Ungogo legislative

Ungogo legislative Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ungogo legislative, Digital creator, Kano.

Birnin Los Angeles Na Ƙasar Amurka Na Cigaba Da Cin Wuta Kimanin Kwanaki 5 KenanRahotanni sun bayyana cewa musabbabin wu...
11/01/2025

Birnin Los Angeles Na Ƙasar Amurka Na Cigaba Da Cin Wuta Kimanin Kwanaki 5 Kenan

Rahotanni sun bayyana cewa musabbabin wutar daga gobarar Daji ce ta yi ƙarfi har zuwa cikin birni, inda take ƙona gidaje da gine-gine.

Zuwa yanzu dai an bayyana cewa adadin gidajen da wutar ta ƙone sun haura sama da dubu 10.

TALLAH: KSBDATA Kamfanin Da Ya Yi Fice Wajen Kasuwancin Data Da Katin Waya

Domin fara sána'ár DATA ko kuma ku dinga saka wa kanku, ku sáuké Mánhájar KSBDATA a PláyStore.
👇👇👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.ksbdata.app

Website
👇👇👇
https://app.ksbdata.com

WhatsApp
👇👇👇
https://wa.me/2349018986971

03/08/2024

Allah ka tsinewa Wanda ya bada shawar aka cire tallafin man fetur tare da rufe boda da Tallafin Dollars.

15/04/2024

Eid Mubarak
To All Muslim Ummah

10/11/2023

Alhmadulillah Gawuna Allah Ya Taya
Riko

001 kano State
18/10/2023

001 kano State

SHEKARU 63 NA KUNCI, TAKAICI, AZABA DA BAKIN CIKI. 😭Babu dan Najeriya mai hankali musamman ma dan Arewa da wannan rana z...
01/10/2023

SHEKARU 63 NA KUNCI, TAKAICI, AZABA DA BAKIN CIKI. 😭

Babu dan Najeriya mai hankali musamman ma dan Arewa da wannan rana zata zame masa ranar murna, acikin shekaru 63 muka zama bayi ababen wofantarwa daga shugabanninmu, akaita zubar da Jinanenmu, akaita sace ahalinmu mata da mazajenmu, akaita sace dukiyoyinmu, aka maida mu barayi saboda kagaggen talaucin da s**a sanya mana.

Abun bakin ciki, cikin shekaru 63 muka zama madamfara, mazambata, 'yan ta'adda, mabarata, 'yan tamore kuma cikakkun karnukan farautan masu jajayen kunnuwa.

Bazan murna ba, domin 'yancin bai bani abunda zan nuna cikin annashuwa ba sai kaburburan ahalinmu, tunanin rashi da batan da makusantanmu s**ayi da rasa muhallanmu da dan abunda zufanmu ya tara mana.

Abunda ke kara bani hawaye idan na kallan irin matsanciyar Yunwa data addabin 'yan uwanmu a kasa mai tarin arzikin ma'adanai da yawan jama'a.

Kaico da isowarmu wannan rana daba ta alfahari ba.

ALLAH KASA ZUCIYOYIN MU SU TAFI AKAN IRIN WANNAN TAFARKIAn manta kuɗaɗen da yawansu ya haura Naira miliyan goma sha biyu...
16/09/2023

ALLAH KASA ZUCIYOYIN MU SU TAFI AKAN IRIN WANNAN TAFARKI

An manta kuɗaɗen da yawansu ya haura Naira miliyan goma sha biyu a cikin Adaidaita sahun da yake tuƙawa, bayan yaga kudin sai ya koma inda ya sauke fasinjan ko zai ganshi amma bai tarar dashi ba, sai ya kai kudaden wajen mahaifiyarsa ya gaya mata cewa manta kuɗaɗen akayi a Adaidaita ɗin sa, nan take mahaifiyarsa tace yaje ya gayawa Mahaifinsa inda nan take Mahaifin yaron yace su koma su sake dubawa ko za'a ga mai kuɗin, da ba'a gani ba sai s**a ajiye kuɗin a gida, basu taba ko sisi ba duk da cewa jiya da kyar s**a samu garin kwakin da s**a ci a gidan nasu kamar yadda Mahaifin yaron ya fada...

Sunji ana cigiya a gidan Rediyon Arewa dake kano, inda nan da nan s**a ɗauki lambar wayar da aka bayar s**a kira ...

A takaice dai yaron da iyayensa sun mayarwa da mutumin da ya manta kudaden abunsa, inda shi kuma ya basu kyautar Naira dubu dari hudu...

Wannan yaro ya kyauta.....

Copied from Rabiu Biyora

Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso na APC ya yi nasara a Kotu kan kujerar Majalisar Tarayya ta Kura da Madobi da Garun Malam.
10/09/2023

Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso na APC ya yi nasara a Kotu kan kujerar Majalisar Tarayya ta Kura da Madobi da Garun Malam.

INNA LILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UNAllah ya yiwa Sheikh Giro Argungu rasuwa, bayan jinya da ya samu a daren jiya Talat...
06/09/2023

INNA LILLAHI WA'INNAH ILAIHIR RAJI'UN

Allah ya yiwa Sheikh Giro Argungu rasuwa, bayan jinya da ya samu a daren jiya Talata, bayan ya kammala tafsirin Magriba zuwa ishaa.

Muna Addu'ar Allah ya jikan Malam, hakika duniyar musulunci tayi babban rashi.

Gwamnatin jihar Gombe ta kammala kashi na farko na raba tallafin kayan masarufi ga mabuƙata a jihar. Kayan na cikin tall...
28/08/2023

Gwamnatin jihar Gombe ta kammala kashi na farko na raba tallafin kayan masarufi ga mabuƙata a jihar.

Kayan na cikin tallafin da gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi don rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.

25/05/2023

Surely Gawuna Is Coming....
Masoya a Kwantar da Hankali

04/03/2023

Gawuna yan Ungogo Suke Fata
Maye Ra'ayin ku akai

05/02/2023

Ungogo
Muna Goyon Bayan Gawuna a Matsayin Gwamnan Kano

Kamar tsaro, aikin inganta lafiya ba na gwamnati bane ita kadai shi yasa ake bukatar masu hali masu zuciya domin a hadu ...
22/09/2022

Kamar tsaro, aikin inganta lafiya ba na gwamnati bane ita kadai shi yasa ake bukatar masu hali masu zuciya domin a hadu a inganta lafiya a Jihar Kano.

Kalaman gwamnan jihar kano kenan Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayin kaddamar da katafaren ginin asibiti, sashen kula da masu ciki da kananan yara a asibitin Waziri Gidado dake Bachirawa Karamar Hukumar Ungogo wanda Alh. Abdullahi Muazu ya gina tare da sadaukar dashi ga gwamnati.

Gwamna ya yaba da namijin kokarin dan kasuwar mai kishin cigaba tare da kira da sauran al'uma dasuyi koyi da irin wannan aikin alkhairi.

Haka Shugaban Karamar Hukumar tare da kwashinan lafiya sun bude makamancin wannan aiki a Asibitin PHC Tudun Fulani inda kungiyar MSF ta fadada asibitin ta hanyar gina sabon block na kula da masu ciki da kananan yara domin inganta lafiya a matakin farko a Karamar Hukumar dama Jihar Kano. Shugaban Karamar Hukumar Ungogo Engr. Dr. Abdullahi Garba Ramat ya nuna jin dadinsa da godiya ga wannan kungiya tare da tabbatar da yin aiki kafada kafada dasu domin kawo ci gaba a fannin lafiya a Karamar Hukuma.

Gwamna ya samu rakiyar mai masaukin baki Engr. Dr. Abdullahi Garba Ramat, takwaransa na Dala, Commissioner na Lafiya dana kananan hukumomi, da sauran manyan jami'an gwamnati

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ungogo legislative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ungogo legislative:

Videos

Share