26/04/2022
Da dumi duminsu
Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Talata, ashirin da biyar ga watan Ramadan, shekarar 1443 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida, ga watan Afrilu, shekarar 2022.
1. Hukumar farautar fataken miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, ta k**a wani babban madugun safarar miyagun ƙwayoyi dangin su Tiramadol da sauransu, na Naira Biliyan Uku da aka danganta da ayarin Ɗan Sanda Abba Kyari har ya ja musu halin da suke ciki a yanzun.
2. Ƙungiyar Tintiɓa ta Dattawan Arewa, ta nesanta kanta da bayanin da ake yi cewa wai ta zaɓi Bukola Saraki da Bala Mohammed a matsayin 'yan takaran da ƙungiyar ta zaɓa a PDP, don su fafata neman kujerar shugabancin ƙasar nan.
3. Bala Mohammed ya ce shi fa bai yarda da wani tsari na karɓa-karɓa ba. Mutum ɗaya zai iya ɗaga wa ƙafa a duniyar nan shi ne Jonathan.
4. Tinubu ya raba wa Kanawa shinkafa buhu dubu ɗaya da ɗari takwas.
5. Bom ya fashe a wata mashawa da ke jihar Yobe, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum a ƙalla biyu sai waɗanda s**a ji rauni.
7. Ana ci ga ba s**ar Amaechi cewa a lokacin da mutane ke hannun 'yan fanshin jirgin ƙasa da ke ƙarƙashin ma'aikatarsa, yana can yana raye-raye da guje-guje yana zagaya fili da sunan neman takarar shugabancin ƙasar nan.
8. Ana ci gaba da s**ar gwamnatn tarayya har da ta jihar Kaduna, a kan har yanzun ba su tintiɓi iyalai ko 'yan uwan waɗanda aka yi fashinsu a jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ba.
9. Malaman jami'a sun ci gaba da bayanin cewa, suna nan suna ci gaba da yajin aiki ba gudu ba ja da baya. Duk da gwamnati ta dakatar da biyansu albashi.
10. Ana nan ana ci gaba da yi wa Dafta Ramatu Abarshi da ɗiyarta, da duk sauran ma waɗanda ke hannun 'yan fashin jama'a addu'ar Allah Ya musu agaji da agajinSa.
11. Ma'aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare an ba su ko taro ba, suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙinsu.
12. Ana ci gaba da taya Macron murnar sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na ƙasar Faransa.
Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buɗa baki lafiya.
Af! Ƙaramar Sallah tana ci gaba da ƙaratowa. Idan mun kai azumin yau, mun kai guda ashirin da biyar. Idan talatin za a yi bana, saura biyar. Idan ashirin da tara za a yi saura huɗu. Ya batun kayayyaki da akan buƙata domin jin daɗin gudanar da shagulgulan sallah? Ya batun ɗilin-ɗilin?
Is'haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.