08/05/2025
Jagororin CPC Sun Bayyana Cikakken Goyon Bayansu ga Shugaba Tinubu A Zaɓen 2027
Tsoffin fitattun ’yan siyasa daga tsohuwar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) da yanzu suke ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu har shekarar 2027, Bisa abin da s**a bayyana a matsayin “Gwamnati mai aiki da tasiri.”
Wannan na ƙunshe ne a wata taron manema labarai na kasa da kasa da aka gudanar a yau a Abuja, inda jagoran tawagar kuma tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ya bayyana cewa tsohuwar tafiyar CPC a cikin APC ta kuduri aniyar ba da cikakkiyar gudunmawa wajen tabbatar da nasarar Gwamnatin Shugaba Tinubu.
Sanata Al-Makura ya bayyana cewa dukkan manyan jiga-jigan CPC da s**a shiga cikin APC na tafiya daidai da juna, babu rikici ko rarrabuwar kai. Ya ce suna da cikakken yarda da tsarin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu, kuma suna da yakinin cewa wannan tafiya za ta ɗora Najeriya kan turbar cigaba.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu juriya da kwarin gwiwa a wannan lokaci da kasar ke fuskantar ƙalubale. Ya roƙi jama’a da su mara wa tafiyar Shugaba Tinubu baya, tare da fahimtar cewa mafita mai dorewa na bukatar lokaci da aiki tare.
Daga cikin manyan jiga-jigan da s**a halarci taron akwai Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda; tsohon Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari; Sanata Abu Ibrahim; tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, Hon. Faruk Adamu Aliyu; da Shugaban Hukumar NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya), da wasu fitattun shugabanni daga sassan ƙasar.