Walkiya Times Hausa

Walkiya Times Hausa Walkiya Times Hausa Jarida ce Cikin Harshen Hausa wacce ke kawo Maku ingantattu labarai...
(5)

Kana Dannawa Kana Salatin Annabi Riba Kan Riba Ga lada Ga dollar Waiyoo daɗi 💰AVA-COIN Kamar NOT-COIN Yake dole Sai Kana...
06/03/2024

Kana Dannawa Kana Salatin Annabi Riba Kan Riba Ga lada Ga dollar Waiyoo daɗi 💰

AVA-COIN Kamar NOT-COIN Yake dole Sai Kanada Telegram Kana Shiga Cikin Wannan Link din Kai Tsaye Zai Kaika Cikin Telegram 👇🏼👇🏼

https://t.me/avagoldcoin_bot?start=7eadd6346b05147c5416

Zaice Kai Start

Kanayi Zasu Turoma Wannan Messenger din Kamar Haka 👇🏼👇🏼👇🏼

Welcome via a friend's invite! 🎉
Your gold mining journey starts now.
Tap "💰 Start Game 💰" to dive in!

Saika Taba inda Aka Rubuta 💰Start Game 💰Zai Nunama Wannan Hoton dana Saka Kan Wannan Wajan Mai Alamar Kwandala da Aka Rubuta GOLD 🪙

Kan wajan Zaka dinga Dannawa Duk Dannawa daya Zasu Baka Point Guda 1 duk Wanda Yai Rajista da Link Dinka Kuma Zasu Baka Point Guda 25k Amman Ana Bukatar Koda Yaushe Ka dinga Dannawa

idan Ka Tara Guda 400k Zaka iya Juyashi Nan Take Ya Koma USDt 65 💰Kuma Ka Tura Duk inda Kakeso

USDT 65 Kwatankwacin Kudin Najeriya 80k Ina lefi Ace Ko a, Wata daya Ka Samu Wannan Bare Kuma Ka dage Ko Sati bazakai ba Zaka iya Samu

Muhd King Cash

Mining $HOT achikin Here Wallet💥 Sun samu goyon bayan Near Protocol, Binance exchange da Gateio. Lallai akwai shagali 😋A...
03/02/2024

Mining $HOT achikin Here Wallet

💥 Sun samu goyon bayan Near Protocol, Binance exchange da Gateio. Lallai akwai shagali 😋

A telegram ake bude Here wallet tareda mining na $HOT, don haka dole ya kasance kunada telegram a wayarku, kuma an kirkire Here wallet ne akan Near Protocol.

Yanda ake bude Here Wallet tareda fara mining din $HOT.

1️⃣ Ku taba wannan link dake kasa, zai mayar daku kan telegram dinku domin bude wallet din. Saiku taba Start.
https://t.me/herewalletbot/app?startapp=498789

2️⃣ Ku taba CREATE WALLET, zai nuna muku passphrase (recovery phrase). Ku tabbatar kun rubuta tareda adana passphrase dinku, sannan ku taba CREATE. Ku jira yakai 100, shikenan kun bude Here Wallet.

3️⃣ Ku taba CLAIM, zai nuna muku wasu rubutu, kawai kuyita taba CONTINUE, har zuwa karshe da zai nuna muku START MINING. Kuyi claiming, shikenan kun fara mining na $HOT.

A farkon fara mining na $HOT, ana bawa mutane WOODEN STORAGE mai yin awa biyune (2 hours) kachal domin mining $HOT, domin yanada saurin chika. Don haka akwai bukatar ku samu manyan storage. Yanda ake samun storage shine

Akwai matakai (levels) 6 na STORAGE

Matakin 0: Wooden storage yanada tsawon awa 2, kuma kyauta ake samunsa dazarar mutum yayi rijista.
Matakin 1: Metal storage yanada tsawon awa 3, sai mutum ya bada 0.2 $HOT sannan ya sameshi.
Matakin 2: Matakin 1: Modular storage yanada tsawon awa 4, sai mutum ya bada 0.5 $HOT sannan ya sameshi.
Matakin 3: Liquid storage yanada tsawon awa 6, sai mutum ya bada 1 $HOT sannan ya sameshi.
Matakin 4: Titanium storage yanada tsawon awa 12, sai mutum ya bada 4 $HOT sannan ya sameshi.
Matakin 5: Gold storage yanada tsawon awa 24, sai mutum ya bada 10 $HOT sannan ya sameshi.

Zanchi gaba da bibiyarsu domin samun updates In Sha Allah

02/02/2024

Kalaman da Ado Yellow Maitibi ya fada ba zamu kyale shiba dole sai shari'a tayi aiki a kansa inji matsakaicin Dattijon Arewa Rabiu Babba Koki. Shin menene ra'ayin ku kan haka?

Na yi reaching target, nan da 24hrs kaya za su sauka 🤑🤑, kai ma za ka iya, ba wahala, faka-faka BlackWhale ake kashewa a...
22/12/2023

Na yi reaching target, nan da 24hrs kaya za su sauka 🤑🤑, kai ma za ka iya, ba wahala, faka-faka BlackWhale ake kashewa a Telegram.

You can contact right away.

KYAWUN ƊAN MACIJI...Wannan matar, ita ta yi ajalin wannan bawan Allahn kamar yadda labari ya bazu.Ka gan ta kyakkyawa. A...
22/12/2023

KYAWUN ƊAN MACIJI...

Wannan matar, ita ta yi ajalin wannan bawan Allahn kamar yadda labari ya bazu.
Ka gan ta kyakkyawa. Amma ta ƙunshe mummunar zuciya mai cike da burika munana!
Babban abin mamakin ma, wai ita da mijinta ne s**a aikata kisan.
Idan zargin nan ya tabbata, babu wani hukunci da ya dace wanda zai zama izina kamar kashe su, su duka ta hanyar da kowa zai shaida.

A yau Alhamis Kotun Ƙolin Najeriya za ta fara sauraren shari’a tsakanin Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na NNPP da N...
21/12/2023

A yau Alhamis Kotun Ƙolin Najeriya za ta fara sauraren shari’a tsakanin Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasir Yusuf Gawuna na APC a Abuja.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙolin bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Nasir Yusuf Gawuna a matsayin gwamnan jihar Kano.

Wa kuke yiwa Fatan yin nasara tsakanin Abba da Gawuna ?

Wannan shi ne Malam Nasir Anka, ƴan bindîga sun yi garkuwa da shi a kwanaki a jiharsa ta Zamfara, amma bayan sun karbi N...
20/12/2023

Wannan shi ne Malam Nasir Anka, ƴan bindîga sun yi garkuwa da shi a kwanaki a jiharsa ta Zamfara, amma bayan sun karbi Naira milyan 2 daga hannun ƴan uwansa a matsayin kuɗin fansa, sun kashê shi.

Allah ya gafarta masa. Ya sa ya huta.

KACICI - KACICI: Wacce Jiha ce a Nageriya mai harafi shida, huɗun farko babu wanda zai so a kira shi da su, biyun ƙarshe...
18/12/2023

KACICI - KACICI: Wacce Jiha ce a Nageriya mai harafi shida, huɗun farko babu wanda zai so a kira shi da su, biyun ƙarshe kuma amsa umarni ne ?

Ƙaddara Ce Kawai Ke Samar Da Shugabannin Irin Buhari, Cewar Shugaba TinubuShugaban ya bayyana cewar, samun shugabanni ir...
17/12/2023

Ƙaddara Ce Kawai Ke Samar Da Shugabannin Irin Buhari, Cewar Shugaba Tinubu

Shugaban ya bayyana cewar, samun shugabanni irin Buhari, na faruwa ne kawai bisa ƙaddarar ubangiji.

Me zaku ce?

MUTANE IRIN SU BULAMA BUKARTI BA ABUN WULAƘANTAWA BANE A AREWADAGA Bashir Abdullahi El-bashLokaci yayi da ya kamata ace ...
16/12/2023

MUTANE IRIN SU BULAMA BUKARTI BA ABUN WULAƘANTAWA BANE A AREWA

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Lokaci yayi da ya kamata ace Arewa mun sauya halinmu na aibata juna da rashin mutunta ra'ayin juna. Idan har mutum ya faɗi wani abu ko yayi wata magana da ka ga cewar kuskure ce ko saɓa da ra'ayinka ko aƙidarka, ka kalla kawai ka wuce ba sai ka ce komai ba ballantana har ka tsaya kana ci wa mutane mutunci dan sun furta magana ko sun bayyana wani ra'ayi wanda kai bai yi maka ba ko ba ka fahimta ba ko kake ganin kuskure ne.

Cin zarafin mutane irin su Audu Bulama Bukarti ba daidai bane, domin mutane ne waɗanda muryoyinsu suke da tasiri ba a Arewa kaɗai ba, duk Duniya ana sauraren sautinsu ana kuma mutunta abubuwan da suke faɗa akan ƙoƙarinsu na kare Arewa da fafutukarsu kan kare ƴanci da haƙƙoƙin al'umma.

Arziƙi ne mai girma, ni'ima ce babba, falala ce ƙatotuwa Allah Ya ba wa al'umma mutane irin su Bulama Bukarti a rayuwarsu, waɗanda suke jajircewa akan gaskiya da neman cigaban al'umma.

Idan har mutane irin su Bulama Bukarti za su yi kuskure ko wani tuntuɓen Harshe a afka musu da maganganun tozartawa da wulaƙantawa gami da neman fitar da su ma daga musulunci gaba ɗaya, tayaya muke tunanin wasu za su taso nan gaba su kwatanta irin abin da su Bulama ke yi kan al'umma ?

Ko kaɗan ba a taɓa samun Bulama da irin wannan tuntuɓen Harshe ko kuskure ba, kenan al'umma ba za su yi wa mutum mai alkhairi ɗari uzuri akan kuskure ɗaya kacal ba ?. Tabbas wannan koma baya ne a Arewa, kamata yayi ace idan har kuskure Bulama yayi a nemi shi cikin sirri a fahimtar da shi ba a aibata shi ba.

Haka ya kamata ga duk wata al'umma da ta samu mutane irin su Bulama Bukarti a rayuwa idan har an ga sun yi wani kuskure to a fahimtar da su ta hanyar da ta dace ba wai a bi su da ɓatanci ba. Wannan shi zai ƙara musu ƙarfin gwiwa da kuma ba wa wasu damar cigaba da shiga harkokin al'umma da ɗaga murya da nemawa al'umma ƴanci da haƙƙoƙinsu.

ZAI YI KYAU GWAMNA ABBA DA MADUGU SU SAKE NAZARIDaga Bello Muhammad SharadaA dan tsahirta na kwana biyu a duba sosai a g...
14/12/2023

ZAI YI KYAU GWAMNA ABBA DA MADUGU SU SAKE NAZARI

Daga Bello Muhammad Sharada

A dan tsahirta na kwana biyu a duba sosai a ga guraren da aka yi kuskure a gyara. A sake dubawa a ga ina aka yi ganganci a dau mataki don a guji gaba. A kalla da idon basira ina ne ya kamata a tabbatar an dauki mataki a yi hakan.

Kada a ji nauyin yin abin da ya dace. Haka Kada a ji kunya ko tsoron masu wargi. Amma kuma shugabanni su sani sun yi rantsuwa da daukar alkawarin zasu yi aiki da adalci da amana. Babu I'll will. Babu sani ko Sabo.

Abin da ya sa na fadi haka, mutanen da ake mulka suna kuka. Ya kamata a saurari kokensu. Sannan kuma jama'a sune gwamnati, aikin farko na gwamnati shi ne samun walwala da tsaron lafiya da rai da dukiyar jama'a. A kula da wannan.

Wata jarida, mallakin kamfanin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ce a cikin sati biyu Gwamna Abba K Yusuf ya rusa dukiya ta kusan naira biliyan 126. A duba lamarin nan, a kalli salon da ake amfani da shi.

KAI KUMA SSG Dr Baffa Bichi, yanzu mulki kuke yi, ba kamfen ba. An gama siyasa, a maida hankali a cikawa mutane alkawuran da aka dauka. A yi musu abin da ya dace da kudinsu kuma a rike amana. Banda hargagi da zumudi da zafin kai. KO ina ake son zuwa za a je

Wannan rubutun na yi shi a ranar 18 GA watan Yuni 2023, wato yau kwana 107.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke Daraktan Gudanarwa da Ayyuka na ma’ikatar ruwa ta jihar, Abubakar Gambo, tare da...
14/12/2023

Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke Daraktan Gudanarwa da Ayyuka na ma’ikatar ruwa ta jihar, Abubakar Gambo, tare da mataimakin sakataren gudanarwa, Baba Yahaya da kuma Nuhu Mansir, wanda tsohon manajan shirin noman rani a KAREFA ne a K
karamar hukumar Tudun Wada, bisa zargin su da yin takardun bogi na samun izinin yi gwanjon wasu manyan injinan rarraba ruwan sha da kuma tankuna.

Ali Haruna Makoda wanda shi ne kwamishinan ma'aikatar ruwan sha ta jihar Kano, yace abinda wadannan mutane s**a aikata ba da yawunsa su kayi ba, kuma tuni yan sanda na cigaba da bincike domin gurfanar dasu a gaban Shari'a.

Rahoto Nasara Radio 98.5 FM

KASHÊMASU MAULIDI: Dole Ne A Biya Su Diyya, Kuma A Tabbatar Cewa Diyyar Ta Kai Gare Su, Sannan Ya Kamata Waɗannan Mutane...
14/12/2023

KASHÊMASU MAULIDI: Dole Ne A Biya Su Diyya, Kuma A Tabbatar Cewa Diyyar Ta Kai Gare Su, Sannan Ya Kamata Waɗannan Mutane (Mutanen Tudun Biri) A Samar Musu Da T**i, Wutar Lantarki, Da Ruwan Famfo, A Yi Musu Makaranta Da Asibiti. Kuma Daga Yanzu Kada Mu Sake Jin A Ce Mana An Yi Kuskure, Inji Jagoran Mabiya Shi'a, Sheikh Ibraheem Zakzaky.

DAGA Usman Umar Katsina

RUSHE SHAGUNAN FILIN IDI: Gwamnatin Kano Ta Amince Za Ta Biya Diyyar Biliyan 3A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta...
14/12/2023

RUSHE SHAGUNAN FILIN IDI: Gwamnatin Kano Ta Amince Za Ta Biya Diyyar Biliyan 3

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya diyyar Naira biliyan 3 ga ƙungiyar ’yan kasuwa masu shaguna a Masallacin idi, kamar yadda kotu ya umarta, sakamakon rushe shagunan ba bisa ƙa’ida ba.

An cimma wannan matsaya ne sakamakon wata buƙata ta neman sulhu da dukkanin ɓangarorin s**a shigar gaban mai Shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja, a ranar 12 ga watan Disamba da kuma ranar 13 ga watan Disamba.

Idan za’a iya tunawa Idon Mikiya ta rawaito cewa, masu shaguna a filin masallacin idi sun shigar da ƙara nai lamba FHC/KN/CS/208/2023 a gaban kotun tarayya dake Kano, sakamakon umarnin da gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayar na rushe musu shaguna.

Masu neman takardar sun shigar da ƙara ga gwamnatin jihar, hukumar tsara birane ta jihar Kano; babban lauyan gwamnati, ‘yan sanda; Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda na shiyyar 1, Kano; Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano; Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya; da NSCDC, Jihar Kano.

Mai shari’a Samuel Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar 29 ga watan Satumba ya umarci gwamnatin jihar da ta biya ‘yan kasuwar naira biliyan 30 a matsayin diyyar Naira biliyan 250 da ‘yan kasuwar s**a nema na lalata musu kadarorinsu ba bisa ƙa’ida ba.

Amma sakamakon ƙin bin umarnin kotu da gwamnatin jihar ta yi, ‘yan kasuwar sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1382/2023 a gaban mai shari’a Ekwo, inda s**a buƙaci a tilastawa gwamnatin ta biya su kuɗaɗen ko kuma a rufe asusun gwamnatin kuma kotun ta bada umarnin rufe wasu asusun gwamnatin jihar dake wasu bankuna sama da guda 20.

Har ila yau, sun danganta asusu da ke hannun waɗanda aka yi garkuwa da su zuwa Naira biliyan 30 don gamsuwa da hukuncin da aka yanke a ranar 29 ga watan Satumba, da sauran sassa, kuma mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Wasu daga cikin waɗanda s**a shiga cikin wannan ƙara sun haɗa da Babban Bankin Najeriya, Akanta Janar na Tarayya, Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, FAAC, UBA, Bankin Zenith, Bankin Unity, Bankin Polaris, da dai sauransu.

Sai dai kuma da aka ci gaba da sauraren ƙarar a ranar Alhamis, lauyan masu ƙarar (’yan kasuwa), Dokta N. A. Ayagi, ya shaidawa kotu cewa sun samu fahimtar juna tsakanin su da waɗanda suke kara.

“Mun sami fahimtar juna tsakanin mu da waɗanda muke ƙara wato gwamnatin jihar Kano, kuma dukkanin mu mun aminta da yarjejeniyar da muka cimma.” A cewar Ayagi

13/12/2023

Allah ya kyauta

WATA SABUWA: An Zargi Sojojin Juyin Mulkin Niger Da Jefa Ƙasar Cikin Mawuyacin Hali Da Rashin TausayiWani babban malamin...
13/12/2023

WATA SABUWA: An Zargi Sojojin Juyin Mulkin Niger Da Jefa Ƙasar Cikin Mawuyacin Hali Da Rashin Tausayi

Wani babban malamin addinin musulunci a ƙasar Niger, Aramma Moumini shi ne ya yi wannan zargi a masallacinsa da ke Birnin Tawa, inda ya bayyana cewa mutanen ƙasar Niger suna cikin wani hali na mummunar rayuwa, komai yayi tsada, amma kuma duk da haka a gefe guda sojawan juyin mulkin ƙasar suna kwashe kuɗin ƙasar suna ba wa mawaƙa da ƴan fim da ƴan jarida na Nageriya suna yaɗa furofaganda domin su kare buƙatunsu.

Malamin ya cigaba da cewa "a zaman da shugabannin ƙungiyar (ECOWAS) s**a yi a makonnan, sun yi wa Sojojin alƙawarin cewa idan har s**a saki Bazoum da mutanensa da suke tsare da su tun bayan juyin mulki sannan kuma s**a saka ranar da za su mayar da mulki hannun farar hula to za su cire duk wani takunkumi da s**a ƙaƙabawa ƙasar".

Malamin ya cigaba da cewa "sai dai abin takaici sojawan juyin mulkin sun yi burus da wannan tayi na ECOWAS, haƙiƙa wannan abin Allah wadai ne, domin idan har da gaske sojawan juyin mulki kishin ƙasar Niger suke suna ƙaunar al'ummar ƙasar ya kamata ace sun amsa wannan tayi amma s**a ƙi". In ji shi.

Shi ma a wani matashi ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam mai Suna Mosa Amaou dake yankin Doso, ya ya yi Allah-Wadai da wannan halin ko'inkula da sojawa ke nunawa al'ummar Niger.

A cewarsa "duka yadda masu juna biyu da mata suke mutuwa saboda ƙarancin ci-maka, rayuwa ta yi tsada, ƴan mata suna guduwa ƙasar Nageriya da sauran ƙasashen makwafta suna karuwanci domin neman na abinci, ya kamata sojojin da s**a yi wannan juyin mulki a ƙasar Niger su karɓi tayin da ƙungiyar ECOWAS ta yi musu, su saki shugaba Bazoum da jama'arsa su miƙa mulki hannun fararen hula a cire mana takunkumi domin su ceto rayuwar al'ummar Niger musamman mata da ƙananan yara". Cewarsa.

13/12/2023

ALLAH KA SAUƘAƘA MIN WANNAN DAMUWAR

Daga Shafin Na Yar Talla

Ana kashe mazajen Aure a yiwa Matan su da Ƴaƴan su Mata fyaɗe. A ƙona gidajen su da dukiyoyin su. A shiga gonakinsu a bankawa amfanin su wuta. A tarwatsa garin ta hanyar kora ragowar Mata da ƙananan yaran dake hannunsu su fantsama duniya ba tare da sun san inda za su nufa ba. 😭

Rayuwarsu ta tsinke ta yadda Allah ne kawai zai ji ƙansu ya tashi kafaɗunsu domin samun ingantacciyar rayuwa nan gaba. Amma a yanzu kam, an datse dukkan wata igiyar dake sarƙafe da rayuwarsu ta hanyar kashe mazajen su da manyan yaran su Maza. Ba su da wata madafa da za ta zame musu abar jinginar da har za su iya dafawa su miƙe. 😭

Ba Mace ɗaya ake magana ba. Ba kuma yara biyu ko uku ake batu ba. Ƙalubale ne na dubban Matan da rayuwar su ta salwanta alhalin dai gashi suna raye.

Suna ji suna gani Ƴaƴan su za su mutu akan idanuwansu sakamakon ciwon yunwa ko kuma wani ciwo da wahalhalu irin wanda s**a tsinci kansu a ciki ke jawowa. Mafi sauƙi a wajen su shi ne yaran su zamanto mabaratan da za su ke nemo musu abin da za su samu su ci. Kun ga kenan a ƙarshe Yaran za su tashi su girma babu wata madafa a rayuwar su. Sakamakon haka, za su tsinci kawunan su cikin munanan halayen da za su zamewa al'umma barazana, musamman idan s**a samu tarihin yadda aka kashe iyayensu ba tare da an taimake su ba. 😭

Duk yadda na so na hakaito irin rayuwar da irin waƴannan bayin Allahn suke tsintar kawunan su nan da nan sai kaina ya fara ciwo. Don wallahi ba zai iya hasashen wahala da ƙalubalen da rayuwarsu ke ciki ba.

Allah ya isan su! 😭😭

12/12/2023
Kalma daya Tak
11/12/2023

Kalma daya Tak

ABUN ALFAHARI: Wakilin Nijeriya A Gasar Musabaqar Kur'ani Ta Duniya, Hafiz Bukhari Sanusi Idris Daga Kano Ya Zo Mataki N...
11/12/2023

ABUN ALFAHARI: Wakilin Nijeriya A Gasar Musabaqar Kur'ani Ta Duniya, Hafiz Bukhari Sanusi Idris Daga Kano Ya Zo Mataki Na Goma Sannan Kuma Shine Mafi Karancin Shekaru A Gasar

An gudanar da gasar ne a kasar Kenya.

Matasan mu da su ke guduwa zuwa wasu ƙasashen don neman aikin yi su dakata da ficewa, na can ma su dawo gida saboda na k...
10/12/2023

Matasan mu da su ke guduwa zuwa wasu ƙasashen don neman aikin yi su dakata da ficewa, na can ma su dawo gida saboda na kusa kawo ƙarshen Talauci a Nàjeriya, Cewar Shùgaba Tinubu

Me zaku cè?

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA ABDULAZIZ ABDULAZIZDaga Shafin Na Yar TallaBan ga wani abin mamaki ba dan an tsince ka cikin masu k...
10/12/2023

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA ABDULAZIZ ABDULAZIZ

Daga Shafin Na Yar Talla

Ban ga wani abin mamaki ba dan an tsince ka cikin masu kare ƙarya. Ka na ban ga abin cece kuce akan furucin ka ba, wanda kai a karan kanka na rantse da Allah ka san ƙarya kake furtawa don kare neman abincin ka.

Kar ka manta da cewa kai ne ka bankaɗo badaƙalar tshohuwar ministiyar kuɗi Kemi Adeosun na rashin yin bautar Ƙasar da ta yi ikirarin tayi, alhali ba ta yi ba. Ƙarshe har sai da aka sauke ta daga muƙamin ta. Daga lokacin ne kuma sunan ka ya fara reto har al'umma s**a farga da kai.

Sannan kuma kai ne ka shiga har cikin ƙurgurmin Daji, cikin da'irar ƴan ta'adda ka yi hira da su. Hakan ya ƙara kaɗa ƙararrawar sunanka ta yadda kunnuwa da dama s**a ji sautin ta.

Abdulaziz ɗan jarida. Tun daga lokacin da aka ji cewa ka karɓi matsayin da aka baka a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu kai da Jega mutane ire-irena s**a san cewa kun tafi. Kuma dole ne daraja da martabar sunan ku ta faɗi.

Ɗan Jarida, ba wai cancanta ce ta sa aka rakito ka ba, gujewa bin ƙwaƙwƙwafin ka a matsayin ka na ɗan Jarida mai bin ƙwaƙwƙwafi ne yasa aka janyo ka dan a daƙile duk wani yunƙurin ka na ɓata sunan Gwabnati da muƙarrabanta. Bisa ga dukkan alamu kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Ka dai dubi yadda s**a toshe bakin Dr. Hakeem Baba Ahmed da muƙami a ofishin mataimakin shugaban Ƙasa. Yau al'ummar Arewa na kukan mutuwa, kuma ƴan Jahar sa ta Kaduna, amma babu damar a jiyo muryar sa yana Allah wadai da Gwabnati.

Hatta Rahama Abdulmajid da ta yi comment da an Kashe Mijinta bisa kuskure don ta goyi bayan kare ƙaryar da ka yi na cewa kuskure sojoji s**a yi. An ba ta muƙami a Gwabnatin nan ne domin toshe bakinta, musamman suna sane da irin rawar da ta taka a tafiyar BRING BACK OUR GIRLS. Yau da ita da Hadiza Bala, wacce ita ce coordinator duk suna cikin Gwabnati sun bar Aisha Yusufu da kwarmato.

To ka sani, ita ce aka kashe mata Miji ta hanyar kuskure, musamman ma da ta kira kuskuren da "FRIENDLY FIRE". Amma kisan al'ummar Tundun Biri ba friendly fire ba ne. Ba kuma kuskure ba ne.

Kai yanzu baka ji kunya ba ka kalli mutum kamar Dr. Ahmad Gumi ka ce wai bai san ya abin yake ba. Shin mantawa ka yi da shi ɗin tsohon Soja ne?

Amma da yake idanuwanka sun rufe da son kare ƙarya, ka manta da cewa ya fi ka sanin gidan Soja da ma yadda sojoji ke aikin su. Allah wadaran hali irin wannan!

To ka sani, mu ba wai mamaki ka bamu ba. Ba mu kuma ga laifin ka ba dan kana kare abincin ka. Amma dai yana da kyau ka san cewa al'umma sun san cewa ƙarya kake karewa. Babu kuma wanda zai yarda da abin da kake ta ɓaɓatu a kai fa ce ƴan Koron ka da suke ci ta ƙarƙashin ka.

Da kana waiwaye, da rayuwar Bashir Ahmad da ka gaji kujerar sa ta zame maka izina. Domin a halin yanzu ko me ya furta ya taɓa furta saɓanin hakan a baya. Mutane kuma suna dawo masa da irin waƴannan maganganun nasa da suke ta cin karo da juna.

A ƙarshe ina mai baka shawara da ka bi rayuwa a sannu don gujewa taka SAWUN BAYA.

09/12/2023

Bahari Yayi Daga Daga da Nigeria

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN:Wannan mutumin da kuke gani ‘ya’yansa 14 amma 13 sun rasu a sakamakon Bam ɗin da sojo...
08/12/2023

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN:

Wannan mutumin da kuke gani ‘ya’yansa 14 amma 13 sun rasu a sakamakon Bam ɗin da sojoji s**a jefawa masu Mauludi a Kaduna, inda ɗaya ne kaɗai ya rayuwa, shi ma kuma ya samu mummunan rauni.

INA TABBATARWA ƳAN AREWA CEWA BILLAHILLAZI BA ZAN BARI JINI DA RAYUKANKU SU TAFI A BANZA BA, CEWAR SHUGABA TINUBUShugaba...
08/12/2023

INA TABBATARWA ƳAN AREWA CEWA BILLAHILLAZI BA ZAN BARI JINI DA RAYUKANKU SU TAFI A BANZA BA, CEWAR SHUGABA TINUBU

Shugaban ƙasa Tinubu Ya Yi Kira A Kwantar Da Hankali A Arewa Zai Ɗauki Duk Wasu Matakan Da Su Ka Dace Wajen Kare Rayuka, Addini, Mutunci Da Dukiyar Al'ummar Arewa. Kamar Yadda Ya Ce: "Na Rantse Da Allah Ba Zan Taɓa Bari Jinin Ɗan Arewa Ya Tafi A Banza Ba".

Shugaban ƙasa Tinubu ya ce "Aikina ne tsare rayukan al'umma. Na jima a cikin harkokin siyasa, na riƙe muƙamin gwamna a babbar Jiha Legas, na yi iya ƙoƙarina wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Ina da ƙwarewa da gogewa a wannan fannin, ina mai tabbatarwa ƴan Arewa cewa zan ɗauko wancan ilimi da ƙwarewa da na samu a matsayin gwamna na tabbatar na tsare Arewa da ƴan Arewa da addini da kima da mutunci da dukiyoyin al'ummar Arewa".

Ya ƙara da cewa "Ba zan yarda da ganganci da sakarci da wasa da rayukan al'ummar Arewa ba, zan tabbatar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen cutar da Arewa da ƴan Arewa. Ni shugaba ne na kowa, ba zan yarda a cutar da wata ƙabila ko wani yanki a mulkina ba. Dukkan matsalolin da aka samu a baya kafin na zama shugaban ƙasa zan tabbatar da cewa na magance su tayadda hakan ba zai sake faruwa ba a gaba". Cewar shugaba Tinubu.

Tinubu ya ƙara da cewa "Ina kira ga ƴan Arewa mu mance da duk wasu munanan abubuwa na rashin daɗi da su ka faru a baya, mu sa Arewa a gaba mu gina ta. Gwamnatina ta shirya tsaf! Za ta sharewa ƴan Arewa hawayen da ke kwaranya a Idanuwansu shekara da shekaru ta fuskar tsaro, ilimi, tattalin arziƙi da sauran fannoni, za mu kawar da duk wata damuwa mu kawo farin ciki da walwala a zukatan al'ummar Arewa". In ji shugaban ƙasa Tinubu.

Wane fata zaku yi masa ?

Ɗaya Daga Cikin Alƙalan Da Su Ka Samu Ƙarin Girma Jiya Ya Mutu Ana Kan Tuhumarsa Da Cin HanciAlƙalin Kotun Daukaka Ƙara ...
08/12/2023

Ɗaya Daga Cikin Alƙalan Da Su Ka Samu Ƙarin Girma Jiya Ya Mutu Ana Kan Tuhumarsa Da Cin Hanci

Alƙalin Kotun Daukaka Ƙara da ke jerin waɗanda su ka samu ƙarin girma jiya ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin mai suna Shagbaor Ikyegh ya mutu ne a jiya Laraba 6 ga watan Disamba ya na da shekaru 65 a duniya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalansa su ka fitar a jiya Alhamis 7 ga watan Disamba a Makurdi babban birnin jihar Benue.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Makurdi da ke jihar amma ba ta bayyana dalilin mutuwar tashi ba.

Ikyegh na daga cikin alƙalan da su ka samu ƙarin girma zuwa Kotun Ƙoli, kuma zai yi ritaya ne a shekarar 2028.

YADDA AKA AJIYE BAMBANCE-BAMBANCE GEFE GUDA A WANNAN KARON DA ALAMA HAƊIN-KAI NA DAF! DA SAMUWA A AREWADAGA Bashir Abdul...
06/12/2023

YADDA AKA AJIYE BAMBANCE-BAMBANCE GEFE GUDA A WANNAN KARON DA ALAMA HAƊIN-KAI NA DAF! DA SAMUWA A AREWA

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Haƙiƙanin Gaskiya Yadda Kan Malaman Musulunci Ya Haɗu A Arewa Su Ka Fito Su Na Allah-Wadai Da Kisan Da Sojoji Su Ka Yi A Ƙauyen Jihar Kaduna Abin A Yaba Ne, Kuma Alama Ce Da Ke Nuna Cewa Haɗin-Kai Na Daf! Da Samuwa A Arewa.

Tabbas kan Arewa na daf! Da haɗuwa. Abin a yaba ne, abin a jinjinawa Malamai ne musamman na IZALAH, duba da yadda kan malaman ya haɗu waje guda su na jaje da yin Allah-wadai da wannan mummunan al'amari na kashe mutane masu Maulidi a ƙauyen Jihar Kaduna wanda aka ce tsautsayi ne.

Ko shakka babu jama'ar Arewa a wannan karo musamman malamai da manyan mutane masu tasiri a sabbin kafafen sadarwa na zamani sun cancanci yabo da jinjina, kuma wannan wata alama ce da ke nuna cewa akwai alamun samun haɗin-kai nan gaba kaɗan a Arewa tayadda za a rika magana da murna ɗaya.

Iftila'i a kan wani ko wasu ba abun murna ba ne domin kai ma ba ka fi ƙarfin wannan iftila'in ya faɗa maka ba. Ba ka fi ƙarfin ka je wajen wani taro ko tashar mota ko jirgi ko ma wani wuri wannan tsautsayi ya faɗa maka ba.

Kenan ba abu ne na murna da jindaɗi ba dan ba kai ya samu ba domin kai ma wata rana zai iya samunka. Farkon Boko Haram irin haka ce ta faru, suna kashe ƴan sanda da sojoji mutane farar Hula suna murna saboda ba su ake kashewa ba amma daga baya sai da masifar ta shafi kowa.

Kenan iftila'i da masifa kan wani ko wasu ba abin farin ciki ba ne, abun a haɗu ne waje guda a haɗa ƙarfi da ƙarfe a nemowa waɗanda abin ya shafa yanci tare da hana afkuwar hakan a gaba. Dole ne kowa ya rika ajiye buƙatarsa a gefe guda ya fifita yankinsa, addininsa da ƙabilarsa fiye da buƙatarsa.

Wannan haɗin-kai da aka fara samu a Arewa na nuna cewa duk yadda ake ganin Arewa ta lalace tabbas wata rana kanmu zai haɗu. Kuma manyanmu ba manyan banza ba ne su na da kima da tasiri fiye da yadda ba a zato. Dole mu yaba da abin da su ka yi.

Akwai Haɗari Babba Idan Aka Yi Amfani Da Ƙarfi Wajen Ƙwace Mulkin Kano A Hannun Abba Gida-Gida, Cewar Sanata Shehu SaniM...
04/12/2023

Akwai Haɗari Babba Idan Aka Yi Amfani Da Ƙarfi Wajen Ƙwace Mulkin Kano A Hannun Abba Gida-Gida, Cewar Sanata Shehu Sani

Mé zakú cé?

Mai Ƙarfin Gani Ne Kaɗai Zai Iya Faɗa Mana Waɗanne Lambobi Ne A NanKu canki lambobin da aka rubuta a jikin Hoton nan.
03/12/2023

Mai Ƙarfin Gani Ne Kaɗai Zai Iya Faɗa Mana Waɗanne Lambobi Ne A Nan

Ku canki lambobin da aka rubuta a jikin Hoton nan.

Address

NO. 567 Kofar Dawanau Road T**in Dandinshe Tudun Fulani Ungogo Local Govt
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Walkiya Times Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Walkiya Times Hausa:

Videos

Share