Hantsi Leka Gidan Kowa

Hantsi Leka Gidan Kowa Labaran da s**a shafi tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar yau da kullum, daga cikin gida Najeriya da kuma kasashen ketare, kasance da Hantsi....
(7)

EFCC ta gurfanar da Matashin Saurayi kuma Budurwa Bobrisky kan cin zarafin Naira Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tatt...
04/04/2024

EFCC ta gurfanar da Matashin Saurayi kuma Budurwa Bobrisky kan cin zarafin Naira

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Legas sun fara bincike kan Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky bisa zarginsa da fesa Naira.

Hukumar EFCC ta gayyaci matashin mai shekaru 31 ne biyo bayan wani rahoton faifan bidiyo na fesawa tare da baje kolin sabbin takardun kudi na Naira a farkon wani fim, Ajakaju, wanda Eniola Ajao, wata ‘yar wasan Nollywood kuma furodusa ce ta shirya a Film One Circle Mall, Lekki Legas a ranar 24 ga Maris, 2024.

Bincike ya kuma nuna cewa ya kuma aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa a wasu wuraren gudanar da bukukuwa a lokuta daban-daban.

Bayan gayyatar da hukumar ta yi masa, ya isa ofishin hukumar EFCC na shiyyar Legas da safiyar ranar jiya Laraba, 4 ga Afrilu, 2024 domin yi masa tambayoyi.

Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike

Najeriya da Senegal
03/04/2024

Najeriya da Senegal

Malam Yusuf Direba shi ne yake tuka ɗaya daga  cikin ma'aikatan dan kasar China mai suna Mr. Shiba da ke unguwar Sharada...
30/03/2024

Malam Yusuf Direba shi ne yake tuka ɗaya daga cikin ma'aikatan dan kasar China mai suna Mr. Shiba da ke unguwar Sharada a birnin Kano.

Da farkon lamarin 'yan Malam Yusuf mai suna Maryam ta kan je duba mahaifinta a wajen aikinsa, kasancdewar ba su da nisa da kamfanin, a irin wannan zuwa ne kuma Mr. Shibu ya lallaba ta da sunan soyayya, har ya aikata wannan aika aika.

Bayan mai afkuwa ta afku sai Mr. Shibu ya damkawa mahaifin Maryam Naira dubu 50 da zumar aje a zubar da ciki, idan an zubar zai ba su Naira miliyan daya.

Sai dai an je asibiti domin zubar da ciki, an ba ta magani ta sha, an yi mata allurai, amma fau-fau ciki ya ƙi zubewa, yarinya kuma ta shiga halin galabaita.

Bayan barazana da ɗan China ya yi wa malam Yusuf cewa zai raba shi da aikinsa idan ya bari wannan labari ya fita ne, shi kuma ya garzaya hukumar Hisbah domin neman ɗauki inda hukumar ta yanke shawarar daurawa Mr. Shibu aure da Maryam a yau Asabarj 30 ga watan Maris 2024, a cewar mahaifin yarinyar.

Wasu daga cikin 'yan dabar da ke addabar al'ummar unguwar Ɗorayi kenan, da rundunar 'yan sandan jihar Kano s**a samu nas...
29/03/2024

Wasu daga cikin 'yan dabar da ke addabar al'ummar unguwar Ɗorayi kenan, da rundunar 'yan sandan jihar Kano s**a samu nasarar daƙume su.

Wane hukunci kuke ganin ya dace da su?

Tallafin dai a biyo bayan karin kudin aikin Hajji na Naira miliyan 1.9 da Hukumar Alhazai ta Najeriya ta yi ba zato ba t...
27/03/2024

Tallafin dai a biyo bayan karin kudin aikin Hajji na Naira miliyan 1.9 da Hukumar Alhazai ta Najeriya ta yi ba zato ba tsammani.

Gwamnan yace a yanzu maniyyatan da s**a yi rajista s**a biya kuɗin ajiya na farko na Naira miliyan 4 da dubu ɗari 7 da kuma masu Naira miliyan 4 da dubu ɗari 5 ga Hukumar Alhazai ta Jiha, za su cika Naira miliyan 1 da dubu ɗari 4 ne daga cikin ƙarin Naira miliyan 1.9 da hukumar NAHCON ta yi musu.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar a tura ɗan tsohon Gwamnan na Kano, Mustafa Rabiu Kwankwaso, zuwa ma’aikatar mat...
26/03/2024

Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar a tura ɗan tsohon Gwamnan na Kano, Mustafa Rabiu Kwankwaso, zuwa ma’aikatar matasa da wasanni.

Sun yi zargin cewa rasitin da ke hannunsu ya nuna cewa “sun kammala biyan kudin aikin hajjin 2024” don haka sun sha alwa...
26/03/2024

Sun yi zargin cewa rasitin da ke hannunsu ya nuna cewa “sun kammala biyan kudin aikin hajjin 2024” don haka sun sha alwashin tabbatar da an dauke su zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar aikin Hajjin 2024 ba tare da sun ƙara ko sisi ba.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a Muhammad Idris yace Gumi bai fi karfin doka ba, don haka gwamnati ta ga ya ...
25/03/2024

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a Muhammad Idris yace Gumi bai fi karfin doka ba, don haka gwamnati ta ga ya dace ta gayyace shi domin amsa tambayoyi.

Hukumar ta bukaci wadanda s**a biya kashin farko na kuɗaɗen da ta ayyana a baya, da su ƙaro Naira miliyan 1 da dubu ɗari...
24/03/2024

Hukumar ta bukaci wadanda s**a biya kashin farko na kuɗaɗen da ta ayyana a baya, da su ƙaro Naira miliyan 1 da dubu ɗari 9, inda adadin a yanzu ya kai Naira miliyan 6 da dubu ɗari 8.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Naira biliyan 1 da miliyan 190 da dubu 790 ne  gwamnatin Kano ta ware domin ciyar da mutan...
24/03/2024

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Naira biliyan 1 da miliyan 190 da dubu 790 ne gwamnatin Kano ta ware domin ciyar da mutane dubu 100 a kowacce rana cikin watan Ramadan.

Yace shi ma haka ya ji ana yaɗa labarin cewa gwamnatin Kano ta ware waɗannan maƙudan kuɗaɗe har Naira biliyan 6, wanda adadin ba gaskiya ba ne.

“Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba, ya zama wajibi a lura da cewa kudaden da aka...
23/03/2024

“Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba, ya zama wajibi a lura da cewa kudaden da aka ware don wannan shiri an tsara su sosai a kowace cibiya” Gwamnan ya yi gargadi.

Gwamnan ya gudanar da ziyarar ne biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna nakasu wajen gudanar da shirin ciyarwa a cibiyoyi daban-daban na babban birnin.

Fiye da mako guda kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin bude kan iyakar da ke tsakanin kasashen b...
22/03/2024

Fiye da mako guda kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin bude kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, yayin da sojojin na Nijar s**a ki cewa uffam kan matakin na Najeriya.

Menene fatanku bayan buɗe iyakokin?

Albishir ga 'yan Najeriya daga kamfanin Facebook.
21/03/2024

Albishir ga 'yan Najeriya daga kamfanin Facebook.

Malamin dai yana maida martani ne kan jerin sunayen da hukumar NFIU ta fitar na ayyana abokinsa Tukur Mamu da wasu mutan...
21/03/2024

Malamin dai yana maida martani ne kan jerin sunayen da hukumar NFIU ta fitar na ayyana abokinsa Tukur Mamu da wasu mutane 14 a matsayin masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

'YAN 9 NA FARKO A DUNIYA DA S**A RAYU Sun yi tattaki daga Maroko, inda aka haife su, zuwa ƙasar iyayensu ta Mali 🇲🇱 Kuma...
19/03/2024

'YAN 9 NA FARKO A DUNIYA DA S**A RAYU

Sun yi tattaki daga Maroko, inda aka haife su, zuwa ƙasar iyayensu ta Mali 🇲🇱

Kuma yanzu, watanni biyu kafin cikarsu shekararsu ta uku, sun yi tafiya ta farko zuwa nahiyar Turai, sun ziyarci kasar Italiya don bayyana a shirin talabijin na na Lo Show dei Record! 👏

Sun burge ku?

Haka zalika Alhaji Aliko Dangote ya raba wa mutane kimanin miliyan 1 buhun shinkafa a sassan Najeriya.
18/03/2024

Haka zalika Alhaji Aliko Dangote ya raba wa mutane kimanin miliyan 1 buhun shinkafa a sassan Najeriya.

SABON LABARIYanzu dai Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa (Mai Ritaya) ne zai zama Shugaban  Majalisar Gudanarwar hukumar,...
18/03/2024

SABON LABARI

Yanzu dai Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa (Mai Ritaya) ne zai zama Shugaban Majalisar Gudanarwar hukumar, yayin da Dokta Idris Muhammad Sani zai zama Babban Sakatare/Shugaba na hukumar kula da almajirai da yaran da basa zuwa makaranta.

MALAM IBRAHIM KHALIL YANA FITINANTAR AL'UMMA TA HANYAR MUNANAN MAGANGANUNSA, DA RAUNANAN FATAWOYINSA.Addini Amana Ne! Ma...
18/03/2024

MALAM IBRAHIM KHALIL YANA FITINANTAR AL'UMMA TA HANYAR MUNANAN MAGANGANUNSA, DA RAUNANAN FATAWOYINSA.

Addini Amana Ne! Malam Ibrahim Khalil Ba Malamin Sauraro Ba Ne!

Malam Ibrahim Khalil Kano yana cikin na gaba-gaba wajen kawo wa al'ummar Annabi (S.A.W) Rudani a cikin al'amuran Addininsu.

An fitinanci wannan al'umma da irin wannan mutum mai fitinantar al'umma ta hanyar munanan maganganunsa, da raunanan fatawoyinsa.

A gefe guda kuma yana daga cikin mutanen da ake yi wa "Mujamala" Kafira! Ta yadda zai furzar da wani Sharri ko wata mummunar katobara, amma sau da yawa wadanda da waninsa ne ba shi ba za su tanka! Har su yi Gurnani, ko su mayar da kakkausan martani, ko su warwarewa al'umma cudanyensa, sai a ja baki a yi gum! Kai har ma karshe ana ganin baiken wanda ya warware shi, ko ya mayar masa da martani.

Mun sani Addinin nan Amana ne! Kuma ko waye ya yi ba daidai ba, hakki ne na ma'abota sani su fito su bayyanawa al'umma daidai, su kuma yi bayanin mummunan tafarki.

Ilimi mai albarka, ilimi na gaske shi ne ilimin da ya amfanar da al'umma, ya saita su ga tafarkin gaskiya, ya nusantar da su hanyar kwarai, ya kawar da su daga barna, ya kange su daga mummunar hanya.

Muna barranta a wajen Allah dangane da wannan mutum da barnarsa! Muna kai koken mu ga Allah a kan ire-irensu. Allah Ya kame mana hannyensu, Allah Ya rufe mana bakunansu, Allah Ya raunata mana muryoyinsu, Allah Ya dakirar mana da motsinsu.

Musa Muhammad Dankwano.
08/Ramadan/1445.

Yanzu haka ɗaliban suna asibitin babban birnin tarayya Abuja suna karɓar kulawar likitoci, kafin miƙa su ga iyalansu.
17/03/2024

Yanzu haka ɗaliban suna asibitin babban birnin tarayya Abuja suna karɓar kulawar likitoci, kafin miƙa su ga iyalansu.

Shin kuna ganin wannan ziyarar da Sha'aban ya kaiwa Ganduje tana da alaƙa da sauke shi daga kan kujerarsa?
16/03/2024

Shin kuna ganin wannan ziyarar da Sha'aban ya kaiwa Ganduje tana da alaƙa da sauke shi daga kan kujerarsa?

Shugabannin Arewa Sun Nemi Tinubu Ya Goyawa Sheikh Gumi Baya, Domin Tattaunawa Da ‘Yan Ta’addan Da S**a Sace Daliban Mak...
16/03/2024

Shugabannin Arewa Sun Nemi Tinubu Ya Goyawa Sheikh Gumi Baya, Domin Tattaunawa Da ‘Yan Ta’addan Da S**a Sace Daliban Makaranta | Hantsi Leka Gidan Kowa

Sojojin Najeriya Sun Kashe Wasu 'Yan Ta'adda Biyu, Sun Daƙile Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane Akan Wasu Motocin Haya Uku ...
16/03/2024

Sojojin Najeriya Sun Kashe Wasu 'Yan Ta'adda Biyu, Sun Daƙile Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane Akan Wasu Motocin Haya Uku A jihar Kogi | Hantsi Leka Gidan Kowa

Daukewar Intanet: Hukumar NCC ta Najeriya ta tabbatar da cewa ana aikin gyaran wayoyin karkashin ruwa |  Hantsi Leka Gid...
16/03/2024

Daukewar Intanet: Hukumar NCC ta Najeriya ta tabbatar da cewa ana aikin gyaran wayoyin karkashin ruwa | Hantsi Leka Gidan Kowa

Atiku ya caccaki Tinubu: Kasafin Kudinka Ne Ya Janyo Talauci, Da Rashin Tsaro Ga 'Yan Najeriya |  Hantsi Leka Gidan Kowa
16/03/2024

Atiku ya caccaki Tinubu: Kasafin Kudinka Ne Ya Janyo Talauci, Da Rashin Tsaro Ga 'Yan Najeriya | Hantsi Leka Gidan Kowa

YANZU-YANZUShugaban ƙasa Bola Tinubu ya sauke Sha'aban Ibrahim Sharada daga shugabancin hukumar kula da almajirai da yar...
15/03/2024

YANZU-YANZU

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sauke Sha'aban Ibrahim Sharada daga shugabancin hukumar kula da almajirai da yaran da basa zuwa makaranta, ya naɗa Lawal Jafar Isa a matsayin sabon shugaban hukumar.

NAJERIYA KENAN!Bayan majalisar dattawan ƙasar nan ta dakatar da Sanatan Bauchi ta Tsakiya Sanata Abdul Ningi sakamakon z...
15/03/2024

NAJERIYA KENAN!

Bayan majalisar dattawan ƙasar nan ta dakatar da Sanatan Bauchi ta Tsakiya Sanata Abdul Ningi sakamakon zargin da yayi mata na badaƙalar kudade.

Bayanai sun fito game da zargin da Sanatan yayi, dake cewa Majalisar Dattawa ƙasar nan ta wawashe Naira 47,5 biliyan 47 da miliyan ɗari 5 ta karkashin ma'aikatar ilimi ta domin gyaran Makarantu 50 ba tare da bayyana guraren da suke ba a Najeriya.

Me za ku ce game da wannan badaƙalar?

Shugaba Bola Tinubu ya nada Dokta Temitope Ilori a matsayin sabuwar Darakta-Janar ta Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta K...
14/03/2024

Shugaba Bola Tinubu ya nada Dokta Temitope Ilori a matsayin sabuwar Darakta-Janar ta Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa (NACA), wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba da aka samu a yayin da ta zama mace ta farko da ta rike wannan muƙami.

A ranar 22 ga Fabrairu, 2024, Dokta Ilori ta hau kujerar a hukumance, inda za ta shafe tsawon shekaru hudu, bayan ta gaji Dr. Gambo Aliyu, wanda ya rike mukamin DG na hukumar NACA daga watan Yunin 2019 zuwa Fabrairun 2024.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin shugabar sashen hulda da jama’a ta NACA, Toyin Aderibigbe, a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a yau.

Wannan umarni na zuwa ne a matsayin matakin aiwatar da kudurorin da ECOWAS ta yanke a lokacin wani babban taronta na mus...
13/03/2024

Wannan umarni na zuwa ne a matsayin matakin aiwatar da kudurorin da ECOWAS ta yanke a lokacin wani babban taronta na musamman da ta gudanar a Abuja.

Tun da farko an shirya farawa ne a ranar Alhamis 14 ga watan Maris, sai dai an sake jingine shirin lamunin, saboda gyare...
13/03/2024

Tun da farko an shirya farawa ne a ranar Alhamis 14 ga watan Maris, sai dai an sake jingine shirin lamunin, saboda gyare-gyaren da ake yi kafin kaddamar da shi, kamar yadda shugaban shirin Sawyer ya bayyana.

Wannan furuci na zuwa ne biyo bayan rokon da Sheik Ahmad Gumi ya yi ga gwamnatin tarayya kan tattaunawa da ‘yan bindigar...
13/03/2024

Wannan furuci na zuwa ne biyo bayan rokon da Sheik Ahmad Gumi ya yi ga gwamnatin tarayya kan tattaunawa da ‘yan bindigar domin a sako ‘yan Najeriya da aka sace.

Address

Kano

Telephone

08076042952

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hantsi Leka Gidan Kowa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hantsi Leka Gidan Kowa:

Videos

Share

Category

Hantsi...

Kasance da jaridar Hantsi... domin samun sahihan labarai na gida Najeriya da kasashen waje cikin sauki...


Other Newspapers in Kano

Show All