04/07/2023
Daka ta! Ka karanta, ka fahimci wani abu game da 'Layer one', 'Layer Two' da kuma 'Layer zero'.
Bitcoin da Ethereum sune projects mafiya girma a tarihin kasuwar Crypto, haka zalika kowanne da akwai dalilai da s**a sa akayisa saboda a magance wata matsala data damu mutane.
Bitcoin:
Babbar matsalar da BTC yake magancewa itace ta matsalar a samar wa da mutane hanyar da zasu ajiye dukiyar su, ko su tura ta ga wani, ko wani waje ba tare da an samu wani ɗan tsakiya ba (kamar bankuna ko gomnati). Ana samun matsalar wahalhalu, iyakance maka abinda kake da iko dashi na dukiyarka, jinkiri, chaji, ko haraji daga bankunan gargajiya da gomnati.
Ethereum: Ethereum tazo a bayan BTC, a irin zubin tsarin da Ethereum take dashi, ana iya amfani da ita wajen yin duk irin waɗancan abubuwan da BTC yake yi, sai dai ba don haka kaɗai akayi Ethereum ba, ba iya manufar da Ethereum suke so su cimma ba, Ethereum an ƙirƙireta ne musamman don a sauƙaƙa wajen amfani ayi amfani da 'Smart contracts' a ƙirƙiri 'Decentralised Application' akan Blockchain ɗin Ethereum.
A takaice dai, Bitcoin shine farkon abinda akayi akan Blockchain, amma ba'a yi shi don a ɗaura wasu 'Applications' ɗin akan ba, shi kawai ya kawo sauƙin transactions ne, yayin da Ethereum kuma tanayin duk abinda Bitcoin takeyi, amma ita ana iya ɗaura abubuwa da yawa akan Blockchain ɗinta. Shiyasa ake samun Coins da yawa dq ake ɗaurawa akan ERC20, amma ka taɓa jin wani Coin akan Bitcoin Blockchain? (Bazamuyi maganar BRC20 ba anan don kar a rikita jama'a).
Bayan zuwan ETH ne fa da wannan technology ɗin aka fara zuwa da Blockchains kala-daban-daban irin su XRP, BNB, Cardano, da sauran su har zuwa yau ɗin nan kowanne da matsalar da yazo yake maganin ta. Waɗannan Blockchains ɗin sune ake kira da LAYER ONE. 1️⃣
LAYER TWO:
Akwai wasu abubuwa guda uku da ake siffanta Blockchain dashi, sune: Decentralization, Security, da kuma Scalability.
Kusan a duk wani Blockchain da muka sani, sai dai ya ɗauki biyu daga waccen siffofin su bar ɗaya,