Funtua Post Hausa

Funtua Post Hausa Wannan dandali munbude shi ne ba Dan komai ba sai Dan yada Alkhairai Rarara Wannan kafa mai albarka,

ABIN ALHERI: Shugaban Karamar Hukuma Ya Gina Asibiti Mai Daukar Gadajen Majinyata 60 A Jihar KatsinaHon. Dr. Habibu Abdu...
30/04/2024

ABIN ALHERI: Shugaban Karamar Hukuma Ya Gina Asibiti Mai Daukar Gadajen Majinyata 60 A Jihar Katsina

Hon. Dr. Habibu Abdulkadir Shugaban Karamar Hukumar Musawa Jihar Katsina, Ya Shimfida Karamin Asibiti Mai Daukar Gadajen Majinyata Sittin 60 A Garin 'Yar-'Kirgi Dake Karamar Hukumar Musawa, A Kokarinshi Na Ganin Ya Inganta Harkar Lapiya A Karamar Hukumarsa.

Kamar Yadda Wakilinmu Jaridar Karaduwa Post, Ya Gano Mana, Shugaban Karamar Hukumar Musawa, Yana Daya Daga Cikin, Shuwagabannin Da S**a Shimfida Ayyukan Alkhairi Raya Kasa Masu Tarin Yawa A Jagorancinshi Na Shekara Biyu,

Wakilin Mu Ya Labarta Mana Akwai Wasu Ayyukan Raya Kasa Masu Tarin Tawa Da Ya Aiwatar Kamar:-

(1) Ya Gina Asibiti A Yar Kirgi, Gingin Ward

(2) Ya Gyara Asibitin Yar-Awala Kurkujan (A) Ward

(3) Ya Gina Hanyar Ruwa Mai Tsayin Gaske A Marabar Musawa, Kurkujan (B) Ward

(4) Yayi Salaf Garin Kurkujan, Kukujan (A) Ward.

(5) Yayi Hanyar Ruwa Mai Tsayin Gaske A Garin Mangafi, Gingin Ward

(6) Yayi Hanyar Ruwa A Tabani/Yar-Raddau Ward

(7) Yayi Salaf A Unguwar Chakaro, Gingin Ward

(7) Yayi Salaf A Garin Kurkujan, Kurkujan (A) Ward

(8) Ya Gyara Kwata Dake A Kasuwar Garin Musawa, Musawa (A) Ward

Wadanan Kadan Kenan Daga Cikin Ayyukan Alkhairin Da Ya Shimfidawa Al'ummarsa Wadanda Maku Kawo Maku A Karon Farko, Zamu Kawo Maku Wasu Anan Gaba.

Dafatan Allah Yayi Mashi Jagora, Allah Yasaka Mashi Da Alkhairi Ameen

~Karaduwa Post

Hon. Malam Ya'u Ahmad Nowa Dandume, Ya Ziyarci (Nigerian Police Compound) Dake Sabon-Layi Cikin Garin Katsina, Wajen Tan...
16/04/2024

Hon. Malam Ya'u Ahmad Nowa Dandume, Ya Ziyarci (Nigerian Police Compound) Dake Sabon-Layi Cikin Garin Katsina, Wajen Tantance Sabbin Jami'an 'Yan Sandan Najeriya Bangare Na Musanman (Specialist).

Ranar Talata 16/04/2024 Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda Shawara Akan Samar Ayyukanyi, Hon. Malam Ya'u Ahmad Nowa Dandume (S.A Employment Promotion), Ya Ziyarci (Nigerian Police Compound) Dake Sabon-Layi Cikin Garin Katsina

Inda Aka Fara Tantance Sabbin Jami'an Tsaron 'Yan Sandan Najeriya Da Za'a Dauka 'Yan Asalin Jihar Katsina Bangare Na Musanman (Specialist), Ma'ana Wadanda S**a Cike Neman Aikin Da Takardar Samun Horo Akan Sana'oi Ko Wata Fasaha, Kamar Teloli, Kafinta, Masu Gyaran Mota, Walda, Masu Daukar Hoto, Da 'Yan Jarida Da Sauransu,

Yayi Ziyarar Ne Domin Gane Ma Idanuwanshi Yadda Aikin Tantancewar Ke Gudana Ba Tareda Tauye Hakkin Kowane Matashi, Mace Ko Namiji Dan Asalin Jihar Katsina Ba, Da Fatan Kammalawa Cikin Aminci Da Nasara.

Allah Ya Baiwa Matasan Jihar Katsina Nasara, Ya Allah Yakara Daukaka Matasan Jihar Katsina Da Ƙasa Baki Daya Ameen

Shamsu Wapa Dandume
Media Aide To Special Adviser
Department Of Employment Promotion
Katsina State

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN Fitatcen Jarumi A Masana'antar Fina-finan Kannywood kuma Mawaki  Yakubu Mohammad Ya S...
03/03/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN

Fitatcen Jarumi A Masana'antar Fina-finan Kannywood kuma Mawaki Yakubu Mohammad Ya Samu Hadarin Mota Akan Hanyar Shi Ta Zuwa Abuja Birnin Tarayya Daga Jihar kano.

Allah Ya Maida Mashi Alkhairi Ya Kiyaye Gaba aba. Ameen ya Hayyu ya Qayyum

YANZU - YANZU: Babbar kotun jihar Kano Mai Lamba biyar karkashin jagorancin Mai Sharia Aisha Mahmud ta bada umarnin a ka...
26/02/2024

YANZU - YANZU: Babbar kotun jihar Kano Mai Lamba biyar karkashin jagorancin Mai Sharia Aisha Mahmud ta bada umarnin a kamo mata mawaƙi Ado Isa Gwanja.

Kotun ta kuma haramta masa waka har sai Yan sanda sun kammala bincike a kansa.

TSADAR RAYUWA: Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya gana da Manyan Shahararrun ƴan Kasuwar Najeriya da s**a haɗa...
26/02/2024

TSADAR RAYUWA: Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya gana da Manyan Shahararrun ƴan Kasuwar Najeriya da s**a haɗa da; Dangote, BUA, Elumelu, Innoson da Sauransu, A Daren jiya Lahadi.

~Karaduwa Post

INDA RANKA:  Shugaban Karamar Hukumar Hadejia Dake Jihar Jigawa Ya Gwangwaje Al-umman da yake wakilta da kyautuka k**ar ...
23/02/2024

INDA RANKA: Shugaban Karamar Hukumar Hadejia Dake Jihar Jigawa Ya Gwangwaje Al-umman da yake wakilta da kyautuka k**ar haka:
1. Likkafani
2. Makara
3. Da kuma motan daukar gawa.

Allah Yasaka Mashi Da Alkhairi Ameen

YANZU YANZU: Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 15 ta yi watsi da bukatar almajiran Malam Abduljabbar Nasiru Kabara da s*...
22/02/2024

YANZU YANZU: Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 15 ta yi watsi da bukatar almajiran Malam Abduljabbar Nasiru Kabara da s**a bukaci a sake nazarin hukuncin kisa da aka yanke wa malamin.

Kamar Yadda Majiyar Karaduwa Post, ta Shaida Mana, Da ma tun farko malamin ya gargadi wadannan dalibai da su kiyayi nemar masa sassauci a hukuncin da aka yanke masa yake kuma jiran a zartas masa.

Allah Ya Kiyaye Gaba Ameen

~Karaduwa Post

"Rundunar sojin Najeriya tayi kakkausar s**a ga masu yunkurin juyin mulki a Najeriya" Rundunar sojin Najeriya, ƙarƙashin...
22/02/2024

"Rundunar sojin Najeriya tayi kakkausar s**a ga masu yunkurin juyin mulki a Najeriya"

Rundunar sojin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin hafsan hafsoshin sojin ƙasa Christopher Musa

Shugaban Hafsan Sojojin, ya bayyana cewa, "Sanin kowa ne samar da soji ne don tallafawa Demokradiyya, dan haka duk wanda a same shi a nufin yunkurin juyin mulki zai fuskanci hukunci bayan aikata haka" Inji- Shi

Menene Ra'ayinku?

Yadda wata mata a Garin Ibadan mai ɗauke da juna biyu ta yanke jiki ta faɗi sak**akon yunwa data ce tana fama da shi.
22/02/2024

Yadda wata mata a Garin Ibadan mai ɗauke da juna biyu ta yanke jiki ta faɗi sak**akon yunwa data ce tana fama da shi.

DA DUMI DUMINSA: "Yan Bindiga Sun Sake Daukar Mutum Goma 18 A Garin Munhaye Faskari.Da Safiyar Yau Alhamis 22/2/2024 Muk...
22/02/2024

DA DUMI DUMINSA: "Yan Bindiga Sun Sake Daukar Mutum Goma 18 A Garin Munhaye Faskari.

Da Safiyar Yau Alhamis 22/2/2024 Muke Samun Labarin Cewa, 'Yan bindiga S**ai Hari A Garin Munhaye Dake Karamar Hukumar Faskari Jihar Katsina

A Cikin Daren Jiya Laraba Inda S**a Dauki Akalla Mutune Goma Sha Takwas 18 Amman Haryanzu Bamu Samu Labarin Asarar Rayuwaka Ba

Allah Ya Kubutar Dasu Cikin Aminci Ameen

~Karaduwa Post

"Ina so ’Yan Uwa ’Yan Najeriya Ku Sanya Amanarku ga Shugaba Bola Tinubu Wallahi Yana Nufin Alheri Ga Al’umma, Yana da Ts...
21/02/2024

"Ina so ’Yan Uwa ’Yan Najeriya Ku Sanya Amanarku ga Shugaba Bola Tinubu Wallahi Yana Nufin Alheri Ga Al’umma, Yana da Tsaftatacciyar Zuciya Mai Kyau Ga 'yan Najeriya. Yanzu Muna Cikin Bangaren Aikin Ceto Ne".

Cewar-_Kashim Shettima Mataimakin Shugaban ƙasar Najeriya

Me Zakuce?

ALBISHIR GA TALAKAWAN NAJERIYA: Muhimman Abubuwan Aka Tauna a Taron Shugaban Kasa da Gwamnonin Jihohi A jiya ne shugaban...
16/02/2024

ALBISHIR GA TALAKAWAN NAJERIYA: Muhimman Abubuwan Aka Tauna a Taron Shugaban Kasa da Gwamnonin Jihohi

A jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima s**a gana da gwamnonin jihohi 36 da wasu ministoci da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin tarayya.

Taron dai ya yi nasarar amincewa da matsaya guda don tinkarar wasu kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu musamman tsadar abinci da rashin tsaro.

Bayan tattaunawa mai zurfi shugaban kasa da gwamnonin sun amince da yin aiki tare don magance matsalolin tsaron da na tattalin arziki da 'yan kasar ke fuskanta.

Ga mahimman abubuwan da shugaban ya gaya wa Gwamnonin su yi:

1. A kan magance matsalar rashin tsaro wanda kuma ke shafar noma da samar da abinci, shugaba Tinubu ya bayar da umarni guda 3.

👉🏽Daukar karin jami'an 'yan sanda domin karfafa rundunar tsaro

👉🏽Hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi da ma Majalisar Dokoki ta kasa don samar da taswirar kafa ‘yan sandan Jihohi maimakon ‘yan banga da ake amfani da su a wasu Jihohin a yanzu

👉🏽 Shugaban ya bukaci Gwamnonin da su karfafa mafarauta tare da ba su mak**ai domin kare dukkan dazuzzuka daga masu aikata laifuka.

👉🏽Yadda za a shigar da samar da 'yan sandan Jiha cikin tattaunawa a Majalisar Tattalin Arzikin Kasa.

2. Akan tsadar kayan abinci kuwa, Shugaban ya ba da umarnin cewa gwamnatocin Jihohi da gwamnatin tarayya su hada karfi da karfe don kara samar da abinci a cikin gida.

Shugaban ya ba da shawarar a hana shigo da abinci da kuma tsayar da farashi na bai daya a lokacin da ya k**ata sannan a karfafa giwar masu samar da abinci na cikin gida don habaka samar da abincin.

3. Shugaban ya shawarci Gwamnoni da su yi koyi da jihar Kano wajen tunkarar masu boye kayan abinci don cin kazamar riba da ‘yan kasuwar ke yi.

Shugaban ya umurci Sufeto-Janar na ’yan sanda, da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, da na ma’aikatar harkokin gwamnati, da su sanya ido a kan rumbun adana kayayyakin abinci a fadin kasar

NASARA DAGA ALLAH: An k**a mataimakin Bello Turji mai suna Lamba lawai daya ne daga cikin manya kwamandojin Turji na gab...
15/02/2024

NASARA DAGA ALLAH: An k**a mataimakin Bello Turji mai suna Lamba lawai daya ne daga cikin manya kwamandojin Turji na gaban goshi.

Jam'ian yan sa kai sun sami nasarar k**a shi, inda a nuna shi cikin wani matsakaicin faifayen video mai mintuna 2.

Yansa kai ɗin sun bayyana cewa, mutum 4 su k**a kwamandojin turji..

Majiyar Funtua Post, Jaridar Karaduwa Post,

Wannan Itace: Bilkisu Safana Sabuwar Jaruma A Masana'antar Fina-finan Kannywood Yar Asalin Jihar Katsina.~Karaduwa Post
01/02/2024

Wannan Itace: Bilkisu Safana Sabuwar Jaruma A Masana'antar Fina-finan Kannywood Yar Asalin Jihar Katsina.

~Karaduwa Post

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya tafi aikin ummura.  Allah ya karawa Anna...
31/01/2024

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya tafi aikin ummura.

Allah ya karawa Annabi Daraja.

"Don Allah Layla Da Sauran 'Yan Uwanta Su Yi Hakuri, Sharrin Śhàìďañ Ne Ya Sa Na Ci Mata Mutùñçi A Kafar Sadarwa"Cewar S...
31/01/2024

"Don Allah Layla Da Sauran 'Yan Uwanta Su Yi Hakuri, Sharrin Śhàìďañ Ne Ya Sa Na Ci Mata Mutùñçi A Kafar Sadarwa"

Cewar Sadiya Marshall, Bayan Ta Shiga Hannun Hukuma

YANZU YANZU: Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta sanar da k**a wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Al...
31/01/2024

YANZU YANZU: Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta sanar da k**a wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Aliyu Muhammed an kuma samu wasu kudade a wajensa da s**a kai kimanin naira miliyan 8.55 da wayoyin hannu guda bakwai.

Me Zakuce?

Sabuwar Jaruma A Masana'antar Fina-finan Kannywood Zahrah Aliyu Saman Doki.
31/01/2024

Sabuwar Jaruma A Masana'antar Fina-finan Kannywood Zahrah Aliyu Saman Doki.

ALLAH DAYA... Kalli Hotunan Yadda Ake Gudanar Kasuwancin Chanjin Kuɗi  A kasar Somalia.Hakan Zaiyiwu A Najeriya Kuwa?~Ka...
31/01/2024

ALLAH DAYA... Kalli Hotunan Yadda Ake Gudanar Kasuwancin Chanjin Kuɗi A kasar Somalia.

Hakan Zaiyiwu A Najeriya Kuwa?

~Karaduwa Post

DA DUMI DUMI: 'Yan ta'addan Daji a Zamfara sun shiga uku Insha Allahu Ayau gwamnan Jihar  Zamfara Hon. Dauda Lawal, ya k...
31/01/2024

DA DUMI DUMI: 'Yan ta'addan Daji a Zamfara sun shiga uku Insha Allahu

Ayau gwamnan Jihar Zamfara Hon. Dauda Lawal, ya kaddamar da 'yan Sakai na Al'umma da akafi sani da 'yan Banga , an Sanya masu Suna "Askarawan Zamfara" daga yanzu zasu fara fattatakar su Bello Turji da su Ado Aleru insha Allahu qarshan su ya zo .

Gwamnonin Jigawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Kano da Mataimakiyar Gwamnan Kaduna duk sun halarci bikin kaddamar da ASKARAWAN ZAMFARA wani Abun Jindadi duk sun aje Maganar Jamiyunsu Domin Ganin Wannan al'amari ya tabbatu.

Ubangiji ya Allah kaba wudannan mutane (ASKARAWAN ZAMFARA) Gagarumar nasara Ameen

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Allah Ya Yiwa Shugabar Ƙungiyar Zawarawan Jihar Katsina Rasuwa Da Safiyar Yau Laraba!...
31/01/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya Yiwa Shugabar Ƙungiyar Zawarawan Jihar Katsina Rasuwa Da Safiyar Yau Laraba!

Allah Yayi Wa matashiya Yar Gwagwarmaya Hajiya Rufa'atu Shu'aibu Sheme Rasuwa, Yau A Wani Asibiti Dake Maiduguri Jihar Borno Bayan Tayi Fama Da jinya.

Allah Ya Gafarta Mata Zunubbanta ameen

ALHAMDULLAH ALHAMDULLAH 'Yan Sanda sun k**a dan bindigan da ya yi garkuwa da 'yan mata 6 'yan gida dayan nan a Abuja tar...
30/01/2024

ALHAMDULLAH ALHAMDULLAH

'Yan Sanda sun k**a dan bindigan da ya yi garkuwa da 'yan mata 6 'yan gida dayan nan a Abuja tare da kashe Nabeeha yayarsu kuma ya karbi kudin fansa a farkon wannan watan a Abuja.

Dan bindigan mai suna Bello, an k**a shi ne a wani otel a garin Tafan jihar Kaduna, ya kuma yi yunkurin baiwa DPOn 'yan sandan yankin toshiyan baki da naira miliyan daya domin a sake shi amma DPOn ya ki amincewa ya karba.

Allah yakawo karshan yan ta'adda a Nigeria

Daga: Ismail Mohammad Goje

Aƙalla ma’aikatan CBN Dubu 1,500 ne zasu koma ofishinsa dake Legas a Ranar Juma’a bayan da aka sake tura su daga hedikwa...
30/01/2024

Aƙalla ma’aikatan CBN Dubu 1,500 ne zasu koma ofishinsa dake Legas a Ranar Juma’a bayan da aka sake tura su daga hedikwatar.

"Eh, har yanzu shirin yana kan aiki kuma za su ci gaba da aiki a Ranar 2 ga Fabrairu, wanda shine makon farko na wata mai zuwa," in ji wani jami'in.

Wannan sabon ci gaba na zuwa ne biyo bayan matakin da sabon shugaban hukumar ya dauka na mayar da wasu sassan ma’aikatun CBN Zuwa cibiyar tattalin arzikin ƙasar domin kare lafiyar ma’aikata, da kara yawan aiki da kuma rage cunkoso a babban ofishinsa.

CBN yace ya zama wajibi a dauki matakin da wasu abubuwa da s**a hada da bukatar daidaita tsarin bankin da ayyukansa da manufofinsa da kuma raba fasahohin don tabbatar da yaduwar hazaka.

Ya kuma kara da cewa yana bin ka’idojin gine-gine, Kamar yadda aka yi ta gargadin manajan ginin, da kuma bincike da shawarwarin kwamitin rage cunkoso na babban ofishin CBN.

Takardar da aka rabawa ma’aikatan ta ce, “Wannan shine don sanar da dukkan ma’aikatan babban ofishin babban bankin na CBN cewa mun ɓullo da wani shiri na rage cunkoso da aka tsara domin inganta yanayin Gudanar da bankin.

"Wannan yunƙurin yana da nufin tabbatar da bin ka'idodin aminci na gini da haɓaka ingantaccen amfani da sararin ofis ɗinmu."

Rahotanni sun bayyana cewa sassan da Gwamnan babban bankin na CBN, Yemi Cardoso ya ba da takardan sauya sheka sun hada da sa ido kan Harƙoƙin banki, da sa ido kan cibiyoyin hada-hadar kudi, sashen kare hakkin masu amfani da kayayyaki, sashen kula da tsarin biyan Kudi, da kuma sashen dokoki na kudi.

Duk da cewa kungiyar dattawan Arewa da wasu kungiyoyin Arewa sun yi Allah-wadai da matakin, wakilinmu ya tattaro cewa Gwamnan CBN ya kuduri aniyar aiwatar da shi, domin ana sa ran za a rage ma’aikata 2,733 Daga 4,233.

Wasu ma’aikatan da abin ya shafa sun fara komawa Legas. “Wasu sun riga sun yi gaba. Sama da kashi 80 cikin 100 na ma’aikatan Sashen Sa ido na Banki an sake tura su aiki kuma iri daya ne ga Sashen Biyan Kuɗi,” inji majiyar.

~KBC Hausa

WATA SABUWA: "Ka yi murabus idan baza ka iya ba"Atiku Abubakar yana ƙalubalantar shugaban Najeriya Bola Tinubu bisa ƙãri...
30/01/2024

WATA SABUWA: "Ka yi murabus idan baza ka iya ba"

Atiku Abubakar yana ƙalubalantar shugaban Najeriya Bola Tinubu bisa ƙãrin taɓarɓarewar tattalin arziki da tsaro.

Me Zakuce?

An yankewa tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 bisa laifin fitar da sirrin...
30/01/2024

An yankewa tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 bisa laifin fitar da sirrin ƙasa.

Za a ɗaure Imran Khan ne tare da tsohon Ministan harkokin ƙasashen wajen ƙasar Mehmood Qureshi.

Me Zakuce?

KAI TSAYE: Daga  Kasuwar Anchau A Karamar Hukumar Kubau Jahar KadunaFarashin mu yau 30th January 2024Masara Me aure 51k ...
30/01/2024

KAI TSAYE: Daga Kasuwar Anchau A Karamar Hukumar Kubau Jahar Kaduna

Farashin mu yau 30th January 2024

Masara
Me aure 51k 50k 49k
Mara aure 48k 47k

Farin wake
72k 71k 70k

Waken soya
47k 46k 45k 43k

Dawa
46k 45k 44k 43k

Barkono
40k 39k 38k

Shinkafa me bawo
40k 38k 35k

Kwalin sugar mazarkwaila
22k 20k 18k 17k

Buhun Tarugu
30k 29k 28k 27k

Taki urea 26k 25500k
Npk 30k 28k 27k

Dauro
46k 45k 44k

Muna rokon Allah yabamu abin saye amin.

Daga: Aliyu Muhammad.

“Lokaci Yayi da zamu aje bambanci ƙabila, Siyasa, Ko addini mu haɗa kai mu marawa Super Eagles baya domin cimma abun da ...
30/01/2024

“Lokaci Yayi da zamu aje bambanci ƙabila, Siyasa, Ko addini mu haɗa kai mu marawa Super Eagles baya domin cimma abun da muka sa gaba.”

- Ahmed Musa Kyaftin ɗin Super Eagles ❤️🤝🇳🇬💪 🦅

~Fagen Wasanni

ABIN A YABA: Kadan Daga Cikin Ayyukan Alkhairin Da Shugaban Karamar Hukumar Dandume jihar Katsina Hon. Basiru Musa, Ya S...
30/01/2024

ABIN A YABA: Kadan Daga Cikin Ayyukan Alkhairin Da Shugaban Karamar Hukumar Dandume jihar Katsina Hon. Basiru Musa, Ya Shimfida A Cikin Watanni Shidda (6 Month) Kachal.

(1) Ya Gyara Makarantar Isamiyya, Dariqatul Huda Sabon-Layi Cikin Garin Dandume

(2) Yana Gyaran Asibitin (CHC-Dandume), Dandume (A) Ward

(3) Ya Gina Hanyar Ruwa (Rainage) Mai Tsawon-Gaske da Kwalbatochi A Layin Alhaji Buhari Mahuta (C) Ward

(3) Yayi Gyara A Asibitin Dantankari (Primary Health Care) Dake Dantankari Ward

(5) Ya Sanya Falwayoyi Tareda Janwo Wutar A Layin Jabiri Cikin Garin Mahuta Mahuta (C) Ward

(6) Ya Gyara Hanyar Ruwa (Drainage A Hawa-Idi Cikin Garin Dandume

(7) Ya Sanya Falwayoyi Da Tareda Janyo Wuta A Layin Alhaji Buhari Cikin Garin Mahuta

(8) Yayi Ciko Da Burji A Layin Abdulkarim Sule Cikin Garin Mahuta.

Daga Shamsu Wapa Dandume

~Karaduwa Post

YANZU - YANZU: Kotun koli ta mayarwa da kuri’un sa 165k.Me Zakuce?
12/01/2024

YANZU - YANZU: Kotun koli ta mayarwa da kuri’un sa 165k.

Me Zakuce?

INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUNAllah Yayiwa Shahararren Darakta A Farfajiyar Masan'antar Fina-Finan Kannywood AMINU S B...
21/11/2023

INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN

Allah Yayiwa Shahararren Darakta A Farfajiyar Masan'antar Fina-Finan Kannywood AMINU S BONO Rasuwa.

Muna Addu’ar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa Kurakuransa Yasa Aljanna Ce Makomarsa. Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Kyau Da Imani.

Address

Zaria Road Funtua
Funtua

Telephone

+2348063061272

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua Post Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Funtua media companies

Show All