban bankin kasar ya fitar kwanan nan.

Alkaluman da babban bankin na CBN ya fitar sun nuna cewa adadin ya tashi daga Naira Tiriliyan 4.4 a karshen watan Yunin 2023 wanda hakan ke nufin ma’auni da tsarin hada-hadar kudi da gwamnati ke bayarwa a yanzu ya kai Naira tiriliyan 8.2 a watan Disambar 2023.

Wannan dai na zuwa ne duk da rahotannin da aka samu na cewa Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta karbo rance daga CBN ba.

Samar da Hanyoyin suna aiki ne a matsayin hanyar da ke ba gwamnati damar samun kuɗaɗen na ɗan gajeren lokaci ko gaggawa daga CBN don magance gibin kuɗin shiga.

Jimlar Hanyoyi da Ma'auni k**ar na Mayu 2023 lokacin da gwamnatin Tinubu ta karbi mulki ya kai Naira tiriliyan 26.95. Koyaya, an kiyaye ma'auni k**ar yadda aka haɗa a matsayin wani ɓangare na bayanan bashi na cikin gida na gwamnatin tarayya.

Wani bincike mai zurfi na bayanan ya nuna ma'auni a karshen watan Yuni 2023 ya kasance Naira tiriliyan 4.36 wanda ke nuna cewa ana iya tura ma'auni na watan da ya gabata zuwa Ofishin Kula da Bashi.

Sai dai daga watan Yulin 2023, ma’auni na karuwa a kowane wata, daga farko zuwa Naira Tiriliyan 4.5 a watan Yuli, sai kuma Naira Tiriliyan 5.1 a watan Agusta, inda ya haye Naira Tiriliyan 5.1 a karon farko.

Ya zuwa watan Satumba, jimillar ta kai Naira tiriliyan 6.4, wanda ke wakiltar karin rance mafi girma na wata guda da kusan Naira tiriliyan 1.3. Daga nan ya haura zuwa Naira Tiriliyan 7.2 a watan Oktoba kafin daga bisani ya tashi zuwa Naira Tiriliyan 7.6 a watan Nuwamba.

YANZU-YANZU: Gini Ya Faɗowa Mutane Unguwar Kuntau Dake Jihar KanoZuwa yanzu tuni aka kai ɗauki wajan don tono mutanen da...
26/04/2024

YANZU-YANZU: Gini Ya Faɗowa Mutane Unguwar Kuntau Dake Jihar Kano

Zuwa yanzu tuni aka kai ɗauki wajan don tono mutanen da gini ya ruftawa a unguwar Kuntau cikin Karamar Hukumar Gwale, a jihar Kano.

Ginin ya rufta ne da safiyar yau Juma’a sa’ilin da ma’aikatan dake aikin ginin s**a fara aikinsu.

Ginin dai sabo ne, kuma ana hasashen asarar rai a wajan kasancewar masu aikin nada yawa.

© AMINTACCIYA

Ƴan bindiga sun kashe mutane uku tare da awun gaba da wasu yayi da s**a kai hari fadar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Muhamm...
26/04/2024

Ƴan bindiga sun kashe mutane uku tare da awun gaba da wasu yayi da s**a kai hari fadar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Muhammad Bunu.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewar mutane ukun da aka sace sun hada da Sarkin Gidan Masarautar Zurmi, Alhaji Yusuf Buhari da wani mai shayi da ke kusa da fada, da wani mutum guda.

Mazauna yankin sun ce bayan fadar sarkin, maharan a daren Laraba, sun kai hari gidan tsohon shugaban mulkin soja na Jihar Nasarawa, kuma tsohon ministan muhalli a gwamnatin Olusegun Obasanjo, Kanar Bala Muhammad Mande mai ritaya.

Shaidu sun ce a lokacin da aka kai harin Kanar Mande mai ritaya ba ya gida, amma Sarkin Zurmi na cikin fadarsa lokacin da ’yan bindigar s**a kaddamar da harin.

A yayin harin, ƴan bindigar sun lalata turken sadarwa, sannan s**a kone wasu injina guda biyu da ke kusa da fadar sarkin.

Wannan Dan Agaji Na Neman Taimakon Jama'a, Yana Fama Fa Rashin Lafiya Kuma Ga Mata Biyu Da Yara Takwas Babu Cin Yau Bare...
26/04/2024

Wannan Dan Agaji Na Neman Taimakon Jama'a, Yana Fama Fa Rashin Lafiya Kuma Ga Mata Biyu Da Yara Takwas Babu Cin Yau Bare Na Gobe

Dan uwa Malam Abubakar Da'awa dan agaji yana neman taimako, tin bayan da muka maido shi daga asibiti, Alhamdulillahi jiki yana kyau.

Saidai yanzu haka iyalansa na cikin kumci na yunwa, domin 'ya'yansa a wasu lokutan har tukunya suke kankarewa saboda karancin abinci.

Inda a wasu lokutan ma yaran s**an gama kukan yunwa su gaji su kwanta babu abinci, wata yarinyar kuma ruwa ta debo tana sha a madadin abinci, haka kuma na tarar duka matanshi biyu sun fita memowa yara abinci ko a samo koba a samo ba.

Ban yi tinanin yanda na tarar da shi ba domin magungunan sa sun kare gashi babu kudin saye, ga rashin abinci, gashi lokacin da likita ya ce a koma da shi ya wuce, wai yana jin kunyar sake meman taimakon al'umma.

Ga mata biyu ga yara 8 kananu ga makarantar yaran ta tsaya sak**akon rashi.

Dan haka don Allah don Annabi SAW ku taimake shi da kayan abinci da kuma abunda zai rinka sayen magani da diresin .

Ga lmbershi nan ta waya
0802 928 8032


Ga masu son taimakon shi ku taimake shi ta wannan account din 👇

Acct.
3025591926,
first bank
Sadiq Umar

Ko kuma ku kira 07060937266
Sadiq Umar Yari
domin jin karin bayani.

Allah Ya sa a dace.

An Fara Aikin Ginin Katangar Gidan Yarin Suleja Da Ta Rushe 'Yan Firsin Sama Da 100 S**a Tsere.
26/04/2024

An Fara Aikin Ginin Katangar Gidan Yarin Suleja Da Ta Rushe 'Yan Firsin Sama Da 100 S**a Tsere.

Gwamnatin Jihar Neja ta fara aikin cikin garin Mokwa. Wannan na cikin ayyuka na kilomita dari 556 da Gwamnatin zata yi a...
26/04/2024

Gwamnatin Jihar Neja ta fara aikin cikin garin Mokwa.

Wannan na cikin ayyuka na kilomita dari 556 da Gwamnatin zata yi a daukacin kananan Hukumomin dake Jihar.

📷 Abdulberqy Ebbo

Abin  Sha'awa: Dansanda Yakamu Da Soyayyar Likita A Garin Minna Idan Ya asamu Da AmincewartaWacce Fata Zakuyiwa wayanga ...
26/04/2024

Abin Sha'awa: Dansanda Yakamu Da Soyayyar Likita A Garin Minna Idan Ya asamu Da Amincewarta

Wacce Fata Zakuyiwa wayanga Masoya ?

Yan banga sun azabtar da wani tsoho dan shekara 60 Wanda yayi sanadin mutuwar sa har lahira a Anambra bisa laifin sayar ...
26/04/2024

Yan banga sun azabtar da wani tsoho dan shekara 60 Wanda yayi sanadin mutuwar sa har lahira a Anambra bisa laifin sayar da tankin ruwa da yayi ya ci da iyalin sa .

DOVE NEWS HAUSA

Yanzu-Yanzu: An samu ruwa sama a wasu sassan garuruwan Gombe, Bauchi, da Zariya.Masu karatu ya abin yake a yankinku?
25/04/2024

Yanzu-Yanzu: An samu ruwa sama a wasu sassan garuruwan Gombe, Bauchi, da Zariya.

Masu karatu ya abin yake a yankinku?

Garin Alawa ta Karamar Hukumar Shiroron Jihar Neja ta zama kufai bayan da mazauna garin s**a tattara s**a fice a safiyar...
25/04/2024

Garin Alawa ta Karamar Hukumar Shiroron Jihar Neja ta zama kufai bayan da mazauna garin s**a tattara s**a fice a safiyar yau.

Wannan ya faru ne dalilin janyewar da Jami'an tsaro s**a yi daga garin kuma yana daya daga cikin garuruwan dake da hatsarin gaske a Jihar.

Har yanzun dai Gwamnatin Jihar bata ce komai ba akai.

Allah yakawo masu Dauki

Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Nemi Ganduje Ya Yi Murabus..suna meman shugabancin jam’iyyar ya koma yankin Arewa ta Tsakiy...
25/04/2024

Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Nemi Ganduje Ya Yi Murabus
..suna meman shugabancin jam’iyyar ya koma yankin Arewa ta Tsakiya

Wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a hedikwatar Jam’iyyar APC mai mulki da ke Abuja, suna neman shugabanta na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya sauka daga muƙaminsa.

Masu zanga-zangar suna kuma kira ga shugaba Bola Tinubu da Sakataren Gwamnati, George Akume, su duba yiwuwar mayar da shugabancin jam’iyyar yankin Arewa ta Tsakiya.

Suna neman Ganduje ya sauka ne kwanaki biyu bayan shugabannin APC na jihohi sun jaddaga goyon bayansu da amincewa ga shugabancinsa.

Shugabannin jam’iyyar daga jihohin da ke faɗin Najeriya sun sanar da goyon bayansu ga Ganduje ne a lokacin ziyarar aiki da s**a kai masa a ofishinsa.

Daga cikin masu zanga-zangar, akwai masu ɗauke da kwalaye da ke ɗauke da rubutun neman murabus ɗin Ganduje, da masu neman shugabancin jam’iyyar ya koma yankin Arewa ta Tsakiya idan ya sauka.

Suna wannan kiraye-kiraye ne bayan dambarwar dakatar da Ganduje da wani tsagin shugabannin mazabarsa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano s**a dakatar da shi.

Sun sanar da dakatar da shi ne kan zargin sa da almundahanar kuɗaɗe da cin hanci da rashawa a lokacin da yake gwamnan jihar da gwamnatin jihar mai ci ke masa.

Muharamu ta mako!Ana ci gaba da muhawara kan kafa 'yansandan jihohi a Najeriya. A yayin da Shugaba Bola Tinubu na Najeri...
25/04/2024

Muharamu ta mako!

Ana ci gaba da muhawara kan kafa 'yansandan jihohi a Najeriya.

A yayin da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ke ganin ya k**ata a samar da 'yansanda mallakar gwamnatocin jihohi, Sufeto Janar na 'yansandan kuma na ganin Najeriyar ba ta yi karfin kafa su ba.

Mene ne ra'ayinku a kan wannan batu la'akari da halin da ake ciki a yankunanku kan yanayi na tsaro?

Yadda Farashin Abinci Ke Ƙara Ruguzowa A Kafitanin Jihohin Najeriya. Ana cigaba da samun rahoton saukar kayan abinci dag...
25/04/2024

Yadda Farashin Abinci Ke Ƙara Ruguzowa A Kafitanin Jihohin Najeriya.

Ana cigaba da samun rahoton saukar kayan abinci daga jihohin Najeriya a kowace rana.

Rahoto daga wani ganau a jihar Yobe wanda ya je sayo abinci da kansa ya shaida mana cewa lallai ya shaida yadda abinci ya sauka a tasa jahar, Ga abinda yake cewa; Sati biyu da s**a gabata farashin buhun Wake Naira 110,000 amma a wannan satin 100,000 yake, yanzu haka da muke magana an ce ya sake saukowa zuwa 80,000.

Masara ma a sati biyu da s**a gabata 55k take amma jiya ta koma 42k.

Dawa da Gero a sati biyu da s**a wuce suna tsakanin 47-50k, ita ma jiya sun koma 40k-38k." In ji Malamin.

Wannan ganau ya ci gaba da cewa. "Shinkafa 'yar India jiya na sayi buhu akan kuɗi 60,000.

A Kasuwar Ngalda ita ma dai a jihar ta Yobe ga yadda aka yi cinikin kayan abincin k**ar haka
1. Buhun Wake 80k,
2. Buhun Masara 45k
3. Buhun Dawa 38k
4. Buhun Gero 41k.

Zulum ya buƙaci sojoji su kafa sansani a dajin SambisaGwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum ya buƙaci rundunar sojin...
25/04/2024

Zulum ya buƙaci sojoji su kafa sansani a dajin Sambisa

Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum ya buƙaci rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya da ta kafa sansani a dajin Sambisa domin magance ayyukan ƴan ta'adda.

Zulum ya yi kiran ne a lokacin da mambobin kwamitin soji na majalisar wakilan Nijeriya s**a ziyarceshi a Maiduguri ranar Laraba nan.

Gwamnan na Maiduguri ya kuma buƙaci rundunar sojin ta kafa sansani a kusa da tafkin Chadi da tsaunin Mandara, wuraren da ke ci gaba da zama maɓoyar ƴan ta'adda.

Ya kuma yi kira ga majalisar wakilan da ta tabbatar ta samar da kuɗin da za a sayi isassun mak**an yaƙi da ta'addanci cikin kasafin kuɗi.

Zulum ya yi alƙawalin cigaba da tallafawa sojoji, inda ya ce zuwa yanzu mayaƙan ƙungiyar Boko Haram kusan dubu 190 ne s**a miƙa kai ga hukumomi.

Kuma ya ce kula da waɗannan tubabbun ƴan Boko Haram wani batu ne da yake buƙatar tallafin dukkanin masu ruwa da tsaki.

Ɗazu ne gobara ta k**a a kasuwar garin Batsari, yayin da kasuwar ke haramar ci ranar Alhamis.Kawo yanzu dai bamu samu ƙa...
25/04/2024

Ɗazu ne gobara ta k**a a kasuwar garin Batsari, yayin da kasuwar ke haramar ci ranar Alhamis.

Kawo yanzu dai bamu samu ƙarin bayani daga waɗanda s**a shaida lamarin ba, amma muna tafe da ƙarin bayani nan gaba.

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta cafke mutum huɗu bisa zargin ƙwacen waya inda aka same su da wayoyin hannu guda bakwa...
25/04/2024

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta cafke mutum huɗu bisa zargin ƙwacen waya inda aka same su da wayoyin hannu guda bakwai da ankwa.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce mutanen da ake zargi sun bayyana cewa suna amfani da babur mai ƙafa uku wajen yi wa jama'a ƙwacen waya.

📷: SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Wannan shi ne ginin gidan gyaran halin Suleja da muka ruwaito muku a safiyar yau cewa ya rushe adaren jiya sak**akon ruw...
25/04/2024

Wannan shi ne ginin gidan gyaran halin Suleja da muka ruwaito muku a safiyar yau cewa ya rushe adaren jiya sak**akon ruwan sama mai karfi da iska.

Wasu bayanai sun ce sama da fursunoni 100 ake nemansu sun gudu sanadiyyar rushewa daginin katangar ya yi.

A wannan gidan gyaran hali ne dai ake tsare da Maryam Sanda.

Yadda wata Budurwa a Nijeriya mai neman na kan ta, ta buɗe katafaren wani Shagon aski da ribar Sana'ar fanke.
25/04/2024

Yadda wata Budurwa a Nijeriya mai neman na kan ta, ta buɗe katafaren wani Shagon aski da ribar Sana'ar fanke.

Address


Telephone

+2349046599842

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DMA Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DMA Hausa News:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share