22/05/2024
Al'ummar jihar Kaduna suna ta tofa albarkacin bakin su akan salon jagorancin gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Kai abin ya kai har wa'inda ba 'yan jihar Kaduna sun tsoma baki cikin wannan muhawarar. Wasu suna yabawa, a wani bangaren kuma suna kushe salon nashi tare da tuna namijin kokarin mai gidansa, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i.
Menene ra'ayinku? Kuna gani kwalliya ta biya kudin sabulu? A lokacin da ake shirye-shiryen ciki shekara daya a karagar mulki.