Dillalan kwaya akalla 1,344 a Jihar Katsina ne suka shiga hannun Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a cikin shekara guda.
Hukumar NDLEA reshen Jihar Katsina ta ce an kama dillalan kwaya da masu safaran nata ne a shekara guda da ta gabata.Kakakin hukumar a jihar, Hassan Abubakar, ya sanar da haka a jiya Alhamis cewa hukumar ta kwace ton 1.3 na miyagun kwayoyi daga hannun wadanda aka kama.
Babban hafsan hafsa sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya danganta fafatawar da ake yi a tsakanin kasashen Amurka, Rasha da China a nahiyar Afirka, da kuma janyewar sojojin Jamhuriyar Nijar daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa, a matsayin lamarin da ya kara ta’azzara kalubalen tsaro a yankin Sahel wanda ya haifar da kwararar makamai da ‘yan ta’adda zuwa Nijeriya.
Air Marshal Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ganawa da hafsoshin reshe da kwamandojin rundunar sojin sama da daraktoci da kuma daukacin manyan jami’an rundunar sojin saman Nijeriya a Abuja.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana yadda a halin yanzu rundunar sojin Nijeriya take kokarin samar da walwala ga jami’anta domin dawo da su hayyacinsu da kuma yin garambawul a aikin soji.Janar din ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai da ya yi a ofishinsa kwanan baya. Mun yi nazarin bidiyon tattaunawar daga kafar yada labarai ta DW.
Shekaru biyu bayan gwamnatin tarayya ta bayyana manufar harshen da ya kamata a rika koyarwa da shi a makarantu, ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba wajen aiwatar da shirin. Makarantu da yawa har yanzu suna amfani da Ingilishi a matsayin harshen koyarwa, kuma an ci gaba da koyar da harsunanmu na gado a matsayin darussa na daban. wanda ya sa harsunan gado suka zama tilas a rika amfani da su wajen koyarwa tun daga aji daya zuwa aji shida na makarantar Firamare.
Daga ketare
An samu wani juyi na siyasa sakamakon rikici tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ya
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa a wata ziyara da ya kai a babban gidan gyara hali da ke cikin garin Kaduna.
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce akwai dakarunta huɗu da kuma dakarun tsaro biyu na gwamnatin jihar cikin mutanen da 'yanbindiga suka kashe a harin da suka kai ranar Lahadi.
Daga ketare_
Hamas ta miƙa martaninta game da daftarin tsagaita wuta a Zirin Gaza da Amurka ta gabatar.
Jam’iyyar PDP ta zargi APC da jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, inda ta ce jama’a a fusace suke game da halin da ƙasar nan ke ciki a halin yanzu.
Rundunar 'yansandan Najeriya ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari a sake kashe babban layin lantarki na ƙasar ba da sunan zanga-zanga.
Daga ketare
Kotu ta kama ɗan shugaban Amurka, Hunter Biden, da laifuka uku d ake tuhumar sa da suka shafi mallakar bindiga.
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar Nijeriya kai tsaye a yau Laraba 12 ga watan Yuni, 2024, domin murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya.Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata.Don haka ne ake ƙarfafa gidajen talabijin, da rediyo, da sauran hanyoyin sadarwa na zamani da su haɗa kai don yaɗa jawabin wanda hukumar gidan Talabijin ta ƙasa (NTA) da hukumar gidan Rediyon Tarayya (FRCN) zasu watsa.
Wasu ɓarayi sun haura gidan wani mutum mai suna Malam Mundi Shuaibu, inda suka yi awon gaba da ragon layyarsa a Unguwar Sabon-Tasha da ke Abuja.
Wata mata a Bayelsa ta kona 'ya'yanta masu shekaru bakwai da shekaru 10 saboda zargin karamar da yawan sata.
Daga ketare
Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Ministocin BRICS Da Kuma Gana Da Takwarorinsa Na Habasha Da Afirka Ta Kudu
Fagen wassanni.
Mutane da dama sun yi mamakin sakamakon wasan Jamhuriyar Benin da Najeriya inda ta doke Najeriyar da ci 2-1 a wasan neman zuwa Gasar Cin Kofin Duniya.
Wani kansila a unguwar Achika da ke kamarar hukumar wudil a kano, Bashir Shehu Aliyu ya ɗauki nauyin maida yara 120 zuwa makaranta.
An sake gano wasu gawarwaki biyu a dajin Kuchimi da ke makwabtaka da karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Daga ketare
Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta gudanar da tarukan tattaunawa na kamfanonin Sin a Sifaniya, da Portugal, da Girka, da sauran wasu kasashen Turai
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da ƙwato motoci biyar daga hannunsu.
Hukumar Daƙile Cin Hanci Da Rashawa a Ma’aikatan Gwamnati, ICPC, ta gurfanar da jami’in Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA), wanda ya sace Naira 298 daga manhajar biyan kuɗaɗen hukumar a cikin 2023.
Daga ketare
Hukumomi a Saudiyya sun sanar da kame maniyyata dubu 300 wadanda ba su da takardun shaidar aikin hajjin bana da ake shirin farawa a makon gobe.
Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Kaura-Namoda/Birnin-Magaji, Aminu Jaji, ya sayi raguna 3000 don raba wa jama’ar mazaɓarsa da kuma ‘ya’yan jami’yyar APC a Jihar Zamfara.Ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin gudanarwar Jaji, Aliyu Abubakar, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka kaddamar da sabon katafaren ginin gidan mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima.Gidan dai ya lakume makudan kudi har Naira miliyan dubu 21.
Kungiyar SERAP mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, tayi Allah-wadai da wannan mataki na gwamnatin Bola Tinubu, tana mai cewa hakan almubazzaranci ne da dukiyar kasa.
Ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a kakar zaben 2023 a Jihar Kaduna, Hon Isa Ashiru Kudan, ya shaida wa kafar BBC cewa sun gode wa Allah da ba a ƙarƙashinsu Majalisar Dokokin Jihar ke bincike kan zargin tafka badakalar da aka tabka a lokacin mulkin Gwamna Nasir El-Rufai ba.
Daga ketare
A ranar 10 ga watan zul hajji ne Sheikh Abdurrahman Sudais ne zai jagoranci Sallar Idi a Masallacin Harami da ke Makkah —
Fagen wassanni.
Daya daga cikin kofin da Mbappe ke fatan ɗauka shi ne Champion League, sai kuma kyautar Ballan d'or, watakila kuma ya samu a Madrid
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya samar da manyan motocin takin zamani 76 da za a raba su ga manoma tare sa zaftare kashi 50 cikin 100 na farashinsa a matsayin tallafi.
Kungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta bayyana cewa an samu ƙaruwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke arewacin Najeriya da suka haɗa da Borno da Katsina da Sokoto da Zamfara da Bauchi.
Daga ketare
Hukumomin kasar Saudiyya sun fara koro maniyyata kan rashin mallakar takardun izinin gudanar da aikin Hajjin 2024.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta cafke wani tsoho, mai shekara 70 da ake zargin ɗan bindiga ne a Zariya.
Aƙalla maniyyata sama da 4,000 ne daga Jihar Kaduna da za su yi aikin Hajjin bana aka kammala jigilarsu a jihar.
Daga ketare
Miliyoyin 'yan Sudan na fuskantar barazanar yunwa saboda yaƙin da aka shafe sama da shekara ɗaya ana yi, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Aƙalla mutum biyu ne suka rasu bayan wata tankar gas, ta yi bindiga a gadar Obiri zuwa Ikwerre da ke Gabas maso Yammacin Fatakwal a Jihar Ribas.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:25 na safe, bayan tankar ta faɗi a lokacin da ta ke ƙoƙarin ƙetare gadar sama, inda ta yi karo da wata mota ɗauke da mutane biyu a ciki.
Tsohon shugaban matasan jam’iyyar APC, Barrister Ismaeel Ahmed ya bayyana matsayin matasa da kuma matsalolin da suke fuskanta a Najeriya a cikin shekaru 25 na mulkin Dimokuraɗiyya ba a ƙasar.
Bayanai daga Jihar Kaduna na nuni da cewa ’yan bindiga sun harbe dan Sarkin Hausawan Janjala ne saboda ya aure budurwar shugabansu.Shaidu sun bayyana cewa bayan tarewar amaryar ne ’yan bindiga suka yi dirar mikiya a gidan dan Sarkin Hausawan Janjala, Safiyanu Ibrahim, suka harbe shi a gaban mahaifiyarsa
Daga ketare
Rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) ta sanar da cewa, mayakan kungiyar Boko Haram 176 ne suka mika wuya, yayin da aka cafke wasu 57 da ake zargin suna da hannu a ayyukan ta’addanci a yankin tafkin Chad.Kwamandan rundunar, MNJTF “Operation Lake Sanity II,” Maj.-Gen. Ibrahim Ali ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a barikin rundunar hadin gwiwa “JTF Operation Hadin Kai” da ke unguwar Maimalari da ke Maiduguri.
Daga fagen wassanni
Kyaftin ɗin Real Madrid da ya lashe gasar zakarun Turai,Nacho,mai shekara 34,zai gana da ƙungiyar domin tattauna makomarsa inda kwantiragin ɗan wasan na Sifaniya zai ƙare a wannan bazarar
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama fitaccen mawaƙin gambara kuma ɗan TikTok, Al-Ameen G-Fresh kan zargin yi wa Alƙur’ani Mai Girma izgilanci.
Hisabh ta kuma zarge shi da yin kalaman batsa a shafukan sada zumunta.Dala360 ta tabbatar da kama G-Fresh.G-Fresh dai ya yi ƙaurin suna musamman a kafar TikTok, inda da yawan lokuta kalamansa ke yamutsa hazo.
Tsohon Shugaban Nijeriya, Janar Abdulsami Abubakar, ya bayyana cewa sojoji ba su da damar aiwatar da juyin mulki a kowacce ƙasa face sai sun samu gudunmawa daga ’yan siyasa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin kafa dokar ta-baci a fannin ilimi da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa a jihar.Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa.Gwamnan zai ayyana kafa dokar tabacin a ranar Talata, inda ya ce matakin na daya daga cikin muhimman alkawuran yakin neman zabensa da ya zayyana a cikin takardarsa mai suna “Alkawari na ga Kano,” wadda aka tsara kuma aka gabatar wa jama’a a shekarar 2022, gabanin zaben 2023.
Daga ketare
Wata mai suna Topi Amma, ma’abociyar sa hula mai malafa da ke garin Tiruvannamalai, birnin da mabiya Hindu ke zuwa don ibada a Jihar Tamil Nadu, tana kawo ruɗani a cikin addini, inda ta raba kan wasu Indiyawa wasu na bauta mata wasu na ɗaukarta a matsayin mahaukaciya da take neman taimako.
Fagen wassanni.
Ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid bayan ya raba gari da PSG.
Muhimmancin Gyara jiki a lokacin Zafi
Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce annobar Ebola ce ta kama gonakin tumatur, wadda ta jawo ƙaranci da kuma tsadar amfanin gonar a faɗin ƙasar.Ministan Noma da Samar da Abinci Abubakar Kyari ya ce suna ɗaukar matakin gaggawa kan cutar da ake kira Tomato Ebola ko kuma Leaf Miner.
Rundunar ‘yansandan jihar Kogi a tsakiyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar biyu daga cikin ɗaliban nan da ‘yanbindga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Kimiyya ta Osare.Rundunar ta bayyana kisan daliban a matsayin abin takaici, ta kuma sha alwashin tabbatar da ceto sauran ɗaliban da maharan kerike dasu
Anyi jana'izar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde.An yi jana'izar ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 28 ga watan Mayu, 2024.Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar akwai mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar da sauran manyan 'yan siyasa, masu rike da mukaman Gwamnati da sauransu
Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya a jiya Lahadin da misalin kafe 9:30am nasafe.
Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.
Daga ketare
Gwamnatin Amurka ta sanar da shirinta na inganta karfin Intanet a nahiyar Afirka zuwa kashi 80 ciki 100 nan da shekarar 2030.
Ranara yara
Ranar Yara ta Duniya