11/06/2021
SAYYIDA MA’ASUMA ‘YAR IMAM MUSAL KAZEEM (AS)
— Saifullahi M. Kabir
Ranar 1 ga watan Zulka’ada, rana ce ta farin ciki da murna ga muminai, saboda a cikinta ne aka haifi Karima, Jalila, Sayyida Fatima Ma’asuma ‘yar Imam Musal Kazeem (AS).
Wannan baiwar Allah mai girma, wacce a cikin ziyararta ake mata kirari da cewa: “’Yar waliyiyar Allah, ‘yar uwar waliyin Allah kuma innar Waliyin Allah.” Ta kasance ‘yar uwa shakikiya (wacce suke uwa daya uba daya) ga Imam Aliyu bin Musar Ridha (AS).
An haifeta ne a garin Madina, a shekara ta 173 bayan Hijira. Ta kasance mafificiya a cikin dukkan ‘ya’yan da Imam Kazeem ya Haifa baya ga Imam Ridha (AS). Ta taso a gidan Imamanci da Wulaya, ta rayu a tsakankanin Limaman shiriya tsarkaka. Kakanninta A’imma, Mahaifinta Imam, Wanta Imam, kuma ta zama Innar Imamai (AS).
Ta kasance daga cikin matan da s**a tsarkake Imaninsu. Tsarkakakkiya, ta taso ne bisa kulawar yayanta Imam Ridha (AS), sak**akon kulle mahaifinta Imam Musal Kazeem da azzalumin sarkin Banul Abbas mai suna Harun ya yi, wanda ya kai ga Shahadantar da shi a cikin wannan Kurkuku din.
Cikin lakubba da ake kiran Sayyida Fatima Ma’asuma, akwai Muhaddasa, Mubaraka, Abida da kuma Karimatu Ahlulbait (AS). Dabi’un wannan tsarkakakkiyar baiwar Allah din ya yi k**a sak da na kakarta Sayyida Fatima Azzahra (SA).
Wannan baiwar Allah din ta kasance wacce ta mori suna, a yayin da aka saka mata sunan Sayyida Zahara (S). Imamanmu masu girma sun muhimmantar da saka suna ‘Fatima’ ga ‘ya’yan da s**a haifa (mata), saboda suna ne na uwarsu, Sayyida Fatima ‘yar Manzon Allah (S).
Kulaini, ya kawo ruwaya a cikin Alkafiy, daga Salmanul Ja’afariy, yace; Na ji Baban Hasan (AS) yana cewa: “Talauci bata shiga gidan da a cikinsa akwai mai suna Muhammad ko Ahmad ko Ali ko Hasan ko Husaini ko Ja’afar ko Dalib ko Abdullahi, ko kuma sunan Fatima a cikin mata.” Dan haka lallai sunan Fatima a wajen iyalan Fatima da masoyanta, suna ne mai girman daraja. Kuma duk wacce Allah ya azurta da sunan abar girma