18/07/2023
MTFE (Metaverse Trading Forex Exchange):
Kusan wata guda nayi magana da abokina dan uwa Barr Abdul-Hadi Isa Ibrahim daya daga cikin masanan da muke alfahari dasu a fagen ilmin Blockchain da Cryptocurrency akan MTFE, AlhamdulilLah ya mana binciken kwakwaf akan MTFE, kuma na gamsu da bincikensa, zamu shiga MTFE da sunan Allah
Kamar yadda kwanakin baya nace zan bayyana sak**akon bincike na akan MTFE da kuma matsaya ta da fahimta ta akai, da ikon Allah yau itace rana ta farko da zanyi hakan, kuma zanyi hakan ne a cikin rubutu guda uku da zan fitar dasu nan gaba, in sha Allah, wannan shine na farko, sai dai mu masu bincike ne, don haka sai a gafarce mu da duk abinda za a gani a cikin binciken mu, ba munyi ne don faranta ran wani ko bakanta ran wani ba.
~ Sak**akon binciken na raba shi Kashi uku, kuma ba zan bayar da karfi wa Technical part sosai ba, zan fi bayar da muhimmanci wa Legal Position na MTFE din ne da kuma what is going behind the scene, wannan rubutun ba shi yake nuna mun kammala bincike ba, sai dai resting position ne so far.
1. Abu na farko, k**ar yadda na fada kwanaki, MTFE ba Crypto bane, dan haka bincike akan sa yana bukatan Extra knowledge, Extra tools and extra time. Dan haka comparing research akan MTFE da Crypto wajen research ba zai bayar da Ma'ana ba.
2. Na biyu, bincike na a yanzu ya nuna mun cewa MTFE tana k**a da Forex Broker, wacce take da tsarin trading guda biyu: Manual Trading da kuma AI ko (Artificial Intelligence Trading Machine), toh amma akwai wata magana guda 'daya a nan wacce zata bayyana maka dalilin da yasa nace MTFE tana k**a da Forex Broker👇
~ Bincike na ya nuna mun cewa AI dake kan MTFE baya Trading, sai dai yana aikin rarraba profits ne, wato AI din yana rarraba Ribar da aka samu ne ga investors a MTFE.
~ Bincike na ya nuna mun cewa MTFE sun zo da wani tsarin da ya sabawa yadda ake ganin Forex Brokers, asalin Forex Brokers suna yawan amfani da Leverage da Merging trading ne, wanda kai tsaye kusan kowa yasan wannan tsarin Haramun ne idan ba wadanda s**a kaucewa tsarin ba.
~ Bincike na ya nuna cewa MTFE suna amfani da wani tsari ne da ake kira (Contract Account Management), yadda tsarin yake shine:
Su masu Kamfanin MTFE suna amfani da Contract Account wajen tara Kudaden Investors a waje 'daya, na farko kenan.
~ Na biyu, sai su dauki wani kaso daga cikin Kudin suje suyi trading a asalin Forex Market, idan sun samu Riba sai suzo su rabawa dukkan investors base on abinda ka saka bisa tsarin alkawarin da s**a zayyana akan duk abinda ka shiga dashi.
~ Bincike na ya bayyana mun cewa MTFE suna da Masana a harkar Forex sama da mutum 'dari 230, wadanda ake tsammanin babu k**ar su a duniya wajen juya kudade a harkar Forex a duniya, wadannan Gurayen sune Kamfanin MTFE ya dauka suke wannan trading tare da dawowa da Kamfani sak**akon trading din.
~ Bincike na ya bayyana mun cewa Masanan suna yin trading din ne a cikin Dakika Dari uku (300 seconds).
Binciken ya nuna mun cewa Kamfanin MTFE yana biyan Investors kaso 40, sai kaso 20 na Kamfanin MTFE, sai Kaso 20 na wadannan Masanan da aka dauko suke aiki wa Kamfanin, sai kaso 10 na Maintenance da kuma kaso 10 na Support Development Department, wato Sashe ne s**a bude domin taimakon wuraren da Gobara ta lalata, ko Ambaliya ko cututtukan Kananan Yara ko wadanda Yake yake ya shafe su a fadin duniya.
~ Bincike na ya nuna mun cewa, bayan MTFE sun hada kudaden investors waje 'daya s**an raba shi kaso goma, sai su dauki kaso 'daya su bayarwa Masana Forex trading suje suyi trading a cikin Seconds 300 da Bankuna da kamfanonin duniya suke shiga kasuwar.
~ Idan s**a samu lost sai su koma su sake dauko kaso 'daya cikin 9 da yayi saura suyi trading, ko suyi 'kari akan abinda ya ragu a trading din farko. Wannan tsari ne dake nuna cewa akwai Hikima da dabara da kwarewa a cikin sa wajen kasuwanci.
~ Har wa yau binciken ya nuna cewa a cikin trading 100 da MTFE za suyi s**an samu 93 percent correct, 7 percent ne kawai ake iya samun jarabawar faduwa a ciki.
~ Nazari da nayi ya nuna basa shiga Kasuwar da dukkan Kudaden Investors, sai dai da wani kaso ko wasu kaso na kudaden da suke ajiye su a Contract Account Management.
Idan sun samu Riba investors s**an gani a profit dinsu, idan an samu faduwa ma haka.
~ Bincike na ya nuna cewa Kamfanin MTFE yana samun riba sosai wanda hakan abu ne me wahala abun ya tsaya a nan kusa ko kwanan nan ko watannin kusa kusa.
Sai dai shigowar AI trading machine a cikin harkar yazo da Abu biyu:
Ya rage yawan faduwa a trading, Kuma ya rage yawan Ribar da ake samu.
Bincike na ya nuna cewa wani lokaci MTFE s**an yi amfani da AI din wajen trading, amma ba kowane Account ne suke masa haka ba, akan yi ba tare da ma ka sani ba.
~ Ya matsayin Profits din da ake samu?
Misali, a Dala 26 zaka samu 0.6 if am not forgotten, amma ya danganci irin Kasuwanci da Ribar da aka samu a Kasuwar, wato babu tabbas yau zaka samu Dala kaza, ta yuwu a samu abinda kake so sama da haka ko 'kasa da haka, wannan tsarin ba laifi bane a Shari'a.
~ Wani zai ce an iyakance Ribar da zaka samu ai, ita kuma kasuwa ba'a iyakance mata Riba. Toh a nan sai muce, su masu MTFE suna cewa idan kana da ilimin Forex ka hau kan Application din kayi da kanka duk abinda ka samu wannan naka ne.
~ Sai 'dan abinda zaka biya na charges da sauran su. Idan kuma baka da ilimin Forex toh kazo kayi amfani da AI Machine dinsu, amma a nan sun bayyana in an samu riba kana da kaza da kaza, idan faduwa ce kana da kaza. So babu laifi don mutum yayi amfani da ilimin sa yayi maka aiki yace kaza a biya shi, idan kuma da ilimin ka zaka yi toh ga kaza da kaza.
~ Wani zai ce idan ka saka Kudi suna daukan 3 percent a farko, wannan ba Haramun bane, domin k**ar Haraji ne ko Tax ko kuma k**ar Kudin da kake biya ne idan ka baza kayan ka a kasuwa.
Domin Kudi s**a kashe s**a samar da Protocol din dake aikin, da Application din da kake daukowa a Play Store, da maintenance duk su suke yi kuma kullum kudade suke kashewa wajen Kula da wadannan abubuwan, babu yadda zaka ce ba zasu karbi Kudi ba.
~ Wani zai ce toh idan sun gudu ya za'a yi kenan ai ba'a san su ba?
Bincike na ya nuna mun suna da Rijista da Gwamnatin kasar Canada (idan ban manta ba), kuma rashin sanin su ba zai mayar da abun Haramun ba. Domin a lokacin da nake magana akan matsayin Decentralization a Musulunci na kawo dogon Hadisin nan da Manzon Allah ya bada labarin mutumin da ya bayar da aron Kudin sa ma wani mutum a wani zamani can da dadewa sosai.
~ Mai bayarwa bai san me karba ba, shima me karba bai san me bashi ba, wanda ya karba ya gagara dawo da Kudin sai ya saka a Kogi a cikin ruwa yayi addu'a yace Allah ka Kai masa Kudin sa duk inda yake. Kaga wannan karshen Decentralization kenan.
~ Wani zai ce Kudin da suke bamu na Riba (Profits) din shin zai zama halal kenan?
Eh zai zama halal domin na farko na bayyana asalin yadda abun yake gudana behind the scenes. Na biyu sun bayyana ga abinda suke yi da Kudin shine Forex trading, kuma wanda babu leverage da merging a cikin sa.
~ Idan kace baka yarda ba sai ka kawo dalilin da zai bayyana ba Forex suke yi ba, idan an samo dalilin sai a duba aga abinda suke yi Haramun ne? idan Haramun ne toh Profits din ya zama Haram, idan ba Haram bane toh profit din ya zama Halal.
~ Idan kuma aka gagara samowa toh dole a tsaya akan abinda s**a ce suna yi ko abinda bincike ya nuna suke yi, domin shine Hujja.
Sa'annan Anouymity baya nuna Haramcin, k**ar Bitcoin ne idan kace lallai sai ka San waye yayi kafin ka yarda toh ba zaka taba yarda ba.
~ Wani zai ce toh ai idan sun juya Kaso 'daya na kudaden investors ai sun samu Riba ina sauran kudin suke kenan? sun zama mallakin Kamfanin MTFE kenan?
No, bai zama ba, domin idan kace kana so ka cire Kudin ka yau toh zaka iya cirewa ba tare da ance ka dawo da Ribar daka samu a baya ba, so Kudin na Investors ne matukan uwar Kudin ka sunan nan kuma an baka Ribar sak**akon trading din. Kuma hakan ba laifi bane matukan zasu dawo su bayar da abinda s**a samu wa investors, misali:👇
Manzon Allah (S.A.W) ya bayar da Kudi Dirhami 'daya wa Sahabin sa Mai suna "Urwa Bin Ja'ad Al-Baariqeey", yace kaje Kasuwa ka Sayo mun Rago zanyi Layya, ko Akuya (a wata Riwayar), Urwa Al-Baariqeey yace sai na tafi Kasuwa da Dirhami daya, sai naje nayi wani tsarin trading sai Dirhami 'dayan ta bani dama na sayi Raguna guda biyu.
~ Sai na siyar da Rago 'daya aka bani Dirhami 'daya, sai na kawo wa Manzon Allah Rago daya da Dirhami 'daya, Manzon Allah yace ya aka yi haka? ga Kudi an dawo dasu ga Rago anzo dashi?
Sai Urwa Al-Baariqeey yace Ya Manzon Allah kaji irin tsarin trading din da nabi nayi wannan nasarar, dabara ce nayi irin ta kasuwa, sai Manzon Allah ya jinjina masa, yayi masa addu'a.
~ Urwa Al-Baariqeey yace tun daga lokacin da Manzon Allah yayi mun addu'ar nan sai na zama ko 'kasa (Soil) na 'diba sai naci Riba akan ta, saboda dabarbarun Trading da na samu Karin su saboda addu'ar Manzon Allah.
Babu lokaci da za muyi Sharhin Hadisin, amma a takaice yana nuna maka cewa tsare tsare da dabarbarun samun Kudi s**an zo kala daban daban, idan baka sani ba kada ka karya ta.
~ Wannan Hadisin, Karanta Sunanut Tirmiziy, Hadisi na 1,258.
~ Ibnu Majaah, a Hadisi na 2,402.
Sheikh Muhammad Naseer yace (Sahihi ne).
~ Na biyu, Urwa Al-Baariqeey yace ko 'kasa ya diba sai ya samu Riba akai idan ya siyar, da wane dalili zaka Haramta Ribar wanda ya samu Kudi daga Forex trading? Ina ganin wanda ya samu Riba daga siyar da 'kasa shi ya k**ata a zamanance irin zamanin mu.
~ Binciken yana nuna mun cewa ba Pyramid scheme ko Ponzi scheme ne da wasu ke tunani ba, ka dai ji abinda yake gudana behind the scene kenan, wannan a irin nawa bincike nan, "If you don't trust mine, write yours".
~ Rubutun zai yi tsawo gaskiya, zan 'dora a rubutu na gaba, abinda nake cewa shine:
MTFE a bincike na a yanzu ba laifi bane, dan haka kuci daga arzikin Ubangiji.
~ Ba kadai bincike nayi akai ba, na ma yi Rijista da MTFE yau Asabar, wanda zai shiga sai yayi amfani da Code dina don nima na samu Ladan da ake samu.... Kamar yadda su ma masu MTFE s**a samun Ladan kudade daga wajen ka idan ka shiga.... Code din shine👇
2742483
Sai dai a kowane lokaci dole ka dinga kula da yin taka tsantsan akan abubuwan dake tafiya a zamanin ka, kada don ance ana samun Kudi kayi ta rawar jiki wajen lallai sai ka shiga da karfi.
~ Bincike na a yanzu ya bani dama da dalilin shiga MTFE duk da cewa ina da sauran maganganu masu a gaba, in sha Allah.
A kowane lokaci idan sak**akon bincike ya Canza to hukunci dole zai Canza.
Na bude group WhatsApp domin MTFE, wanda ya ke da bukata ga link
https://chat.whatsapp.com/GDnHLYH67ixFTzmFdM1KL7
Allah Ya sa mu dace 🙏