Funtua Online Media Reporters

Funtua Online Media Reporters Funtua Online Media Reporters..Call 08029225724 for advertisement, Ceremonies and more.

Innalillahi Wa'innna Ilaihiraju'un!Mun samu labarin Barayi sun shiga Mairuwa dake cikin karamar Hukumar Faskari a cikin ...
23/03/2024

Innalillahi Wa'innna Ilaihiraju'un!

Mun samu labarin Barayi sun shiga Mairuwa dake cikin karamar Hukumar Faskari a cikin daren nan har sun kashe Alh Lado Mairuwa.

Allah ya gafarta ma shi yasa ya huta.

Transforming Education System at State level (TESS).Permanent Member II Hon. Rabiu Idris Funtua on mornitoring of School...
23/03/2024

Transforming Education System at State level (TESS).

Permanent Member II Hon. Rabiu Idris Funtua on mornitoring of School Improvement Grants (SIG) at Barebari Primary school in Funtua Local Government.

Saturday 23/3/2024.

Abin A Yaba! Abin Koyi! Sama da mutane Talatin (30) s**a amfana da Naira Dubu Uku-Uku a wajen Kansila mai kula da Shashi...
23/03/2024

Abin A Yaba! Abin Koyi! Sama da mutane Talatin (30) s**a amfana da Naira Dubu Uku-Uku a wajen Kansila mai kula da Shashin Ma'aikatar Ayuka ta Karamar Hukumar Funtua Hon.Kabir Ya'u (Promotion).

Supervisory Concilor mai kula da shashin Ma'aikatar Ayyuka ta Karamar Hukumar Funtua Hon Kabir Ya'u (Promotion) ya yi abinda ya saba yi a cikin irin wannan lokaci na Wata mai alfarma watan Ramadan.

In da ya ba da umarni a sama wasu yan gwargwamaya Naira Dubu Uku-Uku a cikin Asusun Ajiyar su domin sayen Dabino.

Comrd Imran A Sanusi

"Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Malumfashi/Kafur, Honorable Aminu Ibrahim Kafur ya rabawa al'ummar da ibtila...
23/03/2024

"Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Malumfashi/Kafur, Honorable Aminu Ibrahim Kafur ya rabawa al'ummar da ibtila'in harin yan bindiga ya shafa daga yankin Burdugau da buhunnan shinkafa da masara 300 domin saukaka masu halin matsin rayuwa da suke ciki.

Kamar yadda Katsina Post ta samu, dan majalisar tarayyar ya raba buhunnan kayan abincin ne ta hannun wani kwamiti na musamman da ya kafa.

Tuni dai tallafin ya isa hannun mutanen da ibtila'in ya shafa a garin Malumfashi, Marabar Kankara da kuma Karfi.

Wasu daga cikin mutanen da s**a anfana da tallafin sun nuna godiyar su ga dan majalisar tarayyar tare da shan alwashin cigaba da yi masa addu'ar fatan alheri da kuma rokon Allah ya taimaka masa wajen sauke nauyin da ya dora masa.

Katsina Post

The permanent member // State Universal Basic Education Board Katsina Hon. Alhaji Rabiu Idris Funtua embark on on - the ...
22/03/2024

The permanent member // State Universal Basic Education Board Katsina Hon. Alhaji Rabiu Idris Funtua embark on on - the sport monitoring of selected primary schools in Funtua Local Government Area benefiting from Transforming Education System At the state level ( TESS PROJECT) for construction,Renovations and providing sanitary facilities to uplift the standard level of primary education.

Unguwar Moda Primary school
Maijibga Primary school
Gwouruwa Primary school

Friday 22/3/2024

"Kwamitin majalisa ya goyi bayan kulle makarantun koyon aikin lafiya da asibitocin da basu da lasisi a Katsina.Kwamitin ...
22/03/2024

"Kwamitin majalisa ya goyi bayan kulle makarantun koyon aikin lafiya da asibitocin da basu da lasisi a Katsina.

Kwamitin majalisar dokokin jihar Katsina mai kula da harkokin lafiya ya goyi bayan matakin da Gwamnatin jihar zata ɗauka na kulle dukkanin makarantun koyon aikin lafiya, asibiti da cibiyoyin kiwon lafiyar da basu da lasisi a Katsina.

Shugaban kwamitin, Hon. Abubakar Muhammad Total ne ya jaddada goyon bayan matakin a lokacin da kwamitin ya amshi baƙuncin mai ba Gwamna shawara wajen ɓangaren makarantun kiwon lafiya, Hon. Umar Ma**da da 'yantawagar sa.

Hon. Total ya bayyana cewa babban aikin Majlisa shine kare mutuncin jiha, rayuwa da taimakon al'ummar jihar Katsina.

Yace Majalisa ba zata lamunta da duk wani abu da zai kawo barazana ga jihar Katsina ba.

Da yake magana kan makarantun, Hon. Total yace wajibi ne majalisar ta yi duba kuma ta ba gwamnati gudunmawa wajen magance matsalar bude makarantun bogi dake haifar da koma baya ga kiwon lafiya a jihar Katsina.

Ya tabbatarwa 'yan tawagar amadadin majalisar cewa zasu bada dukkanin goyon bayan su wajen magance matsalar.

Tun farko da yake jawabi, Hon. Umar Ma**da yace akwai rashin ƙwarewa ga makarantun kiwon lafiya da dama da wasu asibitoci mallakin al'umma.

Yace binciken su ya gano cewa akwai aƙalla makarantu koyon aikin lafiya sama da 150 a faɗin jihar Katsina.

Hon. Umar Ma**da yace da yawa daga cikin makarantun basu da lasisi ko ƙwarewar tafiyar da makarantun.

Ya ƙara cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya damu matuƙa akan ƙoƙarin da wasu keyi na gurɓata kiwon lafiya a jihar Katsina.

Hon. Umar Ma**da ya yaba ma majalisar bisa ƙoƙarin da take na daƙile duk wani abin da zai cutar da mutane.

Ya nemi majalisar ta basu dukkanin goyon baya da suke buƙata yayin aiwatar da aikin su na tsaftace ilimin kiwon Lafiya a Jihar Katsina.

Katsina Post ta samu cewa Hon. Umar Ma**da da 'yantawagar sa sun kai ziyara ga sarakunan Katsina da Daura, tare da neman taimakon su.

Katsina Post

21/03/2024

Malam fah ya fusata.

"Ramadan: Yobe Governor, Mala Buni flags off distribution of bags of rice, flour & gallons of cooking oil to 120,000 vul...
21/03/2024

"Ramadan: Yobe Governor, Mala Buni flags off distribution of bags of rice, flour & gallons of cooking oil to 120,000 vulnerable households across Yobe State.

The distribution processes is to be conducted by Yobe SEMA led by Dr. Mohammed Goje.

Northeast Reporters

"MUSLIMS GLOBAL RELIEF, FUNTUA LOCAL GOVERNMENT.Ayau Sha 'Daya Ga Watan Ramadan, Allah Chikin Ikonshi Yabamu Damar Rabaw...
21/03/2024

"MUSLIMS GLOBAL RELIEF, FUNTUA LOCAL GOVERNMENT.
Ayau Sha 'Daya Ga Watan Ramadan, Allah Chikin Ikonshi Yabamu Damar Rabawa Al'umma Taliya,Gero da Masara.
Wannan Qungiya Kamar Yanda Akasani, Ankafata Ne, Don Tallafawa Marayu,Gajiyayyu Da Sauran Al'ummah Masu Matsakaichin Qarfi.
Sama Da Mutum (100) 'Dari ne S**a Amfana Da Tallafin Kayan Abinchi Don Samun Sauqin Rayuwa a Watan na Ramadan.
Ba Mallakar Gwamnati Bache, Ko Wani 'Dan Siyasa, Qungiyache Da Matasa Masu Kishin Garin Funtua S**a Qirqira Da Aljihunsu, Kuma Za'achigaba Da Bada Tallafi Insha Allahu.

'Kofarmu a Bude Take Don Amsar Sababbin Mambobi, Shawarwari Da Kuma Tallafi Ga Wanda Allah Yaba iko.
Ibrahim Usman
P.R.O Muslims Global Relief.
09012759800
09061140530

Marayu da Mabukata sama da mutane Dari (100) s**a amfana da Tallafin Kungiyar MUSLIMS GLOBAL RELIEF FUNTUA a karkashin j...
21/03/2024

Marayu da Mabukata sama da mutane Dari (100) s**a amfana da Tallafin Kungiyar MUSLIMS GLOBAL RELIEF FUNTUA a karkashin jagorancin Malam Abdulrahman.

A ranar Alhamis 21/3/2024. Kungiyar Muslim Global Relief Funtua ta ba da tallafin Taliya da Masara ga Marayu da Gajiyayyu a cikin Karamar Hukumar Funtua.

An gudanar da ba da Tallafin a Farfajiyar Gudindi Model Primary School Funtua.

Da yake nashi jawabin Shugaban kungiyar Malam Abdulrahman ya nuna jin dadin shi da Allah ya basu iko s**a fara wannan aikin alheri sannan ya kuma kara da cewa "ita wannan kungiya ba Gwamnati take daukar dawainiyar taba muke hada taro sisi domin muga mun taimaki al'umma, amma kofa a bude take ga duk wanda ya yi niyar taimaka ma wannan kungiya"

Daga karahe ya yi addu'ar Ubangiji Allah ya cigaba da basu kwarin gwiwar taimakon al'umma.

Wadan da s**a amfana da tallafin sun tofa albarkacin bakinsu tare da gode ma shuwagabannin wannan kungiya tare kuma da yi masu addu'ar Allah ya kara basu kwarin Gwiwar taimakon Marayu da Mabukata.

Funtua Online Media Reporters
21/3/2024

21/03/2024

Kai tsaye daga Gudundi Model Primary school Funtua wajen ba
Marayu da Gajiyayyu sama da Dari (100) tallafin Kungiyar MUSLIMS GLOBAL RELIEF FUNTUA a cikin wannan wata mai alfarma watan Ramadan.l

"Yadda Jihohin Arewa 7 Za Su Kashe Naira Biliyan 28.3 Domin Yin Abinci Azumi A daidai lokacin da watan azumi ke ci gaba ...
20/03/2024

"Yadda Jihohin Arewa 7 Za Su Kashe Naira Biliyan 28.3 Domin Yin Abinci Azumi

A daidai lokacin da watan azumi ke ci gaba da nitsawa, jihohin Najeriya guda bakwai sun ware tsabar kudi har naira biliyan 28.3 domin ciyar da masu azumi a watan na Ramadan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Jihohin guda bakwai sun hada da Katsina da Sokoto da Kano da Jigawa da Kebbi da Naija da kuma Kebbi.

Bayanai sun nuna cewa akwai wasu karin jihohin arewacin da dama da su ma s**a ware kudaden domin ciyarwa duk da cewa dai ba su bayyana a fili ba.

Wannan abu dai ya janyo kace-na-ce a tsakanin al'umma inda wasu malaman addinin ke kiraye-kirayen da a yi bincike bisa lura da irin yawan kudaden da aka ware din.

Jihar Katsina ce dai ta fi kowacce jiha a yawan kudin ciyarwar inda ta ware naira biliyan 10.

Sai kuma jihar Sokoto da ke biye mata da naira biliyan 6.7, sannan jihar Kano kuma ta fitar da naira biliyan shida.

Ita kuwa jihar Jigawa ta fitar da naira biliyan 2.83, sai jihar Kebbi da ta fitar da naira 1.5 biliyan.

Jihar Naija ta ware naira miliyan 976, inda jihar Yobe ita kuma ta ware naira miliyan 178 domin ciyarwa.

Alh Mansur Labaran Kaura shine wanda ya lashe zaben da aka gudanar na kungiyar Makarantu masu zaman kansu ta Kasa Reshen...
20/03/2024

Alh Mansur Labaran Kaura shine wanda ya lashe zaben da aka gudanar na kungiyar Makarantu masu zaman kansu ta Kasa Reshen Karamar hukumar Funtua (NAPPS).

A ranar Laraba 20/3/2024 aka gudanar da zaben Shuwagabannin Kungiyar Makarantu masu zaman kansu na kasa reshen Karamar Hukumar Funtua. Mansur Labaran Kaura shine ya samu nasarar samun zama shugaban kungiyar, an zabi Mansur Labaran Kaura a zabi na babu hamayya.

An gudanar da zaben a Aya Primary school Funtua.

Da yake na shi jawabin sabon Shugaban Alh Mansur Labaran Kaura ya nuna jin dadin shi tare kara gode ma Allah akan yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya aka kuma gama shi lafiya.

Ya kuma kara da cewa "Insha Allahu zai kawo ma wannan kungiya cigaba tako wanne fanni sannan kuma kofa a bude take domin amsar shawarwari"

Daga karshe ya yi addu'ar Allah ya maida kowa gidan shi lafiya.

Jama'a da dama sun tofa Albarkacin bakin su wajan ba da shawarwari ga sabon Shugaban.

Funtua Online Media Reporters
20/3/2024.

20/03/2024

Kai tsaye daga Aya Primary school wajan zaben NAPPS FUNTUA LOCAL GOVERNMENT EXCO ELECTION (2024).

"Idan Allah ya yarda kamar yadda na saba duk Azumi ina tallafa ma abokan Gwagwarmaya da kudin sayen Suga koba yawa wanna...
18/03/2024

"Idan Allah ya yarda kamar yadda na saba duk Azumi ina tallafa ma abokan Gwagwarmaya da kudin sayen Suga koba yawa wannan karon ma Insha Allahu zanyi kokarin ganin nayi haka"

Sakon Supervisory Concilor Works Department Funtua Local Government Hon. Kabir Yau (Promotion).

Anyi kira ga Ma'aikatan Ma'aikatar Ilimi ta Karamar Hukumar Funtua da suyi koyi da Malam Musa S Kasuwa.Anyi wannan kiran...
18/03/2024

Anyi kira ga Ma'aikatan Ma'aikatar Ilimi ta Karamar Hukumar Funtua da suyi koyi da Malam Musa S Kasuwa.

Anyi wannan kiran ne wajan taya Malam Musa S Kasuwa murnar kammala aikin Gwamnati lafiya.

A ranar Litini 18/3/2024. A karrama Malam Musa S Kasuwa akan kammala aikin Gwamnatin daya yi a Ma'aikatar Ilimi ta Karamar Hukumar Funtua (LGEA) wanda shashin Diba ingancin koyo da koyarwa ya dauki nauyi (Department of Quality Assurance) karkashin jagorancin Hajiya Maryam Babajo.

Da yake nashi jawabin Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Funtua Malam Sama'ila Ibrahim Abdu ya yi kira ga Ma'aikata dasu zamo masu koyi da Malam Musa S Kasuwa saboda mutum ne wanda bai wasa da aiki yana rike aiki yadda ya dace.

Ya kuma kara da cewa "shi aikin Gwamnati ya gaji haka idan ka fara shi in dai da rayuwa wata rana sai kaji ance ka gama, saboda haka muyi kokari mu rike domin ganin mun gama shi lafiya.

Daga karshe ya yi addu'ar yadda Malam Musa S Kasuwa ya kammala aikin shi lafiya Allah ya yan baya ma su gama lafiya.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu daga cikinsu akwai Daraktar mai kula da shashin koyo da koyarwa Hajiya Mairo Babajo, Daraktar Shashin wayar da Al'umma Hajiya Rabi SB Shehu, PPO Alh Lawal Danmairo,PRS Malam Nura Tijjani Academic Services Alh Mansur Lawal Maikeke da sauran su.

18/03/2024

Kai tsaye daga Ma'aikatar Ilimi ta Karamar Hukumar Funtua wajan taya M. Musa S Kaauwa murnar kammala Aikin Gwamnati lafiya.

Ramadan: Bauchi reps member, Makama shares food items, tricycle, cash, iPhone, others to thousands of his constituents. ...
17/03/2024

Ramadan: Bauchi reps member, Makama shares food items, tricycle, cash, iPhone, others to thousands of his constituents.

Hon. Hon. Alhaji Kabiru Yusuf Makama is representing Alkaleri & Kirfi federal constituency.

The items distributed includes:
1. N20 millions,
2. Bags of rice,
3. Bags of sugar,
5. Bags of grains,
6. iPhone 11 Pro Max, Redmi A8 , tricycle, among others.

Labari Cikin Hotuna!Hotunan yadda wata kungiyar Mata mai taimakon Marayu da Mabukata mai suna MUHAMMAD BIN ABDULLAHI BIN...
17/03/2024

Labari Cikin Hotuna!

Hotunan yadda wata kungiyar Mata mai taimakon Marayu da Mabukata mai suna MUHAMMAD BIN ABDULLAHI BIN ABDULMUTALIB take tallafa ma Marayu da Mabukata a yau Lahadi 17/3/2024 a cikin Garin Funtua.

Malamai sun yi kira ga Maza suyi koyi da irin kokarin da Mata keyi wajan hada Kungiyoyin taimakon yara Marayu da Mabukat...
17/03/2024

Malamai sun yi kira ga Maza suyi koyi da irin kokarin da Mata keyi wajan hada Kungiyoyin taimakon yara Marayu da Mabukata.

Anyi wannan kiran ne a wajan ba da Tallafi ga Marayu da Mabukata wanda wata Kungiyar Mata mai taimakon Marayu da Mabukata mai suna MUHAMMAD BIN ABDULLAHI BIN ABDULMUTALIB ta kaddamar da ba da Tallafin ta a yau cikin garin Funtua.

A ranar Lahadi 17/3/2024. Kungiyar nan mai taimakon Marayu da Mabukata mai suna Muhammad Bin Abdullahi Bin Abdulmutallib ta gudanar da ba da tallafi ga yara Marayu da Mata mabukata a cikin Karamar Hukumar Funtua.

Karkashin jagorancin Hajiya Maryam Sallamu, Hajiya Mariya Umar Yaro da Hajiya Maimunatu Kabir Sidi,Hajiya Binta Gagare, Hajiya Bilkisu Shuaibu, Alh Rabe Sale, Alh Ibrahim Muazzam, Alh Abdulrahman Kabir Sidi, Alh Umar Ibrahim Nabature, Alh Saadu Tukur.

An gudanar da taron a Gidan Malam Gwani Auwal Idris Maiduguri dake Karaya Road cikin Garin Funtua.

Kungiyar ta raba ma Marayun Maza Yadikan dinkin Sallah Matan kuma an basu Atamfofi domin suyi dinkunanan Sallah tare kuma da taimaka ma Mabukata da kayan Masarufi.

Da take nata jawabin Shugabar Kungiyar ta bayyana irin kokarin da kungiyar take domin gani ta taimaki marayu da mabukata, ta kuma kara da cewa "Kungiyar da mutane Goma ta fara amma yanzu sai dai muce Alhamdulillah! Wannan kungiya tana daukar nauyin yara marayu akan karatun su da kuma bada taimako na yanayin rayuwa, to yau Allah ya kawo mu lokacin da zamu ba da tallafi ga yara marayu da mabukata, ta kuma kara da cewa a shirye suke wajan taimakon Marayu da tun daga Makarantun Firamare harya zuwa Jami'a"

Daga karahe tayi addu'a ga wadan da s**a fara assasa hidimar wannan Kungiya amma yanzu basu raye, tayi addu'ar Allah ya gafarta masu yasa sun huta.

Malamai da yawa sun tofa albarkacin bakinsu tare da nasiha ga al'umma akan alfanun taimakon Marayu da Mabukata.

Malamai sun kara jawo hankali wajan ganin al'umma sun shiga cikin hidimar Marayu domin tana da matukar muhimmanci ranar gobe kiyama.

Daga cikin Malaman da s**a tofa Albarkaci bakin su akwai Malam Usman Usman, Malam Gwani Auwal Idris Maiduguri da sauran su.

Funtua Online Media Reporters
17/3/2024

17/03/2024

Kai tsaye daga Karaya Road a cikin Karamar Hukumar Funtua wajan da kungiyar MUHAMMAD BIN ABDULLAHI BIN ABDULMUTALIB zata tallafa ma Marayu da Gajiyayyu a cikin wannan Wata mai alfarma .

Ciyarwar Ramadan.Jama'a muna maku fatan alheri tare da fatan Allah ya amshi ibadun mu baki daya.Funtua Online Media Repo...
17/03/2024

Ciyarwar Ramadan.

Jama'a muna maku fatan alheri tare da fatan Allah ya amshi ibadun mu baki daya.

Funtua Online Media Reporters

Jama'a muna maku barka da Shan Ruwa tare da fatan Allah ya karbi Ibadun mu yasa muna cikin ƴan'tattun Bayi.
16/03/2024

Jama'a muna maku barka da Shan Ruwa tare da fatan Allah ya karbi Ibadun mu yasa muna cikin ƴan'tattun Bayi.

Labari Cikin Hotuna!Hotunan yadda wata Foundation mai Suna MARYAM MATAWALLE FOUNDATION ta gudanar da ba da Tallafin Azum...
16/03/2024

Labari Cikin Hotuna!

Hotunan yadda wata Foundation mai Suna MARYAM MATAWALLE FOUNDATION ta gudanar da ba da Tallafin Azumi a Dutsen-Reme dake cikin Karamar Hukumar Bakori a Jahar Katsina.

Karkaahin Jagorancin Ibrahim Ya'u.

Funtua Online Media Reporters
16/3/2024

Mutane sama da Ɗari biyu (200) ne  s**a amfana da Tallafin MARYAM MATAWALLE  FOUNDATION karkashin jagorancin Comrd Ya'u ...
16/03/2024

Mutane sama da Ɗari biyu (200) ne s**a amfana da Tallafin MARYAM MATAWALLE FOUNDATION karkashin jagorancin Comrd Ya'u Ibrahim Dutsen-Reme.

A ranar 16/2/2024. Shugaban Maryam Matawalle Foundation Comrd Ya'u Ibrahim ya kaddamar da ba da Tallafi a karkashin Kungiyar MARYAM MATAWALLE FOUNDATION in da mutane sama da Dari biyu s**a amfana da tallafin Dawa da Gero.

Da yake nashi jawabin Shugaban kungiyar Comrd Ya'u Ibrahim ya bayya jin dadin shi da kuma kara gode ma Allah daya kawo mana wannan rana mai matukar mahimmanci.

Ya kara da cewa" wannan kungiya bata a jahar Katsina amma cikin ikon Allah yanzu na kawo ta jahar Katsina yanzu haka wannan Foundation ta taimaka ma mutane kusan sama da Dubu Dari Biyu tsakanin Bakori da Danja a cikin wannan Wata mai alfarma watan Azumin Ramadan."

Ya kuma kara shaida ma al'ummar da s**a halarcin taron cewa "Kungiyar zata fara dafa Abinci domin yin Bula Baki da shi ga masu bukata"

Daga karshe ya yi godiya ga wadan da s**a halarci taron tare da fatan kowa Allah ya mai kowa Gidan shi lafiya.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu sunyi godiya tare da fatan alkhairi ga wannan kungiya, daga cikin wadan da s**a tofa albarkacin bakinsu akwai Malam Aminu Rayyana da Mataimakiyar Shugaban kungiyar Hajiya Saliha Rayyana, Mai Unguwa da Malamai da kuma wadan da s**a amfana da tallafin.

Funtua Online Media Reporters
16/3/2024 .

16/03/2024

Kai tsaye daga Dutsen-Reme dake cikin Karamar Hukumar Bakori in da MARYAM MATAWALLE FOUNDATION take ba da Tallafin Azumin Watan Ramadan karkashin jagorancin Malam Ya'u Ibrahim.

First  Jumu'ah of the blessed Month of   Ramadan, let's read Suratul Kahf.
15/03/2024

First Jumu'ah of the blessed Month of Ramadan, let's read Suratul Kahf.

14/03/2024

Muna ta shan Ruwan Sama a karamar Hukumar Funtua.

Labari Cikin Hotuna!Fuskokin al'ummar da s**a halarci taron kaddamara da tallafin Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jahar K...
14/03/2024

Labari Cikin Hotuna!

Fuskokin al'ummar da s**a halarci taron kaddamara da tallafin Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jahar Katsina Hon. Hamza Suleman Faskari (Wambai).

Yau Alhamis 14/3/2024 a ƙaramar Hukumar Faskari.

Address

Mairuwa Road Funtua
Funtua
MAKERAROADFUNTUA

Telephone

+2348029225724

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua Online Media Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Funtua Online Media Reporters:

Videos

Share