20/02/2022
Tsautsayi ne ya sa na dawo siyasar Kano -- Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce tsautsayi ne ya sanya ya dawo ya ci gaba da yin siyasa a matakin jiha.
Kwankwaso, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattijai da ga 2015 zuwa 2019, ya baiyana hakan ne a wata hira da gidan Rediyon Nasara Radio 98.5 FM a Kano, a cikin wani shiri mai taken "Aƙida ta Gaskiya", a jiya Asabar da daddare.
A cewar Kwankwaso, shi a zatonsa ya bar sanya hannu a cikin siyasar cikin gida Kano, sai dai a matakin ƙasa Nijeriya, amma sai wasu abubuwa su ka tilasta masa ya dawo cikin harkokin siyasa a jihar.
Kwankwaso ya ƙara da cewa tuni shi a lissafin sa ya bar harkar siyasar jiha, inda ya ƙara da cewa, kuskuren da a ka samu a 2015, waɗanda a ka baiwa ragamar mulki a jihar, ba su iya ba, ba su san inda su ka sa gaba ba a siyasa, shi ne ya dawo domin ya kawo gyara da saita al'amura.
A cewar sa, shi da matsayin da ya ɗauka a siyasar Kano shi ne bada shawara, inda ya ƙara da cewa a da ya zaci komai zai yi daidai a siyasar jihar inda sai dai kawai ya shigo jihar domin zumunci da ƴan uwa da abokan arziki ba wai don siyasa ba.
"Tuni mu a lissafin mu mun bar siyasar jiha, amma kuskure da a ka samu shine, waɗanda mu ka sa, ba su gane ba, ba su iya ba, ba su kuma san ina ne gabas ina ne yamma ba a harkar siyasa.
"Su ka zo su ka damalmala kansu, su ka damalmala tsarin mu su ka yi ta abubuwa wanda dole sai mun zo an saita.
"Irin haka ne ya sanya mu ka dawo mu ke so mu samar da shugabanni tsayaiyu, waɗanda su ka gane kuma za su iya su ka runduna.
"Runduna, kowa ya gane cewa wannan tsari namu na taimakawa al'umma da yin mulki bisa adalci. A tabbatar da cewa ya yi laifi an hukunta shi, wanda yayi mai kyau an yana masa.," in ji Kwankwaso.