
02/02/2025
Wasu daga cikin Dokokin kwallon kafa lokacin da muna Yara:
1. Yaron da yafi kowa Girma (Kiba) shine mai tsaron Raga.
2. Mamallakin kwallo (Wanda ya sayi Ball) shine zai yanke wadanda zasu buga wasa.
3. Idan kwallo ta lalace bakaje wajen gyara ta ba, Za adakatar dakai na dan wani Lokaci.
4. Dan wasan da ba a sakawa idan za a fafata wasa shi ake zaba ya dauko kwallo idan ta makale akan Bishiya ko a karkashin mota domin ya fafata a wasa na gaba.
5. Idan har aka batawa mamallakin kwallo rai, To wasa ya kare (Domin zai dauke abarsa ya ware gida).
6. Idan Kaji ciwo a kafar ka sannan ka lura jini yana zuba, A lokacin zakai sauri ka samu tsumma kadaure a matsayin taimakon gaggawa sannan saika cigaba da wasa (Ko kuma ka barbada wa ciwon kasa).
7. Bazaka yanke wanda ya siyo kwallo da yawa ba, Hakan zai iya sa a tsayar da kwallon ya dauke ta ya tafi.
8. Babu ruwan ko kwallo nawa kuka ci, Wadanda s**aci kwallo ta karshe sune da nasara.
9. Babu satar gida (Offsides).
10. Babu Alkalin wasa (Refree).
11. Ana hura mugunta ne idan har muguntar takai mugunta.
12. 'Yan wasan da s**afi kowa iyawa mutum biyu basa wasa a gida daya, Acikin su kowa zai dauki 'Yan wasan da yake so.
13. Idan akazo raban Ball ka kasance na karshe hakan yana nufin baka da amfani kuma kaine zaka tsaya a baya.
14. Idan akazo bugun Fenareti ana zabar Golan da zai k**a raga ne acikin 'Yan wasan da s**afi kowa kokari koda ba Gola bane.
15. Wanda yafi kowa kokari a fili koda yaushe gidan su daya da Mamallakin kwallo.
16. Koda yaushe akwai wani gida wanda indai kwallo ta fada gidan, Ansan cewa wasa ya kare. Don haka dole ku kula!!
17. Domin a banbamce tsakanin kungiyoyi biyu, Daya daga cikin su zai cire riga ko kuma ya nannade hannun Riga (ko kuma rigar makaranta ayi mata Tiri).
Ana tashi wasa ne idan dare yayi ba'a'iya ganin kwallo babu lura da lokacin sallah magrib yayi.
• Fagen Wasan it