26/01/2025
SERAP Ta Maka Gwamnatin Tarayya da NCC A Kotu Kan Ƙarin Kuɗin Waya
Daga Yasir Kallah
Kungiyar SERAP, mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta maka gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya, NCC, a kotu kan ƙarin kashi 50 cikin ɗari na cajin waya, saƙon tes, da data a Nijeriya, inda ta yi zargin cewa ƙarin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar, da tsarin doka, kuma babu hankali da adalci a ciki.
A kwanakin nan ne hukumar NCC ta amince da ƙarin kuɗin, wanda ya ɗaga cajin minti ɗaya na waya daga ₦11 zuwa ₦16.5, farashin data 1GB daga ₦287.5 zuwa ₦431.25, sannan saƙon tes na SMS daga ₦4 zuwa ₦6.
Ƙarin kuɗin ya jawo ce-ce-ku-ce da s**a mai yawa ga hukumar NCC ɗin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ita ma ƙungiyar SERAP ta ruga kotu domin a dakatar da ƙarin.
A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/111/2025 wadda ta shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya, SERAP ta koka a kan ƙarin kuɗin ya keta haƙƙin al'umma na ƴancin magana da samun bayanai k**ar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin duniya s**a ƙunsa.
SERAP ɗin ta roƙi kotun da ta bayyana cewa ƙarin kuɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin duniya na ƴancin ɗan'adam, sannan ta dakatar da aiwatar da ƙarin tare da soke shi baki ɗaya.