Muryar Hausa

Muryar Hausa Domin kawo maku sahihan Labarai a cikin harshen hausa daga ko ina a fadi kasa Najeriya da ma duniya baki daya.


@[282807705155462:0] News online

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN,Allah ya kaddara barayi sun harbi commandern JIBIA YOUTH SECURITY VOLUNTEER wato (GA...
07/11/2024

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN,

Allah ya kaddara barayi sun harbi commandern JIBIA YOUTH SECURITY VOLUNTEER wato (GADDAFI LAWAL) harbi biyu a kafa amman da sauki,

Sannan sun harbi k***n commandern wato BALA Wanda akafi sani da BANACY daya daga cikin ma'aikatan COMMUNITY WATCH CORPS, bisa kaddarawar Allah, Allah ya karbi ransa, za'ayi jana'izarsa k**ar haka:

Wuri:- kofar gidan Alh. Lawal Jambo Jambo, dake unguwar bedi Jibia.
Rana:- Juma'a 08/11/2024
Lokaci:- 08:30am

Muna addu'ar Allah yajikan su ya gafarta masu,
Mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani,
Shi kuma commander muna Addu'ar Allah ya bashi lafiya ya kuma kiyaye gaba.

07/11/2024

Innalillahi wa'innailaihir raj'un Allah ka amintar da al'ummar Jibia ka basu kariya yanzu haka yan'taadda sun mamaye wani yanki na Jibia😭😭

Idan kayi Notcoin ko Dogs ko Hamster ko telegram din ka ya dan kwana biyu to zaka sami airdrop na PAW yanzu ba wahala.Ka...
29/10/2024

Idan kayi Notcoin ko Dogs ko Hamster ko telegram din ka ya dan kwana biyu to zaka sami airdrop na PAW yanzu ba wahala.

Kawai zasu duba abubuwan sama da dadewar telegram din ka su baka PAW abunda zaka kara yi.

Domin yin register:

https://t.me/PAWSOG_bot/PAWS?startapp=j7OKQgW1

Faka faka.

Labari Mai Ratsa Zuciya: Yadda MahaifinaYa Rasa Idonsa - Kira zuwa ga ayi Adalci. A ranar 1 ga watan Satumba, an yi wa m...
18/09/2024

Labari Mai Ratsa Zuciya: Yadda MahaifinaYa Rasa Idonsa - Kira zuwa ga ayi Adalci.

A ranar 1 ga watan Satumba, an yi wa mahaifinmu aiki a Ido domin cire masa yanar Ido(cataract surgery), a bisa al'ada kalar wannan aiki ya kasance sassauka kuma gama gari a wajen kwararrun likitocin da s**a san aikin su. A baya an taba yi masa kalar wannan aikin a shekarar 2016 a idonsa na dama lokacin da ya ziyarce ni a Malaysia bayan na kammala karatu na na PHD, tabbas aikin ya zamto cikin sauki, kuma a cikin kankanin lokaci, saboda haka ne ya sa a wannan karon da na ji labarin za a yi masa kalar aikin a idonsa na hagu ban wani damu ba, kuma ban matsa da tambayoyi ba. Saboda a zato na aikin zai zamto cikin sauki k**ar yadda aka yi shi a chan kasar Malaysia.

A wannan karon mahaifina ya zaɓi sanannen asibitin idon nan, Albasar International Foundation (Wato Asibitin Makkah) da ke nan jihar Kano, wurin da marasa lafiya ke tururwar zuwa daga kusan ko ina a fadin Najeriya. Kuma cikin ikon Allah asibitin ya kasance kusa da mu, domin be wuce nisan mita 800 ba daga gidan mu.

Amma ba mu san cewa nan ba da daɗewa ba wannan sanannen asibiti zai zamto sillar abinda bamu taba tsammani ba —rasa idon mahaifina.

Karin bayani: kafin wannan tiyata, mahaifinmu yana iya gani kusan sama da kaso saba'in da biyar cikin dari da idonsa. Yanar Ido kawai ya ke fama da ita a idonsa na hagu, wanda ke sa shi gani dishi dishi, amma yana gani kuma yana gane komai da Idon. Wannan sanannen abu ne dake faruwa ga mafi yawancin mutane wadanda suke fama da kalar wannan ciwon, wasu s**an karasa ma rayuwarsu da wannan ciwon ba tare da sun je neman magani ba saboda ra'ayi na radin kai ko kuma rashin halin biyan kudin maganin, mafi yawan wadanda suke zuwa domin ayi musu kalar wannan aikin wadata ce ta ke kaisu ba wai tsananin ciwon ba ko kuma tsananin ta'azzarar dusashewar ganinsu ba.

Mahaifinmu, k**ar sauran mutane wadanda ke da ra'ayi ayi musu kalar wannan aikin, ya kasance yana jiran lokacin da ya dace. Yaso

Wato fa ita rayuwar nan inhar kace uwar wani ba zata yi bacci ba to kaima wallahi uwarka ba zata ko rintsa ido, ka shiry...
13/09/2024

Wato fa ita rayuwar nan inhar kace uwar wani ba zata yi bacci ba to kaima wallahi uwarka ba zata ko rintsa ido, ka shirya rashin yin bacci kaima saboda dukkan ku za kuyi asaran daren ku

Nasan cewa mutane dayawa sun san wannan Matar wanda aka fi sani da Babiyana a Tiktok, Babiyana kullum batada aiki sai binciken kwakwaf wajen nemo laifin mutane ko abinda ya faru da wasu ta kawo Tiktok

Tsabar kawo labaran ta, ita da kanta ta sakawa kanta suna "UPDATE". Yau gashi itama duniya ta mata zafi an kawo nata "UPDATE" din duniya wanda nata yafi na kowa muni

An samu wani / wata yaje ya ajiye camera an mata video tsirara haihuwar uwarta kafin a sake video din an bukaci ta biya kudin fansa har 15,000,000 daka karshe video din ya shiga social media kuma video din ya bayyana a Tiktok kusan mutane dayawa sun gani tsirara

Na taba baku wani labari akan wani bawan Allah dana sani kullum bashida aiki sai tozarta wanda aka k**a su suna aikata laifi daka karshe bai gushe ba sanda Allah ya jarabce shi da aikata zina shima aka k**a shi a fili

Duk lokacin daka ce kai bakada aiki sai tozarta mutane to kana daukan labarin bayin Allah kana yawo dashi a duniya to wallahi kaima sai an yi yawo dakai haka alkawarin Allah yake

Yau duniya ta yiwa Babiyana zafi, yau Babiya tana cikin tashin hankali, yau Babiyana hawa Tiktok yafi karfin ta, yau Babiyana tana ladamar kasancewar ta a social media. Mai kawo "UPDATE" yau "UPDATE" din nata ne

Wannan itace rayuwar dama, inhar kace aikin ka kenan tozarta mutane to kaima wallahi sai Allah ya tozarta ka komai dadewa. Ubangiji Allah ya kare mutuncin mu

~ Aliyu Naziru Officer ~

12/09/2024

Yanzu yanzu:Yan bindiga sun shiga Babban Asibitin dake kurfi Jahar Katsina sun tafi da Mutanen da ba'asan adadin su ba.
Allah ya kyauta.

AN SAKO MUTANEN GARIN MAIDABINO: BAYAN BIYAN KUDIN FANSA NAIRA MILYAN Talatin Da Shidda 36........Saura mutane Biyar s**...
11/09/2024

AN SAKO MUTANEN GARIN MAIDABINO: BAYAN BIYAN KUDIN FANSA NAIRA MILYAN Talatin Da Shidda 36........Saura mutane Biyar s**a rage a wajen ƴan ta'addar.

Daga Muazu Hassan

Katsina Times ta samu tabbacin ɓarayin daji da s**a afka garin Maidabino dake ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina, waɗanda s**a tafi da magidanta mutane 85, Mata da Maza banda na goye an sako mutane tamanin a cikin su.

Binciken da Katsina Times tayi a garin na Maidabino ya gano cewa ɓarayin sun sak**a kowane magidanci kuɗin fansar Naira Dubu Ɗari Ukku, daga baya s**a ƙara farashi zuwa kowane magidanci, akan Naira Dubu Ɗari Huɗu da Hamsin.

Katsina Times sun gano ɓarayin basu amshi kuɗin fansa akan jarirai da kuma waɗanda ke goye ba kuma da aka fara kai kuɗin, mata masu goyo da ciki s**a fara saki.

Katsina Times ta gano cewa kowane magidanci shine yayi ƙoƙarin sako nashi da aka k**a, wasu yanka bangarorin gonakin su, s**a sayar, wasu kayan gona,wasu kuma s**a shigo cikin gari s**a nemi taimakon ƴan uwa da abokan arziki.

Katsina Times ta gano, Mutane Biyar s**a rage wajen waɗannan miyagun ɓarayin na daji mutanen Biyar an kasa hada kuɗaɗen da za a amso su.

Katsina Times tayi magana da magidanta Biyar da aka sako, amma sunki magana saboda tsoron abin da zai biyo baya.cewa s**ayi.." kun San har yanzu muna garin Maidabino kuma bamu fi karfin ɓarayin nan ba, su sake dawo wa ba, don haka don Allah ku kyale mu"

Jaridun Katsina Times sune s**a taɓa buga wani bidiyon waɗannan bayin Allah a lokacin suna a daji tare da waɗannan miyagun ɓarayin.

Sama da mutane milyan ɗaya s**a ga bidiyon tsakanin shafukan yanar gizo da na sada zumunta na jaridun Katsina Times da kuma wadanda s**a yi ta daukar shi suna watsawa.

Idan dai ba'a manta ba cikin watan Yuni ne aka sace waɗannan Mutanen tare da yi masu Bidiyo ana barazanar cewa Sai sun biya kuɗin fansa kafin a sake su da kuma buƙatar Gwamnati tayi sulhu da ɓarayin, lamarin da Gwamnatin tace ba zata yi ba matsawar dai ba ɓarayin ne s**a saduda ba.

Kat

Link na a comment👇👇👇👇👇
08/08/2024

Link na a comment
👇👇👇👇👇

01/07/2024

Kuyi kokarin fara wannan mining

Address

Katsina
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share