Engineer lawi technology

Engineer lawi technology Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Engineer lawi technology, Digital creator, Kano.

17/12/2023

Nima nabi sahun su Dr salisu abdulrazak sahell inayin mining na Avive, idan kashirya a samu wannan Alkhairin dakai kaima a duniyar crypto zaka iya bin wannan link din dake kasa kayi register..👇

https://m.avive.world/register/?vcode=s7quzk

Ba kudi zaka saka ba, kawai bude data zakayi kayi mining, kullun ka bude kayi Claiming wanda baifi second 10 ba kayi kagama, a haka zaka tara abinda zai baka mamaki, ana launching nasa, zakaga abun k**ar mafarki..

Allah ya bada sa'a..

19/11/2023

Na ɗauki tsawon lokaci ina bincike game da kamfanonin da ake siyar Data, amma har yanzu ban yi nasarar samo kamfanin da ake siyar da Data mai rahusa a farashi mai sauƙi ba sama da kamfanin Salfat Data ba.

Za ku iya Rigister da Kamfanin Salfat Data ta wannan link da ke ƙasa domin cin moriyar Data a farashi mai sauƙi👇👇

https://salfat.com.ng/user/signup?ref=engrlawi

Sannan bayan ka yi Rijista ta wannan link da ke sama🖕nan take za ka iya garzayawa playstore domin sauke shi a wayarka.

Dr Salisu Abdurrazak Saheel Muna godia kwarai da wannan damar aka bawa al'uma

26/10/2023

Idan kasamu matsala na transactions na kudi a mobile banking irinsu OPay, Palmpay da sauransu kuma babu branch nasu a inda kake kuma duk wata hanya da ake tuntubarsu kabi amma kudinka sunki dawowa, zaka iya tura sakon korafi zuwa CBN tunda sune s**a basu License har ka amince kayi amfani dasu...

Zaka rubuta takardar complain mai kyau da turanci mai kyau, kodai kaje branch na CBN dake garinku ka mika takardar ko kuma katura masu ta email.

Ga email dinsu: [email protected]

Ga sample na yadda zaka rubuta takardar da kyau, amma zaka gyara takardar ka rubuta irin matsalar dakai ka fuskanta da bankin da kuma bayyana masu sunan bankin a cikin letter din, ka tabbata kuma kayi addressing duk wata matsala da ka fuskanta daga bankin kuma kayi Attaching screenshort ko takarda na hujjojinka ko transaction records.👇

Subject: Urgent Complaint Regarding Problem With A Funds Transfer and Lack of Support from Mobile Banking Services.

Date: ...........

The Director,
Consumer Protection Department,
Central Bank of Nigeria,
Abuja, Nigeria.

Dear Sir/Madam,

I am writing to bring to your attention a concerning issue that has arisen due to the lack of physical branches and effective customer support from certain licensed mobile banking services in the country. Recently, I encountered a significant problem with a fund transfer that was mistakenly sent to the wrong recipient. Despite my attempts to rectify the situation through their customer service hotline, I have been unable to secure any meaningful assistance or support.

This unfortunate experience has left me with substantial financial losses and a growing sense of frustration as the mobile banking service in question lacks the necessary infrastructure to address customer concerns promptly.

I believe that as the regulatory authority overseeing these mobile banking services, your esteemed office can help ensure that customers are not left vulnerable to such situations. It is essential that appropriate measures are implemented to safeguard the interests of customers and facilitate a swift resolution of issues arising from fund transfers and potential security breaches.

I kindly request your prompt intervention in this matter to help resolve the situation and prevent similar occurrences for other customers. Your swift action in addressing this issue will undoubtedly restore confidence in the country's mobile banking services.

Thank you for your attention to this urgent matter.

Yours faithfully,

[Sunanka]
[Email, Phone Number]

Allah Yataimaka..

©Salisu Abdurrazak Saheel

22/10/2023

Internet baiwar Allah ta bakin Malam Albani zaria (Allah ya gafarta mashi)..

Yanzu misali kanaso kayi waya da abokinka da yake zaune jahar kano, kai kuma kana zaune kaduna, daga lokacin da ka danna lambar wayarsa ka kuma danna alamar kira, daga wannan lokacin wayarka zata tura signal zuwa ga network provider naka (MTN, Airtel, 9mobile ko Glo) ko wane kalan layi kake amfani dashi, wannan signal din zata sanar da network provider naka cewa kanaso kayi magana da abokinka, sai network providers naka su fara kokarin ganin sun hadaka dashi ta hanya mai kyau, daga wannan lokacin wayar abokinka zatayi Ringing, yana picking kafin kuji muryar juna sai wayar shi itama ta tura ma Network provider da yake amfani dasu cewa ka kira shi yanaso yayi picking.

Wadannan Signals din da suke zuwa wurin Network Providers domin sanar dasu cewa kunason zakuyi waya da juna suna kai wannan sakon ne ta hanyar Network Infrastructure irinsu cell towers da cables.

Daganan sai network provider su tura maku signal na amincewar kuyi magana da junanku kuji muryoyin juna.

Duka wannan process din yana faruwa ne very quickly, da matikar sauri, wannan fasahar itace ake kira da telecommunications, wanda a cikin wannan fasahar akwai abubuwa masu tarin yawa na ban mamaki.

Allah ya kara mana ilimi mai amfani..🙏

©(Dr) Salisu Abdurrazak Saheel

21/10/2023

Abubuwan da za'a iyayi da BVN naka idan wani ya samu..

Kamar yadda muka sani Bank Verification Number wato BVN, lambobi ne guda 11 da suke amfani wurin Identification a bankunan mu a Nigeria, domin tabbatar da asalin mai amfani da asusun banki.

Kamar yadda nasha fada cewa samun BVN naka kadai bazai wadatar ba wurin yi maka kutse a asusun ajiyarka ba, sai dai akwai wasu abubuwa da za'a iyayi dashi idan wani ya sansu.

1. Identity Verification: Bankuna da sauran financial institutions zasu iya amfani da BVN naka wurin verifying na identity naka domin tabbatar da wanda suke hulda dashi ko zasuyi hulda dashi musamman idan ka cike wani form na neman bashi ko domin yin wani transactions.

2. Account Linking: da BVN dinka wani zai iya amfani dashi wurin hadashi da asusun bankuna da yawa, amma wannan yana matikar wahala idan ba mutum yakai babban kwaro ba, kuma duk da haka sai da amincewar bankuna.

3. Fraudulent Activities: a wani bangaren kuma za'a iya samun wasu bata gari da zasu iya amfani da BVN naka wurin gudanar da ayyuka mararsa kyau wurin saka BVN dinka a matsayin Identity nasu ko yin yunkurin kutsawa a wani wuri tareda amfani da BVN naka. Amma duk da haka bankuna sunada tsaro sosai a wannan bangaren, shiyasa ba yadda za'ayi ayi maka sata da BVN naka batareda sanin banki ba.

Allah ya kyauta..🙏

©(Dr) Salisu Abdurrazak Saheel

19/10/2023

Kunshirya dora asusu guda biyu akan Whatsapp daya

12/10/2023

New MTN CHEAT

==> *567*3*8 #
za'a cirema 50 naira
zasu baka kira na sati guda, kullum zakai
minti 9,
har satin ya cika.
==> *567*3*7 #
za'a cirema 75 naira
zasu baka kyautar kira
na sati guda, kullum minti 15
har satin ya cika.
==> *567*3*6 #
za'a cire ma 100 naira,
zasu baka kyautar kira
na sati guda, kullum minti 30
har satin ya cika.
==> *567*3*5*2 #
za'a cire maka 200 naira
zasu baka kyautar kira ta sati
guda
kullum 2 hours, har satin ya cika
==> *567*3*5*1 #
wannan na kwana dayane,
za'a cirema 40 naira
su baka kyautar kira
ta 2hours a ranar.
==> *567*3*4*2 #
za'a cire ma 250
zasu baka kyautar kira
ta sati guda, unlimited
ba iyaka, har satin ya kare.
==> *567*3*4*1 #
wannan shima na kwana dayane
za'a cirema 50 naira,
za'a baka kyautar kira na ranar ba iyaka.
==> *567*3*16*2*1 #
za'a cire ma 500 naira zasu baka
500MB na kwana 30. lawi But ba kowanne layine yake yi ba

27/09/2023

Ilimin Hacking (Kutse)
Gare ku masu son zama hackers.
Kamar yadda nake fada maku shima fa hacking
ilimi ne wanda sai ka koya zaka iya, bawai cika
baki da hacking din Facebook account din mutane
shine hacking ba, wannan kawai dai kana trying
amma ba shine ainahin duniyar hacking ba.
Bari kuji; idan kanaso ka zama shahararren
hacker to fa sai ka tsunduma wajen karantar
bangaren dan'uwa, kuma idan ka koya ka iya to
ya zama hanyar da zaka dinga taimakon
Addininka, basai na maku dogon bayani ba
kungane abinda nake nufi.
Wato kwarewa a hacking yana buqatar ka maida
hankali bangaren koyon wadannan abubuwan da
zan lissafo guda 10 yanzu in sha Allah, wadanda
idan ka iya su to lallai ka tabbata shahararren
hacker.
1. Intermediate Computer Skills; wato yanada
kyau ace ka iya kirkirar Word documents ko kuma
kana iya surf din web, sannan dole ya kasance
kasan yadda zaka dinga amfani da mabanbantan
Commands Lines na Windows, ka iya seta
network, sannan ka iya Editing din Registry din
Computer dinka.
2. Good Networking Skills; wato yawancin
hackers sunfi yin ta'adi a Online sunfi yin barna a
saman yanar gizo dan haka dole ka koyi ilimin
Networking da Terms dinsa k**ar irinsu;
• WEP versus WPS password
• NAT
• MAC Addresses
• Routers
• Ports
• VPN
• IPv6
• DNS
• Subnetting
• DHCP
• Private and public IPs
• Ipv4
• OSI Modelling
• Packets
• TCP/IP
3. Using a Linux operating system; yawancin
hackers sunfi amfani da "Linux OS" saboda tana
barin programs da tweaks a windows da kuma
Mac operating system. Yawancin hacking tools
din sunfi aiki acikin wannan operating system din.
4. Virtualization; kafin ka fara qoqarin yin hacking
farko kafara sanin menene zakayi kuma ka
tabbatar komai kanayin shi akan tsari batareda
kuskure ba, kwararren hacker baya barin kuskuren
da za'a k**ashi, idan kasamu kwarewa kanaso
ka jaraba baiwar naka to karka ce zaka fara da
babban aiki, kafara jarabar Hacking dinka ga
qaramin abu haka, k**ar "Virtualization Software
package" k**ar irinsu; VMWare Workstation.
Wajen amfani da Virtual Workstation hakan zai
baka damar kayi gwajin fikirarka ta hacking
batareda wani hadari ma kuma batareda ka jawo
wa computer dinka wata matsalar ba ko lalace
wa, sbd idan kana koyo kace zakayi hacking din
wani abun bayan baka kware ba to Ido zai raina
fata domin kana iya lalata computer dinka.
5. Tcdump or Wireshark; shi dai Tcdump anfi
saninsa da Command Line Protocol analyser ko
kuma kace Sniffer duk sunansa ne Tool ne na
hacking mai dan bala'in sata. Shi kuma Wireshark
yawanci mutane sunsan shi shima aikinshi iri
daya da Tcdump.
6. Knowledge of security Technologies and
concepts; lallai duk hacker yanada buqatar mafi
muhimmanci acikin Concept and technologies
wanda yake da alaqa da information technology.
Saboda haka yanada kyau kasan Wireless
Technology And Concepts irinsu; "Secure Sockets
Layer" (SSL) Firewalls, Intrusion Detection
System (IDS), Public Key Infrastructure (PK) da
sauransu.
7. Scripting Skills; kasamu damar iya kirkira da
editing din Scripts hakan zai baka damar ka iya
kirkirar naka Tool din, ta yadda zaka zama
Independent! Kana harkarka ba ruwanka da
amfani da tools din wasu, zaka kirkiri kayan aikin
da ba kowa yasanta ba kayi amfani da abinka
wurin kai hari, to idan kanaso ka kware wajen
hakan dole ka maida hankali wajen karantar
Scripting language k**ar irinsu; Ruby on rails, ko
kuma Python.
8. Database Skills; idan kanason kasan yadda
hackers suke kutse su fada cikin rumbun adaba
bayanan mutane ko kuma kanaso ka iya hakan to
yanada kyau kasan shi yaya ma database din
take aiki da sauransu, dan haka yanada kyau ka
samu kwarewa a "Database management system"
k**ar irinsu; Oracle, ko MySQL.
9. Reverse Engineering; shi wannan zai baka
damar ka iya converting piece na malware ko
kuma mai k**a da Exploit into more advanced
hacking tool.
Daga lokacin da ka fahimci yadda "malware da
exploit features suke aiki to tabbas kasamu
damar gane yadda ake cikakken hacking din
computer.
10. Cryptography; wannan skill din yana baka
damar kasan yadda hacker suke samun damar
boye kansu idan zasuyi barna ko ta'asa a wani
wuri to zaka iya gane yadda suke batar da sawu
kaima kuma zaka iya koya, sannan zai baka
damar gane mabanbantan weakness algorithm
wadanda ake amfani dasu wajen Decrypting
Personal information k**ar irinsu; Stored
Password.
Allah ya tsare mu da shairinsu lawi

20/09/2023

Follow the Engineer Lawi Technology channel on WhatsApp:

10/09/2023

Idan Scammers ko Hac-kers s**a mallaki Account Number naka akwai wasu hanyoyi guda 4 da zasu iya bi wurin yunƙurin kwashe maka kuɗi:

1. Social engineering attempts: Ta wannan hanyar hac-ker zai iya amfani da Account number naka wurin ƙoƙarin samun information naka daga wurinka ko daga wurin wasu makusantanka, misali: za iya kiranka a waya ya karanto maka Account Number naka daga farko har ƙarshe, sannan yace maka daga bankinka yake, dan haka yana buƙatar login credentials naka da wasu personal details, da duk wasu sensitive information naka na banki, da niyar cewa za'ayi maka wani gyara ne, kai kuma saboda ya karanto account number naka hakan sai yasa ka amince dashi kuma katura mashi.

Kai tsaye zaiyi amfani da wannan damar ya kwashe komai acikin asusun naka.

Note: Duk wanda ya kiraka a waya ya karanto maka Account Number naka yace maka ka bashi wani Login credentials naka, ka kashe wayarka kawai. idan banki s**a kiraka ce maka zasuyi kaje banki ayi maka duk abinda za'ayi maka acen.

2. Phishing attacks: Idan Hac-ker ya mallaki account number naka, zai iya amfani da wannan damar musamman idan yanada Email naka ko Phone number sai ya tura maka phishing emails ko message mai ɗauke da malicious links wanda kana danna shi zai kaika fake websites nashi mai k**a da Exactly irin bankin da ka buɗe, yace maka ka cike personal information naka na banki zaka samu kyautar 100k daga banki.
kana sakawa shikenan bayananka zasu tafi kai tsaye zuwa gareshi zai iya kwashe ko nawa ne a account naka.

Note: Duk wani Email da za'a turo maka tareda wani Links ka tsaya ka natsu sosai ka duba kaga wanene sender ɗin, kuma ka tabbatar address ɗin na gaske ne.

3. Account verification attempts: Akwai websites ɗin da ake amfani da account number wurin yin verification process na canza information naka na banki, hac-ker zai iya canza password naka da sauran details naka ta waɗannan websites ɗin ta hanyar contacting customer service na bankin naka su kuma zasuyi duk abinda hac-ker ɗin ya buƙace su suyi domin duk a tunaninsu kaine.

Note: Karka biyo ni Inbox kace na faɗa maka Websites ɗin koda wasa bazan faɗa ba.
a kula sosai a duk sanda aka turo maka wani Verification code karka sake wani ya kiraka yace katura mashi.

4. Limited financial transactions: Idan Hac-ker ya samu Account Number naka da kuma wasu information naka irinsu sunanka, address naka, phone number, Sim ɗinka, da BVN, to hac-ker zai iyayin yunƙurin yin Transaction na kuɗi daga bankinka wurin yin siyayya a online, transfer na kuɗi zuwa wani account daban da saka katin waya.

Note: Mu kiyaye sensitive information namu ba kowa zaka bari yasan information naka na banki ba saboda tsaro.

A ƙarshe ina cewa, waɗannan hanyoyin guda 4 sune kaɗai hanyoyin da nasani da hac-ker zai iyayi yunƙurin kwashe maka kuɗi kuma ba lallai yayi nasara ba sai ya samu cikakken goyon bayanka, ko kuma cikakken sakakinka, Mu kula sosai mu dinga sanya strong password, unique passwords, da sanya tsarin two-factor authentication ga accounts namu domin tsare kawunanmu daga faɗawa hannun azzalumai..

Ayi sharing ma sauran yan'uwa..

Allah Yataimaka..🙏

©Salisu Abdurrazak Saheel

30/08/2023

Yadda Wasu Manyan Kamfanunuwan Duniya Suke Mana BasajaShin ko kasan cewa Tecno, Infinix, Itel, da Oraimo duka suna ƙarƙa...
30/08/2023

Yadda Wasu Manyan Kamfanunuwan Duniya Suke Mana Basaja

Shin ko kasan cewa Tecno, Infinix, Itel, da Oraimo duka suna ƙarƙashin kamfanin mutin ɗaya ne mai suna Transsion Holding. Duk abinda ka siya daga cikin waɗannan kana yiwa kamfani ɗaya ciniki ne. A zahirin gaskiya da kuma abinda ya baiyanar mana shine sun kasance "Competitors" ɗin juna ne, kuma hakan yayi tasiri a cikin mutane inda zaka samu a tsakanin mutane wani yace yafi son Infinix, wani yace yafi son Tecno, saboda dama haka halayyar ɗan'adam take.

A ƙarƙashin haka ƴan kasuwa suke da wata dabarar kasuwanci mai suna "Pseudo Competition". Ma'anar hakan shine a matsayin ka na ɗan kasuwa, a ƙarƙashin kamfanin ka saika ƙirƙirar ma kanka "Competitors" ta yadda zaku raba kan mutane wajen kowa yace ga abinda yafi so, amma daga bayan fage ku kuma kun sani duka kayan kamfani ɗaya ne, kowani product aka siya, kuɗin dai zaizo garesu ne. Kamar dai misalin da muka bayar a sama na kamfanin wayo yi cewar Infinix, Tecno, da Itel duka mallakar kamfani ɗaya ne. Kuma kowacce ka siya kana ƙara ƙarfafa kamfani ɗaya ne. Kamar haka kamfanin Peak, Cowbell da Three Crown suke mallakar kamfani ɗaya.

Salo ne na kasuwanci wanda yana da tasiri sosai, kuma yana taimakawa ƙwarai da gaske wajen taimakawa kamfani wajen siyar da kayan sa ga mutane da yawa idan an kwantanta inda sun zuba duka wannan kuɗin akan 'brand' guda ɗaya.

30/08/2023

Wasu idan Account ɗinsu na Facebook ya shiga Restrictions ko kuma aka hanasu comment ko posting na tsawon wasu ƙwanaki wasu ma daga ƙarshe rufe account ɗin nasu akeyi musamman idan Account ɗin an dora shi akan tsarin tsaro na Two Step Verification, to idan mutum ya saɓa dokar Facebook ɗin s**an ɗauki mataki, ɗaukar matakin ne sai mutane sudinga zagin Mark Zukerberg shugaban kamfanin Facebook suna cewa shine ya rufe masu Accounts..😀

Wato akwai wani tsarin Algorithm da aka samar a manhajar Facebook ɗin wanda shine yake ɗaukar matakan rufe account na mutane ko kuma sanya masu wani takunkumi ko mak**antansu. Waɗannan tsarukan suna Detecting “Spam posts/abused” based on "Machine Learning Algorithms," Automatically da zaran ka saɓa dokar Facebook ko akayi masu reports da yawa sai "ML Algorithm" through Natural Language Understanding Steps (NLP) ya hau bincike tareda “parsing” statements ɗin daya fahimci kalmomi ko bayanan da s**a taka dokar Facebook shi kuma wannan tsarin daganan kawai sai ya aikata abinda aka umarce shi da yayi da zaran ya samu waɗannan kalmomin da s**a saɓa ƙa'ida, wato kenan zai goge Account ɗin ko ya jefa Account ɗin Restrictions ko ya saka ma Account ɗin takunkumin yin Comments ko Posts da sauransu, duk komai zai iya faruwa bayan wannan tsarukan na Algorithms da aka tsara yayi detecting.

Dan haka lokacin da ake kulle maka Account ko ake hanaka Comment ko Posting, shugaban Facebook Mark Zukerberg bashida labari..😁

Allah Yataimaka..🙏

©

Tunda OPAY sunki su biyani kudin talla bari nakoma PalmPay..😀Shin kasan asalin masu kamfanin PalmPay Nigeria da kuma CEO...
29/08/2023

Tunda OPAY sunki su biyani kudin talla bari nakoma PalmPay..😀

Shin kasan asalin masu kamfanin PalmPay Nigeria da kuma CEO na kamfanin?

Palmpay dai Mobile Banking ne da ya samu Lasisi daga babban bankin CBN, Palm Pay mallakin wasu kamfanoni ne guda biyu na ƙasashe biyu da ƙasar Chinese da ƙasar Taiwan na ƙasar chinese shine Transsion Holdings, tareda haɗin guiwa da kamfanin NetEase da yake a ƙasar Taiwan.

Shi dai kamfanin Transsion Holdings dake a ƙasar China kamfani ne da yake ƙirƙirar wayoyi ƙirar Atel, Tecno, Infinix, waɗannan kamfanoni biyu sune s**a haɗa kai s**a samar da mobile banking na PalmPay, kuma sunada branch a Nigeria da ƙasar Ghana, a Nigeria babban office nasu yana 20, Opebi Road, Ikeja Lagos, a ƙasar Ghana kuma babban office nasu yana 54, Senchi Street, Airport Residential Area in Accra, Ghana. Chika Nwosu shine CEO na kamfanin PalmPay.

Email: [email protected]
Call: 018886888

Allah Yataimaka..🙏

© Salisu Abdurrazak Saheel

Koda kasamu matsala da banki zaka iya warware matsalar basai kaje bankin ba..Ta yiwu kanada wata matsala da bank ɗin da ...
29/08/2023

Koda kasamu matsala da banki zaka iya warware matsalar basai kaje bankin ba..

Ta yiwu kanada wata matsala da bank ɗin da ka buɗe, kuma ƙila kanada nisa da bankin ko kuma a wurin da kake ma yanzu babu bankin naka dan haka idan kasamu matsala dasu zaiyi wahala ka iya tuntuɓarsu akan lokaci, ta yiwu Account ɗin naka aka rufe ko kuma kuɗi aka turo maka amma sunƙi sauka a Account ɗin naka ko kuma kaine ka tura kuɗin amma sunƙi zuwa bankin da katura su, ko kuma dai wata matsala mak**anciyar haka.
To Lallai irin haka kana buƙatar hanyar da zaka tuntuɓi bankinka cikin sauri ba dole sai kaje bankin ba zasu warware maka matsalolinka InshaAllah.

Sanin kanku ne yanzu yanar gizo ya tara yan Yahoo da Scammers da ɓarayi kala-kala saboda haka idan kace zakayi Searching numbobin wayar bankin naka idan bakayi wasa ba yanzu zaka ɗauki Lambar wani Scammer ɗin da zai iya damfarar ka da sauransu, dan haka dole kana buƙatar neman sahihiyar hanyar da zaka tuntuɓi Customer Care na bankin da kake amfani dashi, hakan yasa zan zayyano maka hanyoyin da zaka tuntuɓi bankuna har guda 16 ta Lambobin wayarsu da WhatsApp Numbers nasu da Email Address ɗinsu, ta yadda zaka iya tuntuɓarsu ta ko wace hanya domin suyi maka abinda kake buƙata a matsayinka na Customer nasu.

Ga jerin Phone Numbers, WhatsApp Numbers da Email Address Na Bankuna Guda 16 Da Zaka Iya Tuntuɓa A Duk Sanda Kasamu Matsala Dasu:

1. First Bank: Phone Numbers: +234-708-062-5000, (0700-34778-2668228), 01-4485500,0708-062-5000
WhatsApp Number: 08124444000
Email Address: [email protected]

2. Access Bank: Phone Numbers: +234-1-280-2500
WhatsApp: +234-90901901
Email Address: [email protected]

3. UBA: Phone Number +234-700-225-5822, WhatsApp Number: 234 903 001 0007
Email Address: [email protected]

4. Jaiz Bank: Phone Number: +234-708-063-5500, +234-9-4605294, Email Address: [email protected]

5. Starling Bank: Phone Numbers: 0207 930 4450,0700 822 0000, WhatsApp Number:+234 906 000 6449, Email Address: [email protected]

6. Unity Bank: Phone Number +2347057 323 226, 1-800-618-2265, WhatsApp: https://www.whatsapp.com/contact/?subject=messenger,
Email Address: [email protected]

7. Fidelity Bank: Phone Number: 0700 343 35489, WhatsApp Number: 0903 000 5252, Email Address: [email protected]

8. FCMB: Phone Number: 0700 329 0000, 01-279 8800, WhatsApp Number: 09099999814-5, Email Address: [email protected]

9. Ecobank: Phone Number: 07005000000, 2347080653700, WhatsApp Number: +234 808 760 3717, Email Address: [email protected]

10. Kuda Bank: Phone Number: 016335832, WhatsApp Number: https://www.whatsapp.com/contact/?subject=messenger, Email Address: [email protected]

11. Zenith Bank: Call: 234-1-2787000, WhatsApp (+234-7040004422).
Email: [email protected]

12. GT Bank: Call:+234-700-4826-66328, 01448000, 070 0482 6663 28, 080 2900 2900, 080 3900 3900, 081 3985 6000.
Email: [email protected]

13. Union Bank: Call: +234-1-271-6816
Email: [email protected]
WhatsApp: 09070070001

14. Heritage Bank: Email:[email protected]

15. Opay Bank: Call: Call 0700 888 8328 or 01 8888328
Whatsapp: +2349165998936
Email: [email protected]

16. Palm Pay: Email: Email: [email protected]
Call: 018886888

Allah Yayi Mana Jagoranci..🙏

El ahmad yahaya

Matsalar da yawancin masu amfani da OPAY suke tsoron ta faru shine idan ɓarawo ya sace wayar nasu bayan kuma akwai Mobil...
29/08/2023

Matsalar da yawancin masu amfani da OPAY suke tsoron ta faru shine idan ɓarawo ya sace wayar nasu bayan kuma akwai Mobile App nasu na OPAY da kuɗaɗensu a ciki, to akwai wani tsari na Emergency da OPAY s**a samar ta yadda zaka iya blocking account ɗin naka..?

Eh tabbas akwai, koda hac-king Opay Account naka akayi, akwai wasu hanyoyi da ake bi ayi Blocking Account ɗin.

Idan ka rasa wayarka kuma kanason kayi blocking ko restricting na account ɗin naka saboda gudun unknown intruders ko scammers su sace maka kuɗaɗe ga yadda zakayi..👇

Ka samu wayar wani abokinka ko ɗan'uwanka ka danna *955 #

Sai kayi Selecting wurin da aka rubuta "Manage Account" daganan Sai ka sake Selecting "Restrict Account" daganan kuma sai ka sake Selecting "Stop debit transactions for others".

Daganan zasu baka dama ka rubuta Wallet Number, wato lambar wayar naka da Payment Pin naka which is 4 Digits numbers. Kana gamawa za'a rufe Account ɗin.

Note: Daga Lokacin da kasamu kayi Welcome Back na layinka zaka iya dawo da Account naka ta hanyar da kabi da wannan wayar ta abokin naka.

OPAY yak**ata su biyani fa, k**ar talla nake masu..😃
Ni kuma inayi ne saboda yan'uwa su amfana, amma kuyi min Tagging OPAY suzo su biyani gaskiya..😃

©

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Engineer lawi technology posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Nearby media companies


Other Digital creator in Kano

Show All