Media 24 News

Media 24 News media24 News wan nan gidan jaridane mai albarka da zai'rika kawomuku labarai masu inganci.

Gwamna Zulum Ya ƙaddamar da Cibiyar koyar da sana’o’i da Gwamnatinsa tayi Nasarar Ginawa a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar ...
30/08/2023

Gwamna Zulum Ya ƙaddamar da Cibiyar koyar da sana’o’i da Gwamnatinsa tayi Nasarar Ginawa a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno.

Wannan Cikakkiyar Cibiyar koyar da sana'o'i Tana da tarurrukan Bita Guda 15, Kowanne na sanye da Kayan aikin horarwa na zamani Wanda ke Gudanar da Sana'o'i iri-iri. Waɗannan sun haɗa da kayan aikin Zamani na Horar da ICT, Ɗinki da zanen kayan kwalliya, Gyaran Gashi da kayan kwalliya, Walda, Aikin famfo Da Gyaran bututu, Aikin kafinta, Ayyukan lantarki, Saka Hasken rana, koyar da Gyaran Motoci da injina, fasahar noma, saka da kwarkwata. Da kuma samar da aluminum, da sauransu.

Media24

K@da ku kus*kura ko da wasa kuce za kuyi ju+yin mulki a Najeriya, kungiyar kare hakkin mus+ulmi (MURIC) ta gar*gadi sojo...
30/08/2023

K@da ku kus*kura ko da wasa kuce za kuyi ju+yin mulki a Najeriya, kungiyar kare hakkin mus+ulmi (MURIC) ta gar*gadi sojojin Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Media24

Kuna tafiya da budurwaka, in ka tsinci wannan a ƙasa na san ba zaka durƙusa  don ka ɗauka ba, kar mutuncinka ya zube, mu...
30/08/2023

Kuna tafiya da budurwaka, in ka tsinci wannan a ƙasa na san ba zaka durƙusa don ka ɗauka ba, kar mutuncinka ya zube, mutunci yafi komai!

Media24

MUHAWARÁ: Wacce jiha ce mazan jihar basa iya riƙe aure sai yawań auri saki a Nájeriya ?Media24
30/08/2023

MUHAWARÁ: Wacce jiha ce mazan jihar basa iya riƙe aure sai yawań auri saki a Nájeriya ?

Media24

Tinubu ya f@ra tatta+unawa da kun*giyar AU, don kw@to mulkin G@bon, ya dawo hannun farar hula.Media24
30/08/2023

Tinubu ya f@ra tatta+unawa da kun*giyar AU, don kw@to mulkin G@bon, ya dawo hannun farar hula.

Media24

MAI GIRMA GWAMNA YAYI ZAMAN MAJALISSAR ZARTARWA TA JIHAR JIGAWA.Majalisar zartarwa ta Jihar Jigawa karkashin Jagorancin ...
30/08/2023

MAI GIRMA GWAMNA YAYI ZAMAN MAJALISSAR ZARTARWA TA JIHAR JIGAWA.

Majalisar zartarwa ta Jihar Jigawa karkashin Jagorancin Mai Girma Gwamna Malam Umar A. Namadi FCA, a yau Laraba 30 ga watan Agusta, 2023 tayi zama a karo na huɗu (4) wanda ta tattuana akan muhimman batutuwa da s**a shafi cigaban Jihar Jigawa baki ɗaya. Majalisar ta amince da waɗannan abubuwan a zamanta nay au;

1. Majalissar ta amince da biyan kuɗin Makaranta ga Ɗalibai 'yan asalin Jihar Jigawa wadda su ke karatu a Jami'ar Tarayya ta Dutse (FUD) Majumdar Bayero dake Kano (BUK) da Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KUST) da Kuma Jami'ar Maiduguri (UNIMAID) akan kuɗi Naira Miliyan dari da sittin da bakwai, da dubu ashirin da hudu da dari tara da Hamsin (N167,024,950.00). Hakan ya yi biyo bayan yanayin da Ɗaliban da iyayensu s**a shiga na rashin iya biyan kuɗin Makarantar da aka ƙara.

2. A Ƙoƙarin Gwamna Malam Umar A. Namadi na inganta fannin noma, Majalissar ta amince da bayar da kuɗi har Naira biliyan ɗaya (N1,000,000,000.00) ga kamfanin saye da sayarwa kayan aikin gona na Jiha wato (JASCO), domin sayo motocin tarakta ( tractors) guda Hamsin da hudu (54) domin inganta harkokin aikin gona a faɗin Jihar Jigawa.

3. Majalissar ta kuma sake amincewa da sayo tirela sabai'in (70 trucks) ta shinkafa( kowace tirela buhuna (600) da Gero da kuma Masara tirela hamsin da hudu (54 trucks) (kowace tirela buhuna (600), sannan da taliya kwali dubu ɗaya (1,000 ) wadda za a raba a fa a ƙarƙashin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha (SEMA) , wadda kaunsa ya tasamma Naira Biliyan uku da milyan dari takwas da dubu arba'in da takwas (N3,848,000.00).

Media24

Yadda ake bude PayPal  account cikin sauki domin send and receive dollars  a Nigeria.
30/08/2023

Yadda ake bude PayPal account cikin sauki domin send and receive dollars a Nigeria.

Purpose of the Document: The purpose of this document is to provide you with clear and concise information about how to navigate and utilize your PayPal

Yadda ake bude dollar account da payoneer domin hada hadar kasuwan ci, Zaka iya budewa domin ajiye dollar account dinka ...
30/08/2023

Yadda ake bude dollar account da payoneer domin hada hadar kasuwan ci,

Zaka iya budewa domin ajiye dollar account dinka da ita.
Kar amanta da share groups da status domin yan'uwa su amfana.

Payoneer is a financial services company that provides online money transfer and digital payment services. It offers individuals and businesses the ability to

Tofa wacce Jihar ce za ta ci. A cigaba da gashi.Media24
29/08/2023

Tofa wacce Jihar ce za ta ci. A cigaba da gashi.

Media24

DA ƊUMI-ƊUMI: Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar NNPP Ya dakatar da Dr Rabi'u Musa Kwankwaso Wanda Ya yiwa Jam'iyyar Takara...
29/08/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar NNPP Ya dakatar da Dr Rabi'u Musa Kwankwaso Wanda Ya yiwa Jam'iyyar Takarar Shugaban ƙasa, Na Tsawon Watanni shida bisa zarginsa da Yin Anty Party.

Media24

LABARI MAI DADI: Gwamnatin Tarayya za ta dauki ma'aikata dubu 300,000 a Najeriya, a kowace jiha za ta dauki matasa dubu ...
29/08/2023

LABARI MAI DADI: Gwamnatin Tarayya za ta dauki ma'aikata dubu 300,000 a Najeriya, a kowace jiha za ta dauki matasa dubu 7,000.

Ma'aikatan zasu yi aiki ne a sabuwar hukumar da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kafa tun a shekarar 2022, mai suna NATCOM. Hukumar zata dauki ma'aikatan ne a kowane bangaren kasar, kuma zata ba su horo na musamman domin dakile yawaitar yawon makamai a Najeriya.

A yanzu haka Gwamnatin Tinubu tace ta kammala shirin daukan matasa 7,000 a jihohi 36, da babban birnin Tarayya Abuja, aiki a karkashin hukumar.

Da zaran hukumar ta fitar da Portal, ko tsarin yadda za ta dauki ma'aikatan zamu sanar muku.

Media24

A ƙarasa mana wannan karin maganar...
29/08/2023

A ƙarasa mana wannan karin maganar...

Kowa ya baiwa idan sa abinci mai kuka hango acikin wan nan photon.
28/08/2023

Kowa ya baiwa idan sa abinci mai kuka hango acikin wan nan photon.

Shugaba Bola Tinubu Ya umurci ma’aikatar Harƙoƙin Wajen Tarayya da ta Dakatar da Gudanar da biza Ga duk jami’an Gwamnati...
28/08/2023

Shugaba Bola Tinubu Ya umurci ma’aikatar Harƙoƙin Wajen Tarayya da ta Dakatar da Gudanar da biza Ga duk jami’an Gwamnati dake Neman Zuwa Birnin New York Domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya ba tare da wata shaida ta Shiga Cikin jadawalin Ayyukan Hukumar ta UNGA ba.

Media24

DA ƊUMI-ƊUMI: Ministan Tsaro Ya Gana Da Abdulsalami, Da Tsohon Hafsan tsaroMinistan Tsaro, Mohammed Badaru, A Yau Litini...
28/08/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Ministan Tsaro Ya Gana Da Abdulsalami, Da Tsohon Hafsan tsaro

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, A Yau Litinin ya Gana da Tsohon Shugaban ƙasa na Mulkin Soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), da Tsohon Babban Hafsan tsaron ƙasa, Janar Martin Luther Agwai.

Sanarwar ta bayyana Cewa ziyarar da Ministan Ya kaine Domin neman shawarwarin kwararru Daga ɓangarorin biyu kan yadda zai tunkari aikin da ke Gabansa na shawo kan matsalolin tsaro da s**a Addabi Kasar Musamman Arewacin Najeriya.

Media24

Yadda ake cike bashin NIRSAL kasamu bashin naira dubu dari biyar (500,000), Cikin sauki.Please kada kumanta da shere sta...
28/08/2023

Yadda ake cike bashin NIRSAL kasamu bashin naira dubu dari biyar (500,000), Cikin sauki.
Please kada kumanta da shere status da groups domin yan uwa su amfana.

Hello brother's and sister's well come back to our website medianews, In this new lesson i will teaching you how to get a convenient loan to day from

Yadd zaka nemi aiki a gender data assistant job na kungiyar world health Organization cikin sauki.Please kada kumanta da...
28/08/2023

Yadd zaka nemi aiki a gender data assistant job na kungiyar world health Organization cikin sauki.

Please kada kumanta da shere groups da status domin yan uwa su amfana.

Hello brother's and sister's well come back to our website medianews, In this lesson i will like to teaching you how to Apply for the Gender Data Assistant

Shari'ar zaben Gwamnan jihar Kano, ta fara daukan zafi. A jiya Asabar Gwamnan jihar, tare da magoya bayanshi s**a gudana...
27/08/2023

Shari'ar zaben Gwamnan jihar Kano, ta fara daukan zafi.

A jiya Asabar Gwamnan jihar, tare da magoya bayanshi s**a gudanar da Addu'ar neman Nasara a kotu. A yau Lahadi suma magoya bayan jam'iyyar APC za su gudanar da taron Addu'ar neman Nasara a shari'ar da ake yi.

Wa kuke yiwa fatan Nasara, tsakanin Gwamna Abba da Nasiru Yusuf Gawuna?

Media24

Hanyoyi guda biyar da zaka iya samun kudi a social media cikin sauki pls kada ku manta da share groups da status domin y...
27/08/2023

Hanyoyi guda biyar da zaka iya samun kudi a social media cikin sauki pls kada ku manta da share groups da status domin yan'uwa su amfana.

Hello brother's and sister's well come back to our website medianews, In our today lesson I will like to teaching you how to make money online in different

Yadda ake update na Npower profile kasamu dubu 90k cikin sauki Pls kada kumanta da shere status da groups domin yan'uwa ...
27/08/2023

Yadda ake update na Npower profile kasamu dubu 90k cikin sauki Pls kada kumanta da shere status da groups domin yan'uwa dayawa su amfana

Hello everyone welcome back to our website medianews, In this lesson i will teaching you how to update your npower (Or Nasim portal ) profile, And get your

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Yayi kira Ga Gwamnatin Tarayya da ta Daƙile wahalhalun da jama’a ...
27/08/2023

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Yayi kira Ga Gwamnatin Tarayya da ta Daƙile wahalhalun da jama’a ke ciki a ƙasar nan biyo Bayan Cire Tallafin Man Fetur.

Ahmed Lawan ya yi wannan kiran ne a jiya Asabar Yayin rabon shinkafa da Gero ga mabukata, marayu, zawarawa, Musulmi, da Kuma al’ummar Kirista 9,000 a Gashua hedikwatar ƙaramar Hukumar Bade ta jihar Yobe.

A cewarsa, Wasu Na Ganin da wuya su Baiwa Iyalansu abinci Sau uku a Rana Saboda tsananin da ake Ciki, Ya ƙara da cewa wasu ma na iya kwana biyu ba tare da wani abin da za su dafa wa iyalansu ba.

Ahmed Lawan ya ce Ya raba kayan Masarufi ne Domin ya zama Maganin rage wahalhalu a Shiyyar da yake wakilta Yobe Ta Arewa.

Media24

Janar Abdulsalami Abubakar, Tsohon Shugaban ƙasar Najeriya, A lokacin da ya Gana da Gwamnatin mulkin sojan Nijar a madad...
27/08/2023

Janar Abdulsalami Abubakar, Tsohon Shugaban ƙasar Najeriya, A lokacin da ya Gana da Gwamnatin mulkin sojan Nijar a madadin kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afrika ECOWAS.

Gwamnatin mulkin sojan ta shaida masa cewa ba za su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki ba, Kuma zasu Buƙaci Shekaru uku kafin su mayar da ƙasar kan turbar Dimokuraɗiyya.

Gen. Abdulsalami Abubakar ya ce hakan ya kara masa kwarin guiwa da yadda Gwamnatin mulkin soji ta yarda a yi magana. Yace yana da kyau ECOWAS ta mai da hankali kan abubuwan da za su Inganta rayuwar al'ummar Nijar, Kamar sake Buɗe iyakokin ƙasar da dawo da wutar lantarki.

Shugaban mulkin Sojan ya kuma Buƙaci ECOWAS da ta samar da abinci, magunguna, da sauran muhimman kayayyaki. Janar Abubakar ya ce zai kai waɗannan bukatu Ga Shugabannin ECOWAS.

Media24

Kwamishinan Matasa Da Wasanni Ya Wakilci Gwamnan Jihar Bauchi a Taron (RANAR HAUSA) ta Duniya A Yau Asabar 26 Ga Watan A...
26/08/2023

Kwamishinan Matasa Da Wasanni Ya Wakilci Gwamnan Jihar Bauchi a Taron (RANAR HAUSA) ta Duniya

A Yau Asabar 26 Ga Watan Augusta, Wanda kuma Rana ce da ta Kasance Ranar da Majalisar ɗinkin Duniya Wato United Nations (UN) ta ware Domin murnar Yaren Hausa Wanda aka mata inkiya da “Ranar Hausa” Kwamishinan Matasa da Wasanni Muhammad Salees Gamawa ya wakilci Gwamnan Jihar Bauchi Sen. Bala Mohammed (Kauran Bauchi, Jagaban Katagum).

Gagarumin taron dai Wanda ake yinsa a duk Shekara, ya Gudana ne a Masarautar Misau kuma ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Misau, Alh. Ahmad Sulaiman (mni) Tare da Hakiman sa, Kwaminishinar Ilimi Ta Jihar Bauchi Dr. Jamila Muhammad, Kantoman riƙo na ƙaramar Hukumar Misau Alh. Salisu Hussein Hardawa, Ɗaya Daga cikin yan Majalisun jiha Daga Jihar Gombe, Sarkin Hausawan Legas Ailan, Manyan baki Daga ko wani faɗin ƙasar Hausa Wanda s**a haɗa da mutan Agadez na Jamhuriyar Nijar.

A yayin jawabin sa, Mai Martaba Sarkin Misau ya nuna murnar sa da aka zaɓi Masarautarsa Domin Gudanar da wannan taron kuma ya nuna matuƙar Godiyar sa Ga Mai Girma Gwamnan jihar Bauchi wanda da yardansa ce aka Gudanar da taron.

A nasa Jawabin Kuma, Wakilin Gwamana, Muhammad Salis Gamawa ya yabawa Wanda s**a haɗa taron, Wato ƙungiyoyin Zauren Al’’ummar Hausawan na Duniya, Arewa Youth and Women for Change, Da kuma Arewa Media.

Ya kuma Tabbatarwa wa Masu taron cewa Gwamnatin Jahar Bauchi ƙarƙashin Jagorancin Sen. Bala Muhammad zata cigaba da bada nata Gudumawar Domin wajen ci gaba da alamuran bunƙasa al’adun Gargajiya da yare a Jihar Bauchi.

Daga ƙarshe an Baiwa wasu ya'yan ƙasar Hausa lambar Yabo Wanda s**a hada da Tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Ibrahim Shekarau, kwamisinar ilimi na jiha Dr. Jamila Dahiru, Kwamishinan na albarkatun ruwa na jihar Jigawa Hon. Ibrahim Hannungiwa, Da Matashin da ya bada albashin sa Domin cigabar jihar Bauchi Halliru Adamu (Circular) Wanda ya sadaukar Da Albashinsa A Gwamnan Jihar Bauchi, Alh. Umar Abdullahi na kamfanin AYM Shafa da sauran su.

Media24

Sabuwar Hanyar da zaka iya juya yaren turanci zuwa yaren hausa cikin sauki.
26/08/2023

Sabuwar Hanyar da zaka iya juya yaren turanci zuwa yaren hausa cikin sauki.

HOW TO CONVERT ENGLISH TO OTHER LANGUAGES

Domin Alfahari da harshen HAUSA, kawo mana karin magana guda uku?Ga nawa👇👇👇1, Chan ga su gada, zomo yaji kidan farauta. ...
26/08/2023

Domin Alfahari da harshen HAUSA, kawo mana karin magana guda uku?

Ga nawa
👇👇👇
1, Chan ga su gada, zomo yaji kidan farauta.

2, Komai aka yiwa tuwo, sai gara ta rama mishi.

3, Hankali da kaya ya fi ban cigiya.

Muna sauraron ku, amma banda Copy and Paste, kowa ya kirkiri nashi da kanshi, zamu gane wa 'yanda s**a iya Hausa da wa 'yanda basu iya ba.

✍️ Media24

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno Ya bada kyautar Naira 30,000 Masu Bautar Ƙasa Corpers 1215 (N36...
26/08/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno Ya bada kyautar Naira 30,000 Masu Bautar Ƙasa Corpers 1215 (N36.4m) Waɗanda A halin Yanzu suke Jihar sa na Tsawon Sati Uku

Baya Ga haka Zulum ya kuma ware buhunan Shinkafa 100, da Shanu 10, buhuna 10 na kilogiram 100 na wake, da Galan Na Man Girki 10 Domin Abinci na Musamman da za'a shirya wa ‘yan Bautar ƙasar a zangon da suke yi na tsawon makonni uku.

Media24

An Saurari Jawabi Na Karshe A Rubuce Game Da Kujerar Gwamnan Jihar Sokoto A Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe.Kotun Saurare...
26/08/2023

An Saurari Jawabi Na Karshe A Rubuce Game Da Kujerar Gwamnan Jihar Sokoto A Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe.

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan jihar Sokoto Ta saurari Jawabi na ƙarshe A Rubuce Game da ƙarar Da Mal Sa'idu Umar na Jam'iyyar PDP ya Shigar kan Gwamna Ahmed Aliyu da Mataimakinsa Idris Gobir.

Mai Shari’a Haruna Mshelia, Ya Saurari Jawabin Kowanne Ɓangare ne A Yau Asabar, Inda ya ƙara da Cewa za'a sanar da Ranar da za'a Yanke Hukunci a Watan Satumba.

Mai Shigar da ƙarar, Mal Umar Na Jam'iyyar PDP Yana kalubalantar Zaɓen Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC Bisa Zargin Rashin Ingantattun Takardun Makaranta Da Kuma magudin zaɓe a Zaɓen Gwamna da aka Gudanar A Ranar 18 Ga Watan Maris.

Lauyan Mal Umar, Aare Akinboro SAN, Ya Buƙaci kotun da ta yi la’akari da shaidun da ke nuna cewa an tabka magudi a zaben da s**a haɗa da tashe-tashen hankula da kuma sabani a cikin takardar Shaidar karatun Ahmed Aliyu.

Lauyan Ahmed Aliyu, Wole Olanipekun SAN, bai Amince da hujjojin Ɓangaren PDP ba, Ya kuma Buƙaci Kotun da ta yi watsi da ƙarar. Yace Aliyu ya Cancanta ya tsaya takara Kuma kuri’un da aka kada masa inganci ne.

Wannan koken dai shine na baya-bayan nan a jerin Kalubalen Shari’a dake fuskantar Sakamakon zaɓen Gwamna na 2023 a Najeriya. A wasu jihohin kuma an shigar da ƙara kan kalubalantar zaɓen Gwamnoni a Kaduna, Kano, da Bauchi Adamawa.

Za'a sanya Ido Sosai kan Sakamakon Waɗannan koke-koke, Domin zasu iya yin tasiri Sosai a fagen Siyasar Najeriya.

Media24

EFCC Da CCB Sun Gayyaci Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci Da Rashawa ta Jihar Kano Kan Kuɗaɗen Hukumar Hukumar Yaki da ...
26/08/2023

EFCC Da CCB Sun Gayyaci Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci Da Rashawa ta Jihar Kano Kan Kuɗaɗen Hukumar

Hukumar Yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da kuma Code of Conduct Bureau (CCB) Sun Gayyaci Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Rimingado, Domin yi masa tambayoyi kan kuɗaɗen Hukumar.

Wasiƙar EFCC Mai ɗauke da kwanan wata 8 ga watan Agusta, 2023, Ta bayyana cewa Hukumar na Gudanar da bincike kan wani lamari da ya zama wajibi a samu wasu karin haske daga ofishin Rimingado.

Wasikar ta bukaci daraktan kudi da asusu na Rimingado ya kai rahoto domin tattaunawa a Ranar 29 ga watan Agusta, 2023, a hedikwatar EFCC dake Abuja. An kuma Buƙaci daraktan ya kawo waɗannan bayanai:

Bayanin jimillar kuɗaɗen da ofishin Akanta Janar na Jihar Kano ya rabawa PCACC Daga Shekarar 2019 Zuwa 2021.

Bayanin jimillar kuɗaɗen da Ma'aikatar Ƙananan Hukumomin Jihar Kano ta rabawa PCACC Daga Shekarar 2019 Zuwa 2021, ciki har da kwangilolin da aka aiwatar da bayanan asusun masu cin gajiyar.

Wasiƙar CCB, mai kwanan wata 16 ga Agusta, 2023, ta Buƙaci Rimingado ya bawa ofishin bayanan kwato, ɓarna, da sarrafa kuɗin PCACC Daga 2016 Zuwa yau.

Binciken da EFCC da CCB keyi na zuwa ne a daidai lokacin da Rimingado ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa daga Tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje. Gwamna Ganduje ya zargi Rimingado da karkatar da kuɗaɗen Hukumar PCACC da kuma yin amfani da Hukumar wajen damfarar abokan hamayyarsa.

Rimingado dai ya musanta Zargin yana mai cewa suna da alaƙa da siyasa. Ya ce ya jajirce wajen yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano, kuma binciken ba zai sa shi yayi kasa a Gwiwa ba.

Ana cigaba da binciken Hukumar EFCC da CCB. Ya Rage a Gani ko za su sami wata shaida ta aikata ba daidai ba Daga Rimingado ko PCACC.

A halin da ake ciki dai, Binciken ya haifar da ayar tambaya Game da ‘yancin cin Gashin kai na PCACC da kuma yadda hukumomin Yaƙi da cin hanci da Rashawa ke Gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a Najeriya.

Media24

Ministan Tsaro, Badaru Abubakar Tare da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, NSA, Nuhu Ribadu da Babban Hafsan tsaro...
26/08/2023

Ministan Tsaro, Badaru Abubakar Tare da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, NSA, Nuhu Ribadu da Babban Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, sun Ziyarci Gwamna Fubara na Jihar Rivers.

Maƙasudin Ziyarar Shine Dakatar da Fasa bututun Mai Ɓarnatar da mai da tashe-tashen hankula a Yankin Neja Delta

Media24

Sabuwar Hanyar da zaka iya samun dollar da pages
26/08/2023

Sabuwar Hanyar da zaka iya samun dollar da pages

HOW TO EARN MONEY WITH FACEBOOK PAGE.

SABUWAR HANYAR DA ZAKA IYA SAYAN DATAR AIRTEL AKAN NAIRA 200 2G
26/08/2023

SABUWAR HANYAR DA ZAKA IYA SAYAN DATAR AIRTEL AKAN NAIRA 200 2G

HOW TO BUY AIRTEL 2GB DATA FOR 200.

Babban Ministan tsaron Najeriya Badaru da karamin Ministan tsaro Bello Matawalle, halarci bikin girmama sojoji 22 da 'ya...
25/08/2023

Babban Ministan tsaron Najeriya Badaru da karamin Ministan tsaro Bello Matawalle, halarci bikin girmama sojoji 22 da 'yan bindiga s**a ka*sha a jihar Niger, tare da jajantawa iyalan su.

📷 Channel Television

Media24

25/08/2023

Ƙungiyar Matasan Jam'iyyar APC Sun Shawarci Bola Tinubu Ya Naɗa Dansa Seyi Tinubu A Mastayin Ministan Matasa

Wasikar da aka ce ta fito Daga ɓangaren matasan jam’iyyar APC na ci gaba da zagayawa, inda ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya naɗa dansa, Seyi Tinubu, a Matsayin Ministan matasa na Gaba.

Wasikar, Wacce ba'a Tantance ba, Tayi ikirarin cewa Seyi Tinubu ne ya fi dacewa da wannan aiki Saboda kwarewarsa da kuma jajircewarsa wajen karfafawa matasa. Har ila yau, sunce zai iya wakiltar muradun matasa a cikin Gwamnati yadda ya kamata.

Karin bayani:👇👇👇

https://medianews.ng/apc-youth-league-advises-bola-tinubu-to-appoint-his-son-seyi-tinubu-as-youth-minister/

DA ƊUMI-ƊUMI Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe dake Jihar Bauchi Ta Sanya Ranar 4 Ga Watan Satumba Domin Yanke Hukunci Kan ...
25/08/2023

DA ƊUMI-ƊUMI Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe dake Jihar Bauchi Ta Sanya Ranar 4 Ga Watan Satumba Domin Yanke Hukunci Kan Shari'ar Kujerar Sanatan Bauchi Ta Arewa

Idan ba'a manta ba dai Sama'ila Dahuwa Kaila Na Jam'iyyar PDP Shine hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta ƙasa INEC Ta Ayyana a Matsayin Wanda Ya lashe Zaɓen

A ɗaya Ɓangaren kuma Siraj Ibrahim Tanko Na Jam'iyyar APC Yana Kalubalentar Nasarar Sa A Kotu Inda Lauyoyin sa S**a bayyana cewa An tafka Aringizon Kuriu A lokacin da aka Gudanar da Zaɓen A Ranar 25 Ga Watan March.

Media24

ILIMI KOGÍ: Miji Ya Gaishe Da Matarsa Sunnah Ce, Ya Jira Ta Zo Ta Gaishe Shi Kuma, Al'ada Ce Ta Malam Bahaushe, Cewar Sh...
25/08/2023

ILIMI KOGÍ: Miji Ya Gaishe Da Matarsa Sunnah Ce, Ya Jira Ta Zo Ta Gaishe Shi Kuma, Al'ada Ce Ta Malam Bahaushe, Cewar Sheik Aminu Daurawa.

Media24

Mataimakin Kakakin Majalisa Kalu Yayi Nasara A Kotu.Kotun Sauraren Ƙararrakin zaɓe dake zama a Umuahia, Jihar Abia, Ta T...
25/08/2023

Mataimakin Kakakin Majalisa Kalu Yayi Nasara A Kotu.

Kotun Sauraren Ƙararrakin zaɓe dake zama a Umuahia, Jihar Abia, Ta Tabbatar da Nasarar Zaɓen Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu.

Kotun dai tayi fatali da ƙarar da Ɗan Takarar jam’iyyar Action Alliance (AA) Ifeanyi Igbokwe ya Shigar, Wanda ya kalubalanci Nasarar Kalu

Karin bayani:👇👇👇

https://medianews.ng/deputy-speaker-of-parliament-kalu-wins-in-court/

Media24

Mataimakin Kakakin Majalisa Kalu Yayi Nasara A Kotu.Kotun Sauraren Ƙararrakin zaɓe dake zama a Umuahia, Jihar Abia, Ta T...
25/08/2023

Mataimakin Kakakin Majalisa Kalu Yayi Nasara A Kotu.

Kotun Sauraren Ƙararrakin zaɓe dake zama a Umuahia, Jihar Abia, Ta Tabbatar da Nasarar Zaɓen Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu.

Kotun dai tayi fatali da ƙarar da Ɗan Takarar jam’iyyar Action Alliance (AA) Ifeanyi Igbokwe ya Shigar, Wanda ya kalubalanci Nasarar Kalu

Karin bayani:👇👇👇

The Electoral Appeals Court sitting in Umuahia, Abia State, has upheld the election of the Deputy Speaker of the House of Representatives, Rt. Horn. Benjamin

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Media 24 News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Nearby media companies



You may also like