Jaridar Walkiya

Jaridar Walkiya Kafar watsa labarai ce ta Hausa da aka samar domin yada labarai da rahotanni da muhimman bayani.

AlhamduLillah: Jinin Ƴan uwa, Abokai da Masoyan mu sun fara taɓa Elrufa'i tun a duniya: Cikin Dalilai 22 da Jami'an DSS ...
12/08/2023

AlhamduLillah: Jinin Ƴan uwa, Abokai da Masoyan mu sun fara taɓa Elrufa'i tun a duniya: Cikin Dalilai 22 da Jami'an DSS s**a bayyana na rashin tantance Elrufa'i guda 8 suna da alaƙa da Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci.

Zargi na 7: Zarge-zargen Danne Haƙƙin Ɗan Adam:

Waɗannan zarge-zarge sun haɗa har da kisan mabiyan jagoran Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zazzaky, a Zariya da Kaduna, cikin 2015.

Yayin da Gwamnatin El-Rufai ta tabbatar cewa ta sa an rufe gawarwaki sama da 300 a ɓoye, IMN ta yi iƙirarin cewa an kashe masu sama da mutum 1,000, kuma wasu ma da sauran ran su aka binne su.

Sojoji ne s**a yi kisan, amma dai lamarin ya samu goyon bayan Gwamnatin El-Rufai.

Maimakon a tuhumi sojoji kan kisan da s**a yi, sai Gwamnati ta k**a El-Zazzaky ta tuhume shi da matar sa da laifin kashe wani soja ɗaya.

A ƙarshe dai kotu ta kori ƙarar, bayan El-Zazzaky da matar sa sun shafe shekaru a tsare. An kasa samun su da laifin kisan, sai aka sallami ƙarar cikin Yuli, 2021.

Zargi na 8: Gabatar Da Kisan ‘Yan Shi’a A Kotun ICC Ya Kawo Wa El-Rufai Cikas Wajen Tantance Shi:

Wannan ƙara da aka shigar a ICC, kotun Majalisar Ɗinkin Duniya, ta karta wa El-Rufai rubutun alamar-tambaya a goshin sa. Kuma har yanzu ICC na gudanar da bincike a kan kisan.

Zargi na 9: Zarge-zargen K**a Mutane Barkatai Ya Na Kullewa Da Sunan Adawa, Ƙwace Kadarori Da Rushe Gine-ginen ‘Yan Adawa:

Zargi na 10: Zargin Amfani Da Ƙarfin Gwamnati Ana Yi Wa Masu Zanga-zanga Rubdugun Da Kan Kai Ga Kisa:

Zargi na 14: SSS Sun Ce An Fi Ƙorafi Kan El-Rufai Fiye Da Sauran Sunayen Ministoci 47:

Sun buga misali yadda aka riƙa ƙorafe-ƙorafe birjik a soshiyal midiya kan sa, sai kuma yadda wasu s**a yi zanga-zanga a Majalisar Dattawa, lokacin tantancewa, suna nuna ba su so a tantance El-Rufai.

Zargi na 15: Ƙorafe-ƙorafe Kan El-Rufai A Kotun ECOWAS, ICC.

Zargi na 16: Ƙorafin Da Hukumar Kare Haƙƙin Musulunci, Islamic Human Rights Commission Ta Aika Wa Tinubu Kan El-Rufai:

Zargi na 17: Samun Tabbacin ICC Ta Ƙarɓi Ƙararrakin Da Aka Maka El-Rufai A Kan Zargin Kisan Kiyashi Da Cin Zarafin Ɗan Adam:

Bangaren rubutun Na Ƴar Talla

Mayan Dalilai 22 da DSS su ka hana a naɗa El-Rufai minista. Mutane da dama sun yi mamakin ganin yadda sunan tsohon Gwamn...
12/08/2023

Mayan Dalilai 22 da DSS su ka hana a naɗa El-Rufai minista.

Mutane da dama sun yi mamakin ganin yadda sunan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito cikin mutane ukun da Majalisar Dattawa ta ƙi tantance su.

Sai dai yanzu wani binciken musamman da PREMIUM TIMES ta yi ya tabbatar da cewa Hukumar SSS ce ta fitar da rahoto a kan sa dangane da waɗansu aika-aika masu nasaba da take haƙƙin ɗan Adam da kuma tulin kwafen ƙorafe-ƙorafen da aka riƙa aikawa a kan sa.

Akwai zarge-zargen sa riƙa yin wasu kalamai ba tare da ya tunanin daidai ko rashin dacewar yin kalaman ba, ballantana kuma tunanin abin da furucin na sa ka iya haifarwa ba.

Yayin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aika da sunayen ministoci 48, Majalisar Dattawa ta maida masa sunaye 45 da ta tantance, amma banda sunaye 3, waɗanda cikin su har da na El-Rufai, wanda ake kallo a matsayin makusanci na ƙut-da-ƙut ga Tinubu.

Tun a gaban Majalisa wurin tantancewa aka fara gantsara wa El-Rufai, amma aka yi rufa-rufa cewa ya rage wa Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin da ya dace kan duk wani wanda ake da rahoton ƙorafe-ƙorafe a kan sa.

Baya ga El-Rufai, Majalisar Dattawa ta ƙi aika wa Tinubu da sunan Sani Ɗanladi daga Taraba da kuma Stella Okotete ɗaga Delta.

Bayan ta tuntuɓi majiyoyi da dama sahihai, PREMIUM TIMES ta fito a karon farko ta zayyana dalilan da s**a hana a tantance El-Rufai.

Majiyoyin mu sun nemi a sakaya sunan su, saboda ba a ba su iznin yin magana da ‘yan jarida ba. Amma kuma sun ce akasarin dalilan da su ka sa aka ƙi tantance El-Rufai, duk jama’a sun san su, ba abin ɓoye ba ne.

Majiya ta ce SSS sun yi ƙorafi kan El-Rufai cewa a baya har zuwa kwanan nan, ya riƙa sakin baki ya na caɓa maganganu ba tare da yi wa bakin sa linzami ba. Kuma maganganun masu barazana a cikin al’umma.

Sai dai kuma majiyar mu ta ce SSS ba su tunkari El-Rufai da zarge-zargen da ake yi masa ba.

1. Rashin Yi Wa Bakin Sa Linzami:

Wannan zargi shi ne muhimmi daga cikin rahoton da SSS su ka yi kan El-Rufai.

Tsohon Gwamnan Kaduna ya yi ƙaurin suna wajen yin kasassaɓa da katoɓara a cikin jama’a. Irin waɗannan maganganu kuwa su ne s**a zame masa ‘baki shi ke yanka wuya’ a yanzu.

Kaɗan daga cikin su akwai kakkausan kalaman da ya taɓa yi kan masu adawa ko rigima da shi, inda ya buga misali da tsoffin shugabannin Najeriya biyu – Marigayi Umaru ‘Yar’Adua da Goodluck Jonathan.

2. Kakkausan Kalaman El-Rufai A Kan ‘Yar-Adua da Goodluck Jonathan:
“‘Shugabanni Biyu Da S**a Ja Da Ni, Ɗaya Ya Sheƙa Barzahu, Ɗaya Kuma Ya Koma Otuake Da Zama”.

A nan El-Rufai bai ambaci sunayen su ba, amma kowa ya san da waɗanda ya ke, kuma kowa ya san ya yi takun-saƙa da su biyu ɗin.

A lokacin da ya yi wannan furucin a cikin jama’a a Kuduna, an riƙa mamaki, har wasu na ganin k**ar mutumin ya na da albatsutsai.

3. Kalaman El-Rufai Kan Yadda Ya Ke Fifita Tsarin Muslim-Muslim A Muƙaman Takarar Gwamna Da Mataimaki A Kaduna:

Wannan kalami na sa ya sha s**a sosai a faɗin ƙasar nan, har ana kallon cewa El-Rufai ya na ƙoƙarin ruruta rabuwar kai da rikicin ƙabilanci ko na addini.

SSS sun ce wannan furuci na El-Rufai ya ƙara faɗaɗa rashin yarda da nesanta amintaka tsakanin Musulmi da Kiristoci a ƙasar nan.

5. Zaɓen 2019: Barazanar El-Rufai Cewa Za A Maida Gawarwakin Masu Katsalandan Zuwa Ƙasashen Su A Cikin Makara:

El-Rufai ya yi furucin a lokacin da ya ke sake takarar gwamna a Kaduna karo na biyu. Ya yi kakkausan kalaman ne kan ƙungiyoyin sa-ido da wasu ƙasashen waje masu magana kan lamarin da ya shafi zaɓe a Najeriya.

Majiya ta ce SSS sun ce saboda wannan furuci da El-Rufai ya yi, yanzu haka an yana shi shiga ƙasar Amurka.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ba ta tabbatar shin an hana shi ɗin ko kuma Amurka ba ta yana shi ɗin ba.

6. Katoɓara Da Saɓon Da El-Rufai Ya Yi A Cikin 2013:

Majiya ta ce SSS ta bankaɗo wani rubutu da El-Rufai ya watsa a cikin 2013, wanda ta ce “saɓo ne ya yi a shafin sa na Tiwita.” Ta ce rubutun ya haifar da ruɗani a ƙasar nan sosai.

7. Zarge-zargen Danne Haƙƙin Ɗan Adam:

Waɗannan zarge-zarge sun haɗa har da kisan mabiyan jagoran Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zazzaky, a Zariya da Kaduna, cikin 2015.

Yayin da Gwamnatin El-Rufai ta tabbatar cewa ta sa an rufe gawarwaki sama da 300 a ɓoye, IMN ta yi iƙirarin cewa an kashe masu sama da mutum 1,000, kuma wasu ma da sauran ran su aka binne su.

Sojoji ne s**a yi kisan, amma dai lamarin ya samu goyon bayan Gwamnatin El-Rufai.

Maimakon a tuhumi sojoji kan kisan da s**a yi, sai Gwamnati ta k**a El-Zazzaky ta tuhume shi da matar sa da laifin kashe wani soja ɗaya.

A ƙarshe dai kotu ta kori ƙarar, bayan El-Zazzaky da matar sa sun shafe shekaru a tsare. An kasa samun su da laifin kisan, sai aka sallami ƙarar cikin Yuli, 2021.

8. Gabatar Da Kisan ‘Yan Shi’a A Kotun ICC Ya Kawo Wa El-Rufai Cikas Wajen Tantance Shi:

Wannan ƙara da aka shigar a ICC, kotun Majalisar Ɗinkin Duniya, ta karta wa El-Rufai rubutun alamar-tambaya a goshin sa. Kuma har yanzu ICC na gudanar da bincike a kan kisan.

9. Zarge-zargen K**a Mutane Barkatai Ya Na Kullewa Da Sunan Adawa, Ƙwace Kadarori Da Rushe Gine-ginen ‘Yan Adawa:

10. Zargin Amfani Da Ƙarfin Gwamnati Ana Yi Wa Masu Zanga-zanga Rubdugun Da Kan Kai Ga Kisa:

11. Zargin Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya:

12. Ƙararraki Da Ƙorafe-ƙorafen Almubazzaranci, ‘Yin Amfani Da Kore Da Iyalan Sa Wajen Yin Wata Harƙalla A Lokacin Ya Na Shugaban BPE Da Ministan FCT Abuja:

PREMIUM TIMES ta gano kotu ta kori irin wannan ƙarar da aka maka El-Rufai. Amma SSS sun ce yanzu haka akwai wata a Babbar Kotun Tarayya.

14. SSS Sun Ce An Fi Ƙorafi Kan El-Rufai Fiye Da Sauran Sunayen Ministoci 47:

Sun buga misali yadda aka riƙa ƙorafe-ƙorafe birjik a soshiyal midiya kan sa, sai kuma yadda wasu s**a yi zanga-zanga a Majalisar Dattawa, lokacin tantancewa, suna nuna ba su so a tantance El-Rufai.

15. Ƙorafe-ƙorafe Kan El-Rufai A Kotun ECOWAS, ICC.

16. Ƙorafin Da Hukumar Kare Haƙƙin Musulunci, Islamic Human Rights Commission Ta Aika Wa Tinubu Kan El-Rufai:

17. Samun Tabbacin ICC Ta Ƙarɓi Ƙararrakin Da Aka Maka El-Rufai A Kan Zargin Kisan Kiyashi Da Cin Zarafin Ɗan Adam:

18. Ƙararrakin Da Aka Maka El-Rufai A Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam Ta Ƙasa, ‘Amnesty International’, Dangane Da Kwace Filaye A Kaduna Bayan Kotu Ta Hana Shi Ƙwacewa:

19. Ƙorafe-ƙorafen Rashin Ganin Darajar Dattawan Arewa Da Ci Masu Fuska:

20. Kasassaɓar El-Rufai Da Ya Taɓa Cewa Tinubu Gogarman Ɗan Harƙalla Ne, Ba Zai Taɓa Zama Mataimakin Tinubu Ba:

19: Yunƙurin Zuga ‘Yan Majalisar Kaduna Su Soke Shari’ar Muslunci A Jihar Kaduna, Don Ya Samu Goyon Bayan Kiristoci:

Yayin da Kakakin Majalisar Kaduna na lokacin, Yusuf Zailani ne ya fito ya yi masa wannan zargin, wani ɗan majalisa na lokacin mai suna Yusuf Salihu, ya ƙaryata zargin.

20. El-Rufai: Ɗan Mage Ba Ka Ɗaɗin Goyo:

Majiya ta ce SSS ta zargi El-Rufai da yawan cin amanar shugabannin da s**a raine shi a gwamnatance. K**ar yadda ya riƙa yi wa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya ɗauko shi ya fara haɗa shi da Obasanjo, sai kuma na baya-bayan nan, Shugaba Muhammadu Buhari.

21. Zulwajahaini: Zargin El-Rufai Ya Na Tufka Da Warwara:

Kwanan nan ya ce ko an ba shi muƙamin minista ba ya so, a bai wa wasu, ga yara nan masu tasowa. Amma ana ambatar sunan sa, sai ya fara shirye-shiryen tafiya tantancewa.

22. Yawan Fito Da Tsare-tsaren Da Ke Gallaza Wa Masu Ƙaramin Ƙarfi Da Lalata Dukiyar Jama’a A Jihar Kaduna.

Sun haɗa da ruguje kasuwa ba tare da biyan diyya ba, kora da rushe gidajen ‘low-cost’ masu sauƙin kuɗi, korar dubban ma’aikata da sauran su. Korar sarakunan gargajiya da sauran su.

Rahoton ya ce mutum maras tausayi k**ar irin haka, bai dace a ba shi muƙamin aikin jama’a a ƙasa ba.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Muyiwa Adekeye, Mashawarcin El-Rufai Kan Yaɗa Labarai, amma bai ce komai ba.

Daga shafin: Na Yar Talla.

Shekaru 9 da kisan mutun 34 a Zariya: Harkar Musulunci ta yi taron tunawa wadanda Jonathan ya kashe musuDaga Fatima Must...
25/07/2023

Shekaru 9 da kisan mutun 34 a Zariya: Harkar Musulunci ta yi taron tunawa wadanda Jonathan ya kashe musu

Daga Fatima Mustapha

K**ar yadda s**a saba a duk shekara, Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda aka fi sani da 'yan shi'a suna gudanar da taron tunawa da taron da s**a kira da 'waƙi'ar Ƙudus' wacce ta auku a ranar 25 ga watan Yulin 2014 a garin Zariya.

A bana ma ba su yi ƙasa a guiwa ba, inda s**a gabatar da taron bayan shekaru tara da aukuwar lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar 2014 ne a yayin zanga-zangar lumana domin nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu a garin Zariya, sojoji s**a afka ma mabiya Harkar Musuluncin inda s**a kashe mutum 34 ciki harda 'ya'yan Shaikh Ibraheem Zakzaky guda uku da wani kirista mai suna Julius Anyanwu da wani mutumin gari da ya taso daga wurin aiki.

A yayin ganawa da manema labarai a yayin taron, dan uwan Shaikh Zakzaky, Badamasi Yaqoub ya bayyana makasudin taron da cewa;
"Tunawa da shahidanmu wanda aka kashe su shekara k**ar tara (9) da s**a wuce. Wato wannan waki'ar ya faru ne a nan Zariya wanda ya zama an kashe mutum 34. Akwai kirista guda daya. Akwai 'ya'yanmu guda uku shi ne; Ahmad, da Hamid da Mahmud".

Ya ƙara da cewa; "muna nan ne domin tunawa da gwaraza wadanda ainihin aka kashe su saboda bin tafarkin Allah".

Ya ci gaba da cewa; "haka hanyar addini take, ba ta canjawa. Zan iya tunawa na je wajen wani Ayatullah a Iraƙi sai yake ce min Saddam ba wani gidan da bai kashe mutum ba, amma yau Saddam ya zama tarihi. Haka ma duk wani Fir'auna da zai tsaya ya yi Fir'aunanci ya kan zama tarihi ne kawai. A don haka kowanne azzalumi akwai ranar karshen shi.

Kazalika, Malama Maryam Gashuwa, shugabar Gidauniyyar tallafawa marayun da aka kashewa iyaye da 'yan'uwa da 'ya'ya, ta ce daga cikin aikace-aikacensu ya haɗa da; "akwai nauye-nauye da yawa. Misali Mu'assatus Shuhada tana daukar nauyin iyalan shahidai, misali karatun 'ya'yan shahidai, wani lokaci rashin lafiyarsu, sannan abinci, wani lokaci akan tallafa, amma ba ana yi ɗari bisa ɗari ba", in ji ta.

Malama Maryam ta ce daga cikin waɗanda suke amfana da wannan tallafin ya haɗa da iyaye, 'ya'ya da matan da aka kashe mazajensu, da akalla sun kai dubu biyu.

Taron na bana ya gudana ne a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya ta jihar Kaduna. Wanda aka soma da misalin ƙarfe 8 na safe da saukar Alƙur'ani mai girma wanda Madrasat Darur Imam Mahdi ta gabatar. Sannan aka buɗe taron da addu'a wanda Malam Musa Tudun Jukun ya yi, sannan Mahdi Salihu Garba ya karanto ayoyi daga Alkur'ani mai girma.

An bai wa Ittihadus Shu'ara dama s**a haskaka wurin da waƙoƙin juyayi na munasabar waƙi'ar Ƙudus. Daga nan Mu'assasoshi, dandamaloli, da Rijalai daban-daban da s**a hada da; Hurras, Intizarul Imam Mahdi, Kasshafatul Imam Mahdi, Jaishi Aliyul Akbar, Ansaru Zakzaky, Rijalu Zakzaky, Harisawa 'yan Orientation, Rijalu Sidi Zakzaky, Fa'iz Club, duk s**a gudanar da bajintarsu' da kareti, da takwaendo da kuma "faretin girmamawa ga shahidan", in ji su.

Sayyid Badamasi Yaqoub a jawabinsa ya jaddada cewa; ma'anar 'La'ilaha illallah Muhammadur Rasulillah' tana ɗauke da jarabawa, ya ce duk wanda ya riƙe wannan kalma gam yana aiki da ita, dole ne fir'aunonin zamani su yake shi kuma ba za su ƙyale shi ba. Domin a cewar Malamin kalmar na koyar da bara'a da wulaya ne.

Taron ya samu halartar al'umma daban-daban daga sassa mabambanta na ƙasarnan.

Karancin Ruwan Sama: Sarkin Kano  ya Umarci al’umma dasu tashi tsaye domin yin Addu’oiDaga Khadija Abdullahi AliyuMai Ma...
25/07/2023

Karancin Ruwan Sama: Sarkin Kano ya Umarci al’umma dasu tashi tsaye domin yin Addu’oi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya uwanda a dage da ci gaba da addu’a domin rokon Allah ya kawo dauki kan karancin ruwan sama da ake fuskanta a sassan jihar Kano.

A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, Mai Martaba Sarkin ya umurci dukkanin Limaman Masallatan juma’a da ke jihar Kano su gabatar da addu’o’i na musamman a dukkanin masallatan da su ke jagoranta don neman yardar Allah ya bamu ruwan sama mai albarka, a jihar Kano da kewaye.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma bukaci dukkanin Masallatan hamsas salawati da malaman makarantun islamiyyu da na tsangayu suma su yi addu’ar samun ruwan saman ba tare da jinkiri ba.

Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: Rashin bayyanar Shaidu Abba Gida-gida a Kotu yasa hana shi fara kariya

Ya kuma umurci dukkan Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni da dukkan shugabannin al’umma da ke fadin jihar nan, su hada kan al’ummar Musulmi a yankunansu domin kai kuka wajen Allah subhanahu wa ta’ala ya yaye halin ƙunci da ake ciki musamman na rashin ruwa da tsadar abinci da rashin tsaro da ake fuskanta a birni da kauyukan mu.

Ya kuma shawarci dukkanin iyaye da su sanya idanu tare da jan kunnen ‘ya’yansu dasu guji aikata rashin da’a da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yawaita tuba ga Allah bisa laifuka da ke gudana wadanda muka sani dama wadanda ba mu sani ba.

Daga nan Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci dukkanin ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah tare da gudanar da harkokin kasuwancin su ta hanyar da shari’ar Muslunci ta tanada.

Haka kuma ya yi kira ga Gwamnati da bin dukkan hanyoyi da s**a dace don saukakawa al’umma da Ubangiji ya ba mu jagorancin su.

An sake tura Malam Idris gidan yari saboda tsaiko da aka samu wajen karbar belinsaRahotanni sun nuna an ci gaba da tsare...
25/07/2023

An sake tura Malam Idris gidan yari saboda tsaiko da aka samu wajen karbar belinsa

Rahotanni sun nuna an ci gaba da tsare Sheikh Idris Abdulazeez a gidan kaso bayan samun tsaiko da aka yi a wajen karbar belinsa.

Ana dai tsare da malamin ne bisa zarginsa da yin furuci gatsai wajen yin kwatance da Manzon Allah (S.A.W) a wani karatunsa.

Ƴan bindiga sun sace Boka a Anambra -Rahoton BBC Hausa
25/07/2023

Ƴan bindiga sun sace Boka a Anambra

-Rahoton BBC Hausa

'Raba wa talakawa kuɗi don rage radadin cire tallafin mai ba shi ne mafita ba'Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya s...
25/07/2023

'Raba wa talakawa kuɗi don rage radadin cire tallafin mai ba shi ne mafita ba'

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya soki tsarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi na raba wa ƴan Najeriya tallafin rage radadin cire tallafin mai.

Ita dai gwamnatin ta ce za ta raba wa ƴan kasar miliyan goma sha biyu ne, daga cikin su sama da miliyan 200, Naira dubu takwas har tsawon watanni shida.

Sai dai a cewar gwamnan na Kaduna, babu fa'ida a wannan al'amari domin ba zai taimaka k**ar yadda ita gwamnatin ke fata ba.

Ya ce ''Abin da muka gano shi ne mu a nan Arewa, kashi 75 cikin 100 na al'ummarmu ba su da asusun ajiya, idan kuma mutum bai da asusun ajiya a banki ta yaya wannan tallafi zai same shi?''

Gwamna Uba Sani, ya ce shi ya sa duk lokacin da aka yi maganar bayar da tallafi a Najeriya sai ka ga ƴan Kudu ne ke amfana, domin yawancinsu, na da bankunan ajiya, da kuma sani kan yadda za su ci gajiyar tsarin.

Farfesa Adamu Gwarzo: Mutum Ne Da Ya Cancanci YaboDukkanin addinai na duniya suna koyar da kyautata wa mutane. Aikata al...
03/07/2023

Farfesa Adamu Gwarzo: Mutum Ne Da Ya Cancanci Yabo

Dukkanin addinai na duniya suna koyar da kyautata wa mutane. Aikata alheri wata alama ce da ba ta gogewa a cikin zuciyar mai karɓa. Na taɓa karanta cewa “zama mutumin kirki yana da lada” a cikin littafin Noel Streatfeild da aka rubuta a shekara ta 1936. A yayin da karin maganar Afirka ke cewa duk wanda ya shuka abu mai kyau ba shakka zai girbi mai kyau, hakika mutanen kirki sun cancanci yabo domin wasu su yi koyi da su.

Kasancewa mutumin kirki yana da ma’anoni daban-daban ta fuskoki mabambanta ga mutane da yawa. Mutumin kirki zai iya daukar ma’anar dukkanin wani mutum da yake saukakawa al’umma radadi, yake kuma taimaka musu wajen cimma burinsu ko kuma yake taimaka musu wajen cimma muradinsu.

Shiga sahun masu gina kasa nauyi ne da ya rataya a kan wuyan dukkannin ‘yan kasa amma mutanen kirki ne kawai suke yin hakan. Gina kasa na da bukatar abubuwa da yawa daga kowanne dan kasa. Za mu iya sanya al'ummarmu ta zama abin da muke so idan har dukkanninmu muka hada hannu da karfe wajen ba da gudummawa ga bukatunta. Da ‘yar gudunmuwar da kowa zai iya bayarwa; za mu iya yin tasiri a rayuwarmu da na wasu. Wani abu mai kyau da ya k**ata mu yi wa ƙasarmu a yanzu shi ne taimaka wa mutane domin biyan bukatunsu na ilimi.

Ilimi yana da matukar kimar da ba shi da farashi, sai dai wadanda s**a fita daban ne kawai suke bayar da gudummawa wajen ci gaban ƙasa da ci gaban ɗan Adam, ba tare da mutane sun zama masu yanke kauna, shiga cikin rashin tsaro da zai dabaibaye su tare da hauhawar tashin hankali ba k**ar tuddai. Mutanen da ke ba da ilimi, masu taimakon al’umma ne; ana kiransu da masu jin kai, domin Allah ne kadai zai iya sakawa irin wannan sadaukarwar da suke yi, ko da kuwa ana biyan masu makarantun kudi, su kuma suna biyan gwamnati da al’umma da kasa baki daya ta kowane fanni. Makarantun da suke ginawa suna samar da ayyukan yi, suna taimakawa gwamnati a nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da ilimi, sannan mafi muhimmanci; masu makarantun suna biyan kudaden shiga kuma suna samar da aikin yi ga ‘yan ƙasa.

Farfesa Adamu gwarzo; matashin Farfesa ne a Arewacin Nijeriya daga jihar Kano wanda ya zama ginshiki ne na sabon ilimin zamani na Nijeriya tare da himma wajen taimakawa da samar da tsarin ilimi da ake da bukata a duniya. Tare da ƙwarewar da yake da shi a matsayinsa na Farfesa, kuma ɗan jarida, mai gudanarwa sannan hamshaƙin ɗan kasuwa, ƙoƙarin Gwarzo wanda ba ya gajiyawa ya kawo sabon tsari a Afirka. Gwarzo dan kasuwa ne na ilimi wanda gudunmawarsa a duniya ta sauya yanayin akidar ilimi a Afirka.

Tare da kafa Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN) a Maradi dake Jamhuriyar Nijar da wata jami'a a Togo, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya kafa kyakkyawar tubali a fannin ilmantarwa a Afirka.

Tare da sha'awarsa da himmarsa wajen haɓɓaka ilimi domin biyan buƙatun aikin yi na zamani a cikin harsuna daban-daban; jajircewar Gwarzo ya sake farfado da wani fata ga 'yan Nijeriya na kafa wata jami'ar Amurka a Kano, domin cika bukatar dalibai da ka’idojin aikin yi a duniya. Jami'ar tana ba da darussa fiye da 15.

A kwanan nan, a wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hannun Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) a ranar 9 ga watan Yuni, 2023, ta bayar da lasisin gudanarwa ga Jami’ar Canada ta Nijeriya da ke Abuja da Jami’ar Franco-British International University, dake Kaduna wanda dukkaninsu mallakin Farfesa Adamu Gwarzo.

Jami’ar da ta yi fice ta farko a Nijar, dake Maradi ita ce kan gaba wajen sauya tsarin ilimin Afirka domin dacewa da tsarin ilimi na karni na 21 ta hanyar hada harsunan koyarwa da karatu. Jami'ar da aka ba wa sunan matar tsohon shugaban Nijeriya a tsakanin Nuwamba, 1993 - Yuni, 1998 (Marigayi Janar Sani Abacha), Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), a Maradi ita ce jami’a mai zaman kanta ta farko a duk faɗin Afirka da aka kafa domin faɗaɗa harsunan duniya masu tsada a cikin ƙasashen Afirka tare da sabbin hanyoyin koyarwa.

Nasarorin da Farfesa Adamu Gwarzo ya samu ba wai kawai na fadada ilimi ne a Afirka ba, illa karamcinsa na kawo nesa a kusa tare da taimaka wa mutane wajen ganin sun cimma burinsu na ilimi da kuma taba rayukan miliyoyin mutane ta hanyar gidauniyarsa.

Tare da dimbin miliyoyin masu neman shiga jami’o’i a Nijeriya; Adamu Gwarzo ya rufe gibin tsallakawa jami'o'in kasashen waje. Kokarinsa na kashe tarin dalolin Amurka domin taimakawa ilimi, marasa karfi, mata tare da rage tasirin sauyin yanayi yana kawo sauyi a Afirka. Burinsa shi ne inganta ilimi, sha'awarsa ita ce cike fatan UNESCO da kuma tsarin ci gaba mai dorewa (SDGs) a Afirka.

Ta hanyar gudunmawarsa mara yankewa da yake bayarwa ga ilimi; Farfesa Gwarzo yana da lakabi da yawa na nuna godiya gare shi, an rubuta sunansa da ruwan zinare domin tunawa da shi na har abada, kuma Allah ya albarkace shi bisa irin sadaukarwarsa. Shugaban jami’o’in masu zaman kansu a Nijeriya ya samu yabo da dama da s**a hada da wanda ya jagoranci samar da jami’o’in harsuna biyu a Afirka, da lambobin yabo na Sarautun gargajiya da dama da kuma lambobin yabo na kasa da kasa.

Gidauniyar Adamu Gwarzo ta zama hanyar rage radadi ga mutane, ta hanyar gidauniyar ana kashe miliyoyin kudade domin biyan bukatun jama'a da kuma kawo taimako ga kasashen Afirka. Taimakon da yake bayarwa ga ilimin Nijeriya yana da matukar muhimmanci da kowa ke iya gani kuma har ya shaida irin wannan taimakon jin kai da Gwarzo ke bayarwa a Afirka.

A shekarar 2021, Gidauniyar Adamu Gwarzo ta ba da gudummawar mota kirar bas mai cin mutane 66 na alfarma wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 50 da kuma motar daukar marasa lafiya ta Naira miliyan 20 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano Wudil (KUST). Haka kuma gidauniyar ta bayar da kyautar mota kirar bas mai cin mutane 60 ga Kaduna Polytechnic, haka zalika, gidauniyar ta bayar da kyautar motar alfarma mai kujeru 66 da kudinta ya kai Naira miliyan 50 ga jami’ar Al-Istiqama dake Sumaila ta jihar Kano. Sannan gidauniyar ta Gwarzo ta bayar da tallafin motocin bas masu kujeru 60 na Mercedes-Benz ga jami’ar Bayero da ke Kano da kuma jami’ar gwamnatin Nijar.

Baya ga haka, bisa sha'awar da yake da shin a tallafawa wajen buga littattafai, gidauniyyar Adamu Gwarzo ta tallafa wa buga littattafai guda biyu da kudi har naira miliyun biyu. Littafan sune; “Pantami: The Trials and Triumphs of a Digital Economy Maestro,” na Mal. Yushau Shuaib da kuma “eNaira Revolution: A Peep into Nigeria’s Cashless Future,” wanda Mista Abdulrahman Abdulraheem ya rubuta. A shekarar 2022, Gidauniyar Gwarzo ta bai wa mata marasa karfi 100 na jihar Kano tallafin naira dubu hamsin (N50,000) ga kowaccensu. A shekarar 2022, Gidauniyar Gwarzo ta ba da tallafin Naira Miliyan 1 ga dalibin Nijeriya da yake karantar fannin likitanci da ya makale a kasar Rasha.

Tausayin Farfesa Adamu Gwarzo ba ya aunuwa kuma duk yana yin wannan ne saboda Allah da kuma ci gaban Afirka. A watan Yuni Gwarzo ya bai wa wani jami'in tsaronsa kyautar gida bisa gaskiya da rikon amanarsa. Gwarzo yana tausaya wa talakawa, yana taimakon marasa karfi, yana kuma kwantar da hankalin mutane ba tare da la’akari da kabilarsu, yankinsu ko addininsu ba. Ana ɗaukarsa a matsayin mutum mai ban mamaki wanda hangen nesansa shi ne gina al’umma ta kowanne fanni. Tabbas shi mutum ne da Allah ya yi a Nijeriya domin ya kawo ci gaba, ya kuma warware matsaloli da kuma koma bayan ilimi tare da kawo sauyin yanayi a Afirka, da wadannan, Farfesa Adamu Gwarzo ya cancanci yabo da addu'a.

Auwal Ahmed Ibrahim malami ne a Kaduna Polytechnic, a sashen Mass Communication, kuma ana iya samunsa ta [email protected]

Shaikh Zakzaky ya yi Allah-wadai da wulaƙanta Alkur'ani a Sweden Daga Zailani Mustapha Jagoran Harkar Musulunci a Nijeri...
03/07/2023

Shaikh Zakzaky ya yi Allah-wadai da wulaƙanta Alkur'ani a Sweden

Daga Zailani Mustapha

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi tir da Allah-wadai da yadda wasu mutane s**a wulaƙanta Alkur'ani mai girma.

Wannan bayani ya fito ne daga ofishin Shehin Malamin a wani saƙo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Asabar 1 ga Yulin 2023, inda Shehin Malamin ya ce tabbas abin da ya faru labari ne mara daɗi, kuma hakan ya raunata zuciyar al'ummar Musulmi da masu neman ƴanci a duniya.

Shehin Malamin ya ƙara da cewa; abin da ya faru cin fuska ne ga Musulunci da Musulmi. Inda ya nemi dukkanin masu neman ƴanci a duniya da ka da su yi shiru kan lamarin nan. Kuma dole ne a hukunta waɗanda s**a aikata hakan.

Shehin Malamin dai ya fara da cewa; "wannan labari mara daɗi na cin zarafin Alƙur'ani mai girma a ƙasar Sweden, ya raunata zukatan dukkanin musulmi da masu neman 'yanci na duniya", inji sakon .

Ya ci gaba da cewa; "Tabbas kona Alƙur'ani mai tsarki ba wai cin fuska ne ga Musulunci da musulmi ba, cin fuska ne ma ga dukkanin addinan duniya da mabiyansu. Don haka, ya zama wajibi ga duk wani mai ƴanci da kada ya yi shiru akan wannan aiki".

Ya karkare da cewa; "Mun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da waɗanda s**a aikata shi kuma muna kira da a gaggauta hukunta su".

Sheikh Muhammad Hassan Ya Zama Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Jami’ar MAAUNShugabar Kwamitin Amintattu na Jami’ar M...
04/05/2022

Sheikh Muhammad Hassan Ya Zama Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Jami’ar MAAUN

Shugabar Kwamitin Amintattu na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Hajiya Dr Maryam Sani Abacha ta bukaci mahukumtan jami’ar da su nada Sheikh Muhammad Hassan a matsayin babban limamin masallacin Juma’a na jami’ar.

Sheikh Hassan shi ne Limamin gidan Marigayi Janar Sani Abacha dake kan titin Gidado, Nassarawa GRA, Kano.

Bukatar nadin Sheikh Hassan a matsayin Babban Limamin Masallacin Juma’a na MAAUN na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Talata 3 ga watan Mayu, 2022, mai dauke da sa hannun Maryam Abacha, kuma aka rabawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba.

Dakta Maryam Abacha ta bayyana cewa a cikin wasikar, bukatar ta ta taso ne bisa hujjar cewa Sheikh Hassan yana da ilimin addinin Musulunci da ake da bukata da kuma cancantar gudanar da Sallah a Masallacin duba da kasancewarsa mai haddar Al-Qur'ani kuma amintacce.

A cewarta, Sheikh Hassan yana da ilimin da ake bukata a fannin Fikihu, Shari'a da kuma iya harshen Larabci.

“a don haka muna so mu tabbatar wa duniya cewa Sheikh Muhammad Hassan shi ne babban limamin masallacin Juma’a na MAAUN Kano, muna taya shi murna da farin ciki tare da yi masa fatan shiriyar Allah,” in ji Maryam Abacha a cikin wasikar.

An haifi Sheikh Hassan a garin Gamborin Gala da ke jihar Borno a shekarar 1966. Ya kammala karatun kur'ani a shekarar 1972, ya kuma kammala haddar Alkur'ani a shekarar 1985.

Hakazalika a shekarar 1991 ya sake rubuta kur'ani mai tsarki da hannunsa sannan a shekarar 2018 ya halarci taron manyan limamai na masallatan Juma'a a kasar Morocco.

Yadda 'Yan Sanda S**a Kawo Mana Hari A Yayin Muzaharar Kudus A Zariya - Harka IslamiyyaWakilin almajiran Shaikh Ibraheem...
04/05/2022

Yadda 'Yan Sanda S**a Kawo Mana Hari A Yayin Muzaharar Kudus A Zariya - Harka Islamiyya

Wakilin almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a Zariya, Shaikh Abdulhamid Bello a hirar da ya yi da manema labarai a Zariya jim kadan da kammala sallar Idi ta bana a ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 a makarantar Fudiyya dake Babban Dodo Zariya, Shehin Malamin ya yi karin haske dangane da abin da ya faru a ranar Kudus a Zariya.

Shehin Malamin ya fara da cewa; “Taron tunawa da ranar Qudus wani taro ne na shekara-shekara wanda musulmin duniya da masu hankali ke nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da suke cikin mawuyacin hali a kowacce rana a hannun Sahayoniyawan Haramtacciyar kasar Isra'ila. A bana an gudanar da muzaharorin ne a kusan dukkanin manyan biranen duniya. A Nijeriya an gudanar da muzaharorin ne na lumana a garuruwa sama da hamsin. Babu inda aka kai wa muzaharar hari sai a Kaduna da Zariya wanda ya yi sanadin shahadar mutum daya a Kaduna tare da raunata dimbin ‘yan uwa musulmi maza da mata da harsashi mai rai da jami’an tsaron Nijeriya s**a yi. Hakazalika an k**a mutane da dama da s**a hada da mata da kananan yara, da dama daga cikinsu da raunukan da ke barazana ga rayuwarsu sak**akon harbin da ‘yan sanda s**a yi tare da garkame su a hannun ‘yan sanda ba tare da samun kulawar likitoci ba”, ya labarta.

Har wala yau Shehin Malamin ya ce; “muzaharar ta bana a Zariya sun kai mata hari ne bisa makircin cewa muzaharar ta kona ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari da wata mota. A tarihin yake cewa an kwashe sama da shekaru arba’in (40) ana gudanar da muzaharorin ranar Kudus a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky inda a kodayaushe ake tashi lafiya lau har sai dai idan jami’an tsaro ne s**a zo s**a kawo wa masu muzaharar hari. A don haka abin takaici ne yadda bayan kai harin ga ‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda suke amfani da ‘yancinsu na gudanar da muzaharar lumana, amma kuma har ‘yan sandan za su iya ci gaba da tuhumar masu muzaharar da laifin da wasu ‘yan iska da aka dora wa alhakin tayar da hargitsi s**a aikata domin a k**a su da laifi tare da tabbatar da kuma tabbatar da munanan laifukan da s**a aikata”, ya lurantar.

Shaikh Abdulhamid Bello ya ce; idan dai za a iya tunawa, kimanin watanni ashirin da s**a gabata a Kaduna a yayin gudanar da tarukan tunawa da Ashura an dauki jami’an ‘yan sanda a kyamara suna cinna wa motar su wuta, inda ya ce; “wannan wani hali ne da ‘yan sandan Nijeriya s**a kware a kai suke kuma yi domin tabbatar da zaluncin da suke yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Me ya sa jami’an tsaron Nijeriya ba za su karkatar da duk karfinsu da dukiyarsu wajen yakar ‘yan fashin daji da sauran miyagun da s**a addabi zaman lafiyar Al’umma ba”, ya tambaya.

Da ya waiwayo kan batun ranar Kudus kuwa, Shehin Malamin ya ce; “Batun ranar Qudus ta duniya ta goyon bayan ‘yan uwanmu Palastinu lamari ne na imani da mutuntaka. A maimakon zama namun daji da nuna rashin wayewa ta hanyar kai hari ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, me ya sa gwamnatin Nijeriya ba za ta shirya irin na ta muzaharorin ba na nuna goyon baya ga haramtacciyar kasar Isra'ila da Sahayoniyawan da s**a yi kwacen kasar da ba na su ba suke zubar da jinin al'ummar Palastinu da ake zalunta?

“Muna so mu bayyana tare da jaddada cewa ba mu da hannu a cikin kona mota da kuma makircin karya da suke yadawa na kona ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari. A don haka muna kira da a gaggauta sakin duk wanda ke hannun ‘yan sanda. Hakazalika muna son mu yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sakin takardun fita na Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat domin ba su damar kula da yanayin da suke ciki na rashin lafiya”, ya karkare.

Address

Inna Shopping Complex, Gaskiya Road Zaria
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Walkiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Walkiya:

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Zaria

Show All