10/09/2024
Wani Matashi Mai Fasahar Ƙere-Ƙere Ya Ja Hankalin Al'umma A Kafofin Sa Da Zumunta.
Daga Kamalacy Malumfashi.
Ibrahim Muhammad Sallama, matashin yaro ne mai shekara 20 mazaunin unguwar Fayamasa dake cikin ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Allah ya yi masa wannan baiwa ta fasahar ƙera ababe kala-kala musamman waɗan da su ka shafi ababen hawa, kamar irin manyan motoci jirajen sama, mashina, da makamantansu.
Wanne irin fata kuke yiwa matashin?
📸 Ɗan Hausa