HNN Hausa

HNN Hausa HNN News Muryar Al'umma, Ku kasance damu domin Samun Ingantattun Labarai da Rahotanni a fadin duniya

Wasu da ake zargin ‘yan fa-shi da ma-kami ne s**a ka-she wani jami’in ‘yan sandan Najeriya mai suna Insfekta Sunday Baba...
25/04/2024

Wasu da ake zargin ‘yan fa-shi da ma-kami ne s**a ka-she wani jami’in ‘yan sandan Najeriya mai suna Insfekta Sunday Baba a yayin wani fa-shi da ma-kami a Rumuolumeni da ke jihar Ribas a daren Laraba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ce ta tabbatar da wannan bayanin ta shafin ta na dandalin sada zumunta.

Buni ya mayar da martani ga kazamin fada da ya faru tsakanin sojoji da mahaya KekeGwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya y...
15/04/2024

Buni ya mayar da martani ga kazamin fada da ya faru tsakanin sojoji da mahaya Keke

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi kira da a kara samun daidaito tsakanin sojoji da fararen hula a Gashu’a.

Buni ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake mayar da martani kan wata arangama tsakanin sojoji da mahaya Keke NAPEP a ranar Lahadi a garin Gashu’a wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, tare da jikkata da dama.

Ya bayyana da cewa abin takaici ne yadda irin wannan lamari ke faruwa a daidai lokacin da jihar ke samun zaman lafiya a fadin jihar.

"Abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne yadda ake asarar rayuka a cikin wani yanayi da za a iya kaucewa," in ji shi.

Yanzu-yanzu: FG ta amince da ranar Alhamis a matsayin karin hutu don bikin Eid-El-Fitr Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ay...
09/04/2024

Yanzu-yanzu: FG ta amince da ranar Alhamis a matsayin karin hutu don bikin Eid-El-Fitr

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Alhamis 11 ga Afrilu, 2024 a matsayin karin hutu a hukumance domin gudanar da bikin Eid-El-Fitr na bana.

08/04/2024

BAYANI AKAN ZAKKAR FIDDA KAI (ZAKÃTUL FITR)

Tare da: Dr. Jabir Sani Maihula (Hapizahullah)

Kungiyar SERAP, ta kaddamar da shari’a a kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan rashin kiran da aka yi wa...
07/04/2024

Kungiyar SERAP, ta kaddamar da shari’a a kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan rashin kiran da aka yi wa Sanatan Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi.

SERAP ta kuma kai karar Akpabio bisa gazawarsa wajen mika takardar kasafin kudin ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, domin gurfanar da shi gaban kuliya.

Ningi ya kara da cewa ba a iya gano Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.

'Yan sanda sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina
06/04/2024

'Yan sanda sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Jamiyyar NNPP ta sauya tambarin ta (Logo) daga kayan Marmari zuwa hoton littafi da hula, tare kuma da sauya Taken Jamiyy...
05/04/2024

Jamiyyar NNPP ta sauya tambarin ta (Logo) daga kayan Marmari zuwa hoton littafi da hula, tare kuma da sauya Taken Jamiyyar zuwa Education for All.

Hakan na zuwa ne bayan wani taro da Jamiyyar ta gudanar na yan majalisar zartarwa na Ƙasa a dakin taro na A-Class dake Maitama babban birnin tarayya Abuja.

A gobe ne ake saka ran Jamiyyar zata gudanar da taro na kaddamar da shugabancin jam'iyyar na Ƙasa, k**ar yadda wakilinmu Jabir Ali Danabba ya rawaito mana.

An bukaci shugabannin Afirka da su yi koyi da Faye, yayin da shugaban Senegal ke bayyana kadarorinsa a bainar jama'aAn b...
03/04/2024

An bukaci shugabannin Afirka da su yi koyi da Faye, yayin da shugaban Senegal ke bayyana kadarorinsa a bainar jama'a

An bukaci shugabannin Afirka da su yi koyi da sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ta hanyar bayyana kadarorinsu a bainar jama'a.

Wata kungiyar farar hula, The Resource Center for Human Rights and Civic Education, CHRICED, ce ta yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata domin bikin rantsar da Faye a matsayin shugaban kasa.

Nasarawa za ta ba da gudummawa ga asusun tarayya ta hanyar Noma, Ma'adinai - Gov Sule Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nas...
01/04/2024

Nasarawa za ta ba da gudummawa ga asusun tarayya ta hanyar Noma, Ma'adinai - Gov Sule

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce dabarun gwamnatinsa shi ne karfafa gudummawar da jihar ke bayarwa ga asusun tarayya ta hanyar bunkasa harkar noma da ma’adinai.

HOTO MAI SOSA ZUCIYA: 'Ya Ce Ga Daya Daga Cikin Sojojin Nijeriya Da Aka Ķàśhe A Jihar Delta
30/03/2024

HOTO MAI SOSA ZUCIYA: 'Ya Ce Ga Daya Daga Cikin Sojojin Nijeriya Da Aka Ķàśhe A Jihar Delta

Duk manufofin gwamnati Tinubu alama ce na raba Najeriya ne, ba hada kan Najeriya ba, wannan dalilin yasa Tinubu ya ɗako ...
28/03/2024

Duk manufofin gwamnati Tinubu alama ce na raba Najeriya ne, ba hada kan Najeriya ba, wannan dalilin yasa Tinubu ya ɗako na uku a kasa daga yankin inyamurai don tabbatar da manufarsa ta Raba kasa. Kowa ya sani cewa, Akpabio yana da zarge-zarge da ake masa na cin hanci da rashawa amma duk da haka ya dako shi ya bashi mukamin shugaban majalisar Dattawan Najeriya.

Kowa yaga yadda ake kwashe wasu muhimman ma'aikatu daga Arewacin Najeriya ana kaisu kudancin kasa, k**ar wasu sashi na babban Bankin kasa, da wasu sashi na zirga-zirgar jirgin saman Najeriya.

Idan ba haka ba taya zai zama ana cikin zaman lafiya zai kwashe muhimman wurare ya mayar da su yankinsa duk da cewa, ba kaunarsa akeyi ba a kudancin kasar. Inji Shu'aibu Mungadi.

Ya bayyana haka ne a wani shirin talabijin na farin wata da ake gabatarwa a gidajen Rediyo Vision FM kwanakin baya.

Tsadar Rayuwa: Ƴan Najeriya na cikin ɓacin rai yayin da yawancin mutane  ke mutuwa don neman abin da za su ci'Yan Najeri...
27/03/2024

Tsadar Rayuwa: Ƴan Najeriya na cikin ɓacin rai yayin da yawancin mutane ke mutuwa don neman abin da za su ci

'Yan Najeriya da dama ne s**a rasa rayu-kansu a cikin 'yan kwanakin da s**a gabata yayin da suke fafutukar cin gajiyar kayan abinci da gwamnati ke rabawa a yayin da ake fama da yunwa a kasar.

New Party Alert: People's Congress PartyThe People's Congress Party (P*P) enters Nigeria's political arena, pledging uni...
23/03/2024

New Party Alert: People's Congress Party

The People's Congress Party (P*P) enters Nigeria's political arena, pledging unity and progress. With a focus on transparency, security and education, they aim to tackle challenges through evidence-based governance. As they navigate registration with INEC, the P*P's commitment to serving all Nigerians signals a potential shift in politics. Stay tuned for updates on their journey.

23/03/2024

"Wanda ya azumci Ramadan sannan ya bi shi da kwanaki shida na Shawwal, k**ar ya azumci rayuwarsa ne." - Sahih Muslim, Littafi na 6, Hadisi na 1164

'Yan bin-diga: An ka-she mutane da dama, an yi garkuwa da su a kasuwar Nijar Wasu ‘yan Bin-diga dauke da Maka-mai sun ka...
22/03/2024

'Yan bin-diga: An ka-she mutane da dama, an yi garkuwa da su a kasuwar Nijar

Wasu ‘yan Bin-diga dauke da Maka-mai sun ka-she tare da yin garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba a kauyen Madaka da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.

An k**a Robinho da laifin yin fya-ɗe a Brazil An k**a tsohon dan wasan Manchester City da Real Madrid, Robinho a ranar A...
22/03/2024

An k**a Robinho da laifin yin fya-ɗe a Brazil

An k**a tsohon dan wasan Manchester City da Real Madrid, Robinho a ranar Alhamis a Brazil, bayan da ya sha kashi a kotu a minti na karshe na jinkirta ci gaba da hukuncin daurin shekaru tara da aka yanke masa kan laifin yi wa wata mata fya-ɗe shekaru goma da s**a gabata.

Anyi ta ho mu gama tsakanin wasu jiragen kasar Ghana 2ATP Hausa
20/03/2024

Anyi ta ho mu gama tsakanin wasu jiragen kasar Ghana 2

ATP Hausa

Dangote na Ciyar da Mutane Dubu 10 a Kano Kowace Rana* Ya Raba Buhunan Shinkafa Milyan Daya a Fadin Nijeriya Rahotanni s...
19/03/2024

Dangote na Ciyar da Mutane Dubu 10 a Kano Kowace Rana

* Ya Raba Buhunan Shinkafa Milyan Daya a Fadin Nijeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyarsa ta Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmin kimamin Dubu 10 kowace rana a jiharsa ta asali, wato Kano.

Har ila yau, gidauniyar ta kara wa’adin ne ta hanyar raba buhunan shinkafa Milyan Daya da kudinsu ya haura Naira Bilyan 13, a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, domin rage radadin yunwa a kasar.

Manufar hakan, k**ar yadda gidauniyar ta bayyana ita ce, domin sassauta wa Milyoyin ‘yan Najeriya wahala a cikin kalubalen tattalin arziki a kasar.

Wannan baya ga rabon biredi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma 15,000 a kullum ga mazauna Legas, abincin da aka fara kuma ya dore tun 2020 a lokacin COVID.
Abincin da aka dafa na Ramadan kyauta ya hada da Shinkafa (dafa-duka), farar Shinkafa da miya, Dafa-dukan Taliya, Wake hade da kaza da kuma naman Shanu, a hada da kwalbar ruwansha ga kowane mutum.

Ana dai rarraba abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen gyaran hali da kuma gidajen marayu, da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.

Wani wanda ya ci gajiyar wannan tallafi da jinkan al'umma da gidaunyar ta Dangote ke yi, mai suna Musa Maikatako, mazaunin garin Tarauni, ya nuna jin dadinsa da wannan karamcin da ya ce ya taimaka ma sa wajen yin buda-baki cikin sauki.

Maikatako, wanda a bayyane yake cikin farin ciki, ya ce cin abinci kyauta zai rage wahalhalun da jama’a da dama ke fama da shi a yau, musamman ma idan aka yi la’akari da matsalar tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abincin zai taimaka matuka wajen tallafa wa talakawa, irin mu, ta yadda muke samun mu yi buda baki akalla tare da abinci mai kauri da za mu ci.

"Na san mutane da yawa a jihar nan wadanda za su iya yin buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan a

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bude iyakar Najeriya da Nijar da ke Kamba a jihar Kebbi, a wani mataki na yin biyayya ga ...
17/03/2024

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bude iyakar Najeriya da Nijar da ke Kamba a jihar Kebbi, a wani mataki na yin biyayya ga umurnin shugaban Najeriya

Zargin kasafin kudi: ACF ta yi Allah wadai da dakatarwar da aka yi wa NingiKungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi Allah-w...
17/03/2024

Zargin kasafin kudi: ACF ta yi Allah wadai da dakatarwar da aka yi wa Ningi

Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi Allah-wadai da dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa tsohon shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, Sen Abdul Ninigi, inda ta ce muradun Arewa na cikin hadari.

Har ila yau, 'yan ta'ad-da sun sake yin garku-wa da mata 15, namiji daya a Kudancin Kaduna
17/03/2024

Har ila yau, 'yan ta'ad-da sun sake yin garku-wa da mata 15, namiji daya a Kudancin Kaduna

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada hannu da kungiyoyi masu daraja irin su Rotary In...
16/03/2024

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada hannu da kungiyoyi masu daraja irin su Rotary International a kokarin da ake yi na kawar da duk wani nau’in cutar shan inna da rage yawaitar mace-macen mata da jarirai a kasar nan.

📷 Buhari Sallau

Hukumar Kwastam Ta K**a Maka-mai, Muggan Kwa-yoyi, Kayayyakin Sojoji A Tashar Jirgin Ruwa ta LegasHukumar hana fasa kwau...
16/03/2024

Hukumar Kwastam Ta K**a Maka-mai, Muggan Kwa-yoyi, Kayayyakin Sojoji A Tashar Jirgin Ruwa ta Legas

Hukumar hana fasa kwauri ta Tin-Can Island na hukumar kwastam ta Najeriya ta k**a wasu Maka-mai da albu-rusai da ake zargin ana safarar su cikin kasar nan ta barauniyar hanya.

15/03/2024

Majalisar Dattawa ba ta karya wata doka ba wajen ƙarin kuɗi a kasafin kudin 2024 ba.

Inji-Atiku Bagudu

Ri-kici yayin da EFCC ta bi sahun tsohon gwamnan Kogi, Bello kan zargin cin han_ci da rashawa na N100bn An samu rudani a...
14/03/2024

Ri-kici yayin da EFCC ta bi sahun tsohon gwamnan Kogi, Bello kan zargin cin han_ci da rashawa na N100bn

An samu rudani a ranar Alhamis a babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan da aka yi wa kwaskwarimar tuhume-tuhume da ake yi wa Alli Bello da Daudu Suleiman, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Rana ta 4 ga watan Ramadan daga garin Makkah: Albarkacin wannan wata Allah ka yaye wa kowa abunda ke damun sa.!!
14/03/2024

Rana ta 4 ga watan Ramadan daga garin Makkah: Albarkacin wannan wata Allah ka yaye wa kowa abunda ke damun sa.!!

INNALILAHI 😭: Allah ya yiwa mahaifiyar jarumin Kannywood, Shamsudeen Dan'iya rasuwa, Kuma za'a yi jana'izar ta yau Alham...
14/03/2024

INNALILAHI 😭: Allah ya yiwa mahaifiyar jarumin Kannywood, Shamsudeen Dan'iya rasuwa, Kuma za'a yi jana'izar ta yau Alhamis a Jihar Kaduna.

Sanarwar daga Ali Nuhu Mohammed

Muna rokon Ubangiji Allah ya gafarta mata da Rahama.

Atiku ya musanta cewa ya fice daga PDP, ya tunkari TinubuDan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubak...
12/03/2024

Atiku ya musanta cewa ya fice daga PDP, ya tunkari Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya fice daga jam’iyyar.

Atiku ya bayyana rahoton a matsayin barna da babu gaskiya a ciki, inda ya jaddada cewa yana biyayya ga PDP.

Makarantu a jihohi 14 na Najeriya na cikin haɗarin satar ɗalibaiGwamnatin Najeriya ta gano wasu makarantu a jihohi aƙall...
11/03/2024

Makarantu a jihohi 14 na Najeriya na cikin haɗarin satar ɗalibai

Gwamnatin Najeriya ta gano wasu makarantu a jihohi aƙalla 14 da kuma birnin Abuja, da ke da raunin da za a iya kai musu hari, yayin da ake samun ƙaruwar satar ɗalibai a ƙasar.

Hajiya Halima Iliya, shugabar shirin samar da kuɗaɗen bayar da kariya ga makarantu na ƙasa, ta ce hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.

A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa-maso-gabashin ƙasar.

Jihohin da wasu makarantunsu ke cikin haɗarin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, Kebbi, Sokoto, Filato, Zamfara da birinin Abuja. A cewar hukumar.

A ranar Alhamis da ya wuce ne ƴanbindiga s**a sace ɗalibai 270 na makarantun firamare da sakandire a ƙauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne wasu ƴanbindigar s**a sace ɗaliban makarantar tsangaya kimanin 15 a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ɗaruruwan ƴangudun hijira a Ngala da ke jihar Borno da ake zargin ƴanBoko Haram da aikatawa.

Iyaye da ƴan’uwan ɗalibai da sauran waɗanda aka sacen na ci-gaba da roƙon gwamnati ta kuɓutar da su.

BBC hausa

Gobe Litinin za a tashi da azumi a ƙasar Saudiyya biyo bayan ganin jinjirin watan Ramadan.
10/03/2024

Gobe Litinin za a tashi da azumi a ƙasar Saudiyya biyo bayan ganin jinjirin watan Ramadan.

Address

Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Media/News Companies in Zaria

Show All