Funtua News24

Funtua News24 Funtua News24 Domin samun labarun garin Funtua da kewaye a lokacin da suke faruwa.

Duk Wanda Yasan Yayi Rejister To Ba Sai Yakaraba .Mai girma mistar harkaki jinkai da rage radadin talauci,  Dr bette edu...
06/10/2023

Duk Wanda Yasan Yayi Rejister To Ba Sai Yakaraba .

Mai girma mistar harkaki jinkai da rage radadin talauci, Dr bette edu, tace za'ayi amfani da tsohon register da akayi ne abay wajen biyan kudi sannan za'akara mutum 3m daga wurarenda ya dace a fadin kasar, register zai fara daga wannan watan da muke ciki na October Sannan za'abiya nan bada jimawa ba

RRR Ga Lambobin Wasu Jahohin Najeriya

Kowa yayi kokari yacika idan kuma kataba cikawa bakasamu kajira

Abia – *969*44 #
Bayelsa – *969*53 #
Kogi – *969*26 #
Imo – *969*235 #
Rivers State – *969*50 #
Ebonyi – *969*44 # *969*40 # for Ohaukwu-ebonyi
Ekiti – *969*52 #
NASARAWA STATE: – *969*90 #
Lagos – *969*98 #
Katsina – *969*77 #
Gombe code- *969*76 #
Adamawa – *969*22 #
Maiduguri – *969*10 #
Osun State – *969*54 #
Oyo – *969*20 #
Bauchi – *969*113 #
Abuja – *969*67 #
Sokoto State. *969*84 #
Yobe -*969*12 #
Anambra – *969*22 #
Akwa Ibom – *969*52 #
Cross River – *969*54 #
Kebbi – *969*86 #
Taraba – *969* 66 #.

04/10/2023

'Yan bindiga sun sace dalibai mata guda biyar cikin daren jiya Talata na jami'ar FUDMA, da ke karamar hukumar Dutsinma jihar Katsina. Muna Addu'ar Allah ya kubutar dasu cikin aminci, Allah ya kawo mana karshen wannan musifan.

YANZU YANZU: Al'ummar arewa, sunyi ƙira ga BBC Hausa kan cewa Nan da awanni 24, idan basu ɗora zanga-zangar lumana da al...
02/10/2023

YANZU YANZU: Al'ummar arewa, sunyi ƙira ga BBC Hausa kan cewa Nan da awanni 24, idan basu ɗora zanga-zangar lumana da al'ummar Arewacin Najeriya da Sukeyi ba a shafukan su na sada zumunta, zasu daina bibiyar labaran su mai gaba ɗaya.

Wani ƙira zakuyi wa BBC Hausa...?

Da Dumi DumiSojoji Sunyi Juyin Mulki a Nijar.Hakan Yafaru ne tayanda wasu sojoji kalilan s**a fito gidan TV s**a bayyana...
27/07/2023

Da Dumi Dumi

Sojoji Sunyi Juyin Mulki a Nijar.

Hakan Yafaru ne tayanda wasu sojoji kalilan s**a fito gidan TV s**a bayyana Hakan,

Sunce Sunyi Hakan ne saboda irin kuncin da ake ciki da Kuma tattalin Arzikin kasar na shirin karyewa

Ku biyomu domin Jin ingantaccen labari game da abunda ke kafuwa.

22/07/2023

An gudanar da karatun KUR'ANI tare da yima kasar najeriyar addu'o in Zaman lafiya sakamakon shigowar sabuwar shekarar musulunci a babban Masallacin Juma'a na bakin shataletalen tsakiyar garin Funtua a karkashin Malaman Darika na garin funtu.

Taron ya ya samu halartar Malamai, alarammomi da kuma almajirai haka kuma magajin Garin Funtua ya samu halartar taron kuma anyi an gama lafiya.

Allah ya bamu zaman lafiya.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya karbi bakuncin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso...
18/07/2023

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya karbi bakuncin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a gidan gwamnatin jihar Katsina, ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023.

18/07/2023

YANZU-YANZU: Gwamnatin Nijeriya Ta Fasa Rabawa Talakawan Ƙasar Naira Dubu 8 Na Tsawon Wata 6 Da Tace Za Ta Rabawa Mutane Miliyan 12

Daga Comr Abba Sani Pantami

Farashin kayan masarufi ya ƙara tashi a NajeriyaYa yanayin yake a yankin ku?
17/07/2023

Farashin kayan masarufi ya ƙara tashi a Najeriya

Ya yanayin yake a yankin ku?

Da Dumi DumiKotu ta bayar da umarnin sakin tsohon kwamishinan Ganduje
15/07/2023

Da Dumi Dumi

Kotu ta bayar da umarnin sakin tsohon kwamishinan Ganduje

Da Dumi Dumi Jirgin sojoji Nigeria yayi Hatsari
14/07/2023

Da Dumi Dumi

Jirgin sojoji Nigeria yayi Hatsari

A cikin makon nan ne hukumar Kare Haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) ta amince da ƙudirin hukunta duk mutumin da y...
14/07/2023

A cikin makon nan ne hukumar Kare Haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) ta amince da ƙudirin hukunta duk mutumin da ya nuna ƙiyayya ga wani addini, inda ta nemi ƙasashe su yi hakan.

An gabatar da ƙudirin ne bayan ƙone-ƙonen Al-Ƙur'ani da wasu ke yi a baya-bayan nan.

Ya kuka ji da matakin?

YÀNZÙ - YANZÙ: Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Naira 8,000 Duk Wata Ga Talakawan Najeriya Mutum Miliyan 12 Na Tsawon Watann...
13/07/2023

YÀNZÙ - YANZÙ: Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Naira 8,000 Duk Wata Ga Talakawan Najeriya Mutum Miliyan 12 Na Tsawon Watanni 6, Inji Shugaban Kasa Bola Tinubu.

Da zaran sun fitar da yadda tsarin samun kudin zai kasance Insha'Allahu zamu sanar muku.

DAGÀ: Comr Abba Sani Pantami

BABBAN LABARI Babban Hafsan sojojin Nigeria Lagbaja ya umarci rundunar sojoji ta 82 akan lallai su bincika su kamo yan I...
13/07/2023

BABBAN LABARI

Babban Hafsan sojojin Nigeria Lagbaja ya umarci rundunar sojoji ta 82 akan lallai su bincika su kamo yan IPOB a duk inda suke buya a yankin South East.

Sannan ya nemi Gwamnonin yankin North West akan su janye hannunsu akan batun sulhu da Bandits domin bawa sojoji damar kurmushe yan kidnapping dake addabar yankin.

Lagbaja bai tsaya anan ba, yayi kira ga sojoji akan lallai su kawo karshen masu haifar da rikice rikicen dake jihar Plateau...

- Rabiu Biyora

LÁBARI MAÍ DADI GA TALAKAWAŃ NÀJERIYA Shúgaban ƙasa Bola Tinubu, ya rubutawa majalisar wakilai wasiƙa yana néman ta amin...
12/07/2023

LÁBARI MAÍ DADI GA TALAKAWAŃ NÀJERIYA

Shúgaban ƙasa Bola Tinubu, ya rubutawa majalisar wakilai wasiƙa yana néman ta amince mishi domin ya rabawa 'yan Najeriya Naira biliyan 500 domin rage musu radadin halin da s**a shiga kan cire tallafin Man Fetur.

A zaman majalisa na yaune kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta wasikar shugaban kasar a zauren majalisar. Idan s**a amince da wannan kudirin tabbas talakawan Najeriya zasu amfana musamman idan aka bi tsarin tsohuwar Gwamnati.

Fatanmu Allah yasa wannan kudirin ya tabbata, Allah yasa duk wa 'yanda suke da alhaki akan Approval din su amince da wuri.

DAGÁ: Comr. Abba Sani Pantami

SAKON AL'UMMAR SABUWAR ABUJA SOKOTO BYE PASS FUNTUA LG KATSINA STATE ...ZUWA GA SABABIN SHUWAGABANNI MU TUN DAGA CHAIRMA...
12/07/2023

SAKON AL'UMMAR SABUWAR ABUJA SOKOTO BYE PASS FUNTUA LG KATSINA STATE ...

ZUWA GA SABABIN SHUWAGABANNI MU TUN DAGA CHAIRMAN DANMAJALISAR JAHA HAR ZUWA SANATAN WANNAN YANKI DAN MAJALISAR TARAYYA .....

Sabuwar Abuja Unguwar Dake Cikin Garin Funtua mai dauke da adadin gidaje masu yawa da tare al'umma masu dinbin Yawa ..

Al'ummar wannan Yanki suna da Buqatuwar Abubuwan more rayuwa da yawa duba da yadda unguwar sabuwar unguwace kuma tana yamma da Garin Funtua..

Daga Cikin Abubuwn da Al'ummar wannan Yanki suke fatan Samu daga wannan sabuwar Gwamnati Mai Albarka Wanda Al'ummar wannan Yankin ke fatan Share masu hawayen su.

= MATSALAR WUTAR LANTANKI :-
Matsalar wuta lantarki Babbar matsalar dake cima Al'ummar wannan Yankin Tuwo a kwayar musamman wadanda ke zaune a chan kasan unguwar , a halin Yanzu Transformer Daya ce kawai Ke aiki a wannan Unguwa duk da yawan Al'umma da gidajen dake rayuwa a wannan Yankin..

Wanda a gwamnatin baya Ayi ma Al'ummar Wannan Unguwa Alqawura Ba adadi Amma cikar tayi wahala.

Al'ummar wannan ungw suna kira da wanna Gwamnati data dubawa wannan Al-amari na matsalar wutar lantanki a wannan unguwar...

=MATSALAR HANYA DA HANYOYIN RUWA:-
Duba da yanayin Unguwa sabuwar Unguwa ce Al'ummar Wannan Yanki suna da Buqatar hanya da Hanyoyin Ruwa Duba da yanayin Damina Damuke Ciki Akwai wahala mai yawa idan akayi ruwa ga Al'ummar wannan unguwa....

=PRIMARI SCHOOL:-

Wannan unguwa na da buqatar Primary School duba da yadda unguwar take da yara Qanana Wanda Population Na su Yafi Na sauran Al'ummar dake Rayuwa a wannan uguwar , hakan zai saukaka masu damar zuwa makaranta cikin lokaci da rage fargabar iyaye sabida tsallaka t**i a yayin Zuwa makaranta....

Wadannan Sune Muhimman Abubuwan Da zan iya hakaitonawa ....

Amma Ba ina Nufin Sukadai ne buqatun Al'ummar wannan yakin ba..

ALLAH YASA SHUWAGABANNIN DA SAURAN WAKILAN MU SUJI WANNAN KOKE KUMA ALLAH YABASU IKON DAUKAR MATAKI DON GANIN SUN SHAREWA AL'UMMAR WANNAN UNGUWA HAWAYAN SU

RUBUTAWA 
Abdulmali

LÀBARI MAI DADI: Majalisar wàkilai ta dòkatar da karin kudin karatu a jami'o'in Gwamnatiń Tarayya da ake shirin kakabawa...
11/07/2023

LÀBARI MAI DADI: Majalisar wàkilai ta dòkatar da karin kudin karatu a jami'o'in Gwamnatiń Tarayya da ake shirin kakabawa talakawa. Majalisar tace karin kudin makarantar babbar illa ce domin dalibai da dama za su hakura da karatu a kasar.

Muna Addu'ar Allah ya basu ikon tabbatar da wannan babban aikin, domin na tabbata zai taimaki talakawan Najeriya.

DAGÀ Comr Abba Sani Pantami

Saƙo Na Musamman Ga Ƴan S-Power Na Jihar Katsina..Za a tantance waɗanda za a ɗauka aiki kamar yadda gwamnatin jihar Kats...
11/07/2023

Saƙo Na Musamman Ga Ƴan S-Power Na Jihar Katsina..

Za a tantance waɗanda za a ɗauka aiki kamar yadda gwamnatin jihar Katsina ta ayyana.

A Ranar Laraba 12-07-2023 da Alhamis 13-07-2023 za a yi "Screening" watau tantancewa domin tabbatar da haƙiƙanin Ƴan S-Power da zasu zauna jarrabawar malanta a jihar Katsina.

An tsara wuraren da za a yi tantancewar zuwa gida bakwai 7

Kowane Ɗan S-Power zai yi Amfani da ƙaramar hukumar shi da aka bashi S-power a ƙarƙashin ta ba wacce yayi transfer ya koma ba domin sunansa a can zai fita Sai Ya garzaya Zonal Office ɗin da aka fidda domin yima Ƴan local Government ɗin sa Screening domin a tantance shi.

Wannan saƙo ya shafi S-Power Graduates ne kaɗai.

Allah yabada Sa'a Amin.

Daga Muhammad Aminu Kabir

“Mutanen Yammacin Afrika sun daura tulin nauyin jagorantarsu a kan sabon shugabanmu.Aikinmu ne a matsayin ‘yan kasa mu m...
11/07/2023

“Mutanen Yammacin Afrika sun daura tulin nauyin jagorantarsu a kan sabon shugabanmu.

Aikinmu ne a matsayin ‘yan kasa mu mara masa (Bola Tinubu) baya, ka da mu ba shi kunya.

Ina rokon Ubangiji ya sa wa’adinsa ya dawo da martabar ECOWAS a matsayin jagora.”

- Muhammadu Buhari a kan Bola Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta koka ganin yadda yawan shan mai a kasar ya ragu da fiye da lita miliyan 18 a wata.A cewarta, hakan ...
10/07/2023

Gwamnatin Tarayya ta koka ganin yadda yawan shan mai a kasar ya ragu da fiye da lita miliyan 18 a wata.

A cewarta, hakan bai rasa nasaba da cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayu.

Kafin cire tallafi ana shan mai fiye da lita biliyan 11 amma yanzu bai wuce lita miliyan 18.5 bayan an cire tallafi.

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta zargi gwamnan jihar Osun da tauye haƙƙin Musulmin jihar.Daraktan ƙungiyar Farfe...
10/07/2023

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta zargi gwamnan jihar Osun da tauye haƙƙin Musulmin jihar.

Daraktan ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan zargin.

Ya kuma zargi Gwamna Ademola Adeleke da yi wa ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), aiki.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Kano, Eng. Abba K. Yusuf, ya naɗa Malam Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin shugaban hukumar Hi...
10/07/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Kano, Eng. Abba K. Yusuf, ya naɗa Malam Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin shugaban hukumar Hisba.

Hakan na nufin Threads, wanda mallakin kamfanin Meta ne ya doke tarihin da manhajar ChatGPT ta OpenAI ta kafa na samun m...
10/07/2023

Hakan na nufin Threads, wanda mallakin kamfanin Meta ne ya doke tarihin da manhajar ChatGPT ta OpenAI ta kafa na samun mafi yawan masu amfani a cikin ƙanƙanin lokaci.

Address

Tudun Malamai
Funtua
830101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua News24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Funtua News24:

Share