19/07/2020
'KISSA;
An Ruwaito Cewa; Wata Rana Wata Mata Ta Zo Wurin IMAMU AL-HASSANUL BASARIY(R.A), Ta Ce;
"'Diyata Ce Ta Rasu Kuma Gashi Hankalina Bai Kwanta Ba, Ina Son Inganta a Cikin Mafarkina Domin Sanin Halin Da Take Ciki",
Sai IMAMUL-BASARIY(R.A) Ya Sanar Da Mahaifiyar Yarinyar Nan Adadin SALATIN Da Zata Karanta Wata 'Kila Ta Ga Halin Da 'Yarta Take Ciki, Ya Sanar Da Ita SALATIN, Sai Kuwa Ta Je Ta Karanta, Sai Ta Ga 'Yarta Sanye Da Tufafin Wuta Da Ankwa a Wuyanta Da Kuma Mari a 'Kafafuwanta, Sai Matar Nan Ta Ji Tsoro, Ta Firgice,
Sai Ta Sanar Da IMAMU HASSANUL BASARIY(R.A), Ya Nuna Damuwarsa Matuqa a Gareta, Ana Cikin Wannan Halin Ne Ba'a 'Dauki Lokaci Mai Tsawo Ba Sai IMAMU HASSANUL BASARIY(R.A) Yayi Mafarkin(Wannan Yarinyar) Tana a Cikin Aljanna Akan Gado(Na 'Kasaita) Ga Kuma Kan Sarki(Irin Wanda Sarakuna Ke Sanyawa a Kawunansu) Akan Wannan Baiwar ALLAH.
Sai Ta Ce;"Ya IMAMU! Ko Ka Gane Ni Kuwa???"
Sai Ya Ce;"A'a Baiwar ALLAH Ban Gane Ki Ba",
Sai Ta Ce;"Ai Ni Ce Wannan Matar Da Ka Sanar Da Mahaifiyata SALATI Don Ta Ganni a Cikin Mafarkinta",
Sai IMAMU AL-BASARIY(R.A) Ya Ce Da Ita;"To Menene Sababin/Sirrin Al'amarinki???"
Sai Ta Ce;"Wani Bawan ALLAH Ne Ya Zo Gittawa Ta Makabartarmu Sai Yayi SALATI Ga ANNABI(S.A.W) Yayi Hadiyyar Ladan Salatin Gare Mu(Mamatan) Kuma Ya Kasance a Cikin Makabartarmu Akwai Mutane 'Dari Biyar Da Sittin(560) Da Suke a Cikin Tsananin Azaba Sai Aka Yi 'Kira; A 'Dauke Mana Azaba Sanadiyyar SALATI Ga ANNABI(S.A.W) Da Wannan Bawan ALLAH Yayi Da Niyyar Hadiyya a Gare Mu".
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WA'ALA AALIHI WA SAHBIHI WA SALLIM!
(Don Ganin Wannan Hikayar Sai a Duba;
*. IHYAA ULUM AD-DEEN- IMAM ABU HAMID AL-GHAZALI Volume 4, Shafi Na 492.
*. AT-TAZKIRATI FI AHWALIL MAUTA WA UMURIL AKIRATI - MUHAMMAD BN F***J AL-MALIKIYYIL QURDABI, Shafi Na; 67).
Ya ALLAH! Don Albarkar Tulin Sirrin Dake Tattare Cikin SALATI GA ANNABI(S.A.W), ALLAH Ka Nisanta Tsakaninmu Da Wahala Kowacce Iri Ce Anan Duniya Da Kuma a Gobe Qiyama Ameeen.