BIDIYO: An ga ma'aikatan Bankin Zenith suna gudu ta katangar baya yayin da kwastomomi suka kewaye kofar don samun kudi.
Ya Rushe Gidan Da Ya Gina Wanda Ya Kai Darajar Miliyan 300, Saboda Ya Saki Matarsa
Daga Aliyu Adamu Tsiga
Sun samu saɓani da matar shi, har abun yakai ga ta ce masa ya saketa idan har wance ta haihefi shi da jini ta kira sunan Mahaifiyarsa. Shi kuma da jin haka kawai sai ya saketa, saboda daman yana faɗa mata duk lokacin da tai kuskuren zagin Mahaifiyarsa to da ga wannan lokacin zaman su ya ƙare duk abun da zatai masa kar ta kuskura ta saka Mahaifiyarsa a ciki.
Bayan ya saketa sai tace mashi to ya maganar gidan da muke ciki kasan dai filina ne, ya ce sani amma kuma ni ne na gina, ta ce to ita filin ta takeso kawai ko kuma ya bar mata gidanta. Shi kuma da yaji haka sai ya fita abin shi, ta ɗauka cewa ya bar mata gidan bayan kwana biyu ta gana sakankancewa ta saki jikinta ta zauna bata tunanin komai.
Sai ga gogan naka zuwan da zai yi sai gashi da tawagar motocin rusau, su katafila da dai sauran su. Tsohuwar matar ta fito hankalinta a tashe me zan gani haka, ta fara yi mishi irin kisisinar nan tasu ta mata shi kuma gogan naka bai ko ɗaga kai ya kalle ta ba ya ce wa, mutanen da yazo dasu a cire komai da ke ciki haka kuwa akai.
Gogan ya bada umarnin rushe wannan gida wanda yakai darajar miliyan 300, ai kuwa suka cigaba da rushe shi, seda suka rushe gidan tas sannan ya samu bakin yi ma tsohuwar matar tashi magana ya ce mata toh ga filin kinan da kika buƙata.
Shin me zakuce kan wannan hukuncin ?
Ni dai Wallahi ya yi min dai-dai.