28/05/2023
Na Tsunduma Harkar Damfara ne Don in Kuntata wa Mahaifina - Lauyan Bogi
Wani Ayanrinde Abdulgafar, mai shekaru 25, da rundunar 'yan sandan jihar Osun ta cafke na Hukumar Tsaro da Kare Farar Hula ta Najeriya (NSCDC) bisa bayyana kansa da yake a matsayin lauya ya ce, yana yin hakan ne don ya cusgunawa mahaifinsa.
Abdulgafar, wanda aka bayyana fuskarsa a hedkwatar rundunar NSCDC na jihar Osun cikin Osogbo ranar Asabar, ya bayyana yadda ya fara harkallar damfarar al'umma a farkon wannan shekarar.
Yayin amsa tambayoyin manema labarai, ya ce, "Mahaifina ya yi watsi dani tun ina karami, kuma na hakura da karatu ina aji na biyu a jami'a saboda rashin kudin cigaba da karatuna.
"Na yanke shawarar tsunduma harkar damfara, ta hanyar badda k**a a matsayin lauya tare da yaudarar jama'a don in cusgunawa mahaifina. Na damfari mutane sama da N200,000 tun daga lokacin da na fara."
Yayin bayyana wanda ake zargin, Kwamandan Jihar, Agboola Sunday, ya ce, Abdulgafar, yayin da yake sanye da kayan lauyoyi, ya je kotuna da dama a Osun da jihar Kwara don damfarar mutanen al'ummar da s**a yarda dashi.
Ya ce, rundunar tayi nasarar cafke wanda ake zargin a wani hotel ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, 2023, a Illorin, jihar Kwara, yayin da ta hada tawaga tare da rundunar NSCDC bayan ya aikata laifin a Babbar Kotun Tarayya, Akure da Babbar Kotun Jiha a Osogbo da Illorin.
Ya ce: "Wanda ake zargin ya gabatar da kansa a matsayin Lauyan shari'a ga wani direba ranar 23 ga watan Mayu 2023, wanda ya bukaci ya tekoshi da farko zuwa Babbar Kotun Jiha a Osogbo kafin ya nufi Babbar Kotun Jiha a Akure.
"Wanda ake zargin, sanye da cikakkiyar shigar lauyoyi ya shiga kotun, ya gaisa da lauyoyi daga bisani ya tunkari wata mai na'uarar cire kudi (POS) a harabar kotun, inda ya amsa tsabar kudi naira dubu dari da hamsin da ikirarin zai tura ma ta.
"Ya amsa wayar direban don amfani da na'urar shiga yanar gizonsa don taimaka masa tura kudin. Ya shiga harabar kotun daga nan ya yi layar zana, kawai sai aka ganoshi a Illorin, jihar Kwara."