Katsina Daily News

Katsina Daily News Domin Samar Da Labarai Da Dumu-duminsu

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukuncin a rataye dan Chinan da ya kashe Ummita a Kano
26/03/2024

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukuncin a rataye dan Chinan da ya kashe Ummita a Kano

'Yan garin Gwarjo ta ƙaramar hukumar Matazu sun roki a sa su cikin addu'a Allah Ya kawo masu sauƙin hare-haren da 'yan b...
26/03/2024

'Yan garin Gwarjo ta ƙaramar hukumar Matazu sun roki a sa su cikin addu'a Allah Ya kawo masu sauƙin hare-haren da 'yan bindiga s**a matsa wa garin tare da rokon Gwamnatin Mai girma Gwamna Malam Dikko Umar Radda PhD ta taimaka don girman Allah.

MATSALAR TSARO A GARIN GWARJO DA KEWAYEN GARIN!

Wannan gari mai suna GWARJO Karamar hukumar Matazu jihar Katsina, gari ne mai cike yawan jama'a amma kuma barayi 'yan bindiga sun takura mashi kusan kowane dare s**an shigo mamu su dauki Mutane ko su kashe Mutum ko Dabbobi da sauransu.

'Yan Kungiyar sakai, Ƙaramar hukuma, Shugabannin Gari, Kungiyoyin Matasa da kuma Dattawan Gari suna bakin kokarin su amma abin yaci tura, Wallahi kullum akwai kalar barazana da ake yi mana idan dare yayi, shin wai mu ba mutane bane!, Ku sani cewa akwai sakayya don girman Allah a taimaka.

Kungiyar GWARJO YOUTH FOUNDATION kungiya ce ta matasan garin Gwarjo, suna so a isar masu da sakon godiya ta musamman ga Mai girma Gwamna Malam Dikko Umar Radda PhD da Shugaban Karamar hukumar Matazu Hon.Shamsuddeen Muhammad Sayaya akan Jajircewarsu da fatan kawo karshen wannan tashin hankali da yardar Allah, sannan kuma kungiyar tana rokon mai girma Gwamna ya taimaka ma garin da gudunmuwar Jami'ai ko garin da kewayensu zasu samu sauƙin hare-haren, muna godiya.

Daga karshe kungiyar tana addu'a Allah ya kawo mana karshen wannan tashin hankalin, Allah ya kawo mana Zaman lafiya a karamar hukumar Matazu dama jihar Katsina baki daya Amin.

Reported by:
GWARJO YOUTH FOUNDATION

Hadisinmu Na Yau Talata 16 Ramadan 1445 (26 March 2024)Anas RA ya ruwaito:Zaid bin Thabit RA ya ce; Mun yi Suhur da Anna...
26/03/2024

Hadisinmu Na Yau Talata 16 Ramadan 1445 (26 March 2024)

Anas RA ya ruwaito:
Zaid bin Thabit RA ya ce; Mun yi Suhur da Annabi SAW. Sannan muka tashi domin yin sallah, Na tambaya; Menene tazarar tsakanin Suhur da kiran sallah? Ya ce; Tazarar ta isa a karanta ayoyi hamsin na Al-Qur'ani.

Narrated Anas RA:
Zaid bin Thabit RA said, "We took the Suhur with the Prophet SAW. Then he stood for the prayer." I asked, "What was the interval between the Suhur and the Adhan?" He replied, "The interval was sufficient to recite fifty verses of the Qur'an."

Sahih Al-Bukhari.

Yanzu-yanzu: Majalisar Dokokin jihar Katsina ta umurci a garƙame duk wasu makarantun koyon jinya da unguwar zoma da aka ...
25/03/2024

Yanzu-yanzu: Majalisar Dokokin jihar Katsina ta umurci a garƙame duk wasu makarantun koyon jinya da unguwar zoma da aka buɗe a jihar Katsina ba bisa ka'ida ba

Mai Girma Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya, ya Jagoranci zaman zauren Majalissa na yau Litinin 25/03/2024, inda aka Tattuna akan Muhimman Batutuwa

Majalissar tayi kiran Gaggawa zuwa ga Ɓangaren Zartaswa (Executive Arm) da’a Dakatar da duk wata Makarantar koyon Karatun Jinya da Ungozomanci (School of Nursing and Midwifery) wanda Gwamnati bata basu Lasisin Gudanarwa ba, da Makarantun Karatun Kiwon Lafiya (School of Health) wanda basu da Rijista da Gwamnati a faɗin Jihar Katsina

Kiran ya biyo bayan wani zaman Gaggawa da Majalissar Dokoki tayi da Ƙungiyar Likitoci ta Jihar Katsina, inda Mambobin Ƙungiyar s**a koka, kan yadda irin wannan Makarantun suke yaye Ɗalibai wanda basu Cancanta ba, wanda a cewarsu, hakan yana haifar da Ɓarna a ɓangaren kiwon lafiya, inda har s**a bada misalai iri daban-daban, wanda irin wannan Ɗaliban s**a haifar wajen kula da marassa lafiya

Kakakin Majalissa da sauran abokan aikin sa, s**a amince da wannan Ƙudurin cikin Gaugawa, Kakakin Majalissa ya ba akawun Majalissar Umarnin a turawa ɓangaren Zartaswa domin a dauki matakin Gaggawa akan Al’amarin.

Amadadin Al,ummar Dargage word dake k**ar hukumar Zango Muna kira ga Alhaji Kabiru Yusuf Barage daya amsa kiran Al,ummar...
25/03/2024

Amadadin Al,ummar Dargage word dake k**ar hukumar Zango Muna kira ga Alhaji Kabiru Yusuf Barage daya amsa kiran Al,ummar mazaabar Dargage word dake karamar hukumar Zango domin wakilcemu amatsayin kamsila muna kyautamasa zato na alheri

Da fatan mun sha ruwa lafiya Allah Ya karba mana

Sako daga Matasan Barage

Saura awa nawa ko minti a sha ruwa garin da kake yanzun haka?
25/03/2024

Saura awa nawa ko minti a sha ruwa garin da kake yanzun haka?

Cikin Hotuna: Yadda gwamnatin jihar Kaduna ta karɓi daliban Kuriga a gidan gwamnatin jihar, da aka karbo hannun yan bind...
25/03/2024

Cikin Hotuna: Yadda gwamnatin jihar Kaduna ta karɓi daliban Kuriga a gidan gwamnatin jihar, da aka karbo hannun yan bindiga, bayan sun sace su tsawon kwanaki a hannunsu

Nafilfili: Na cikin kyawawan ayyuka da ake buƙatar mai azumi ya lizimta don samun gagarumar lada a wannan wata na Ramada...
25/03/2024

Nafilfili: Na cikin kyawawan ayyuka da ake buƙatar mai azumi ya lizimta don samun gagarumar lada a wannan wata na Ramadan

Tunasarwar yau za ta yi magana kan muhimmancin nafil-fili da ake son mai azumi ya lizimta a cikin wannan wata na Ramadan

Yauma k**ar kullum kar a manta mai daukar nauyin wannan tunasarwar shi ne Hon Jamilu Muhammed Lion

Nafil-fili: Ana so mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman kiyamul laili, saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara tabbata a gareshi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya tsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da s**a gabata". Bukhari ne ya ruwaito shi(1).

Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wanda yayi sallah dare tare da liman har
yagama za'a rubuta masa ladan kiyamullaili(2).

Kuma anfison duk wanda zai yi kiyamullaili ya tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) ya ce:
_____________________________________
(1) Bukhari K = 31, B = 70, H = 2009, da
Muslim K = 6, B = 25, H = 760.
(2) Targib Wattarhib wanda Albani yayi wa
tahkiki lambar (1078).

"Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadhan fiye da sauran sallolin dare, yace: Manzon Allah (S.A.W) yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a daya, kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikin ta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari. Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A) yazo yana neman izni ayi sallar Asuba. Ahmad ya ruwaito wannan hadisin

Yanzu-yanzun: Sarkin Kano ya karɓi bakuncin Peter Obi a fadarsa dake cikin birnin Kano
25/03/2024

Yanzu-yanzun: Sarkin Kano ya karɓi bakuncin Peter Obi a fadarsa dake cikin birnin Kano

25/03/2024

Day 18 - Ramadan Tafsir day 15 (1445/2024) tare da Sheik Dr Ahmad Gumi daga masallacin Sultan Bello Kaduna

Gardamar da ake ta yi wasu na cewa an biya kudin fansa wajen ceto daliban Kuriga, wasu na cewa ba a biya ba, wannan maga...
25/03/2024

Gardamar da ake ta yi wasu na cewa an biya kudin fansa wajen ceto daliban Kuriga, wasu na cewa ba a biya ba, wannan maganar ba ta da wani amfani - Inji Gwamnan Kaduna Uba Sani

Babbar magana: An ƙara kashe 'yansandan Najeriya shida a jihar DeltaRundunar 'yansandan Najeriya ta tabbatar da kashe wa...
25/03/2024

Babbar magana: An ƙara kashe 'yansandan Najeriya shida a jihar Delta

Rundunar 'yansandan Najeriya ta tabbatar da kashe wasu jami'anta shida a jihar Delta.

A watan Janairu ne 'yan bindiga s**a sace wasu 'yansanda uku da ke kan aiki, lokacin da aka kira su wani waje da ake hatsaniya a Ohoro cikin Ƙaramar Hukumar Ughelli ta arewa.

Jami'an uku na cikin tawagar 'yansada shida da aka kai wajen duba ababan hawa a Ughelli kan titin Patani.

Makonni kaɗan aka sake kai wasu 'yansandan domin ceto abokan aikinsu da aka sace.

Yayin wannan aiki ne aka yi wa 'yansandan kofar rago aka kashe su a wajen dajin Ohoro da ke ƙaramar hukumar Ughelli.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, kakain 'yansandan jihar Muyiwa Adejobi, ya ce an gano gawarwakin jami'an shida da aka kashe, ana kuma ci gaba da neman wasu jami'ai shida na daban.

"An gano gawar waɗannan jami'an ne lokacin da ake binciken haɗin gwiwa tsakanin 'yansanda da sauran jami'an tsaro," in ji Adejobi.

"Rundunarmu ta mayar da hankali wajen neman sauran jami'anmu shida, a gefe guda kuma mun tuntubi duka iyalansu kan wannan batu.

"Waɗanda s**a mutu sun hada da Sifeto Abe Olubunmi da ya fara aiki 1 ga watan Agusta, 2003, Septo Friday Irorere 1 ga watan Janairun 2003, Sajan Kuden Elisha 17 ga watan oktoba 2011, Sajan Akpan Aniette shi ma 17 ga watan Oktoba 2011, Sajan Ayere Paul 17 ga Oktoba 2011, sai kuma Sajan Ejemito Friday wanda shi ma ya fara aiki 17 Oktoba 2011.

"Jami'an da ake ci gaba da nema kuma sun haɗa da Sefeto Onoja Daniel enlisted da Sefeto Onogho Felix da Sefeto Emmanuel Okoroafor enlisted da Sufeto Joel Hamidu.

"Akwai kuma Sajan Moses Eduvie da kuma Sajan Cyril Okorie,” in ji sanarwar

Ya ce za a yi bikin binne waɗannan jami'ai a Abuja ranar 5 ga watan Afrilu.

Ya zuwa yanzu an k**a mutum biyar da ake zargi da hannu cikin kashe jami'an.

Jama'a barkanmu da asuba da fatan mun tashi cikin ƙoshin lafiyaKu rubuta sunayen wadanda kuke so a yi masu tashin gwauro...
25/03/2024

Jama'a barkanmu da asuba da fatan mun tashi cikin ƙoshin lafiya

Ku rubuta sunayen wadanda kuke so a yi masu tashin gwauro, tun kafin lokaci ya ida ƙurewa, don a taimaka masu kar su makara.

Hadisinmu Na Yau Litinin 15 Ramadan 1445 (25 March 2024)Sahl bin Sa'ad ya ce:Na kasance ina yin Suhur tare da iyalina sa...
25/03/2024

Hadisinmu Na Yau Litinin 15 Ramadan 1445 (25 March 2024)

Sahl bin Sa'ad ya ce:
Na kasance ina yin Suhur tare da iyalina sannan sai in hanzarta domin inyi sallar Asuba tare da Manzon Allah SAW.

Narrated Sahl bin Sa'ad RA:
I used to take my Suhur meals with my family and then hurry up for presenting myself for the (Fajr) prayer with Allah's Messenger PBUH.

Sahih Al-Bukhari.

Babbar magana: Hukumar Alhazai ta kasa ta sanar da ƙarin N1.9m ga duk maniyyacin da zai je Saudiyya sauke faralin aikin ...
24/03/2024

Babbar magana: Hukumar Alhazai ta kasa ta sanar da ƙarin N1.9m ga duk maniyyacin da zai je Saudiyya sauke faralin aikin hajji a bana, inda yanzun kudin kujerar ya koma N6.8 million maimakon N4.9m da ta fara ƙayyadewa a can farko

Hukumar ta kuma bayyana cewa duk wanda ya fara zuba kudin ajiya da ya gaggauta zuwa ya ciki kadin kafin nan da 28 March 2024 din nan da muke ciki

Ta bayyana dalilin karin kudin da yana yin canjin kudin Nijeriya zuwa na kasashen waje da ake fama da shi tsawon lokaci a kasar nan

Daliban jihar Katsina dake karatu a Jami'ar Tarayya ta Gusau FUGUS sun roki masu madadun ikon na jihar Katsina da su tal...
24/03/2024

Daliban jihar Katsina dake karatu a Jami'ar Tarayya ta Gusau FUGUS sun roki masu madadun ikon na jihar Katsina da su tallafa ma wasunsu da kudin rijistirashin kada karatunsu ya durƙushe

ĎALIBAN JAHAR KATSINA
DAKE KARATU,

>>A jami,ar tarayya dake Gusau (FUGUS) akwai dalibai Kusan dubu daya Yan asalin jihar katsina

>>Sama da dalibi 500 dakyar suke biyan tsohon kudin makarantar.

>>100 da ýan kai kuma wallahi ko wancan lokacin sai ana dab da exam idan an samu wani ya biya masu ko cikin abokannsu sun basu rance wanda basu iya biya daga baya saidai a yafe masu.

Abun da ya ķara tayarmana da hankali irin yadda wani ya fađaman cewa wallahi ya haqura da karatun kuma aji uku yake (300lv), to yanxu irin wadan nan mutum nawa ne muke dasu cikin alumma, Babban masifar itace mutum ya Bata lokacinsa da yawa gashi yau anzo stage en da in baa taemakeshi bah sae dae ya haqura.

Ko shakka babu daliban dake karatu Federal university Gusau suna bukatar agajin gaggawa daga duk mai halin taimakawa.

Muna kira ga duk mai halin taimakawa don Allah ya taimaka.

Muna kiraga,
Yan Siyasarmu
Yan kasuwa dasu taimaka Dan Allah,
👇
Duk dalibin da ka đauki nauyin karatun shi koda da 30% ne wallahi bazai ta6a manta ka a rayuwa saboda duk abunda zai zama kana daga cikin silar zamewar shi✅

Muna roqon dukkan Wanda yasan akwae wata hanya da zaa iya bi domin ganin a ceto dalibae da karatu kan iya gagararsu to ya taemako mana da hanya.
Kira na musamman ga shuwagabannin alumma irinsu Mae Daraja Gobna Mal Dikko Ummar Radda, Distinguish Senator Muktar Dandutse, Distinguish Senator Nasir Sani Zango, Distinguish Senator Abdulaziz Musa yar'adua, tare da Yan majalisun tarayya masu wakiltar alummar jahar katsina, da kuma entire Majalisar jaha, commissioners, S.A kae dama dukkan wani Mae madafun Iko ciki da wajen jahar, mu qara tunawa da cewa duk Wanda ya taemaki wani Allah zae taemake shi.
Wlh akwae Wanda a cikin alummarmu na jahar nan, daukar nauyin nan gaba daya na daliban nan wlh Bazae rage komae a cikin dukiyar da Allah ya albarkace shi da eta.

Bamuce sisinka ka bamu bah, Amman kawomaka remitta ta adadin mutanen da kake da iKon yimawa, domin mu ke cikin daliban nan muka San halin da ake ciki.

Daga karshe Muna Addua Allah ya bada iKon taemakawa, wanda ya taemaka Shima Allah ya taemakeshi.
🖋
Comrd Musa Isah Abba
NAKATSS President FUGUS Chapter

Jama'a barkanmu da shan ruwa da fatan Allah Ya karba manaShin za ka iya yarda ka fara buda baki da abinci k**ar wannan b...
24/03/2024

Jama'a barkanmu da shan ruwa da fatan Allah Ya karba mana

Shin za ka iya yarda ka fara buda baki da abinci k**ar wannan ba tare da ka sha kunu ba?

Ina mika saqon barka da shan ruwa zuwa ga Al,umar mazabata ta Dargage dake karamar hukumar Zangon Daura dama daukacin ja...
24/03/2024

Ina mika saqon barka da shan ruwa zuwa ga Al,umar mazabata ta Dargage dake karamar hukumar Zangon Daura dama daukacin jama,ar karamar hukumar Zango baki daya Allah ya karbi ibadunmu na yau da kullum

Saqo daga Alhji Kabiru Yusuf Barage

Muhimmancin ciyar da mai azumi a wannan watan na RamadanCiyar da mai Azumi abin Buda baki: Yana daga cikin mafificiyar i...
24/03/2024

Muhimmancin ciyar da mai azumi a wannan watan na Ramadan

Ciyar da mai Azumi abin Buda baki: Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi kokari wajen bawa dan uwansa abin bude baki saboda hadisin da Annabi
(S.A. W) yake cewa: "Duk wanda ya ciyar da mai Azumi abin da zai yi bude baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba". Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih(1).

Daukar nauyi fi sabilillah Hon Dr Jamilu Lion

Abin alkairi: Dangote ya kaddamar da rabon buhunan abinci na naira biliyan sha biyar a Kano don saukaka wa alumma a kan ...
24/03/2024

Abin alkairi: Dangote ya kaddamar da rabon buhunan abinci na naira biliyan sha biyar a Kano don saukaka wa alumma a kan halin da ake ciki na matsin tattalin arziki

"Cikin yan kwanakin nan na gani a midiya ana ta yamadidin cewa wai gwamnatinmu ta ware N6m don ciyarwar azumi, wanda kum...
24/03/2024

"Cikin yan kwanakin nan na gani a midiya ana ta yamadidin cewa wai gwamnatinmu ta ware N6m don ciyarwar azumi, wanda kuma ba haka bane, abin da muka ware don ciyarwar azumi a watan Ramadan gaba daya shi ne N1.197bn Inji gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

24/03/2024

Bidiyo: Yadda shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Faskari Hon Khalid Bilbis yake ta rabon kudi a mahaifarsa ta Bilbis, bayan ya rabar tallafin makudan kuɗaɗe ga shuwagabannin jam'iyya da sauran al'umma sama da mutum 300

Sponsored

Gwamnatina za ta tabbatar ta ba makarantu da dalibai kariya sosai - Inji Tinubu yayin da yake murnar kubutar da daliban ...
24/03/2024

Gwamnatina za ta tabbatar ta ba makarantu da dalibai kariya sosai - Inji Tinubu yayin da yake murnar kubutar da daliban Kuriga da sojoji s**a yi a yau

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana nasarar ceto daliban Kuriga da yan bindiga s**a sace a jihar KadunaRundunar ta bayya...
24/03/2024

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana nasarar ceto daliban Kuriga da yan bindiga s**a sace a jihar Kaduna

Rundunar ta bayyana cewa ɗalibai 137 ne ta ceto 76 mata sai kuma 61 dalibai maza

Rundunar ta bayyana cewa ta sami wannan nasarar ne a farkon safiyar yau Lahadi, kuma ba da jimawa ba za ta damka daliban ga gwamnatin jihar Kaduna

Wannan na zuwa ƙasa da awanni 48 da rundunar sojin kasar ta bayyana nasarar ceto almajirai 16 tare da wasu mata da yan bindiga s**a sace a jihar Sokoto

Yadda shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Faskari Hon Khalid Adamu Bilbis, ya tara mutane makil a mahaifarsa ta ga...
24/03/2024

Yadda shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Faskari Hon Khalid Adamu Bilbis, ya tara mutane makil a mahaifarsa ta garin Bilbil ya ci gaba da raba masu makudan kuɗaɗe ba kakkautawa, kuma bai ware sai yan jam'iyyarsa ba, duk wanda ya zo wurin ya karɓi kasonsa

Bidiyon na nan tafe

Sako daga masoya PDP dawodawo

24/03/2024

Tashin hankali: Shugaban ƙaramar hukumar Faskari ya sheda wa BBC Hausa cewa yan bindiga sun kara yin sansani a cikin karamar hukumar, lokacin da yake tabbatar masu da harin Mairua da kuma kashe Alh Lado Mairua da wani mutum ɗaya daidai lokacin sallar tarawi

Wani bayani mai ban tausayi da ɗaga hankali game da harin da yan bindiga s**a kai wa masallata a Mairua har s**a kashe A...
24/03/2024

Wani bayani mai ban tausayi da ɗaga hankali game da harin da yan bindiga s**a kai wa masallata a Mairua har s**a kashe Alh Lado Mairua da makwabcinsa

Bayan sun kashe Alh Lado Mairua da makwabcinsa ana lokacin da suke tsaka da sallar tarawi, yan bindigar sun kuma Dauki iyalanshi guda biyu, Matar shi Daya Mai Suna HAJ. RABI da Diyar shi mace Mai Suna MARYAM ita Maryam Budurwace Mai kimanin shekaru 18 zuwa 19 .

A lokutan baya da s**a shiga gidan Alh. LADO sun Taba Daukar ita Maryam din Har Saida aka Biya kudin Fansa,
Zuwan su na yau bayan sun kashe Alh Lado Mairua da makwabcinsa, sun Harbi Mutum biyu, Daya a Hannu Daya A baki.

Shi Wanda akan Harba a Hannu da sauki anje a sibiti an yi dressing, shi Kuma Wanda akan Harba a Baki yana General Hospital Funtua an bashi Gado.

Kuma Sun kwashi wayoyin Mutane da dama Wanda sunkai kima nin #134,000.
Farkon Shigowar su Garin Mairua sun Fara shiga Gidan Marigayi Alh. Ibrahim Umar Kantoma ne, Yaya ga Marigayi Alh. LADO, inda s**a yi Garkuwa da Uwar Gidan da Jikokinshi Yara mata Guda Biyu inda daga bisa ni S**a Kubuta daga Hannunsu, sai dai Sun Dauki Kayan Sawa da Takardu Na Makaranta na Yara Maza da National I D Card da Voter Card, da Jakunkuna Guda biyu s**a Dauka a Gidan da s**a Fara shiga." Kamar yadda iyalan wadanda harin ya shafa Umar Ibrahim ya kara yi wa Katsina Daily News karin bayani

Gwamnan Bauchi ya yi wa fursunoni 96 dake ɗaure a gidan yari afuwa, ya biya masu kudin tara N7m, tare da raba masu N13m ...
24/03/2024

Gwamnan Bauchi ya yi wa fursunoni 96 dake ɗaure a gidan yari afuwa, ya biya masu kudin tara N7m, tare da raba masu N13m a matsayin tallafi su je su k**a sana'a

Yanzu-yanzu Gwamnan Kaduna ya ce sun ceto daliban makarantar Kuriga ga baki ɗayansu kaf, da yan bindiga s**a sace suna t...
24/03/2024

Yanzu-yanzu Gwamnan Kaduna ya ce sun ceto daliban makarantar Kuriga ga baki ɗayansu kaf, da yan bindiga s**a sace suna tsaka da karatu

Kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na X ya ce wani abin jin daɗi babu yaron da ya yi ko kwarzane har s**a yi nasarar ceto su

Hadisinmu Na Yau Lahadi 14 Ramadan 1445 (24 March 2024)Nana Aisha RA ta ce:Bilal ya kasance yana kiran Sallah a cikin da...
24/03/2024

Hadisinmu Na Yau Lahadi 14 Ramadan 1445 (24 March 2024)

Nana Aisha RA ta ce:
Bilal ya kasance yana kiran Sallah a cikin dare, sai Manzon Allah SAW ya ce; Ku ci gaba da cin abincinku har sai Ibn Ummi-Maktum ya kira Sallah, domin shi ba ya kira sai asuba ta yi.

Narrated Aisha RA:
Bilal used to pronounce the Adhan at night, so Allah's Messenger PBUH? said, "Carry on taking your meals (eat and drink) till Ibn Um Maktum pronounces the Adhan, for he does not pronounce it till it is dawn.

Sahih Al-Bukhari.

Address

Nagogo Road Kofar Durbi Katsina
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina Daily News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Katsina Daily News:

Videos

Share