25/04/2024
ABIN DUBAN SHINE AKAN ME KA MUTU NE
Kada ka yi mamaki don Allah ya karɓi tubanka bayan daɗewarka acikin saɓonsa, sannan kuma kada kayi mamaki don yayi maka azaba bayan daɗewarka acikin bauta masa"
Sunnar Allah maɗaukakin sarki itace: bawa zai kwashe shekaru masu ɗinbin yawa yana saɓa masa, yana yi masa shirka, da duk wani nau'in saɓon da zai fusata Allah, amma acikin ɗan ƙan-ƙanin lokaci Allah zai iya yafe masa dukkanin zunubansa da zarar ya tuba, hakama zai kwashe ɗinbin shekaru masu tarin yawa yana bauta masa, yana kaɗaita shi, da duk wani nau'in kyautatawa, amma cikin ɗan ƙan-ƙanin lokaci Allah zai iya ɓata masa dukkanin aiyukansa da zarar ya fusata Allah buwãyi.
Kayi taka-tsan-tsan da lamarin ubangiji, ba'a wasa da ubangiji, ba kuma a raina shi, yana sakawa kowa da irin aikin da ya kasance yana aikatawa ne anan duniya.