Taskira - H Online Tv

Taskira - H Online Tv Mun samar muku da Taskira Online TV domin samun Ingantattun labarai, rahotanni da kuma sharhuna kan
(4)

GARE KU MASU AMFANI DA FACEBOOK: Ku yi Following Anas Saminu Ja'en ku ziyarci shafin sa ga shi can ya yi magana mai muhi...
09/12/2024

GARE KU MASU AMFANI DA FACEBOOK: Ku yi Following Anas Saminu Ja'en ku ziyarci shafin sa ga shi can ya yi magana mai muhimmanci akan Monetizating Facebook ɗin ku har ku fara samun kuɗi dashi.

Ya ce a wannan lokaci da ake cikin matsin tattalin arziƙi a ƙasashe irin Najeriya bai k**ata matasa mu tsaya a bar mu a baya ba wasu na can suna samun kuɗaɗe masu ɗumbin yawa a wannan Sahar ta Facebook.

Lokaci ya yi da za mu farka, Insha Allah zan dage wajen wayar muku da kawunan ku tunda abu ne da kowa ma zai iya yi!!!.

A tura saƙon zuwa gaba don wasu su amfana suma 🙏🏻🙏🏻

Ƙasar Ghana ta koyi yadda ake gudanar da sahihin zabe daga Najeriya - Inji Shugaban INEC na ƙasa Farfesa Mahmoud Yakubu ...
09/12/2024

Ƙasar Ghana ta koyi yadda ake gudanar da sahihin zabe daga Najeriya - Inji Shugaban INEC na ƙasa Farfesa Mahmoud Yakubu ya faɗa

Me za ku ce game da wannan iƙirarin na shugaban zaɓen Najeriya?

MAGANAR JIYA TA DAWO: "Ina faɗawa ƴaƴana  duk lokacin da za su yi aure cewa, idan mijin su ya mare su, to su rama marin"...
09/12/2024

MAGANAR JIYA TA DAWO: "Ina faɗawa ƴaƴana duk lokacin da za su yi aure cewa, idan mijin su ya mare su, to su rama marin" in ji Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll k**ar yadda Daily Trust ta rawaito.

Hotunan yadda Mai Martaba Sarkin Kano Na 15 Alh. Aminu Ado Bayero, Ya gyara gidan Sarki da ke yankin Nassarawa G.R.A a j...
09/12/2024

Hotunan yadda Mai Martaba Sarkin Kano Na 15 Alh. Aminu Ado Bayero, Ya gyara gidan Sarki da ke yankin Nassarawa G.R.A a jihar Kano.

Yanzu ta tabbata Sarki biyu ne a Kano ko jama'a?

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, Ya shiga Unguwarnin Kofar Mata, Yakasai, Rimi da Zango, A yau ra...
09/12/2024

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, Ya shiga Unguwarnin Kofar Mata, Yakasai, Rimi da Zango, A yau ranar 9 ga wata Disamba 2024.

Kazalika, Ya bada umarnin gudanar da bincike da k**a duk wanda yake da hannu akan faɗan Daba a unguwarnin.

📸 Facebook/Abdullahi Haruna Kiyawa

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Tare Da Mahaifiyarsa Sun Jagoraci Ƙaddamar Da Fara Ginin Babban Masallacin Juma’a agarin Kahu...
09/12/2024

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Tare Da Mahaifiyarsa Sun Jagoraci Ƙaddamar Da Fara Ginin Babban Masallacin Juma’a agarin Kahutu Dake Jihar Katsina.

Daga Baba Abdullahi

Tawagar Jarumai da Daraktocin Kannywood kenan yayin da ta isa birnin Jiddah na ƙasar Saudiyya domin halartar taron Baje-...
09/12/2024

Tawagar Jarumai da Daraktocin Kannywood kenan yayin da ta isa birnin Jiddah na ƙasar Saudiyya domin halartar taron Baje-Kolin Fina-finai na “Red Sea International Film Festival” na ƙasar, yayin da wani fim ɗin Kannywood mai suna ”Mamah” ya samu nasarar shiga ɗaya daga cikin fina-finan da za a haska a wannan taro.

Rahama Sadau da Falalu A. Ɗorayi na daga cikin wannan tawaga.

Taron wanda a yau ne ake sa ran haska fim ɗin na Kannywood, an fara ne tun ranar 5 ga wannan wata na Disamba kuma za a rufe a ranar 15 ga wata.

📸Falalu A. Ɗorayi

ALLURAR CIKIN RUWA: Har Yanzu A Kasuwa Nake, Ba Ni Da Aure, Duk Wadda Rabonta Ya Tsaga Ta Zo Ta Yi Wuf Da Ni, Inji Malam...
09/12/2024

ALLURAR CIKIN RUWA: Har Yanzu A Kasuwa Nake, Ba Ni Da Aure, Duk Wadda Rabonta Ya Tsaga Ta Zo Ta Yi Wuf Da Ni, Inji Malam Dogo

Wane fata zaku yi masa?

Hotunan yadda Mai Martaba Sarkin Kano na 14 da 16 Khalifa Mallam Muhammad Sanusi II, Ya halarci Saukar karatun Al-Qur'an...
09/12/2024

Hotunan yadda Mai Martaba Sarkin Kano na 14 da 16 Khalifa Mallam Muhammad Sanusi II, Ya halarci Saukar karatun Al-Qur'ani mai girma a Makarantar Majeeda Litaaleemil Qur’an da ke
Darmanawa, A ranar Lahadi 8 ga watan Disambar 2024.

Ban Taɓa Ganin Matasa Masu Haɗin Kai Da Ƙaunar Junansu Kamar Abokan Comr Abba Sani Pantami BaDaga Aliyu HaidaraBabu shak...
09/12/2024

Ban Taɓa Ganin Matasa Masu Haɗin Kai Da Ƙaunar Junansu Kamar Abokan Comr Abba Sani Pantami Ba

Daga Aliyu Haidara

Babu shakka idan har sauran matasa za su hada kan su k**ar yadda abokan Comr Abba Sani Pantami s**a yi, to ko shakka babu za a samu cigaba sosai a bangaren harkokin matasa a kasar nan.

Makasudin yin wannan rubutu nawa shine yadda cincirindon abokan matashin s**a taso daga jihohin su daban-daban domin halartar daurin aurensa, duk da matsanancin yanayi da muke ciki a wannan lokaci. Sannan kuma kusan 90 daga cikin su sun sha ankon bikin gwanin ban sha'awa.

Daga bangare na na yi matukar samun tarba ta musamman daga wajen wadannan matasa duba da irin kyakkyawar alakar dake tsakanina da su, duk da cewa da yawan su ba mu taba ganin juna ba.

Sannan zan yi jinjina ta musamman ga abokan ango na cikin gida masu masaukin baki, duba da yadda s**a gudanar da hada-hadar shagulgulan bikin, tare da baiwa bakin da s**a zo daga jihohi daban-daban kyakkyawar kulawa, ta hanyar ba su masauki mai kyau sannan kuma abinci ba kakkautawa.

Babu abinda zan ce ga tawagar wadannan matasa, saidai na ce Allah ya kara hada kan su, Ya kuma kara musu kaunar juna da kuma taimakon junansu.

Jinjina ta musamman ga uban gayya wato Ango Comr Abba Sani Pantami, Comr Haidar H Hasheem, Comr Nura Siniya, Muhammad Kwairi Waziri, Hafiz Ali Kabade, Zaharaddeen Gandu, Muhammad Cigari Kumo, Abubakar Shehu Dokoki, Magaji Fandallafih, Shehi Lawal da sauransu.

Sanata Kawu Sumaila ya kaddamar da gwajin hakar rijiyoyin noman rani guda 100 da injinan suma guda 100 a yankin kano ta ...
09/12/2024

Sanata Kawu Sumaila ya kaddamar da gwajin hakar rijiyoyin noman rani guda 100 da injinan suma guda 100 a yankin kano ta kudu a karamar hukumar Ajingi.

Sen. Kawu Sumaila ya tabbatar musu cewa cikin karamin lokaci za’a dawo a karasa guda 500 hade da injinan Noman ranin a Ajingin da kuma sauran wasu LGA’s na Kano ta kudu.

📷 Sen. Abdullahi Muhd Sumaila :

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kasa Gyara Gidan Sarki Nassarawa Bayan Kuɗaɗen Da Ta WareDaga Ayman AdoKwanakin baya gwamnatin j...
09/12/2024

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kasa Gyara Gidan Sarki Nassarawa Bayan Kuɗaɗen Da Ta Ware

Daga Ayman Ado

Kwanakin baya gwamnatin jiha ta yi zaman council, bayan an tashi daga zaman Kwamishina yaɗa labarai ya gayawa ƴan jarida cewa a zaman an ware kuɗaɗe kusan Naira milyan ɗari domin sabunta katangar gidan Sarki da ke Nassarawa kusa gidan gwamna.

Kuma yau kusan watanni Uku da fitar da wancan kuɗin amma aikin ya gagara, ƙarshe dai Mai Martaba Sarki ya gaji da jiran gwamnati, gashi yana gyara katangar sa da kansa.

Ko ina makomar waɗancan kuɗaɗen da aka ce an ware ??

A ilmin finance, akwai bambanci tsakanin "Revenue", "Capital", "Income" da kuma "Assets"Akwai rubuttukan dana gani suna ...
09/12/2024

A ilmin finance, akwai bambanci tsakanin "Revenue", "Capital", "Income" da kuma "Assets"

Akwai rubuttukan dana gani suna maganar cewa a dokar harajin da take gaban majalisa akwai haraji akan "inheritance" wato "Gado" a hausance.

Amma sashin da wadanda s**a yi wannan rubutun s**a dogara da shi wato chapter 2, part 1, section 4(3) yana magana ne akan families income ne. Kuma shi wannan sashin an kwafo shi ne kai tsaye daga dokar harajin PITA 2004 as amended section 2(5).

Shi "inheritance" wato "gado" ana rabon either "Capital" ko "Asset" abin nufi dukiya ake rabawa ba riba wato "income". Shi kuma wancan sashin wanda dama can ya na cikin dokar harajin mu da take aiki a yanzu akan "income" yake magana.

A cikin dokar harajin da ake aiki da ita a yanzu akwai maganar "community income" da "family income" wanda haraji ne da ake karba akan ribar da family ko community s**a samu a dunkule. Misali da kai da matar ka, abokan ka, 'yan uwanka ko kuma jama'ar wani kauye ko unguwa suna kasuwanci a dunkule kuma zai yi wuya a ware ribar da aka samu ta waye to sai a chaji haraji akan total ribar da s**a samu.

Wannan doka a yanzu tana section 2(4) da kuma section 2(5) na Personal Income Tax Act 2004 as amended.

Batun Cewa Ba A Magana Idan Mutum Yana Wanka A Bandaki Ba Gaskiya Ba Ne, Domin Annabi SAW Ma Yana Magana A Bandaki - Inj...
08/12/2024

Batun Cewa Ba A Magana Idan Mutum Yana Wanka A Bandaki Ba Gaskiya Ba Ne, Domin Annabi SAW Ma Yana Magana A Bandaki - Inji Sheikh Lawan Triumph

08/12/2024

🎥 Farfesa Mustapha Bagudo Muhammad, Ya bayyana cewar tsoron da ƴan Arewa suke na gyaran dokokin Najeriya haraji abin tsoron bai kai yadda ake rurutawa ba.

Idan kana maganar mutunci a Jihar Kano, ka kai ɗan Sarki ne? Don haka maganar mutunci babu shi a wajen yan Kwankwasiyya ...
08/12/2024

Idan kana maganar mutunci a Jihar Kano, ka kai ɗan Sarki ne? Don haka maganar mutunci babu shi a wajen yan Kwankwasiyya - Inji Hon. Abdullahi Abbas Shugaban Jam'iyyar APC na Kano.

Jihohi 4 ne kacal s**a jawo masu zuba jari a Najeriya a watanni 9 na 2024Jihohin sune: 1. Lagos: $4.80bn2. FCT: $2.43bn3...
08/12/2024

Jihohi 4 ne kacal s**a jawo masu zuba jari a Najeriya a watanni 9 na 2024

Jihohin sune:
1. Lagos: $4.80bn
2. FCT: $2.43bn
3. Kaduna: $1.95m
4. Enugu: $184,229
5. Ekiti: $117,850

Ya mama jimilar Jimilla: $7.23bn

Inji hukumar ƙididdiga ta

Naira ta kara samun daraja a kasuwar canjin kuɗaɗen wajeDala ta karye a karo na uku a jere, inda juya aka canza e da ita...
08/12/2024

Naira ta kara samun daraja a kasuwar canjin kuɗaɗen waje

Dala ta karye a karo na uku a jere, inda juya aka canza e da ita kan N1,567/$1.

Wannan shine karo na farko da aka canja dala ƙasa da N1,600 Tun watan Oktoba, lokacin da aka canja ta kan N1,561.7.

Ko Dalar za ta ci gaba da karye wa?

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskira - H Online Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Taskira - H Online Tv:

Videos

Share