Rariya

Rariya Wannan jarida Rariya, an yi tunanin samuwar ta don masu amfani da harshen Hausa duk inda suke a duni
(2)

"Saboda Šhaķiýanci Irin Na Musa Mai Sana'a Ya Sa Ni Na Dinga Yin Bilicin Don Na Yi Fari Saboda Wai Zan Fito A Wani Fim D...
09/12/2024

"Saboda Šhaķiýanci Irin Na Musa Mai Sana'a Ya Sa Ni Na Dinga Yin Bilicin Don Na Yi Fari Saboda Wai Zan Fito A Wani Fim Dins A Matsayin Mahaifiyar Sani Danja, Ashe Karya Yake Ma Babu Fim Din"

Ya Allah Ka Jikan Marigayi Fadar Bege; Wadanne Wakokinsa Kake Tunawa A Duk Sanda Ka Ci Karo Da Hotonsa?
07/12/2024

Ya Allah Ka Jikan Marigayi Fadar Bege; Wadanne Wakokinsa Kake Tunawa A Duk Sanda Ka Ci Karo Da Hotonsa?

ALLAH SARKI: Wadannan Sune Iyalan Marigayi El-Muaz Birniwa Da Ya Rasu Ya BariAllah Ya ba su yadda za su yi.
07/12/2024

ALLAH SARKI: Wadannan Sune Iyalan Marigayi El-Muaz Birniwa Da Ya Rasu Ya Bari

Allah Ya ba su yadda za su yi.

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Wani Alaramma Makaho, Masanin Kur'ani Dake Ja Wa Malamai Baki Ya Rasu A Garin Ankpa...
07/12/2024

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Wani Alaramma Makaho, Masanin Kur'ani Dake Ja Wa Malamai Baki Ya Rasu A Garin Ankpa Dake Jihar Kogi

Allah Ya gafarta masa.

Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Nada Manyan Mukamai A Hukumomin NUC, NERDC, NEPAD Da Kuma SMDFShugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinu...
07/12/2024

Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Nada Manyan Mukamai A Hukumomin NUC, NERDC, NEPAD Da Kuma SMDF

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabanni a hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa, (NUC), hukumar bincike da bunƙasa harkokin ilimi, (NERDC), da asusun ma’adanan ƙasa, da haƙar ma’adanai, (SMDF/PAGMI), da hukumar samar da haɗin gwiwa domin cigaban Afrika, (NEPAD).

A rahoton da Rariya ta samu daga mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Furofesa Abdullahi Yusuf Ribaɗo a matsayin shugaban hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa.

Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Furofesa Salisu Shehu a matsayin babban sakataren hukumar bincike da haɓaka ilimi ta ƙasa.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da naɗin Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri a matsayin shugaban hukumar samar da haɗin kai domin bunƙasa Nahiyar Afrika.

Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Yazid Shehu Umar Ɗanfulani a matsahin babban sakataren asusun ma’adanai da haƙar ma’adanai na ƙasa.

Sanata Babangida Hussaini (Walin Kazaure) Ya Kaddamar Da Rabon Littafi Da Sauran Kayan Karatu Domin Tallafawa Harkar Ili...
07/12/2024

Sanata Babangida Hussaini (Walin Kazaure) Ya Kaddamar Da Rabon Littafi Da Sauran Kayan Karatu Domin Tallafawa Harkar Ilimi A Kananan Hukumomi 12 Dake Mzabarsa A Jihar Jigawa.

Haka kuma Sanatan ya baiwa makarantar Sakandiri ta mata dake Garin Garki Sabuwar Mota Kirar Toyota Hiace (Hummer).

KUNCIN RAYUWA: Wata Kungiya Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci Da Kayan Rubutu Ga Marayu, 'Yan Gudun Hijira Da Dalibbai M...
07/12/2024

KUNCIN RAYUWA: Wata Kungiya Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci Da Kayan Rubutu Ga Marayu, 'Yan Gudun Hijira Da Dalibbai Marasa Galihu A Jihar Sokoto

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto

Wata kungiyar ƴan kasa masu kishin cigaba ta "Concerned Citizens of Likes Minds (CCLM)" ta kaddamar da rabon tallafin kayan abinci da kayan karatu da rubutu ga Marayu da ɗalibai, 'yan gudun hijira da sauran mabukata a jahar Sokoto.

Ita dai kungiyar "Concerned Citizens Of Likes Minds (CCLM)" kungiya ce da aka assasa wadda ke da wakilci a ko'ina a faɗin Nijeriya daga.

Kungiya ce da aka samar domin tallafawa al'umma musamman marayu da masu karamin karfii da ɗalibai, domin ganin an inganta rayuwar su kamar kowa a ko'ina a faɗin Kasar nan.

Wannan ne yasa kungiyar tayi tattaki ta garzayo Sokoto inda aka kaddamar da kayan Abinchi a gidan marayu, da kayan Abinchi ga ƴan gudun hijira, tare da kaddamar da littafan karatu da rubutu ga wasu makarantu na jahar Sokoto, karkashin jagoranchin shugabar kungiyar Chairlady Hajiya Madina.

Wannan dai anyi shine duka cikin namijin kokarin shugaban ma'aikatan Tsaro na kasa (Chief Of Defence Staff) Christopher Musa ga jahar Sokoto domin saukakawa rayuwa musamman a wannan Lokachi da ake fama da tsananin rayuwa da rashin tsaro.

Sakataren kungiyar na ƙasa, Comrd Ibrahim Riskuwa ya yi kira ga wadanda s**a amfana da su yi amfani da abinda s**a samu ta hanya mai kyaw, tare da jan hankalin ɗalibbai da su mayarda hankali ga karatu wurin zama jekadu na gari abin alfahari ga Sokoto da Nigeria baki ɗaya

IKON ALLAH: Makaho Da Baiwar Da Ko Wasu Masu Idon Ba Su Da ItaDaga Abdullahi Garba Eliki Taura1. Ibrahim Idris Makaho ne...
26/11/2024

IKON ALLAH: Makaho Da Baiwar Da Ko Wasu Masu Idon Ba Su Da Ita

Daga Abdullahi Garba Eliki Taura

1. Ibrahim Idris Makaho ne.

2. Ya haddace Al-Qur'ani.

3. A wannan shekarar yafi kowanne dalibi cin jarabawar jamb a Shuwarin jihar Jigawa.

4. Yana koyar da mutane a garinsu.

5. Babu platform din da bashi da account Facebook, WhatsApp, Instagram, X da sauransu.

6. Yana TV games Kamar Mortal Kombat, SEGA da sauransu kuma ko masu ido basa beating dinsa.

7. Yana gyaran waya.

8. Yana sanaar Data, domin ya tabbatar mana saida ya shiga yayi processing komai zai turamin 3GB na hanasa.

9. Mun fada masa sunayenmu duk waddanda s**a sake magana yaji muryarsu zaice wanene, kuma ance ko bayan shekara mutum ya dawo zai Fadi sunansa.

Yanzu ya samu admission a Sule Lamido University rashin typewriter ya hanasa tafiya. A yau shugabannin kungiyar Daliban NAJISS sun samar masa da typewriter zai koma zai dora da karatunsa.

There's indeed ABILITY in dis-ABILITY

Abdullahi Garba Eliki Taura,
Shine Najiss National President.

CIGIYA Sama Da Mako Guda Kenan Da Ta Bar Gidan Mijinta Ita Da Yaronta Dan Shekara Daya, Amma Har Yanzu Babu LabarinsuWan...
26/11/2024

CIGIYA Sama Da Mako Guda Kenan Da Ta Bar Gidan Mijinta Ita Da Yaronta Dan Shekara Daya, Amma Har Yanzu Babu Labarinsu

Wannan kanwata ce. Sunanta Maryam Sa'idu. Ta bar gidan mijinta tun ranar 17/11/2024 tare da yaronta dan kimanin shekara daya kuma mun neme ta duk inda ya kamata amma ba a samu wani labari game da ita ba.

Jama'a muna neman addu'a kuma muna bada cigiya. Sannan Dan Allah a taimaka a yada (sharing) wannna posting din ko Allah zai sa a ganta.

Da fatar Allah Ya sa a ganta, Amin Ya Hayyu Ya Qayyum.

Ga lambobin da za a kira idan Allah Ya sa an ji wani labari nata;
080 3942 777
09066694380
07067394415
08105525143

Ko kuma a kawo ta kai tsaye zuwa gidan Alhaji Saidu dake filin Magajiya Gusau jihar Zamfara.

Daga Abba Sa'idu

Abubuwa Guda 5 Idan Allah Ya Sa Yarinya Ta Mallake Su To Da Wuya Ta Bayar Da Ciwon Kai A Alaka Ta Mu'amalar Neman Aure K...
26/11/2024

Abubuwa Guda 5 Idan Allah Ya Sa Yarinya Ta Mallake Su To Da Wuya Ta Bayar Da Ciwon Kai A Alaka Ta Mu'amalar Neman Aure Ko Bayan Aure

Daga Zoohrah Oummu Deederht

1) Saukin Hali da kwantar da kai da Tawadi'u (Jin ita ba komai bace kamar kowa take), da girmamawa, gami da qarancin Buri da hange hangen abin da bata da shi.

2) Tarbiyya irin ta Islama (ta kunshi komai me tsarki Halattacce).

3) Furuci: Harshe me sauki, wata akwai kaifin harshe, idan ta yi wata maganar ko barci sai da kyar.

4) Ilimin sanin Allah gwargwado da kokarin aiki da shi (wannan yana wiya, sai me rabo).

5) Iya zama da mutane wato mu'amala.

Na zauna da yara ýan mata da yawa, kuma duk inda na rayu da su, su shaida ne bana taba yin shiru kan abin da na ga zai cutar da yarinya a rayuwar ta na dabi'a, na kan so inga mace ta sauke duk wani hayaki da kuwwar shaiďan da take buga ta, na san ta haka ne kaďai za a ji dadin zama da ita duk inda ta shiga a duniya, don bata san inda Allah zai kai ta ta rayu ba, ba ta san kalar rayuwar da za ta tarar ba, ba ta san kalar mutanen da za ta rayu da su ba, ta haka ne za a ji daďin mu'amala da ita ta kusa ko ta nesa, kuma zaman ya yi karko.

Amma idan kina jin Ki very High! Wanna ciwo ne babba wanda idan ba'a sauke ba akwai damuwa a gaba.

Yana da kyau .ace da Aji na sosai, amma ba kyau mace da taurin kai da girman kai da ďagawa, akwai banbanci.

Allah Ya shirya mana zuri'a kan hanya madaidaiciya. Amin.

Masu Cewa Abba Ya Tsaya Da Kafarsa, Me Ya Sa A Lokacin Yakin Neman Zabe Ba Ku Ce Masa Ya Tsaya Da Kafarsa Sai Bayan Ya Z...
26/11/2024

Masu Cewa Abba Ya Tsaya Da Kafarsa, Me Ya Sa A Lokacin Yakin Neman Zabe Ba Ku Ce Masa Ya Tsaya Da Kafarsa Sai Bayan Ya Zama Gwamna?

Tambayar Sheik Bello Yabo

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Matashiyar Mahardaciyar Al'qur'ani Mai Girma Ta Rasu A Katsina Allah Ya Yi Wa Matashi...
22/11/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Matashiyar Mahardaciyar Al'qur'ani Mai Girma Ta Rasu A Katsina

Allah Ya Yi Wa Matashiyar Mahardaciyar Al'qur'ani Mai Girma, Hafsat Muntari Imam Rasuwa Da Yammacin Jiya Alhamis A Katsina.

Za A Yi Jana'izarta Da Misalin Karfe 9:00 Na Safiyar Yau Juma'a A Gidansu Dake Unguwar Liman A Cikin Garin Katsina.

Allah Ya Jikanta Da Rahama!

Gwamna Ahmad Aliyu Ya Kaddaramar Da Hukumar Hisba A Jihar SokotoA yayin da shugaban hukumar Hisba na jihar Kano Sheikh I...
22/11/2024

Gwamna Ahmad Aliyu Ya Kaddaramar Da Hukumar Hisba A Jihar Sokoto

A yayin da shugaban hukumar Hisba na jihar Kano Sheikh Ibrahim Daurawa ya samu halartar kaddamar da hukumar a jihar Sokoto

Wanne fata zaku yi musu?

Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto

04/11/2024
Duk Tsadar Da Kujerar Aikin Hajji Za Ta Yi, Ya Allah Ka Sa Muna Cikin Masu Rabon Ziyartar Ɗakinka Mai Alfarma Cikin Wann...
15/10/2024

Duk Tsadar Da Kujerar Aikin Hajji Za Ta Yi, Ya Allah Ka Sa Muna Cikin Masu Rabon Ziyartar Ɗakinka Mai Alfarma Cikin Wannan Shekarar

CIGIYA: Wannan Motar An Sace Ta Jiya A Kaduna. Dan Allah Wanda Allah Ya Sa Ya Gan Ta Ya Kira Wannan Lambar +234803397310...
08/09/2024

CIGIYA: Wannan Motar An Sace Ta Jiya A Kaduna. Dan Allah Wanda Allah Ya Sa Ya Gan Ta Ya Kira Wannan Lambar +2348033973101

Don Allah a taya mu yadawa (sharing) ko za a dace.

KO ZA KA IYA AUREN MACE SOJA?
08/09/2024

KO ZA KA IYA AUREN MACE SOJA?

MUHAWARA: Ko Kana Da Ra'ayin Auren Mace Soja?

Address

Abuja
700345

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rariya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Rariya:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Abuja

Show All