08/07/2022
ALLAHU AKBAR: Khuɗubar Annabi Muhammadu S.A.W Ta Ƙarshe, Wadda Ya Yi Wa Al’ummarsa A Ranar Arafat 9 Ga Watan Zul-Hijja
Daga Zaharaddeen Gandu
Annabi Muhammad SAW yayi khuɗubar ga al-ummarsa a ranar Arafat 9 ga watan Zhul-Hijja, shekara 10 bayan Hijrar Annabi SAW a saman dutsen Arafat, wadda wannan khuɗubar ta kasance khuɗubar ƙarshe ta Manzon Allah SAW, Fiyayyen Hallita ya cigaba da khuɗubantar da al-ummarsa cewa;
“Ya ku mutane! Ku bani hankalinku, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka, ku saurari abin da nake gaya maku da kyau, kuma ku isar da abin da zan gaya maku ga waɗanda basa wannan wuri a yau”.
“Ya ku mutane! k**ar yadda kuka riƙi wannan wata na aikin hajji da wannan rana ta arfa, da kuma wannan gari na Makka da girma, kuma abin tsarewa, to haka kuma ku riƙi ran Musulmi da dukiyoyinsu da girma abin karewa".
“Ku maida wa mutane kayan da s**a baku Amana, kar ku cuci kowa, kar ku yi zalunci, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, haƙika Allah zai yi sakayya a kan ayukakanku, Allah (SWT) ya hana cin riba, (wato kuɗin ruwa) saboda haka, duk abin da aka ƙulla ta kuɗin ruwa sai an warware shi”.
“Ku yi hattara da shaiɗan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran ɓatar da ku a kan manyan abubuwa na saɓo, saboda haka ku guji bin shi a kan ƙanana”.
“Ya ku jama'a haƙiƙa kuna da haƙƙi bisa matayenku, amma suma suna da haƙƙi bisa kanku, to haƙƙinsu ne a kanku da kuciyar da su, sannan ku tufatar da su a kan jin ƙai. Ku bi da su kyakkyawar biyarwa, ku kuma tausasa musu, domin su majiɓintan al-amurran ku ne, kuma mataimakan ku, hakki ne a kansu da kar su yi abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci zina”.
“Ya ku jama'a ku yi kyakkyawan bauta ga Allah (SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, ku azumci watan Ramadan, ku bada zakka, ku aikata aikin hajji in har kun sami damar yi”.
“Ku sani fa, ko wanne musulmi ɗan uwan musulmi ne, dukkan ku dai dai kuke, ba wanda yake da fifiko saman wani, sai wanda yafi wani tsoron Allah, da aikata kyawawan ayyukka”.
“Ku tuna fa ya ku jama'a wata rana za ku tsaya gaban Ubangijinku, domin sak**akon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara, kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na babu raina”.
“Ya ku jama'a ba wani Annabi ko Manzo da zai zo bayana, kuma babu wani Addini da zai zo bayan addinin musulunci, saboda haka, kuyi tunani sosai a kan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta sosai”.
“Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga Al-Qur'ani da kuma Sunnah ta. In kun bi wannan ba za ku ta ɓa ɓata ba, duk abin da ya shige muku duhu komai na cikin Al-Qur'ani da kuma Sunnah ta”.
"Duk wanda ya ji wannan saƙo to ya jiyar da waɗansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa waɗanda za su ji magana daga ƙarshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abin da nake faɗa”.
"Ya Allah Ubangijin halittu, ka zamo shaida a gareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka”. Inji Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu S.A.W a khuɗubarsa ta ƙarshe.
Sannan ina kira ga 'yan uwana musulmai da ku yaɗa wannan khuɗubar ga 'yan uwa musulmai domin ta ƙara yaɗuwa k**ar yau akayi ta.
Allah ka sadamu da Annabi Muhammadu S.A.W, Ya Allah ka biya wa kowa buƙatunsa na Al-khairi.