05/07/2023
Da Duminsa; Dikko Radda ya tabbatar da za a yi Jami'ar University Of Health Science Katsina a Funtua
A zaman da wasu masu ruwa da tsaki na shiyar Funtua s**a yi da mai girma gwamman jihar Katsina yau Laraba a birnin tarayya Abuja, sun rika kuma gwamman ya amsa za a gudanar da Jami'ar Health Science a garin Funtua.
Kamar yadda Alh Akilu Hassan ( Babaye) Saddaunan Funtua da Dokajin Funtua MD Engnr Tukur Lawal s**a tabbatar wa Katsina Daily News wannan labari mai daɗi da tawagar wakilan shiyar ta Funtua s**a ziyarci gwamma Radda don neman ganin an kafa Jami'ar a shiyar Funtua, sun kuma cimma matsayar da a aje jami'ar a yankin Funtua, kuma gwamma Radda ya amince da bukatunsu, k**ar yadda majiyar ta tabbatar mana.
Daga cikin wadanda s**a halarci zaman da gwamna a Abuja akwai dan majalisar wakilai na mazabar Funtua/Dandume Hon Muntari Dandutse, da tsohon dan majalisar mazabar Hon Dr Mansur Abdulkadir, da ɗan Majalissar Funtua Hon Total.
Sauran sune dan majalisar Faskari Engr Samaila Muazu Bawa da shugaban karamar hukumar Faskari Hon Musa Ado da na Sabuwa Hon Faruk Hayatu da Engr Tukur Lawal da ɗan Masanin Funtua Alh Dr Umar da Amiru Sunusi da sauransu da dama.
Haka kuma a lokacin da Katsina Daily News ta tuntubi ɗaya daga cikin yan tawagar da s**a zauna da gwamna Radda a yau game da jami'ar Hon. Sama'ila Muazu Bawa PhD ya tabbatar mana na da hakan inda ya ce;
"Lallai yanzu muka gama meeting da HE mun nema kuma ya ce za a je ai formalising relocating dinta to Funtua. Ya yi approving" inji Hon Sama'ila Bawa Faskari
Tuni dai gwamnatin tarayya ta sa wa jami'ar hannu inda wasu takardu dake yawo a yanar gizo sun nuna yadda har gwamnatin tarayyar ta fara nada muk**ai ga shuwagabannin da za su gudanar da jami'ar
Idan jami'ar ta tabbata, za ta zama ita ce jami'a ta farko a shiyar Funtua wadda ke da kananan hukumomi 11 daga cikin ƙananan hukumomi 34 da muke da su a jihar Katsina.
of Funtua 01.