RA'AYI RIGA

RA'AYI RIGA BARKA KU DAZUWA YAN UWANA,WANNAN SHAFIN ANBUDE DON KOWA YA FADI RA'AYINSA

*LABARIN KARYA NE*Wani hoton taya murna da ake ta yadawa a kafafen yada labarai na zamani game da nadin mataimakin mai T...
10/03/2024

*LABARIN KARYA NE*

Wani hoton taya murna da ake ta yadawa a kafafen yada labarai na zamani game da nadin mataimakin mai Tafsiri a Sultan Bello Kaduna wannan magana bata da tushe ballantana asalin.

Wadansu masu son tana fitina ne, masu son kawo fitina da kullum son rusa da'awar Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ne s**a kawo wannan magana.

Kwamitin Shurah na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi basu san da wannan nadin ba, Daliban Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ba su san da wannan nadin ba, Daliban Dr Ahmad Gumi basu san da wannan nadin ba. Ballantana shi kanshi Sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi bai san da wannan ba.

Saboda haka, duk wani munafiki da ke tunanin a bacci ko a zahiri zai kawo wata fitina domin wargaza karantarwa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya sani Allah ya fishi kuma In Sha Allah ba zai samu nasara ba.

Muna girmama shugabanci da Sarakunan Musulunci, kuma mun san wannan munafunci da munafikai da shigo shigo ba zurfi da wasu mutane guda biyu s**a shirya don kawo rudani a wannan masallaci, marauta ba za yarda da shi ba.

Ya k**ata duk wanda zai zama mataimakin mai Tafsiri a Sultan Bello Kaduna ya kasance dalibin Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, mu ganshi gaba gaba wurin karatunsa da karantarwasa, mu ganshi yana karantar da littatafansa ya zamanto daliban Marigayi da daliban sheikh Dr Ahmad Gumi sun sanshi a makarantar.

Saboda haka komawaye ya ke son kawo wannan fitinar Allah ya sa ta kare a kansu,

Allah ya kare mu daga dukkan wata fitina da ake son kawo mana a wannan jama'a ta Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Salisu Hassan Webmaster
Head of Media and Publicity Department
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Initiative for the propagation of Sunnah.
08038892030
29 Sha'aban 1445AH
10/03/2024

Ga Satan Da Dalilin Cikan Dubun Wannan Me Hoton Kamar Yadda Muhammad Adamu Ya Bayyana a Shafin Sa Na Fesbuk.Ya taho shag...
08/03/2024

Ga Satan Da Dalilin Cikan Dubun Wannan Me Hoton Kamar Yadda Muhammad Adamu Ya Bayyana a Shafin Sa Na Fesbuk.

Ya taho shagon mu yace amasa printing wani lecture note na phd kusan 400 pages, kafin a fara sai yace nayi masa POS transfer na ₦1500, sai yace na kara tura masa ₦300 acikin account din.

Byan an fara masa printing sai aka aike ni na shawo kayan spiral binding da za'a saka masa.

Da na dawo ana cikin yimasa binding sai yace yana son passport( shine dalilin samun hoton sa ) amma white background yake so saboda ya ga white background daidai yake da inda aka ajiye POS kuma haka kawai ba zai kaiwa can ba.

Bayan na dauke shi hoto zanyi masa printing, duk hankali mu ya dauko wurin aikin sa (sai shi kuma yayi aikinsa, ya ajiye muna wata POS ya dauki tamu).

Sai ya dan fita ya dawo yace mu bashi ashirin zai sayi ruwa, mukace babu sai ya fita, fitar da bai dawo ba kenan, printing na kusan 18k plus muka yimasa ya barmu dasu sannan ya cire kudin POS namu 152k dake ciki.
Daga karshe sai anyi nasarar cafke shi a garin Kaduna jiya

Yau juma'a 27 ga watan Sha'aban Allama Dr Ahmad Abubakar Gumi ze bude tafsirin da ya saba gabatarwa a masallacin Sultan ...
08/03/2024

Yau juma'a 27 ga watan Sha'aban Allama Dr Ahmad Abubakar Gumi ze bude tafsirin da ya saba gabatarwa a masallacin Sultan Bello dake Unguwan Sarki Kaduna.

Ana sa ran shugaban kungiya Sheikh Abdullahi Bala Lau ze halarci bude karatun.

Kamar mutumen kirki koh?To POS ya sace ya  ajiye wata ya cire kudin dake ciki ₦152,000.Zaku ji yanda abun ya faru anjima...
07/03/2024

Kamar mutumen kirki koh?

To POS ya sace ya ajiye wata ya cire kudin dake ciki ₦152,000.

Zaku ji yanda abun ya faru anjima in sha Allah.

Ko kun san shi?

Yadda ta kaya kenan tsakanin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da mai girma gwamnan Kano HE. Abba Kabir Yusuf.Daga Shafin Mal...
04/03/2024

Yadda ta kaya kenan tsakanin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da mai girma gwamnan Kano HE. Abba Kabir Yusuf.

Daga Shafin Malam Daurawa.

ALHAMDU LILLAH
AN SAMI YIN SULHU, ƘARƘASHIN JAGORANCIN INUWAR HAƊIN KAN MALAMAI DA ƘUNGIYOYI,
PROFESSOR BARODO
SHAIK ABDULWAHAB
PROFESSOR SALISU SHEHU
PROFESSOR BABANGIDA
PROFESSOR SA'IDU DUKAWA.
DR MUAZZAM KHALID BUK
DR ENGR BASHIR HANAN
SHAIKH SHEHU MAI HULA
S**A WAKILCI SAURAN MALAMAI,
ALLAH YA SAKA MUSU DA ALKHAIRI

Inna lillahi'wa inna ilaihir rajiun!Yanzu da safen nan mota ɗauke da Awaki tayi mummunar Hatsari a Tashan-Yari "Tsohuwa"...
04/03/2024

Inna lillahi'wa inna ilaihir rajiun!

Yanzu da safen nan mota ɗauke da Awaki tayi mummunar Hatsari a Tashan-Yari "Tsohuwa"
(Makarfi Kaduna), sama da mutane 20 ne s**a rasu!

Hoto: Real Ahmed Branco Gazara

Rev Fr Ejike Mbaka, Yayi kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ya tashi tsaye ya cika alkawuran yakin neman zabensa na ma...
07/02/2024

Rev Fr Ejike Mbaka, Yayi kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ya tashi tsaye ya cika alkawuran yakin neman zabensa na magance Rashin tsaro da wahalhalu a Najeriya.

Ya kuma yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya tashi tsaye wajen magance matsalar ta’ammali da man fetur a kasar nan.

Da yake jawo hankali kan kafofi da ke da tasiri a harkar man fetur a Najeriya, Mbaka ya bukaci a dauki kwakkwaran mataki don wargaza musu tsugunar da dukiyar kasa.

Sakon Mbaka ya sake bayyana da ma’ana na da’a, inda ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikonsa da karfin hali da kuma yakini. Daga halin da malamai da likitoci masu fafutuka ke ciki, zuwa ga sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi wajen yakar ‘yan tada kayar baya, Mbaka ya fito fili ya bayyana irin abubuwan da ‘yan Nijeriya ke fuskanta na yau da kullum.

Yayin da Rashin tsaro ke mamaye sassan al’umma, da ke kawo cikas ga ayyukan noma da kuma ta’azzara yunwa,

Mbaka yayi kira ga jama’a da su bada hadin kai mai ma’ana da karfafawa. Ya jaddada gaggawar magance gazawar tsarin da kuma samar da yanayi mai dacewa ga cigaba da wadata ga kowa da Kowa.

Rashin Tsaro a Abuja: Yadda Jami’an ‘Yansanda S**a Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 2...
07/02/2024

Rashin Tsaro a Abuja: Yadda Jami’an ‘Yansanda S**a Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

A yayin da sace-sacen jama’a ke kara k**ari a babban birnin tarayya Abuja, an k**a wasu jami’an ‘yansanda bisa zargin kwatar naira miliyan 29.9 daga hannun wani mazaunin Abuja.

Lamarin, a cewar Harrison Gwamnishu, dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, ya faru ne a watan Janairu.

Gwamnishu, k**ar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo ta shafinsa na X (Twitter) cewa, jami’an ‘yansandan sun yi garkuwa da dan kasuwar ne a Abuja inda s**a tsare shi har sai da ya mika musu dukkan kudaden da ke cikin asusun bankinsa. Daily Trust ta rahoto

Daga nan ne s**a dage sai ya kira ‘yan’uwa da abokan arziki su ci gaba da tura masa kudi kafin a sako shi.

Da yake tsokaci kan wannan lamari a ranar Talata, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, yayin da yake tabbatar da k**a wasu daga cikin masu laifin, ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da bincike kan lamarin kuma za ta tabbatar da adalci.

“Muna kan binciken lamarin, kuma za a yi adalci, k**ar yadda aka k**a wasu da ake zargi.” k**ar yadda ya rubuta.

Masu Gurasa Sun Yi Zanga-Zanga Kan Tsadar Fulawa A KanoMasu gurasar sun koka kan yadda tsadar fulawar ta shafi kasuwanci...
03/02/2024

Masu Gurasa Sun Yi Zanga-Zanga Kan Tsadar Fulawa A Kano

Masu gurasar sun koka kan yadda tsadar fulawar ta shafi kasuwancinsu.

Masu sana’ar Gurasa a Jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin jin dadinsu kan yadda fulawa ta yi tsada a jihar.

A cewar Shugabar Kungiyar Masu Sana’ar Gurasa, Fatima Auwal Chediyar ‘Yan Gurasa, ta ce sun shiga yajin aiki har sai farashin fulawa ya daidaita a jihar.

Gobarar tankar gas ta kashe mutum 2, ta jikkata 200 a Kenya
Cire tallafin man fetur alheri ne ga Najeriya — Ministan Labarai
“Farashin fulawa wadda ita ce kashin bayan sana’armu ta yi tsada, kullum idan muka je saya farashi na karuwa, farashin buhun a yanzu ya kai Naira 40,000, me za mu yi?”

Ta bayyana cewa, galibin masu sana’ar mata ne marasa aure da ke daukar nauyin iyalansu, inda ta ce hakan na barazana ga rayuwarsu.

“A baya muna karbar fulawa a kan bashi, muna biya bayan mun sayar amma a yanzu hakan ba ya samuwa.

“Dalilin wannan zanga-zangar ta lumana ita ce, jawo hankalin hukumomi cewa muna fuskantar babbar matsala, nan gaba kadan ba za mu iya kasuwanci ba idan ba a yi wani abu a kai ba.”

Ta kuma jaddada cewa ba su da wani zabi da ya wuce su daina kasuwancin su zubawa sarautar Ubangiji ido.

“Yawancin mutane masu karamin karfi suna amfani da gurasa a maimakon burodi don haka ba mu kadai hakan za ta shafa ba, har da talakawa da s**a dogara da mu.”

Ƴan  Najeriya Na Koka Yadda Kayan Masarufi S**a Yi Tsada A Faɗin Ƙasar A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa y...
03/02/2024

Ƴan Najeriya Na Koka Yadda Kayan Masarufi S**a Yi Tsada A Faɗin Ƙasar

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna yadda a baya ake sayar da buhun shinkafa N45,000 yanzu ya koma N70,000, buhun fulawa daga N35,500 yanzu ya koma N44,000.

Sai buhun s**ari da a baya ake sayar da shi N62,000 yanzu ya koma N75,000 da kuma buhun siminti da a baya ake sayarwa kan kuɗi N5,200 yanzu ya koma N7,000.

Daga Abubakar S AbusadiqTunda sarkin nan yazo Dr. Gumi yake wa'azi akan sharrin da yake so ya kawo cikin Saudiyya, Ikon ...
24/01/2024

Daga Abubakar S Abusadiq

Tunda sarkin nan yazo Dr. Gumi yake wa'azi akan sharrin da yake so ya kawo cikin Saudiyya,

Ikon Allah ashe wasu malamai acikin ƙasar mu basa so ace sun k**a hanyar ɓata,

Sai abun yazo dai-dai da wani shubha da suke so su kauda tunanin mutane akan Asalin abunda ya dace, yanzu dai duk musulmi mai imani yasan ƙasar Saudiyya sun k**a hanyar yahudu da nasara,
sai dai munafiki ne bai sani ba k**ar yanda kowa ke iya gani,

Kamfanin simintin Dangote yakai darajar ƙarfin jari na Naira Tiriliyon 10 na Kasuwa. Kamfanin wanda yana ƙasa da ƙarfin ...
24/01/2024

Kamfanin simintin Dangote yakai darajar ƙarfin jari na Naira Tiriliyon 10 na Kasuwa. Kamfanin wanda yana ƙasa da ƙarfin jari na kasuwa da Tiriliyon 7 kuma yana ƙasa da Kamfanin MTN dana Airtel a watan Disambar data gabata, amma a yanzu ya ɗare su.

Kuma shine kaɗai Kamfani da yake cikin Manyan Kamfanoni 10 da suke Nahiyar Afrika a ƙarfin jari na Kasuwa, wannan shine sak**akon abinda kake samu idan ka siyarma da Mutane ingantattun kaya.

Kamfanin Siminti na Dangote ya cancanci wannan nasara saboda ya samar da ingantattun siminti ga Mutanen Nahiyar Afrika na tsawon sama da shekaru 20. Muna kara taya Kamfanin siminti na Dangote murna.

'Yan bindiga sun sako 'yan matan nan biyar daga cikin shida da s**a sace a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin taray...
21/01/2024

'Yan bindiga sun sako 'yan matan nan biyar daga cikin shida da s**a sace a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Farashin Dala ya kai Naira dubu 1,355 a kasuwar bayan fageNairar Najeriya na ci gaba da shan kashi.
19/01/2024

Farashin Dala ya kai Naira dubu 1,355 a kasuwar bayan fage
Nairar Najeriya na ci gaba da shan kashi.

Morning
15/01/2024

Morning

Za’a kammala titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano nan da watanni 24 – UmahiGwamnatin Tarayya ta Ware Naira Biliyan 17 Ga Ka...
14/01/2024

Za’a kammala titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano nan da watanni 24
– Umahi

Gwamnatin Tarayya ta Ware Naira Biliyan 17 Ga Kamfanin Julius Berger Domin Gudanar da aikin titin Abuja Zuwa Kaduna Zuwa Kano domin a Gaggauta kammala aikin.

Ministan ayyuka David Umahi, ya ce nan da watanni 24 za a kammala dukkan sassan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Sanata David Umahi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya kai ziyarar duba hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ministan wanda ya samu rakiyar Ministan Kudi da daidaita tattalin arziki Wale Edun ya bayyana cewa gwamnati ta yi sabon wa’adin ne bayan cimma yarjejeniya da dan kwangilar aikin hanyar Julius Berger.

Ku tuna cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da kwangilar ne a shekarar 2018 a kan za’a kammala a cikin watanni 36 amma ta kasa cika alkawari.

Umahi, ya dora alhakin jinkirin da aka samu a kan rashin kudi, yana mai tabbatar da aniyar gwamnati na kawo karshen hanyar a kan lokaci.

Ya ce, “Julius Berger ya amince ya kammala tafiyar kilomita 15 a kullum saboda an amince da sabuwar ranar.

MASU IYA MAGANA NA CEWA ILIMI SHINE GISHIRIN ZAMAN DUNIYA.A karkashin hakan ne muke masu sanar daku cewa makarantar Nimb...
07/01/2024

MASU IYA MAGANA NA CEWA ILIMI SHINE GISHIRIN ZAMAN DUNIYA.

A karkashin hakan ne muke masu sanar daku cewa makarantar Nimble Minds Academy da ke Badiko masu lambar adireshi k**ar haka: No. 4 Saap Crescent Badiko New Extension ke sa ke farin cikin sanar da ku cewa ta bude sabon reshen ta dake Dogon Bauchi Road Daura Da Kwanar Mai Shayi Anguwan Sanusi Kaduna.

Domin karin bayani ku tuntubi wannan lambar 08032742011

Masu kallo me nene ra'ayin ku akan wannan film din na Labarina?
06/01/2024

Masu kallo me nene ra'ayin ku akan wannan film din na Labarina?

Yayin da Ake Shan Daka a Najeriya, Buhari Ya Bayyana Dalilin Farin Ciki da Ya Yi Bayan Cire Tallafi Yayin da ake fama da...
02/01/2024

Yayin da Ake Shan Daka a Najeriya, Buhari Ya Bayyana Dalilin Farin Ciki da Ya Yi Bayan Cire Tallafi

Yayin da ake fama da tsadar man fetur a Najeriya, tsohon shugaban kasa, Buhari ya ce haka dai-dai ne Buhari ya bayyana haka ne a birnin Katsina a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba yayin wani babban taro kan matasa Tsohon shugaban ya ce hakan ya yi masa dadi saboda yawan ziyara da mutane ke kai masa za ta ragu sosai

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi. Buhari ya ce kara kudin mai din ya rage yawan masu kai masa ziyara tun bayan barinsa kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Mene Buhari ya ce kan cire tallafin Tinubu?

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba a birnin Katsina yayin wani taro da aka gudanar.

Buhari ya ce hakan ya masa dadi saboda masu yawan kai masa ziyara garin Daura da ke jihar Katsina tun bayan barinsa kujerar mulki za su ragu. Ya kara da cewa cire tallafin mai din ya kara farashin mai din wanda ya ke tsammani zai rage baki zuwa gidansa da ke Daura. Sai dai ya ce hakan bai rage komai ba ganin yadda s**a nemo wata hanyar tara kudade don kai masa ziyarar, kasar yadda DCL Hausa ya yada bidiyon.

Buhari ya ce ya san wahalar Najeriya da dadinta Ya ce: "Wahalar Najeriya da dadinta na sani, alhamdulillahi na dawo gida na zauna mutane suna ta zuwa suna gaida ni a kullum.

Da Tinubu ya kara kudin mai ina murna saboda baki za su ragu, amma sai su shirya su tara kudi su hau jirgi su fado min." Idan ba a mantaba, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu yayin karbar rantsuwar k**a aiki a matsayin shugaban kasa. Tun bayan cire tallafin, 'yan kasar s**a shiga wani mummunan yanayin wahalar rayuwa da tsadar kayayyakin masarufi, cewar Leadership.

Tinubu ya nuna rashin jin dadin sa kan yawan yara ‘yan Najeriya har miliyan 20 da ba sa zuwa makarantaDecember 30 2023A ...
30/12/2023

Tinubu ya nuna rashin jin dadin sa kan yawan yara ‘yan Najeriya har miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta

December 30 2023

A ranar Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana fargabarsa kan yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, k**ar yadda kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya rubuta a wata sanarwa.

“Dole ne mu magance wannan matsalar ta hanyar kafa karin makarantu, daukar malamai, da kuma samar da akalla abinci daya a rana ga yaran makaranta.

Najeriya na da kimanin yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta, k**ar yadda UNESCO ta kiyasta a shekarar da ta gabata, duk da cewa gwamnatin Najeriyar ta ce adadin na iya raguwa. Indiya ce kadai ke da yara da ba sa zuwa makaranta fiye da Najeriya, a cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.

Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya na kara ta’azzara sak**akon rashin tsaro da ke ci gaba da addabar al’umomi da dama a arewacin Najeriya, lamarin da ya fidda dubban jama’a daga gidajensu da kuma kai ga rufe makarantu.

Shawarar da shugaba Tinubu ya bada ya hada da samun goyon bayan gwamnatocin jihohi don samun nasara akan haka. Galibin makarantun firamare da sakandare na gwamnati mallakar gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi ne wadanda kuma ke da alhakin daukar ma’aikata da gudanar da irin wadannan makarantu.

Tinubu ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su maida hankali wajen ba ilimi kyakkyawar kula da kasu a jihohin su domin kawo karshen wannan matsala.

Kashim Shettima Ya Roƙe Al'ummar Arewacin Najeriya dasu kasance masu haɗin kai A junansu Domin daƙile faɗace-faɗacen Kab...
29/12/2023

Kashim Shettima Ya Roƙe Al'ummar Arewacin Najeriya dasu kasance masu haɗin kai A junansu Domin daƙile faɗace-faɗacen Kabilanci da kawo karshen fatara da Ya Addabi Arewacin kasar.

A jawabin da ya Gabatar a Garin Masaka na Jihar Nasarawa, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, Yayi kakkausar s**a, Ya bayyana matuƙar buƙatar al'ummar Arewacin Najeriya su tashi tsaye Domin daƙile fatara Talauci da Rashin tsaro da ya addabi yankin arewacin kasar

Da yake kaddamar da Gagarumin titin Masaka-Luvu Mai tsawon kilomita 5 a Ƙaramar Hukumar Karu, Kashim Shettima ya jaddada muhimmancin Haɗin kai a tsakanin ‘yan Arewa, Inda ya Buƙace su dasu haɗa kai Domin Yakar waɗannan Manyan Ƙalubale.

Da yake nuna damuwarsa kan abubuwan da s**a faru a baya-bayan nan, Musamman abin da ya faru a jajibirin Kirsimeti a Jos, jihar Filato, Mataimakin Shugaban ƙasar ya jaddada muhimmancin zaman lafiya wajen samar da ci gaba. "Baza a samu ci gaba mai ma'ana ba in ba zaman lafiya ba," inji shi.

Shettima, Ya amince da buƙatar ɗaukar Matakin Haɗin Gwiwa, Yayi kira da a kawo Ƙarshen rikicin Cikin Gida a Arewacin Najeriya. "Me yasa muke faɗa a tsakaninmu alhali Gwagwarmayar da muke yi itace ta yaƙi da fatara, da koma bayan da muka samu? Dole ne mu haɗa kai don samun ci gaba," inji shi da Gaske.

A matsayin babban bako na musamman a wajen taron, Shettima ya yabawa Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa bisa ƙoƙarin da yake yi na wanzar da zaman lafiya a yankin. Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su guji ayyukan da ka iya jefa al’ummar ƙasar cikin rikici.

KBC Hausa

Ko kunsan da zaman chairman Maroka Sarkin Marokan Lere?
29/12/2023

Ko kunsan da zaman chairman Maroka Sarkin Marokan Lere?

Daga Shafin Nasir Aliyu BabanyayaINNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN Yaro da muka wallafa a wannan kafa da ake cigiyar s...
28/12/2023

Daga Shafin Nasir Aliyu Babanyaya

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN

Yaro da muka wallafa a wannan kafa da ake cigiyar sa jiya da daddare mai suna Ibrahim Muntaka Muhammad da aka nemeshi aka rasa a gaskia wanda biki s**a zo daga kaduna a Safiyar yau an tsinci gawarsa a gona a agoro tudun wadan Zaria an kwakule mishi ido.

Allah muke roko da ya jikansa da Rahma, ya kuma tona asirin wayanda s**a aikata wannan barna.

28/12/2023

Masana sun ce Idan TUZURU ya riƙa, baya jin gorin aure.

Ya abun yake?

Daga Shafin Yusuf Kubaraci.Allah ne kadai zai yiwa wannan budurwa sakayya da hisabi tsakanin ta da waɗanda s**a mata mum...
27/12/2023

Daga Shafin Yusuf Kubaraci.

Allah ne kadai zai yiwa wannan budurwa sakayya da hisabi tsakanin ta da waɗanda s**a mata mummunar zato wajen chanza ma'anar fassaran wannan suna data rubuta a bayan rigan ta RABAKAYA

RABAKAYA Ba kalmar iskanci bane k**ar yanda mutane suke tunani suke ta yada hoton wannan baiwar Allah suna daukar alhakin ta

RABAKAYA babban family ne a jigawa wanda suna da nasaba da Masarautar Hadejia kuma wannan suna family name dinsu ne k**ar yanda kowa suke da nasu family name din su

Na tabbata duk iskancin yarinya ba zata taba rubuta wannan sunan a bayan rigan ta da niyyar iskanci ba saboda tasan dole wannan hoton zai zagaye duniya daka karshe har iyayen ta su gani

Kamar yanda aka chanza fassaran kalmar KUNU haka aka chanzawa wannan budurwa ma'anar sunan data rubuta, duk wanda yasan ya mata mummunan fassara yayi gaggawa ya neme ta domin yafiya. Muna mata fatan alkhairi mu kuma Allah ya shirya mu da ita baki daya

A Arewa ne za kaga butan Massallaci ma bai tsira ba.
27/12/2023

A Arewa ne za kaga butan Massallaci ma bai tsira ba.

Gwamnan jahar Ondo Mr Rotimi Akeredolu lokaci yayi.Gwamnan ya rasu ne da sanyin safiyar laraban nan a jahar Legas.
27/12/2023

Gwamnan jahar Ondo Mr Rotimi Akeredolu lokaci yayi.

Gwamnan ya rasu ne da sanyin safiyar laraban nan a jahar Legas.

Sojin mulki a Jamhuriyar Nijar sun musanta labarin da wasu kafofin yaɗa labarai na kasar Faransa s**a yi cewa sojojin su...
26/12/2023

Sojin mulki a Jamhuriyar Nijar sun musanta labarin da wasu kafofin yaɗa labarai na kasar Faransa s**a yi cewa sojojin sun sanar da wa’adin da za su yi kafin su miƙa mulki ga farar-hula.

Majalisar Sojoji ta ƙasar (CNSP), cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook ranar Litinin da maraice, ta ce labarin kanzon kurege ne kuma babu wata yarjejeniya da s**a cim ma da ECOWAS dangane da batun miƙa mulki.

Hoto: Liberty Hausa

Daga Shafin Nasiru Salisu Zango.Yau take Kirisimeti…Yau ce ranar da abokan zaman Mu Kiristoci suke bikin sallar su wato ...
25/12/2023

Daga Shafin Nasiru Salisu Zango.

Yau take Kirisimeti…
Yau ce ranar da abokan zaman Mu Kiristoci suke bikin sallar su wato kirisimeti, Ina da abokai da abokan aiki da dama da suke mabiya wannan addini da alkur‘anin Mu ya Kira su Nasara,kuma duk shekara Idan lokacin Sallar Mu yayi s**an taya ni murna har ma wasu su kawo hasafi su bani.
Nasan babu tantama addinin Mu ya aminta Mu zauna da su lafiya mazan cikin mu ma su auri matan su, abincin su ma kur‘anin Mu mai girma yace halal ne gare mu.

Shin yau na iya kiran su nayi musu barka da kirisimeti ko shiru zan yi duk da cewar lokacin tawa sallar sun min barka na amsa?
Dan Allah Malamai ku yi mana fashin Baki domin da yawan mutane na cikin duhu, dan wasu sun ce yin barka da kirismeti a baki ba yana nufin zuciyar ka ta karbi salon ibadar su bane wasu kuma sun ce mana haram Kar Mu sake Mu ce musu kanzil a irin wannan lokaci.
Dan Allah ayi mana fashin baki.
Shin Wanda ya auri kirista s**a kwana tare daki daya yau, tana farin cikin sallar ta ya iya cewar sweetheart Happy Christmas ko kuwa gum zai yi ya basar?
Allah ya kara mana kaunar ma‘aiki SAW, shugaban masu adalci na duniya Wanda ba‘yi ba kuma baza‘ayi k**ar sa ba.Muhammadur rasulullah.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya soki wani rahoto da ke cewa ya dauki matakin sauya fasalin Nair...
25/12/2023

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya soki wani rahoto da ke cewa ya dauki matakin sauya fasalin Naira 200, 500 da 1000 ba tare da izinin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ba.

Ya ce ya umarci lauyoyinsa su gurfanar da mai bincike na musamma, Jim Obazee, game da zargin da ya yi masa cewa ya bude asusun bankunan kasashen waje 593 ba tare da sanin Buhari ba

Address

AT 1 Gamagira Road, Kwanar Mai Shayi Unguwan Sunusi
Kaduna

Telephone

+2348126615281

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when RA'AYI RIGA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to RA'AYI RIGA:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Kaduna

Show All

You may also like