IMACS TV

IMACS TV IMAMU AHMAD CENTER FOR STUDIES TV
(2)

’Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Masu Yawa A Neja’Yan bindiga sun kashe mutanen da ba a san adadinsu ba a wani hari da s*...
22/03/2024

’Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Masu Yawa A Neja

’Yan bindiga sun kashe mutanen da ba a san adadinsu ba a wani hari da s**a kai wata kasuwa da ke unguwar Madaka a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce maharan sun kai hari kasuwar ce da misalin karfe 3 na ranar Alhamis, lokacin da ake tsaka da cin kasuwa, inda s**a bude wuta kan mai uwa da wabi.

Ya zuwa yanzu dai, babu wani cikakken rahoto game da harin.

Dtaya daga cikin mazauna yankin, ya ce mutane da dama da ba tantance adadinsu ba sun rasu a sak**akon harin.

Harin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wasu yan bindiga s**a kai hari garin Pangu, inda s**a kashe Hakimin gundumar da wasu mutum hudu.

Jin ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Birgediya Janar Mohammed Bello Abdullahi,ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Kazalika, shi ma kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, jin ta bakinsa ya ci tura.

Wadanda s**a kashe sojoji 17 a Delta sun arce da mak**an su duka – Mahukunta Rundunar sojin Najeriya ta ce ‘yan bindigar...
22/03/2024

Wadanda s**a kashe sojoji 17 a Delta sun arce da mak**an su duka – Mahukunta

Rundunar sojin Najeriya ta ce ‘yan bindigar da s**a kashe sojoji a jihar Delta sun kuma yi awon gaba da mak**an su bayan sun kashe

Babban kwamandan runduna ta 6 ta sojojin Najeriya, Jamal Abdussalam, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, k**ar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Laftanar Kanar Jonah Danjuma, ya bayyana.

Da yake magana a lokacin da Manajan Daraktan Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Samuel Ogbuku, ya kai masa ziyarar ta’aziyya a hedikwatar sashin da ke Barikin Fatakwal a ranar Alhamis, Manjo Janar Abdussalam, ya ce sojojin za su cigaba da farautar waɗanda s**a aikata wannan mummunar aiki a wannan yanke har sai sun kamo su sun kuma kwato mak**an da s**a yi arce da su, su kuma an hukunta su.

Ya ce babban hafsan sojin kasa, Taoreed Lagbaja ne ya bayar da wannan umarni ga sojojin da ke aikin a wannan tsibiri.

Shugaban sojojin ya ci gaba da cewa sojojin za su ci gaba da kasancewa a cikin wannan ruwa har sai an k**a waɗannan mutane da kuma kwato mak**an da suma arce da.

A ƙarshe ya yi kira ga mutane da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri ta yadda za a kamo waɗannan ƴan bindiga sannan a kwato mak**an da s**a arce da su aka kuma hukunta su.

Dimokuradiyyar Najeriya Na Cikin Hatsari — BugajeShugaban Kungiyar Samar da Shugabanci Nagari  a Arewa (AM2G) Dokta Usma...
22/03/2024

Dimokuradiyyar Najeriya Na Cikin Hatsari — Bugaje

Shugaban Kungiyar Samar da Shugabanci Nagari a Arewa (AM2G) Dokta Usman Bugaje, ya ce dimokuradiyyar Najeriya na cikin mawuyacin hali.

A cewarsa, dimokuradiyyar Najeriya ba ta samar da irin ci gaban da al’ummar kasar nan ke tsammani ba.

Bugaje, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne, ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Kaduna a ranar Alhamis.

Ya yi wannan kalami ne a wani martani na dakatar da Sanata Abdul Ningi da Majalisar Dokokin kasar nan ta yi, bayan ya zargi Sanatoci da yin cushen tiriliyan 3.7 a kasafin kudin bana.

Bugaje, ya ce dimokuradiyyar Najeriya ba ta haifar da abin da ake so musamman a kan matasa ba, wadanda ake burin su yi karatu domin zama wasu a gobe.

“A bayyane yake cewa dimokuradiyyarmu tana cikin mawuyacin hali. Dimokuradiyyarmu ba ta samar da ci gaban da ake bukata ba. Duba da irin majalisun dokokin da muke da su tabbas ba inda za mu je. Dimokuradiyyarmu tana jefa ’yan kasa cikin talauci, da yawan ‘yan kasar nan tsarin dimokuradiyyarmu ne ya jefa su cikin kangin talauci.

“Dimokradiyyarmu ta rasa dalilinta, kimarta na raguwa. Mutuncin dimokuradiyyarmu na sake yin kasa,” in ji shi.

Bugaje ya kara da cewa, akwai bukatar a gaggauta dawo darajar dimokuradiyyar kasar nan a zukatan ‘yan kasa.

Ya ce majalisa na da hannu wajen sama da fadi da dukiyar al’umma a kasafin kudi yayin da ‘yan Najeriya ke fama da talauci da rashin aikin yi da sauran matsaloli da s**a yi wa kasar nan katutu.

A gefe guda kuma, ya soki Sanatocin Arewa kan rashin goyon bayan tsohon shugabansu Ningi da sakataren kungiyar, Kawu Sumaila.

A yau Juma'a Ake Kyautata Zaton Nijar Za Ta Bude Iyakokinta Da NajeriyaRahoanni daga jamhuriyar Nijar na cewa, a sun shi...
22/03/2024

A yau Juma'a Ake Kyautata Zaton Nijar Za Ta Bude Iyakokinta Da Najeriya

Rahoanni daga jamhuriyar Nijar na cewa, a sun shirya bude iyakanta da Najeriya ta takwas bayan Shugaban kasa

A ci-gaba da kokarin lalubo hanyar ceto tattalin arzikin Najeriya daga mawuyacin hali, Shugaba Bola Tinubu ya haramta wa...
22/03/2024

A ci-gaba da kokarin lalubo hanyar ceto tattalin arzikin Najeriya daga mawuyacin hali, Shugaba Bola Tinubu ya haramta wa jami'an gwamnati yin tafiya zuwa ketare na watanni uku sak**akon dubban miliyoyin da ake kashewa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsara kashe Naira miliyan bakwai domin zırga- zirga zuwa kasashen waje, a yayın da mataimakinsa zai kashe miliyan dubu 1.2 k**ar yadda kasafin kudin Najeriya na bana ya tanada. Sai dai a wata sabuwar sanarwa, fadar gwamnatin kasar ta dakatar da duk wata tafiya zuwa waje. Babban jami’i na fadar mulki Femi

Gbajabiamila ya ambato bukatar rage kisan kudi don neman inganta tattalin arziki a cikin muhimman dalilan matakin da ke da niyyar aike sako.

Tun daga farkon watan Afrilu ne, shugaban kasar Najeriya ya umarci tsayar da zirga-zirgar har na tsawon watanni guda uku a karon farko, kuma duk wata tafiya ta wajibi na bukatar amincewa ta shugaban kasar akalla tsawon makonni biyu kafin yin ta. Sabon umarnin na kara fitowa fili da irin girman rashin kudin da ke cikin Najeriya a halin yanzu. Dr Isa Abdullahi da ke zama kwarrare a fannin tattalin arziki ya ce matakin ya yi daidai da kokarin ceto kasar daga cikin yanayi maras kyau.

22/03/2024

YA IBADA ?

DA DUMI-DUMI: Nijar ta buɗe bodar ta da NajeriyaGwamnatin juyin mulki na Nijar sun amince a bude iyakokin Jamhuriyar Nij...
22/03/2024

DA DUMI-DUMI: Nijar ta buɗe bodar ta da Najeriya

Gwamnatin juyin mulki na Nijar sun amince a bude iyakokin Jamhuriyar Nijar da Najeriya bayan kasancewa a kulle tsawon lokaci duk da Gwamnatin Najeriya ta janye mata takunkumi ta bude boda Nijar ta ƙi bude tata bodar sai yau...

LABARI: Gwamnatin Najeriya ta ƙirƙiro yan sandan kula da ma’adanaiZa a tura jami'ai 60 zuwa kowace jiha kuma babban aiki...
22/03/2024

LABARI: Gwamnatin Najeriya ta ƙirƙiro yan sandan kula da ma’adanai

Za a tura jami'ai 60 zuwa kowace jiha kuma babban aikinsu shine sanya ido da bayar da tsaro ga wuraren haƙo ma’adanai a faɗin Najeriya,

Yan sandan su 2,200 an ciro su ne daga jami'an NSCDC sannan za a ƙaro wasu daga sauran ɓangarorin cibiyoyin tsaro, sannan cibiyarsu za ta zama a ƙarƙashin ma'aikatar kula da ma’adanai ta Najeriya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya firgita matuka dangane da farmakin da sojojin Isra'ila s**...
21/03/2024

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya firgita matuka dangane da farmakin da sojojin Isra'ila s**a kai a asibitin Al-Shifa na Gaza, a cewar Florencia Soto Nino mai magana da yawun Guterres a ranar Laraba.
Florencia ta ce "Muna nanata cewa dole ne dukkan bangarorin su bi dokokin jin kai na kasa da kasa, kuma asibitoci za su iya rasa matsayinsu na wurin ba da kariya idan ba a yi amfani da su don ayyukan jin kai ba."
Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD wato OCHA ya bayyana cewa, a ranar Laraba ne farmakin da sojojin Isra’ila ke kai wa ciki da kewayen asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza ya cika kwanaki uku a jere. Rundunar sojin Isra'ila ta ce, an kashe Falasdinawa kusan 90 dauke da mak**ai tare da tsare wasu 300 da ake zargi.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Laraba cewa, ana shirin kai farmaki a Rafah, da ke can cikin kudancin Gaza, amma kaddamar da harin "zai dauki wani lokaci."
Firaministan ya fada a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo cewa "nan ba da jimawa ba" zai amince da shirin kwashe fararen hula daga Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.5 ke samun mafaka. (Yahaya)

Yayin da dubban Falasdinawa dake arewacin zirin Gaza ke tserewa zuwa kudanci, sak**akon yakin da sojojin Isra’ila s**a k...
21/03/2024

Yayin da dubban Falasdinawa dake arewacin zirin Gaza ke tserewa zuwa kudanci, sak**akon yakin da sojojin Isra’ila s**a kaddamar na murkushe kungiyar Hamas tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, masharhanta da dama na ganin lokaci na kara kurewa, na kawo karshen wannan tashin hankali, duba da cewa ga alama matakan sojin da Isra’ilan ke dauka ba abu ne da zai kare a nan kusa ba.
Ya zuwa yanzu, hare-haren sojojin Isra’ila sun kora sama da mutune miliyan guda wani lungu dake kudancin Gaza, inda birnin Rafah ya zamo “Gaba kura baya sayaki” ga masu tserewa hare-haren Isra’ila.
Duk da jan hankali da aka sha yi masa, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya dage cewa sai sojojinsa sun kaddamar da hare-hare a Rafah. Alkaluma sun nuna cewa, kafin wannan tashin hankali, Rafah na da kimanin mutane 275,000 ne kacal, amma yanzu mutane sama da miliyan 1.4 ke cunkushe a cikinsa, a yanayi na matukar bukatar jin kai.
Majalissar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun nuna damuwa game da mummunan tasirin da hare-hare a Rafah za su yi ga fararen hula. A daya hannun kuma, a baya bayan nan ita ma kasar Sin ta bayyana damuwa, game da yadda rikicin Falasdinu da Isra’ila ya haura watanni 5, kana yanayin jin kai a wurin ke kara tabarbarewa, don haka ta bayyana wajibcin gaggauta tsagaita wuta nan take, da yin iyakacin kokarin kiyaye rayukan fararen hula, da kuma rage matsalolin jin kai.
Mun san dai da fari, Amurka na sahun gaba wajen marawa Isra’ila baya a wannan yaki mai muni, amma a yanzu ta fara sauya matsaya, har ma an jiyo shugaba Joe Biden na Amurkan na cewa, kaiwa birnin Rafah hare-hare zai zama kuskure mai matukar muni.
La’akari da goyon baya da Amurkan ta nunawa Isra’ila tsawon lokaci kan wannan batu, ta hanyar maimaita dakatar da kudurin kwamitin tsaron MDD game da tsagaita wuta a Gaza, da tarin mak**ai da ta rika aikewa Isra’ila, da ma yadda kalaman sauya matsayar ta s**a fara sanya Isra’ilan nuna alamun sassautawa. Muna iya cewa idan akwai wani karfi da zai iya

Hoto 📸 Wani Yaro A Wajen Tashen Watan Azumin Ramadan A Ranar Alhamis 21/4/2023 A Unguwar Dala dake Jihar Kano📸IMACS TV T...
21/03/2024

Hoto 📸 Wani Yaro A Wajen Tashen Watan Azumin Ramadan A Ranar Alhamis 21/4/2023 A Unguwar Dala dake Jihar Kano

📸IMACS TV T@followersrs

DA DUMI-DUMI: Gwamnonin jihohi 16 sun goyi bayan a ƙirƙiro ƴan sandan jihohi a Najeriya Kodayake dai ba a lissafa Gwamno...
21/03/2024

DA DUMI-DUMI: Gwamnonin jihohi 16 sun goyi bayan a ƙirƙiro ƴan sandan jihohi a Najeriya

Kodayake dai ba a lissafa Gwamnonin jihohin ba amma Ministan kasafi da tsare-tsare Atiku Bagud ya ce suna jiran ragowar Gwamnoni jihohi 20 tare da babban birnin tarayya Abuja su ma su fadi tasu matsayar kafin a yanke hukunci na ƙarshe akai.

Kuna goyon bayan a ƙirƙiro ƴan sandan jihohi a Najeriya....?

DA DUMI-DUMI: Facebook zai fara biyan ƴan Najeriya daga watan Yuni 2024Babban jami’in Kamfanin Meta Sir Nick Clegg ya sh...
21/03/2024

DA DUMI-DUMI: Facebook zai fara biyan ƴan Najeriya daga watan Yuni 2024

Babban jami’in Kamfanin Meta Sir Nick Clegg ya shaidawa Tinubu cewa nan da watan Yuni 2024 masu amfani da Instagram a Najeriya za su fara samun kudi ta hanyar monetization.

Mahanga ta ruwaito Kamfanin Meta dai shine mamallakin dandalin sadarwa na Instagram, da WhatsApp, da kuma Facebook, sun bayyana haka ne a lokacinda tawagar kamfanin s**a gana da shugaba Tinubu yau Alhamis a Abuja

LABARI: Access Bank na Najeriya zai sayi Babban Bankin ƙasar Kenya wato National Bank of Kenya...
21/03/2024

LABARI: Access Bank na Najeriya zai sayi Babban Bankin ƙasar Kenya wato National Bank of Kenya...

INDA RANKA: Wata Kirista ta tsinci kanta a asibiti bayan ta suma sau Biyu kafin karfe 4 na rana daga gwada yin azumin Ra...
21/03/2024

INDA RANKA: Wata Kirista ta tsinci kanta a asibiti bayan ta suma sau Biyu kafin karfe 4 na rana daga gwada yin azumin Ramadan

Wata kirista Eniola Fagbemi wacce ke auren wani musulmi a Kudu ta yi kurarin cewa azumin musulmi bashi da wuya tunda suna yin sahur kuma su sha ruwa lokacin magriba, don haka tace za ta jaraba don ta tabbatar masa,

Mahanga ta ruwaito Sai dai bayan Eniola ta yi sahur wajajen 4:30 na asuba tun wajen karfe 12 na rana ta fara fita hayyacinta, kan kace kwabo ta suma sau Biyu wajajen ƙarfe 4 na yamma ba arziki aka kwashe ta sai asibiti,

Allah ya taimaka an ceto rayuwar ta a asibitin Saanu Hospital dake garin Mokola

Kuyi following shafin =>> IMACS TV domin samu labari na gaba....

A karon farko likitoci a Amurka sun dasa wa mutum kodar alade
21/03/2024

A karon farko likitoci a Amurka sun dasa wa mutum kodar alade

Saudiyya na tunanin sake gina Falasdinu da yaki ya rugurguza
21/03/2024

Saudiyya na tunanin sake gina Falasdinu da yaki ya rugurguza

Rikicin kabilanci ya janyo mutuwar mutane 42 a Chadi
21/03/2024

Rikicin kabilanci ya janyo mutuwar mutane 42 a Chadi

Muhawara Katse tafiye-tafiyen ketare da gwamnatin Najeriya ta yi wa ministoci, zai zama hanyar tsumi da yaki da cin hanc...
21/03/2024

Muhawara

Katse tafiye-tafiyen ketare da gwamnatin Najeriya ta yi wa ministoci, zai zama hanyar tsumi da yaki da cin hanci a gwamnatin Tinubu ta Najeriya?

Ban hana ku, ku yi aikinku ba, amma ina son ku daga wa ministocina da wadanda na nada muk**ai su sarara domin su mayar d...
21/03/2024

Ban hana ku, ku yi aikinku ba, amma ina son ku daga wa ministocina da wadanda na nada muk**ai su sarara domin su mayar da hankalinsu kan ayyukan da ke gabansu- Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan majalisar Najeriya

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kai wata ziyara  sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja, a ...
21/03/2024

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kai wata ziyara sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja, a ranar Laraba.

Me ku hasashe daga wannan ziyara ta Malam Nasiru El-Rufa'i?

21/03/2024

IMACS TV

A kowacce dakika (second), lita 11 zuwa 18.5 ta ruwan zamzam ce ke bubbugowa daga rijiyar Zamzam wadda ke dab da dakin K...
20/03/2024

A kowacce dakika (second), lita 11 zuwa 18.5 ta ruwan zamzam ce ke bubbugowa daga rijiyar Zamzam wadda ke dab da dakin Ka‘aba a birnin Makkah na Saudiyya.

📸 Inside the Haramain

Gwamnatin Najeriya ta ce mawallafin jarida Tukur Mamu na cikin jerin mutanen da take zargi da tallafa wa ‘yan bindiga sa...
20/03/2024

Gwamnatin Najeriya ta ce mawallafin jarida Tukur Mamu na cikin jerin mutanen da take zargi da tallafa wa ‘yan bindiga safarar kudade k**ar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Katsina Dikko Radda zai tura motoci masu sulke fagen daga domin tumurmusa ‘yan bindigar da s**a addabi jiharsa d...
20/03/2024

Gwamnan Katsina Dikko Radda zai tura motoci masu sulke fagen daga domin tumurmusa ‘yan bindigar da s**a addabi jiharsa da ke fama da garkuwa da mutane gami da satar shanu.

📸Isah Miqdad

Jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu jihohi hudu na arewa sun kashe naira biliyan 28 kan ciyar da talakawa abinci a w...
20/03/2024

Jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu jihohi hudu na arewa sun kashe naira biliyan 28 kan ciyar da talakawa abinci a watan azumin Ramadana.

Shin wadannan kudade na kaiwa ga mutanen da s**a dace kuwa?

INDA RANKA: Matar aure a Lagos ta kwara wa mijinta tafas@sshen ruwan tumat¡r saboda ya zane ɗiƴarsu da bulalaAttajirin m...
19/03/2024

INDA RANKA: Matar aure a Lagos ta kwara wa mijinta tafas@sshen ruwan tumat¡r saboda ya zane ɗiƴarsu da bulala

Attajirin mai kudin nan dake Lagos Architect Onyelowe Dandison ya wallafa bidyo kwance a asibiti cikin raɗaɗ¡n zaf¡ yana cewa "Idan na mutu yau ku sani matata wacce na auro da kudina nake kula da ita iya ƙarfina ita ta w@tsa mani tafas@sshen ruwan tumatir saboda kawai na ladaftar da ɗiyarmu na za^ne ta da bulala"

An yabawa Tinubu kan yadda ya fara gyaran gadar da aka rusa ta tun a yaƙin basasaTun alif 1970 lokacin rikicin basasa ak...
19/03/2024

An yabawa Tinubu kan yadda ya fara gyaran gadar da aka rusa ta tun a yaƙin basasa

Tun alif 1970 lokacin rikicin basasa aka lalata gadar wacce itace ta sada jihohin Kudu maso gabas, jihar Abia zuwa Imo sannan zuwa jihar Akwa Ibom.

Bugu da ƙari Shugaban ƙasar ya kuma bayar da aikin gyaran titin Ubakala zuwa -Umunwanwa- zuwa Udo Adobi zuwa Achingalli wanda shima baya biyuwa tun bayan gama yakin basasa a 1970

Abdourahamne Tiani ya aika sakon taya murna ga Vladmir Putin bisa ga sake lashe zaben shugaban kasar RashaA jamhuriyyar ...
19/03/2024

Abdourahamne Tiani ya aika sakon taya murna ga Vladmir Putin bisa ga sake lashe zaben shugaban kasar Rasha
A jamhuriyyar Nijar, shugaban kasar Abdrouhamane Tiani, ya aika da sakon taya murna a ranar jiya Litinin 18 ga watan Maris din shekarar 2024 zuwa ga shugaban kasar Rasha Vladmir Putin, da ya sake lashe zaben shugaban kasa.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Bayan zaben shugaban kasar Rasha da aka gudanar a makon da ya gabata tare da nasarar shugaba mai ci na Rasha Vladmir Putin da kashi 87. 97 cikin 100 na kuri’un da ’yan kasar s**a jefa, bisa ga sak**akon da babbar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Rasha ta bakin shugabarta madam Ella Pamfilova ta tabbatar ta gidan talabijin din kasar a ranar Lahadi 17 ga watan Maris din shekarar 2024 bisa ga nasarar shugaba Vladmir Putin.
Kamar sauran shugabannin kasashen duniya, shugaban kasar Nijar ma Abdrouhamane Tiani, ya aika sakon taya murna ga takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin. Sakon na cewa, “bisa ga wannan nasara ce, a matsayina na shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP nike isar da jinjina ta musamman da taya murna ga shugaban kasar Rasha, Vladmir Puti bisa ga wannan nasara.”
Sakon kuma, ya ci gaba da cewa, kasar Nijar, domin neman ’yancin kanta da na al’ummarta, da kuma bunkasuwarta, ba za ta kasa a gwiwa ba, na nuna alfaharinta na ganin taimakonku kan hanyar da kasar Nijar ta dauka domin ci gabanta, da yaukaka huldar dangantaka tare da kasar Rasha domin ganin Nijar ta cimma wannan nasara ta kokowar neman ’yancin kanta da kishin kasarta, in ji wannan sako a karshe.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.

19/03/2024

Yadda Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya s**a jidi Naira tiriliyan 13.95 ba bisa ƙa’ida ba – Rahoton bincike

Aƙalla Naira tiriliyan 13.95 ne Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati s**a jida ba bisa ƙa’idar da Kundin Dokokin Najeriya ya shar’anta ba.

Rahoton da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya fitar ne kan yadda hukumomin gwamnati s**a kashe kuɗaɗe a shekarar 2020.

Rahoton ya fallasa cewa jidar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba ya kawo naƙasu da tawaya wajen kasa tantance daidaiton gano kuɗaɗen da aka fitar aka yi aiki da su har Naira 13,955,069,757,335.00.

Wannan gurungunɗuma dai ta karya Dokar Kuɗaɗen Gwamnati ta 2009, wadda ta ce “Kada gwamnati ta ciri kuɗi daga asusun bankuna kai-tsaye. Idan kuma aka cira, to ma’ajin hukumar ko ma’aikatar zai fuskanci hukuncin biyan kuɗaɗen bankin zai caja.”

Sai dai kuma wata sabalula da asarƙala ita ce an bayyana kuɗaɗen a matsayin aro da ayyukan haƙƙin gwamnati.

Ma’aikatar Muhalli ce aka fi yin wannan karya doka, inda aka jidi Naira biliyan 350.85.

Mai bi mata ita ce Hukumar Binciken Ingancin Abincin da ake Ajiyewa, wato Nigeria Stored Products Research Institute,

Ofishin Biyan Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, wanda ya jide Naira biliyan 27.95.

Benin da Ilorin ne na su adadin da aka jida na su da yawa, k**a daga Naira biliyan 107.50 jimlace.

Mai Binciken Kudi na Gwamnatin Tarayya Shaakaa Chira ya ce an jide wadannan kuɗaɗe ba tare da sahalewar gwamnati ba.

Ƙarin abin mamaki kuma shi ne duk ba su yi bayanin ayyukan da aka yi da kuɗin ba.

Chira ya ce karkatar da kuɗaɗen ya faru ne saboda rashin kaƙƙarfar masu sa-ido kan adadin kuɗaɗen da ma’aikatu za su fitar.

Tsarin fitar da kuɗaɗen gwamnatin tarayya ya ƙara da cewa ya gano maƙasudin ƙin bin ƙa’ada wajen cirar kuɗaɗe ne saboda an riƙa watsa wasu kuɗaɗen cikin aljihun masu cirar kuɗaɗen.

Sai dai kuma wata ƙwararriya kan sha’anin bin ƙa’idar cirar kuɗaɗe mai suna Adenike Aloba, ta ce ya k**ata a ƙara wa Ofishin Akanta Janar ƙarfi, ba kawai ya tsaya ya na yin kira ko zare ido kaɗai, kaɗai ko cewa a maido da kuɗaɗen da gaggawa kaɗai.

Send a message to learn more

Address

Masjid Imamu Ahmad Bin Hambal Bayan Dala, Dala Local Government.
Kano
IMAMUAHMADCENTERFORSTUDIES6

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when IMACS TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to IMACS TV:

Videos

Share

Category


Other Newspapers in Kano

Show All

You may also like