18/05/2023
Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasa 16 Da Ake Tunanin Tinubu Zai Nada Ministoci In Aka Rantsar Dashi
Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa na nuni da cewa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fara duba tsarin majalisar ministocinsa da kuma ta masu kula da tattalin arziki.
Ga jerin sunayen su kamar haka;
1, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje (Kano) Ministan harkokin noma da raya yankunan karkara
2, Gwamna Nyesom Wike (Ribas) - Ministan harkokin cikin gida.
3, Dakta Kayode Fayemi - Ministan harkokin kasashen waje.
4, Farfesa Peter Okebukola - Ministan Ilimi.
5, Malam Nuhu Ribadu Ministan harkokin 'yan sanda.
6, Sanata Aisha Binani - Ministar wutar lantarki.
7, Babatunde Ogala - Ministan shari'a.
8, Wale Edun - Ministan kudi, kasafi da tsare-tsare.
9, M**o Boyo - Ministan mai.
10, Ayo Abina - Karamin ministan tsare-tsare.
11, Femi Gbajabiamila - Shugaban ma'aikata.
12, Yewande Sadiku - Ministan masana'antu.
13, Farfesa Yemi Oke
14, Iyin Aboyeji
15, Dayo Israel
16, Uju Ohanenye
Kamar dai yadda majiyar wacce ba a bayyana sunanta ba ta bayyana, wadannan su ne sunayen manyan ‘yan siyasar da ake tunanin Tinubu zai ba ministoci, da kuma ma'aikatun da za a tura su:
Sai dai jaridar The Guardian ta wallafa cewa akwai wasu daga cikin ministocin gwamnatin Buhari da s**a aika kokon bararsu zuwa ga Tinubu. Ta ce wasunsu tun kan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Faransa s**a rika aika masa da sakonni na neman a sanyasu cikin wadanda za a yi tafiyar da su.
✍️ Comr Abba Sani Pantami