Sheikh Abdulaziz Ibrahim Almisry

Sheikh Abdulaziz Ibrahim Almisry Assalamualaikum Warahmatullahi wa Barkatuhu. Insha ALLAH zakuringa ganin Karatukan Malam ta wannan S

22/11/2023
17/11/2023

Darasi na 009

17/11/2023

Muhadhara mai taken:
البدع فى الدين

17/11/2023

Muhadhara mai taken:
الشعر والموسيقى فى الدين

DA KAI DA MUTANE SUWA S**A HUTA BAYAN KA MUTU?Manzon rahama (s a w) yace: bawa mumini yana hutawa bayan ya mutu daga wah...
16/11/2023

DA KAI DA MUTANE SUWA S**A HUTA BAYAN KA MUTU?

Manzon rahama (s a w) yace: bawa mumini yana hutawa bayan ya mutu daga wahalhalun duniya da cutarwarta zuwa ga rahamar Ubangiji, shi kuma bawa fajiri wato mai sabo, bayine suke hutawa da garuruwa da itatuwa da dabbabi dashi, bayan mutuwarsa. Sahihul Bukhari (6512).

Dan uwa kar ka yarda munin aikinka yasa ace an huta dakai bayan ka mutu.

Allah kasa mune zamu huta bayan mutuwa ba hutawa za'ayi damu ba.

14/11/2023

WA'AZIN MATA .

Daga Masallacin Juma'ah na garin Lambu Tofa L.G.A. Jihar Kano

Sheikh Abdul'aziz Ibr

YAN UWANTAKAR ADDINIYan uwa kamar gabobin jikine in daya yayi ciwo kowace gaba ciwon ya shafeta, lallai ciwon zaluncin d...
11/11/2023

YAN UWANTAKAR ADDINI

Yan uwa kamar gabobin jikine in daya yayi ciwo kowace gaba ciwon ya shafeta, lallai ciwon zaluncin da ya shafi mutanen Gaza ya shafemu, muna jin radadin zuciya da qunci a cikin zukatanmu don yan uwanmu.

ALLAH ga bayinka ya Allah, ka saka musu ka kawo musu dauki ta inda bamuyi zato ba.

KUJI TSORON CIN WUTA BAL BAL (masu cin dukiyar marayu)Wata baiwar Allah ta bani labarin yadda yan uwan mijinta s**aiwa d...
09/11/2023

KUJI TSORON CIN WUTA BAL BAL
(masu cin dukiyar marayu)

Wata baiwar Allah ta bani labarin yadda yan uwan mijinta s**aiwa dukiyar marayu cin kaca, s**ai mata fata fata, sun sayar da kaddarar marayun yadda s**aga dama s**a raba kudin kuma hankalinsu kwance.

Ina jin korafinta ina tuna girman masifar ga masuyi, dan uwa wallahi dukiyar maraya cinta da zalunci bala'i kake ciwa kanka, don kuwa wuta kake ci bal bal hurarra, haka Allah madaukakin sarki ya fadi, masu cin dukiyar marayu bisa zalunci illa iyaka suna cin wutane a cikinsu, kuma zasu shiga wuta.

Zalunci ga kowaye haramun ne b***e maraya marar uba, abun tausayi bawan Allah, haba dan uwa kaji tsoron Allah ka kiyaye dukiyar marayun da aka baka amanarta kar kacita da zalunci, in bazaka iya rikewa ba kar ka karba tun farko, don kuwa sharri zata zama gareka, ya zakaji in kai ka mutu akayiwa ya'ya'nka haka?

Allah ka jikan iyayen marayu ka kare musu dukiyarsu daga azzalumai.

Da ɗan Adam yasan ranar mutuwarsa da bai gama rayuwa cikin jin dadi ba, da rayuwarsa bata cika burinta ba anan duniya, d...
08/11/2023

Da ɗan Adam yasan ranar mutuwarsa da bai gama rayuwa cikin jin dadi ba, da rayuwarsa bata cika burinta ba anan duniya, da kuma manufar halitta bata tabbata ba, amma cikin iko da tausayin ubangiji sai ya boye mana ranar mutuwa, don muyi rayuwa mai dadi, bukatarmu ta biya.

~ Sheikh Abdul'Azeez Ibrahim Almisry

NI'IMACE BABBA RASHIN SANIN RANAR MUTUWA
08/11/2023

NI'IMACE BABBA RASHIN SANIN RANAR MUTUWA

FADAKARWA, TUNATARWA DA WA'AZANTARWA
08/11/2023

FADAKARWA, TUNATARWA DA WA'AZANTARWA

BAKA DA MASOYIN DA YAKAI MAI TALLATA MAKA ALHERIDuk masoyanka cikin dangi da iyalai masoyan kane amma basu kai masu tall...
07/11/2023

BAKA DA MASOYIN DA YAKAI MAI TALLATA MAKA ALHERI

Duk masoyanka cikin dangi da iyalai masoyan kane amma basu kai masu tallata maka alheri ba, koda kuwa basa cikin danginka, ba soyayyar da ta kai nunawa mutum wani aiki na alheri anan duniya don ya ribaci sakamakon sa a lahira.

Dan uwa kar ka rudu da duniya in an sanar dakai alheri yi iyakar iyawarka da kyakykyawar manufa Allah yasan niyyarka zai kuma saka maka bisa niyyarka, kar ka fassara mai maka nuni da alheri a matsayin mai takura maka, a'a maimakon haka kamata yayi ka masa tukuici don gobe kiyama sai kafi kowa farin ciki da alherin da ya maka nuni zuwa gareshi.

Duk abunda ka mallaka na magada ne, abunda ka aikata na alheri shine naka, kar kayiwa kanka mugunta alhali kana da dama a yau, kar kace ai nayi aikin alheri da yawa, a'a baka san wanda Allah zai karba ba, cigaba da aikata alheri har karshen rayuwarka, don kuwa shine kadai ribarka.

Dan uwa mai wa'azi da kiran mutane zuwa ga alheri kar kayi zuciya kuma kar ka gaza, amma kasani za'a maka fassara iri iri, kar wannan ya dameka kowa da irin tunaninsa, tsarkake niyyarka nemi yardar Allah don kuwa itace ribarka.

Allah sakawa masu mana nuni ga alheri da alheri.

~ Sheikh Abdul'Azeez Ibrahim Almisry

07/11/2023

Tafsirin Al-Qur'ani cikin Suratul Tahrim Darasi na 01

04/11/2023

19. ADDURARU ALBAIHIYYA.

Dr. Usman Ibrahim Sulaiman Giad

BUSHARA GA MASALLATAManzon Allah (s a w) yace: ba wanda zai shiga wuta matukar yana sallah kafin fitowar rana da kuma ka...
02/11/2023

BUSHARA GA MASALLATA

Manzon Allah (s a w) yace: ba wanda zai shiga wuta matukar yana sallah kafin fitowar rana da kuma kafin faduwarta. (Sahihu Muslim).

Musulmi masu sallah kunji dadinku, karka ka yarda sallar la,asar ta kaika bayan magariba haka kar ka bari sallar asuba ta kaika safiya bayan fitowar rana, lallai kowace sallah da lokacinta kar ka bari lokacin ya wuce ba tare da wani uzuri na shari'a ba.
Allah ka azurtamu da yin sallah akan lokacinta.

MUCI GABA DAYI MUSU ADDU'AMai imani zaiyi tsananin baqin ciki da zubar da hawaye kai harma ya gagara barci in yaga irin ...
02/11/2023

MUCI GABA DAYI MUSU ADDU'A

Mai imani zaiyi tsananin baqin ciki da zubar da hawaye kai harma ya gagara barci in yaga irin wulaqanci da tozarci da cin mutunci ga mata da yara da magidanta da basuji ba basu gani ba na kisan gillah da isra'ila takeyi ga yan uwanmu musulmi falasdinawa.

Kuma duniya tasa kyamara tana daukar hoto ana gani ana jin dadi, amma an gagara yin komai don kare rayukansu da dukiyarsu, abunda ake iyayi kawai shine daukar hoton abunda yake faruwa.

Allah ka kawo musu mafita ka nuna mana ikonka akan azzalumai masu zubar da jinin bayinka bisa zalunci, Ubangiji kaine mahaliccinsu ka kawo musu agajinka da rundunar mala'iku da ba'a ganinsu.

Allah ka qasqanta isra'ila da duk masu goyon bayansu koda a
cikin musulmai suke ya Allah, don Allah kar mu gajiya dayi musu addu'a, Allah ka sani iya abunda zamu iya kenan, Allah ka shaida muna tsananin qin zalunci da azzalumai.

IN TUNANINKA ME ZA'A SAKA MAKA DA SHI NE KAR KAYI ALHERIUbangiji ya tabbatar dan adam akwaishi da butulci ga wanda ya ma...
02/11/2023

IN TUNANINKA ME ZA'A SAKA MAKA DA SHI NE KAR KAYI ALHERI

Ubangiji ya tabbatar dan adam akwaishi da butulci ga wanda ya masa alheri, don haka ba yadda ka iya dashi sai wanda Ubangijin ya kare, amma kar ka zaci rashin butulci ga dan Adam, in zaka masa ko menene ka masa don Allah, dabi'ace a jinin mutane.

Kayi don Allah shi zai saka maka da mafificin sakamako kuma zai iya turo wani ya maka alherin da kayi zato daga wanda ya maka butulci.

30/10/2023

Sheikh Habibu Yahaya Kaura. Wa'azi a Masallacin Kukadi Misau

28/10/2023

037 TAFSIR SURATU HIJRI

Imam Muh'd Fadlu Nasir

Masallacin JIBWIS Unguwar Gado, Bauchi

27/10/2023

Shugaba Imam Muhammad Manga Abba Misau

27/10/2023

Shugaban Majalisar Malamai tare da Alaramma Yusuf Abdulkadir Goje

27/10/2023

WALIMAH GOMBE 2023

Walima kai tsaye da yake gudana daga Masallacin Bolari Gombe

27/10/2023

Alkali Ridwan Abubakar tare da Alaramma Yusuf Sulaiman Jama'are

27/10/2023

Malam Tata Azare tare da Alaramma Umar Alhassan

27/10/2023

Malam Ya'u Sallau Hardawa tare da Alaramma Muhammad Idris Misau

27/10/2023

Wa'azin Katagum Zone daga masallacin JIBWIS Federal Low-cost Misau
27/10/2023

25/10/2023

TA'ALIKI

Mai Wa'azi na (5).

Dr. Shu'aibu Abubakar.

25/10/2023

RIKICIN FALASDINAWA A YAU TSAKANIN GASKIYA DA KARYA.

Mai Wa'azi na (4).

Imam Abdurrahman Ibrahim Idris

25/10/2023

KASANTUWAR KASAR SHAM A TSAKANIN YAHUDAWA DA MUSULMI.

Mai Wa'azi na Uku (3).

Dr. Ibrahim Adam Umar Disisna.

25/10/2023

YADDA MANZON ALLAH (S.A.W) YASHA FAMA DA YAHUDAWA A MADINA.

Mai wa'azi na biyu (2)

Sheikh Shaya'u Yusha'u

25/10/2023

YADDA AL-QURANI MAI GIRMA YAKE KALLON YAHUDAWA.

Dr. Usman Ibrahim Sulaiman Giade

Address

Bauchi
Bauchi

Telephone

+2348065780464

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Abdulaziz Ibrahim Almisry posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sheikh Abdulaziz Ibrahim Almisry:

Videos

Share