07/10/2023
JIBWIS tayi garan bawul ga wasu daga cikin kwamitocin ta
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi garan bawul ga wasu daga cikin kwamitocin Kungiyar. A lokacin da yake bayyanawa Majalisar koli (EXCO) ta kungiyar a birnin Hadejian jihar Jigawa.
Sheikh Bala Lau yace anyi Wadannan gyare-gyaren ne domin ayyukan kungiyar su ci gaba da tafiya ba kaukautawa.
1-Kungiyar ta kafa sabon Kwamiti wanda zai Kula da Marayun Masu Da’awa, ma'ana kula da iyalan Malamai in sun rasu, inda Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau zai jagoranta da Kansa wato (Chairman Board of Directors)
Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo shine mataimaki. Kazalika kungiyar ta zabo mambobin kwamitin irin su Sheikh Yakubu Musa Hassan, Sheikh farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, Alhaji Auwal Rano (A.A. RANO), Tsohon ministan sufuri Alhaji Mu'azu, Alhaji Auwalu Lawan Gombe, Alhaji Ibrahim Katsina, Alhaji Sani Sambo Lagos, Daraktan agaji Mustapha Imam Sitti, a karshe Sheikh Dr. Kabiru Gombe shine Sakataren kwamitin.
Sai Management na wannan kwamiti, Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia shi zai kula da kwamitin a dukkan mataimakai, Dr. Fa'iz Bashir kuma shine Sakataren kwamiti.
2-Kwamitin masallatai wanda Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ke jagoranta, ya samu sabon Sakataren kwamitin Dr. Salisu Barau.
3-Sheikh Habibu Yahaya Kaura shine ya Zama sabon shugaban kwamitin ayyuka (Chairman Working Committee) na Kungiyar bayan rasuwar Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu.
Inda Malam Ramalan Azare ya Zama mataimakin Shugaban kwamitin. Sheikh Ibrahim Idris Darus-sa'ada ya Zama sabon Sakataren kwamitin.
4-Sheikh Dr. Isma'ila kumo, shine ya Zama sabon shugaban kwamitin wal-wala (Chairman Walfare Committee) na Kungiyar.
5-Kwamitin Da'awa wanda Sheikh Yakubu Musa Hassan yake jagoranta, ya Samu sabon mataimaki shine Sheikh Umar Jega, sannan Sheikh Dr. Jameelu Zarewa ya Zama sabon Sakataren kwamitin.
6-Kungiyar ta kafa sabon kwamiti na Ilimi mai zurfi (Higher Education) inda Sheikh Professor Abdullahi Sale Pakistan yake jagoranta. Sheikh Dr. Magaji Fadlu Zarewa shine Sakataren kwamitin
7-Sai kwamitin ilimi da ilimantarwa (Basic Education) wanda Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi R/lemo zai jagoranta, inda Malam Usman Alhaji Sale potiskum ya Zama Sakataren kwamitin.
8-Sheikh Abubakar Abdussalam Baban gwale ya samu karin girma daga Sakataren kwamiti zuwa sabon shugaban kwamitin Seminar ta kasa. Inda Sheikh Saifuddeen Yakubu Musa zai Zama Sakataren kwamitin.
Shima Alh. Usman Ibrahim yola, Karin girma ya Samu daga Sakataren kwamiti zuwa sabon shugaban kwamitin marayu na kasa. Inda Alhaji Abdullahi Abdulmalik Diggi ya Zama mataimakin Shugaban kwamitin. Dr. Malami Garba ya zama Sakataren kwamitin.
A karshe Daraktan agaji na kasa, Engr. Mustapha Imam Sitti ya mika rahoton aikin da Shugaban kungiya ya saka su game da wasu lamura da s**a shafi gidan Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu. Haka zalika Engr. Salisu Muhammad Gombe, ya mika rahoton aikin da Shugaba ya saka su a jahar Bauchi.
JIBWIS NIGERIA