04/04/2022
Matsalar tsaron ta fi karfin Buhari -
Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a jiya ya bayyana rashin tsaro da ke addabar kasar a matsayin 'babbar matsala', kuma ya ce ya k**ata masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe domin magance matsalar.
Tsohon shugaban ya furta kalaman ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta a jihar Ogun, yayin da yake karbar Dakta Ugochukwu Williams, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP da tawagarsa.
Tsohon shugaban ya ce matsalar tsaron ta gagari gwamnatin Muhammadu Buhari. "Idan wani ya zo nan ya ce ina son ganinka, zan amsa ma sa da cewa gani, saboda halin da muke ciki a Najeriya yafi karfin wani mutum daya ya ce yana da mafita. Na yi imanin sai mun zauna tare kuma mun duba al'amarin tare."
Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ruwaito shi yana cewa, "Cikin wannan halin babu wanda ke da cikakken tsaro ko a kan hanyar mota, ko a cikin jirgin kasa, ko ma a filin jirgin sama. Lalali akwai babbar matsala."
"Ya k**ata dukkan 'yan Najeriya su sani cewa mun fda cikin wata matsalar da ta gagari gwamnati mai-ci, amma bai k**ata mu bari matsalar ta fi karfin Najeriya ba, inji shi".
-BBC