30/08/2022
Educational Post: Ma'ana: Wasikar Ilimi 000-2
_____________________
What is Proof Of Work (Pow) and Proof Of Stake (Pos)?
__________________________
Ma'ana: Menene "Proof Of Work (Pow)" Da Kuma "Proof Of Stake (Pos)"?
Karka ruda kanka!!. Da zarar kaji ana magana akan "Proof Of Work and Proof Of Stake" to kawai ana magana ne akan "Consensus Machanisms"!. Idan ance (Consensus Machanisms) ana nufin abubuwan da suke temakawa "Blockchain" wajan tabbatar da 'Transactions'. Ko kuma nace amfanin "Consensus Machanisms" shine tabbatar da duk wani "Transactions" da akeyi akan Blockchain. Sannan kafin nayi magana akansu naso ace nayi Rubutu akan "Blockchain Consensus Algorithms", domin idan mutum yasan "Blockchain Consensus Algorithms" nasan sai yafi saurin fashimtar wa yannan abubun wa yanda ake kiransu da "Proof Of Work and Proof Of Stake"!. Domin gaskiya zaiyi wuya ace mutum yasan "Blockchain Consensus Algorithms" amma baisan "How Proof Of Work and Proof Of Stake Works" ba!?, Zaiyi wuya gaskiya. Domin ta wata fiskar zan'iyacewa duk kusan daya suke!!.
Sannan, Proof Of Work and Proof Of Stake sune kawai daman "Consensus Machanisms" da ake amfani dasu a CryptoCurrency da kuma Defi Application.
~Amma bari nayi bayanin su dalla-dalla.
What is Proof Of Work (Pow)?
____________________
Idan ance "Proof Of Work (Pow) to kawai ana magana akan yadda duk wani "Transactions" da yake wanzuwa akan -Blockchain Technology- tare da temakon "miners" ko kuma nace "validators" gurin samar da Hash ta hanyar amfani da "Hash Functions"!. Da temakon Miners da kuma Validators ake tabbatar da duk wani ~Transactions~ akan Blockchain, ko kuma nace Miners da kuma Validators sune suke tabbatar da duk wani Transactions dake wanzuwa akan Blockchain Technology.
Duk wani Transactions da akeyi akan Blockchain "Miners sune sukeyin Validating Transactions din", indai wannan Coin/Token din an dorashi akan wannan "Consensus Machanism" na Proof Of Work (Pow). Idan ance 'Miners', bafa ina nufin kai ko niba wanda yakeyin Mining din "PI-NETWORK" ko "Satoshi Core Mining". Wannan shima bangarene babba wanda yake bukatar lokaci mai tsayi gurin bayanin shi. idan kaji ina magana akan miners a wannan fagen to Ana maganane akan masu ainishin yin Mining, kamar masu yin Mining Bitcoin. Sunayin amfanine da manyan Computers da kuma Electricity 🔌 gurin yin Mining din. Miners/Validators sune suke "Solve din Puzzle Sannan suyi Validate din Transaction". Sannan Miners/Validators sune sukeyin "Generating din Hash a Blockchain". Sannan duk wani Transaction das**ai "Validate dinshi To the Block" to akwai wani "Rewards" da zasu samu. Suna samun Rewards din ta "Transaction Fee". Sannan "Through Proof Of Work" anayin Mining din wasu sabbin Coins/Tokens, kamar Lokacin da aka samar da Bitcoin kunga ai Mining dinshi akeyi a sameshi. Sannan har yanzu akwai wasuyin Mining dinshi Sannan kuma suna samun Rewards.
Sannan duk wani wanda yasan yadda akeyin Mining din Bitcoin to sai yafi gane wannan bayanin sosai. Amma a takaicen-ta-kaicewa zan iyacemuku….
Proof Of Work (Pow) shine "Consensus Machanism" na farko da aka samar a Crypto, sannan anyi amfani dashine farko akan Bitcoin. Sannan "Proof Of Work (Pow) is more secure 🔐 than "Machanisms" kamar irin su Proof Of Stake (Pos).
Sannan an samar da wannan tsarin na 'Proof Of Work' a shekara ta 1993, wasu mutane biyune s**a samar dashi masu suna (Moni Naor and Cynthia Dwork) a 1993!.
To dai banaso bayanin yayi yawa sosai.
Amma dai a takaice "Proof Of Work" shine -First- "Cryptographic Consensus Machanism" da aka samar tin kafin "Proof Of Stake (Pos).
Allah Yasa Angane!?
Bari yanzu kuma mu koma kan "Proof Of Stake (Pos) shima muyi bayaninshi a takaice.
What is Proof Of Stake (Pos)?
__________________________
Proof Of Stake (Pos) wani "Consensus Machanism" ne shima da ake amfani dashi gurin Validating din Transactions. Amma shi Proof Of Stake (Pos) bawai kamar "Proof Of Work (Pow)" bane wanda akeyin amfani da wasu manyan Computers da kuma wutar lantarki (Electricity) mai karfi gurin gurin yin Mining ko Validating din Transactions ba. A wannan tsarin na 'Proof Of Stake' abinda ake bukata Miner ko Validator yayi shine, yase wani adadi (Amount) na Coin/Token yayi staking dinsu zuwa ga wani Lokaci mai tsayi ko gajere wanda hakanne zai bashi dama gurin duba sabbin "Blocks Of Transactions" yayi adding dinsu zuwa kan Blockchain!!.
A takaice zan'iya cewa Proof Of Stake (Pos) wata hanyace wacce zata bawa ma mallaka wani Coins damar suyi Stake dinsa zuwa wani lokaci, sannan kuma idan sunyi Staking din zasu samu damar samar da "Validator Nodes" dinsu, domin sudinga Validating Transactions.
Idan ance "Staking" shine kamar ka bayar da Coins dinka domin a dinga yin Verifying na Transactions akan wannan Block din naka na Coin din. Zakayi "Locked 🔐 Up" din Coins din nakane zuwa wani lokaci, Sannan iya lokacin da ka'iba sai yayi Sannan zaka samu damar sake yin "Access" din Coins din naka. Ma'ana duk wani Coin da kayi Staking dinsa to bazai iyuba kace zakai "Trading" dashiba. Sai dai idan kayi Unstake dinsa Sannan zaka samu damar yin Trade dashi.
Sannan a akan wannan tsarin na Proof Of Stake (Pos), ana zabar wanda zaiyi Validating Transaction shine "Randomly"!. Ma'ana bawai wani kawai wanda akeso za'a zababa Sannan abar wanda bashi akesoba. Bakamar yadda tsarin Proof Of Work yaceba.Kawai dai a Proof Of Stake (Pos) adadin da kayi Stake din zai sake baka damar yin nasara gurin saurin samun wani Transactions da ake bukata kayi Validate dinshi.
Da zarar ansamu wani "Block Of Transaction" wanda ake neman Validator yayi "Validate" dinsa to "Proof Of Stake Protocol" zai zabi Validator Node domin ya bibiyi Block din, to kuma shi "Validator" din shine wanda zai duba Block din yaga shin wannan Transaction din dai dai ne (Accurate) kuwa!?, Da zarar yaga Transaction dai dai ne (Accurate) to sai yayi "Adding din Block din akan Blockchain". Sannan bayan yayi Adding Block din zuwa ga Blockchain din zai samu Rewards domin wannan Validating Transaction din da yayi.
Sannan akwai wani hatsari (Risk) wanda da zarar Validator din yayi zai iya rasa duk Asset dinsa ma'ana duk Coins din da yayi Staking!, Ko kuma wani abu daga cikin abinda yayi Staking din a matsayin Jankunne (Penalty/Punishment). Da zarar yayi Validate din wani Transaction ko ince Information wanda "It's inaccurate" akan Blockchain to zai iya gamu da abinda na fada muku na rasa duk Asset din ko kuma wani adadi daga cikin abinda yayi Staking a matsayin Jankunne (Penalty/Punishment).
Daga yazama dole sai Validator ya tabbatar da abu kenan kafin yayi Adding dinshi akan Blockchain.
Misalin Proof Of Stake (Pos) shine ku kalli yadda Cardano (ADA) sukeyi, kusan Cardano (ADA) shine CryptoCurrency mafi sanuwa wanda aka dorashi akan wannan tsarin na Proof Of Stake (Pos). Duk wani wanda yakeda Cardano (ADA) zai iyayin Staking dinsa Sannan ya samar da "Validator Node" dinsa. Sannan da zarar ana bukatar yin Validating din wani Transaction akan Cardano (ADA) to "Protocol" dinta Automatic zai zabi Validator, shikuma Validator din zai duba Transaction din kafin yayi Adding dinshi akan Blockchain ya tabbatar da cewa "It's Accurate" to sai yayi Adding Block din akan Blockchain. Sannan sai ya karbi Rewards dinshi. Ma'ana bayan yayi Validating din Transaction din zaiga ya sake samun wasu karin Cardano (ADA) akan abinda yake dashi a matsayin Rewards dinshi na wannan aikin da yayi na Validating Transaction din.
Proof Of Stake (Pos) ya zama sananne a cikin 'yan shekarun nan saboda "Significantly lower energy usage and greater potential for scalability". Sannan Proof Of Stake (Pos) baya bukatar wata wutar lantarki (Electricity) gurin yin Validating din wani 'Transaction', ko kuma nace dole sai da wasu manyan Machines dafin ace Miners/Validators sun tabbatar da Wani "Transaction".
Sannan gaskiya akwai wasu abubuwa da Proof Of Stake (Pos) yazo dasu wanda shi Proof Of Work (Pow) baizo da shiba.
Hakanne yasa zakuga manyan "Projects" wanda akeji dasu a Duniya kamar irin su "Ethereum (ETH)" zakuga suna kokarin mayar da "Ecosystem" nasu kan wannan tsarin na Proof Of Stake (Pos). Sannan ba su kadai neba, yanzu duk wasu Projects zakuga ana dorasune akan Proof Of Stake (Pos). Domin gaskiya yanzu Proof Of Work (Pow) yazama tsohon yayi, duk da cewa wasu manya masana "Blockchain Technology" sunce Proof Of Work (Pow) is more secure 🔐 than, Proof Of Stake (Pos).
Sannan akwai matsaloli da yawa da ake fuskanta a Proof Of Work (Pow), wanda a Proof Of Stake duk babusu. Gaskiya idan nace sai na fadi komai nasan wannan rubutun zai dau tsahon lokaci ban gamaba, Sannan kuma masu karantawa zaku gaji da karan tawa.
Bari na farku haka anan gaba munci gaba.😊
Hakamma nasan wasu zasuce rubutun yayi yawa. Amma dai a daure a karanta.
Idan nayi kuskure kuma, ina neman afuwarku yan uwa.🙌
Allah Ubangiji Ya Datar Damu.
✍️✍️✍️
Aminu Dayyib Zakariyya