Barima Hausa

Barima Hausa Barima Hausa. Yancin Samun Labari. Yancin Fadar Gaskiya. Hakkin yan kasa. Ku kasance damu don samun labarai masu inganc 08091119611 News 24 Hour
(6)

current News, Advertising works because people don't buy things they don't know about. Advertising gives additional exposure to products, which increases sales, especially when the advertising is highly targeted to a related demographic group of viewers. Online advertising is an efficient way to reach both a global market as well as a local market. Even if you only have a physical storefront locat

ion and are not online at all, it pays to advertise on the net because many people today rely on the Internet to find local businesses.

07/03/2024

Ku yi hakuri bisa rashin wutar lantarki da ake fama da shi, Gwamnati ta roki ƴan Nijeriya

Ministan ma'aikatar samar da hasken wutar lantarki a Najeriya, Bayo Adelabu ya ce yana cike da damuwa kan yadda ɓangaren samar da wuta ke ci gaba da taɓarɓarewa a faɗin ƙasar.

Ministan na lantarki ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna ɓacin ransa kan raguwar wutar lantarki da ake samu duk da irin kokari da ake yi a ɓangaren.

“Dangane da haka ne na gayyaci shugabannin kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC), da kuma Babban Darektan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), zuwa wani muhimmin taro,” in ji ministan.

Ya ce makasudin kiran taron shi ne tattaunawa kan taɓarɓarewar wutar lantarki a yankunansu da kuma ganin an samar da mafita mai ɗorewa kan hakan.

Mista Adelabu ya ce ma’aikatarsa ta yi ta matsa wa masu samar da wutar lantarki da su ƙara kokari a ayyukansu, abin da ya sa ma har aka ƙara karfin megawat na wuta zuwa 4000.

Ya ce duk da irin ci gaba da aka samu, wasu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun kasa rarraba wutar lantarki da TCN ke bayarwa yadda ya kamata, yayin da ake ƙara samun masu satar da kayayyakin wutar lantarki musamman a yankuna kamar Abuja, Benin, Fatakwal, da kuma Ibadan.

Ya ce ba za su lamunci rashin samar da wuta ba daga kamfanonin da alhakin haka ya rataya a wuyansu, kuma za a ɗauki mataki mai tsanani a kansu, ciki har da soke lasisi.

Ministan ya ce ana ci gaba da tsare-tsare na ganin an warware basuss**an da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki da iskar gas, wanda hakan zai rage wahalhalun da ake fama da su.

Don haka, ya buƙaci jama’a da su ƙara hakuri yayin da ake aiki tukuru wajen magance waɗannan matsaloli da kuma samarwa ƴan Najeriya wutar lantarki yadda ya kamata.

BBC Hausa

Azumin Ramadhan : Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Roki 'Yan Kasuwa Su Rage Farashin Kayan AbinciA wajen kaddamar da litt...
05/03/2024

Azumin Ramadhan : Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Roki 'Yan Kasuwa Su Rage Farashin Kayan Abinci

A wajen kaddamar da littafin tarihin "Daulolin Kasar Hausa" wanda Farfesa Sa'idu Muhammed Gusau ya wallafa, Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira na musamman ga' yan kasuwa da su sassauta kan farshin kayan abinci da ragowar kayan masarufi.

An yi taron ne a masarautar Zazzau, ranar Lahadi, in da Sarkin Kanon ya nuna irin alheran da 'yan kasuwa za su samu daga Allah idan su ka tausayawa bayinSa a wannan wata mai alfarma na Ramadhan.

Haka kuma ya kara yin kira ga mawadatan cikin al'umma da su taimakawa talakawa ganin yadda rayuwa ta kara zama a matse.

"Ina rokon' yan kasuwar mu kamar yadda na saba kan su dubi irin taimako da dauki da albarka da za su samu daga Mahaliccinmu idan su ka rage farashin kayan abinci da ragowar kayan masarufi. Musamman ganin kusantowar wata mai Alfarma na Azumin Ramadhan," in ji Sarkin.

Ya ce" Mu na rokon mawadatanmu da su taimakawa al'umma wajen rage musu radadi na wannan rayuwa. Cikin sahalewar Allah."

Sarkin ya yabawa Farfesa Gusau wajen fito da tarihin Daulolin Kano da Sakkwato da Zazzau da Zamfara da Katsina da Kebbi

An yi sowa sosai lokacin da Sarkin yake wannan kiran da yake nuna tausayi da son al'umma dake zuciyar Sarkin. Kamar yadda wasu jama'a da mu ka tattauna da su s**a fada jim kadan bayan tashi daga taron.

Mawallafin littafin Farfesa Gusau ya godewa Mai Martaba da duk iyayen kasa da su ka halarci taron.

An gano robar tekawe na da matsala ga lafiyar ɗan adam. - Majalisa Majalisar Wakilai ta bukaci a haramta amfani da robob...
15/02/2024

An gano robar tekawe na da matsala ga lafiyar ɗan adam. - Majalisa

Majalisar Wakilai ta bukaci a haramta amfani da robobin cin abinci na 'tekawe' a Najeriya saboda barazar da robobin keyi ga lafiyan ɗan adam.

A cewar wani bincike da dan majalisa yayi ya tabbatar da cewa, akwai wani sinadari mai suna "styrofoam" Yana da illa ga rayuwar yan Adam domin shi yana hana abu lalacewa da wuri.

Haka zalika yana taka rawar gani wajen kawo lalacewar muhalli wajen toshewar magudana da sauransu.

11/11/2023
22/10/2023
22/10/2023
03/10/2023

Siyasa ko Addini?

Address

Kano
234

Telephone

+2348091119611

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Barima Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Barima Hausa:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Kano

Show All