Al-Ihsan TV

Al-Ihsan TV Mun himmatu wajen kawo muku shirye-shirye da labarai da damiduminsu

27/11/2022

PREMIER HORSE RACING TORNAMENT 2023 SEASON BIRNIN KEBBI

25/11/2022

BIRNIN KEBBI TOURNAMENT

13/11/2022

Zamu fara tona asirin Annamiman cikin gwamnatinmu idan basu dena ba inji Dr Nasiru Yusuf Gawuna

07/11/2022

Alasan Ado Doguwa ya nemi afuwar jama'ar jahar Kano kan abun da ya faru tsakaninsa da dan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo

Doguwa: I remain APC, I will be in APC for lifeHe said those alleging he was set to defect from the party were peddling ...
06/11/2022

Doguwa: I remain APC, I will be in APC for life

He said those alleging he was set to defect from the party were peddling what he called “catastrophic fake news”.

Ado Doguwa who represents Doguwa/Tudun Wada Federal Constituency of Kano State in the House of Representatives spoke when he paid a solidarity visit to the APC Presidential Candidate, Asiwaju Bola Tinubu, in Abuja on Sunday.

The House Majority Leader visited Tinubu in company with the state House of Assembly member and the two local government chairmen from his constituency as well as other prominent leaders from the state.

Assuring Asiwaju Tinubu of his support and the fact that he remains in the APC, he said Kano State Governor Abdullahi Umar Ganduje is in safe hands.

He said “ÄPC remains my party, my destiny. I’m not leaving the party for any other. I remain in the APC because victory is for the party.

“I also believe we have a presidential candidate in Asiwaju Tinubu who has the sagacity, capacity and experience to turn around the economy, the fortune of the country, the same way he did in Lagos. I believe that under Tinubu, Nigeria will do well in the comity of nations.

“Kano is under the able leadership of Governor Ganduje who I call an engineer because the wonderful things he has done in the state and the way he has turned Kano to a model. He has improved on and created additional infrastructure. Ganduje is everything to us in Kano.

“With Governor Ganduje leading the charge, we will deliver the state to APC, to Asiwaju Tinubu. We have done this before in Kano State. During the cancelled 1993 election, we voted for the MKO Abiola/Babagana Kingibe of the then SDP against the candidature of our son, late Alhaji Bashir Tofa, of the defunct NRC. Tofa was not just a Kano man, he was an eminent statesman. Kano votes on the basis of ideology. History will repeat itself again Kano. Mark my words.”

Asiwaju Tinubu thanked Ado Doguwa for the visit, promising to stand by him and the people of the state for their support.

He recalled that he had come a long way with Ado Doguwa, from their days in the 1992 National Assembly, he in the Senate and Doguwa in the House of Representatives, describing the House Majority Leader his son and a dependable ally.

Tinubu Media Office,

Tunde Rahman.

November 06, 2022

Ba a ayyana Ganduje cikin rahoton EFCC ba, gwamnatin Kano tayi s**a, ta ce nemi Sahara Reporters ta nemi afuwartaGwamnat...
06/11/2022

Ba a ayyana Ganduje cikin rahoton EFCC ba, gwamnatin Kano tayi s**a, ta ce nemi Sahara Reporters ta nemi afuwarta

Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah wadai da kakkausan kalamai da wata kafar yada labarai ta intanet, Sahara Reporters ta yi na cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cikin uku. Gwamnonin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta sanyawa hannu a kan cewa sun yi awon gaba da kudade a gidajensu.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar ya nuna cewa, yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ba ta ambaci sunan su ba. Gwamnonin, Sahara Reporters sun ci gaba da yin irin wannan zancen na karya.

Ya ce rahoton da ba shi da tushe don labarin bincike, ko dai hasashe ne na mawallafa ko kuma wani yunkuri na bata sunan gwamna da gangan.

Malam Garba ya yi nuni da cewa Gwamna Ganduje bai samu biliyoyin Naira da aka boye a cikin kudaden da za a yi amfani da su wajen shiga tsaka mai wuya na biyan albashin ma’aikata ba.

Kwamishinan ya kara da cewa jihar Kano na daya daga cikin jahohin tarayya da suke biyan albashin ma'aikatanta a koda yaushe, ba kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta fitar ba, yace an fara biyan albashin ma’aikata tun tuni

Don haka ya yi kira da a janye labarin ba tare da bata lokaci ba, wanda gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari'a.

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya yiwa mahaifiyar dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar Kano a karkashin jami...
05/11/2022

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya yiwa mahaifiyar dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar Kano a karkashin jamiyyar NNPP, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, Hajiya Rabi Abdullahi rasuwa .

Za'ayi mata sallah a masallacin Alfurqan dake Alu Avenue Nasarawa GRA da misalin karfe 4 na yamma.

Allah yajiqanta da rahama yasa aljanna makoma, Ameen.

Dr. Hamisu Sadi Ali,
Kano State NNPP Secretary

05/11/2022

"Ubangiji Allah kar Ka jarrabeni da lokacin da Ganduje zai ce da ni bari, na ki bari" Alasan Ado Doguwa

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya ya mayar da kwamishinan yan sandan Kano Jahar Ebonyi bisa zargin ayyukan cin hanciD...
04/11/2022

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya ya mayar da kwamishinan yan sandan Kano Jahar Ebonyi bisa zargin ayyukan cin hanci

Daily Nigeria

04/11/2022

Alasan Ado Doguwa ke ganawa da magoya bayansa

04/11/2022

Alasan Ado Doguwa ke gudanar da taro yanzu haka da magoya bayansa

Kar ku bari Kwankwasiyya su yi amfani da karamin rikicin mu, APC ta Kano ta gargadi mambobintaJam’iyyar APC a jihar Kano...
03/11/2022

Kar ku bari Kwankwasiyya su yi amfani da karamin rikicin mu, APC ta Kano ta gargadi mambobinta

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta zargi ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta New Nigeria People’s Party (NNPP) Kwankwasiyya da yin amfani da wata ‘yar rashin jituwa a jam’iyyar APC mai mulki domin haifar da rashin jituwa.

Ta ce yayin da dattawan jam’iyyar s**a sasanta rikicin cikin ruwan sanyi, ‘yan Kwankwasiyya da ke tsoratar da karfin jam’iyyar APC a jihar suna ta yada farfaganda don shawo kan lamarin yadda ya kamata.

Sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba wanda ya kasance kakakin yakin neman zaben Gawuna/Garo ya fitar a yau Alhamis

Ya ce akwai sahihan bayanai da ke nuna cewa kungiyar har ta kai ga lalata fastoci da sunayen wasu jam’iyya, ta yin amfani da lamarin da aka riga aka warware shi a matsayin shan taba da sunan jam’iyyun da ke da sabani a cikin jam’iyyar APC.

Malam Garba ya yi nuni da cewa a ‘yan kwanakin da s**a gabata ‘yan Kwankwasiyya sun yi ta raba hotuna tare da ba su ma’ana mara kyau a kokarinsu na bata sunan jam’iyya mai mulki a jihar.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, duk da cewa jam’iyyar tana da hakkin samun kasonta na rashin jituwar cikin jam’iyyar da ya zama ruwan dare a dukkan jam’iyyu, bai kamata a bar ‘yan adawa su yi amfani da su wajen kara haifar da fitina ga jam’iyyar ba.

Ya ce a yayin da al’ummar kasar nan ke tunkarar shekarar zabe, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, suna son ‘ya’yan jam’iyyar su dage da tabbatar da hadin kan ta don ci gaba da tafiya a kan turbar da ake ganin za ta iya kaiwa ga nasara a dukkan matakai.

A yau ne Laraba Jagororin Jam'iyar APC daga yankin Karamar Hukumar Doguwa, s**a ziyarci Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ku...
02/11/2022

A yau ne Laraba Jagororin Jam'iyar APC daga yankin Karamar Hukumar Doguwa, s**a ziyarci Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar Gwamna a Jam'iyar APC Dr.Nasiru Yusuf Gawuna a gidansa don bashi hakuri dangane da al'amarin da ya faru yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar.

📷Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

30/10/2022

Unveiling of Premier Horse Racing Campany

30/10/2022

Taron Kamfanin Sukuwar Dawaki na Premier Horse Racing dake gudana yanzu a jahar Kano

30/10/2022

Taron Kamfanin Sukuwar Dawaki na Premier Horse Racing

Ɗan Chinan nan da ake zargi da kisan tsohuwar budurwasa mai suna Ummukhulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita a J...
27/10/2022

Ɗan Chinan nan da ake zargi da kisan tsohuwar budurwasa mai suna Ummukhulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita a Jihar Kano, ya musanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotu.

26/10/2022

Three Osinbajo Support groups under the leadership of Alwan Hassan, endorsed endorsed Asiwaju Bola Ahmed Tinubu as their Presidential candidate

22/10/2022

Zuwan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bude ofishin yakin neman zaben Gawuna/Garo

17/10/2022

Wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne, sun farwa magoya bayan Jam'iyyar a yayin da ake tsaka da gudanar da taron dan takarar Shugaban Kasa na Atiku Abubakar a jahar

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin sakin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.A ranar Alhamis ko...
13/10/2022

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin sakin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

A ranar Alhamis kotun daukaka kara ta wanke Nnamdi Kanu daga laifin da gwamanti ke zargin sa na tayar da zauna tsaye da ta’addanci da kuma jagorantar haramtacciyar kungiya.

Lauyansa, Ifeanyi Ejiofor ya sanar ta shafinsa na Facebook cewa, “Mun yi nasara, Kotun Daukaka Kara ta wanke ta kuma saki Nnamdi Kani.”

A ranar 23 ga Disamba, 2015 aka fara gurfanar da shi gaban kotu, kafin daga bisani kotu ta bayar da belinsa a ranar 25 ga watan Afrilu, 2017.

Daga baya ya saba sharadin belin nasa, ya ki zuwa halartar zaman kotu, kafin daga bisani jami’an tsaro su taso keyarsa daga kasar waje.

A lokacin da yake zaune a kasar waje, gwamnati ta zarge shi da tunzura mutane a Nejeriya su dauki doka a hannunsu

AMINIYA

Yau litinin a garin kofa Hon Abdulmumin jibrin kofa ya kaddamar da takarar sa Dan majalissar tarayya wanda zai wakilci y...
11/10/2022

Yau litinin a garin kofa Hon Abdulmumin jibrin kofa ya kaddamar da takarar sa Dan majalissar tarayya wanda zai wakilci yakin kiru da bebeji a zabe mai zuwa 2023 taron wanda ya samu halartar dubban jama'ar yakin kiru da bebeji kuma aka gudanar a gidan sa dake garin kofa karamar hukumar bebeji.

Yayin taron dai kofa yayi amfani da wannan damar wajen karbar mutane sama da dubu biyu wadanda s**a dawo jam'iyyar NNPP kwansiyyya kuma sakayi alakwarin aiki tukuru wajen bawa Dan takarar shugabancin kasar karkashin tutur NNPP Engr dakta Rabiu musa kwankwaso kuri'a miliyan biyar da kuma ganin jam'iyyar tayi nasara tun daga sama har kasa.

Taron ya samu halartar yan takarar majalissar jiha Kiru Hon Abubakar Usman Rabula Dana Bebeji Hon Ali Muhammed Tiga Hajiya azumi namadi bebeji, hon gambu sallau, dankaka usaini bebeji shugabannin jam'iyyar NNPP na KIRU DA bebeji dattawan jam'iyyar matasa da mata da sauran Al'ummar yankin na KIRU DA bebeji wadanda s**a fito kwansu da kwarkwata domin hallatar wannan taron.

Jigo a jam’iyyar   ta kasa, kuma mukusancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Professor Yemi Osinbajo , Alhaji Alwan Has...
09/10/2022

Jigo a jam’iyyar ta kasa, kuma mukusancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Professor Yemi Osinbajo , Alhaji Alwan Hassan, ya gana da kungiyoyin matasa maza da mata daban-daban dake fadin jahar Kano, a kokarin da yake yi wajen inganta rayuwarsu da kuma yada manufar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Tinubu da dan takarar gwamnan Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da ma sauran 'yan takara na jam’iyyar dake jahar Kano baki daya

Dan majalisar tarayya Mai wakiltar yankin karamar hukumar Nassarawa, Alhaji Nasir Ali Ahmed da hadin gwiwar mataimakin s...
09/10/2022

Dan majalisar tarayya Mai wakiltar yankin karamar hukumar Nassarawa, Alhaji Nasir Ali Ahmed da hadin gwiwar mataimakin shugaban karamar hukumar Danbatta, Nasiru Bello Danbatta, sun dauki nauyin gyarawa mutane fiye da 200 hakoransu 👇👇👇

Maiakatar ayyuka ta tarayya ta fara gyaran gadar Ado Bayero dake birnin Kano.Da yake duba aikin, babban jami’in ofishin ...
09/10/2022

Maiakatar ayyuka ta tarayya ta fara gyaran gadar Ado Bayero dake birnin Kano.

Da yake duba aikin, babban jami’in ofishin ma'aikatar na Kano, Injiniya Yahaya Baba Ali, yace ana sa ran kammala aikin nan da wata biyu masu zuwa.

Ya yi karin haske kamar haka 👇👇

An fara gyaran gadar Ado Bayero dake birnin Kano

Gwamnatin Najeriya ta amince da yi wa Kungiyar ASUU kishiya.Ministan kwadago da samar da aikin yi na Najeriya, Chris Ngi...
04/10/2022

Gwamnatin Najeriya ta amince da yi wa Kungiyar ASUU kishiya.

Ministan kwadago da samar da aikin yi na Najeriya, Chris Ngige ya ba da takardar shaida ga kungiyar ma'aikatan koyarwa a jami'o'in Najeriya, wadda kungiya ce ta malaman jami'o'in tarayya da na jihohi.

Kungiyar mai suna CONUA a takaice ana ganin kai tsaye za ta kasance kishiya ga babbar kungiyar malaman jami'o'in Najeriya wato ASUU.

Wani jami'in gwamnatin Najeriya ya wallafa cewa an kafa kungiyar CONUA ne a shekara ta 2018 a jami'ar jihar Osun.

Kungiyar ASUU da gwamnatin Najeriya na kai ruwa rana saboda yajin aikin sai-baba-ta-gani da malaman jami'o'in s**a shiga tsawon wata takwas ke nan yanzu, suna neman sai lallai gwamnati ta biya musu bukatunsu.

Duk da wani kokari da ban-baki da tattaunawa daga gwamnati sun kasa shawo kan kungiyar malaman kungiyar ASUU dakatar da yajin aiki.

Baya ga kungiyar CONUA, ministan kwadagon ya kuma amince da kungiyar likitoci masu koyarwa ta kasa (NAMDA)

BBC

Address

Maiduguri Road, ARTV Building
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Ihsan TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Al-Ihsan TV:

Videos

Share

Nearby media companies