AlMizan

AlMizan A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora. An organ of the Islamic Mov
(6)

Bayar da tallafin wutar lantarki kashi 85 na ƙara nuna Tinubu mai son jama'a ne, inji Minista IdrisMinistan Yaɗa Labarai...
06/04/2024

Bayar da tallafin wutar lantarki kashi 85 na ƙara nuna Tinubu mai son jama'a ne, inji Minista Idris

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki kashi 85 cikin 100 da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke yi ya ƙara nuna gwamnatin a matsayin dimokiraɗiyya mai son jama’a.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a jawabin sa na buɗe Taron Ministoci Karo na 4 a Cibiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa da ke Abuja.

Ministan ya ce: “A kwanan baya, Gwamnatin Tarayya ta fitar da wani tsari na cigaba a fannin samar da wutar lantarki, wanda ke da nufin bunƙasa wadatar wutar lantarki ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

“Wani muhimmin al'amari na wannan tsarin shi ne gwamnatin Tinubu na ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ga kashi 85 na masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayin gwamnatin dimokaradiyya mai son jama'a tare da yin ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kashi 15 na masu amfani da wutar lantarki kawai.”

Tun da farko, Ministan ya bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu ta samu a baya-bayan nan. A cewar Idris, “Tun bayan ganawar da muka yi da ku (’yan jarida) na baya-bayan nan an samu gagarumar nasara a tattalin arziƙinmu, kasancewar dukkanmu shaida ne kan yadda ta hanyar aiwatar da wasu sauye-sauye na tattalin arziƙi, kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta daidaita, sannan kuma naira yana samun ƙarfi kullum.

“Kafa Majalisar Daidaita Tattalin Arziƙi da Tawagar Gudanar da Tattalin Arziƙi na Shugaban Ƙasa na kwanan nan ya jaddada ƙudirin Shugaban Ƙasa don samar da wani tsari mai muhimmanci na gudanar da tattalin arziƙi wanda ke yin amfani da ƙwarewa da fahimtar manyan masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu. Waɗannan ƙungiyoyin za su zama dandamali don tattaunawa mai ƙarfi, bincike, da yanke shawara don haɓaka ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa, samar da ayyukan yi, da wadata ga dukkan 'yan Nijeriya.

“Ƙaddamar da Asusun Raya Gine-gine na Sabunta Fata (RHIDF) yana da niyyar tara kusan naira tiriliyan 20 don saka hannun jari a sassa masu muhimmanci kamar su tattalin arziƙi, sufuri, noma, da Fasahar Sadarwar Bayanai (ICT) da sauransu.

“Asusun yana neman tallafawa ayyukan da ke haɓaka ci gaba, samar da guraben aikin yi, da haɓaka fitar da kayayyaki zuwa ketare.”

Idris ya ƙara da cewa, “Ayyukan da asusun zai sa a gaba sun haɗa da gina babbar hanyar Legas zuwa Calabar da aka fara kwanan nan, titin Sokoto zuwa Badagry, Legas zuwa Kano, hanyar jirgin ƙasa na Gabas da zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da na jiragen sama a faɗin ƙasar.

“Don faɗaɗa hanyoyin samun ilimi a matsayin makamin yaƙi da talauci, Shugaban Ƙasa ya sanya hannu kan ƙudirin dokar Lamunin Ɗalibai ta 2015, ta zama doka. Wannan yunƙurin ya wuce doka kawai - hanya ce ta juyin juya hali don kafa tsari na dindindin wanda zai tallafa wa neman ilimi daga matasanmu.

Allah ya bayyanar da Fatima Hasan cikin aminci!Assalamu alaikum.Yan'uwa muna barar adu'arku ga yar'uwarmu Fatima Hassan ...
03/04/2024

Allah ya bayyanar da Fatima Hasan cikin aminci!

Assalamu alaikum.
Yan'uwa muna barar adu'arku ga yar'uwarmu Fatima Hassan wacce aka fi sani da (baby).
Yau kwana takwas kenan muna neman ta ba mu gan ta ba sakamakon Ta bar gida nan U/Mu'azu za ta je Kawo amso magani sakamakon rashin lafiya da take fama da ita, shi kenan ba mu kara jin labarin ta ba.
Mun kira wayarta a kashe.
Mun bibiyi wajan masu maganin, babu wani labari
Don Allah yan'uwa a sa ta a addu'a Allah ya bayyanar da ita albarkacin wannan wata mai alfarma.
Sannan don Allah duk wanda yake da labarinta ya taimaka ya tuntube mu ta wadannan lambobin.
Kuma don Allah 'yan'uwa a taya mu yadawa.
08147775815
07063843532
07019335881
Sako daga Nura Muhammad Unguwar Mu'azu

KADA MU SHAGALA BAYIN ALLAH! MU TASHI, MU MIKE, MU NEMI YARDAR ALLAH!!SALLOLIN NAFILA A DARAREN 21, 22, 23, 24 DA 25 GA ...
01/04/2024

KADA MU SHAGALA BAYIN ALLAH!
MU TASHI, MU MIKE, MU NEMI YARDAR ALLAH!!

SALLOLIN NAFILA A DARAREN 21, 22, 23, 24 DA 25 GA RAMADAN

🌹🌹🌹🌹🌹🥀🌹🌹🌹🌹🌹

DAREN 21

1.Wanka na tsarki da niyyar Ibadah. An so ya kasance kafin sallar Magrib.

2. Sallah Raka'a 8 - Fatiha 1 , Surah 1 wadda ta sawwaka.

3. Sallah Raka'a 2 , Fatiha 1, Suratul Ikhlas 7 a kowace raka'a. Istighfari 70 bayan sallama.

4. Sallah Raka'a 100 - Fatiha 1, Suratul Ikhlas 10 ko 11 a kowace raka'a.

5. Karanta Addu'ar Jaushinul kabeer. [Addu'ar da Mala'ika Jibril ya zo ma Manzon Allah (sawa) a Ranar Yakin Badar]

Ana son mutum ya raya wannan dare da ibada.

Idan da hali goman karshe na watan Ramadhan a yi Itikafi a masallaci.

DAREN 22

Sallah Raka'a 8, Fatiha 1, Surah 1 wadda ta sawwaka.

DAREN 23

1. Wanka na Tsarki da niyyar Ibadah. An fi so ya kasance kafin sallar Magrib

2. Sallah Raka'a 8, Fatiha 1, Surah 1 wadda ta sawwaka.

3. Sallah Raka'a 2, Fatiha 1 Suratul Ikhlas 7 a kowace raka'a. Istighfari 70 bayan sallama.

4. Karanta Suratul Ankabut, Suratul Rum, Suratul Hamim Dhukan,

5. Karanta Suratul Qadr 1000

6. Sallah Raka'a 100, Fatiha 1, Suratul Ikhlas 10 ko 11 kowace raka'a

7. Yawaita Du'a'ul F***j.

8. Ziyaratul Hussain (as)

9. Karanta Addu'ar Jaushinul kabeer

DAREN 24

Sallah Raka'a 8, Fatiha 1, Surah 1 wadda ta sawwaka.

DAREN 25

Sallah Raka'a 8, Fatiha 1 Suratul Ikhlas 10 ko wace raka'a.
🎄🎄🎄🎄🎄🌺🎄🎄🎄🎄🎄

©️ SahihulAsrWaz-ZamaanInstituteYola

[email protected]

KADA MU SHAGALA BAYIN ALLAH! MU TASHI, MU MIKE, MU NEMI YARDAR ALLAH!!Saboda yau da dare Litinin 22 ga Ramadan shi ne da...
01/04/2024

KADA MU SHAGALA BAYIN ALLAH! MU TASHI, MU MIKE, MU NEMI YARDAR ALLAH!!

Saboda yau da dare Litinin 22 ga Ramadan shi ne daren 23, wato daren Lailatul Kadri na karshe ga wannan hadisin don mu dauki darasi:

An karbo daga Annabi (S.A.W) ya ce: Annabi Musa (Alaihis Salam) ya ce: Ya Ubangijina ina son kusancinka. sai Allah Ya ce: Kusancina ga wanda ya farka (raya) a Daren Lailatul kadari ne.
Sai Annabi Musa (AS) Ya ce: Ya Ubangijina Ina nufin (buƙatar) rahamarKa. Sai Allah Ya ce: Rahamata ta tabbata ga wanda ya yi rahama ga miskinai a daren Lailatul kadari.
Sai Annabi Musa (AS) ya ce: Ina son tsallake siradinka. Sai Allah Ya ce, Wannan ga wanda ya yi sadaka da abin sadaka a daren lailatul kadari ne.
Sai Annabi Musa (AS) ya ce: “Ya Ubangijina ina so daga itatuwa da ‘ya’yan itatuwan a Aljannah. Sai Allah ya ce: “Wannan ga wanda ya yi Tasbihi a daren Lailatul kadari ne.
Sai Annabi Musa (AS) Ya ce: Ya Ubangijina ina son in tsira daga wuta. Sai Allah Ya ce: “Wannan ga wanda yake neman gafara a daren Lailatul kadari ne.
Sai Annabi Musa (AS) ya ce: “Ya Ubangijina ina son yardarKa. Sai Allah Ya ce: Yardata tana ga wanda ya sallaci raka'a biyu a daren Lailatul kadri.
📚Bihar Al-Anwar 95:145.
..عن النبي ص أنه قال: *قال موسى ع: الهي اريد قربك، قال: قربي لمن استيقظ ليلة القدر، قال: إلهي أريد رحمتك قال: رحمتي لمن رحم المساكين ليلة القدر، قال: إلهي أريد الجواز على الصراط، قال: ذلك لمن تصدق بصدقة في الليلة القدر، قال: إلهي أريد من أشجار الجنة وثمارها، قال: ذلك لمن سبح تسبيحة في ليلة القدر، قال: إلهي أريد النجاة من النار، قال: ذلك لمن استغفر في ليلة القدر قال: إلهي أريد رضاك، قال: رضاي لمن صلى ركعتين في ليلة القدر*.
📚بحار الانوار ٩٥ : ١٤٥.

28/03/2024

KADA MU SHAGALA BAYIN ALLAH!
MU TASHI, MU MIKE, MU NEMI YARDAR ALLAH!!

SALLAR DAREN SHA TARA GA WATAN RAMADAN, DAREN LAILATUL QADRI.

Yau Alhamis 18 ga watan Ramadan shi ne dare na farko daga cikin dararen lailatul Qadri, wato daren 19, 21, da 23. Wadannan sune darare na lailatul Qadri.

AYYUKAN DAREN YAU 19 GA WATAN RAMADAN

1. Ana so a yi wanka irin na Ibada a daren yau. Kuma an fi so a yi shi a farkon daren.

2. Karanta Ziyarar Imam Husain (AS). Yana daga cikin ayyuka mafi girma a wannan dare.

3. Tsine wa makashin Wasiyyin Manzon Allah (Imam Ali (AS) sau 100. "Allahumma ila'an man qatala Amirul Muminin" kafa 100.

4. Tunawa da kisan da aka yi wa Imam Ali (AS).

5. Karanta Du'a'ul Jaushanil Kabir mai dauke da sunayen Allah 1000.

6. Karanta Du'a'ul Khumail

7. Karanta "Inna Anzalnahu" kafa 1000

8. Karanta "Astagfirullaha rabbi wa atubu ilaihi," kafa 100.

9. Akwai A'amal din da ake dora Alkur'ani a kai. Yayin da ake karanta addu'ar ana tawassuli da Allah da Manzo tare da Iyalan gidan sa.

10. Sallah mai raka'a 50, Fatiha da Izazul a kowace raka'a

11. Sallah mai raka'a 2 Fatiha da Kulhuwallahu 7 a kowace raka'a. Bayan Sallama sai a karanta "Astagfirullaha Rabbi wa atubu ilaihi" kafa 70 .

12. Sallah mai raka'a 100, sallama 50. Fatiha da Kulhuwallahu 10 a kowace raka'a. Akwai Falala mai Yawan Gaske.

Ya zo a ruwaya cewa, duk wani wanda ya yi wannan Sallar, ba zai tashi daga inda ya yi Sallar ba har sai Allah ya gafarta masa zunubansa tare da na Iyayensa. Sannan Allah zai aiko da wasu Mala'iku wadanda za su rubuta masa lada har shekara mai zuwa. Kuma za a sa wasu daga cikin Mala'iku su yi ta gina masa hamshakin gida a cikin Aljannah tare da 'dasa masa bishiyoyi a cikin gidan Aljannah. Duk wanda ya yi wannan ba zai bar Duniya ba har sai Allah ya nuna masa duk wadannan abubuwan.

Daga Jawad Adamu Tsoho


Dole ne mu daina barin bambancin addini da ƙabilanci yana raba kan mu a matsayin mu na ‘yan ƙasa, inji Ministan Yaɗa Lab...
27/03/2024

Dole ne mu daina barin bambancin addini da ƙabilanci yana raba kan mu a matsayin mu na ‘yan ƙasa, inji Ministan Yaɗa Labarai

Wata tabbatacciyar hanya ta samun haɗin kan ‘yan Nijeriya wadda ba ta bari bambancin ƙabilanci, addini, da siyasa ya raba kan mu ba ita ce ta samar da wani labari mai ban sha’awa na ƙasa, mai ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya, inji Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai.

Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai ga ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, shi ne ya ruwaito hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce Idris yana jawabi ne a wajen taron farko na Masu Magana da Yawu wanda Cibiyar Hulɗa Da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya a ranar Talata a Abuja.

Da yake jawabi kan taken taron, wato “Canza Labari, Canza Al’umma”, ministan ya ce bisa la’akari da bambance-bambancen da Nijeriya take da shi, akwai buƙatar a samar da haɗin kan ƙasa wanda ya zarce ƙabilanci, addini, da siyasa ta hanyar ƙirƙiro da labari mai ban sha’awa na ƙasa, wanda ke ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Ya ce babban gangamin wayar da kan jama’a na ma’aikatar sa mai taken “Kundin Tsarin Ɗabi’un Nijeriya” wanda nan ba da daɗewa ba Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da shi, ya ƙunshi yarjejeniyar zamantakewa tsakanin ƙasar da ‘yan ƙasar, kuma zai kasance wani shiri na tsarin ɗabi’un ƙasa wanda ke bayyana ‘yan Nijeriya da kuma ƙarfafa halayen su a matsayin su na ’yan ƙasa.

Idris ya ce, “Abu na musamman game da wannan Kundin Ɗabi’un shi ne yarjejeniya ce ta zamantakewa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa kuma tana ɗauke da Manyan Wajibai Bakwai na ƙasar Nijeriya ga ‘yan ƙasa da kuma Alƙawura Bakwai na ‘yan ƙasa ga da ƙasar su. Jigon Kundin Ɗabi’un shi ne dole ne gwamnatin da zaɓaɓɓu da naɗaɗɗun wakilai ke wakilta ta cika wasu muhimman alƙawura don samun muhimman alƙawura daga 'yan ƙasa.”

Haka kuma ya yi tsokaci kan amana a matsayin ginshiƙin hanyar sadarwa mai inganci kuma mai ɗorewa, yana mai cewa yayin da makomar sadarwa ke nuni ga fasaha, fasahar za ta iya yin tasiri mai ma’ana ne kawai idan aka ɗora ta kan amana.

Ya ce: “Amana ta kasance muhimmin abu wajen gina dangantaka; na kai, na ƙungiya, har ma da na al’umma.

"A matsayin mu na masu magana da yawu, muna buƙatar mu yi ƙoƙari na gaske don gina amana da maido da fata tagari a duk inda muke. Dole ne ginawa da kiyaye amana ya zama wani nauyi da ya rataya a wuyan kowa."

Tsaro: Gumi bai fi ƙarfin doka ba, an riga an yi masa tambayoyi, inji Gwamnatin TarayyaGwamnatin Tarayya ta tabbatar da ...
26/03/2024

Tsaro: Gumi bai fi ƙarfin doka ba, an riga an yi masa tambayoyi, inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tuni jami’an tsaro s**a yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, tambayoyi kan kalamansa na baya-bayan nan kan ‘yan bindiga a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja a ranar Litinin.

A cewar ministan: “Gwamnati za ta yi komai don samun duk wani bayani da ake buƙata don magance matsalolin mu, jami’an tsaro suna nan suna aiki.

“Sheikh Gumi ko wasu mutane ba su fi ƙarfin doka ba. Idan yana da wasu shawarwari ƙwarara da s**a dace kuma masu inganci da jami’an tsaro za su yi aiki da su, to za su ɗauka, amma idan suna tunanin shi ma yana yin wasu kalamai ne na ganganci, za a tsawata masa. Babu wanda ya fi ƙarfin doka.”

Idris ya ƙara cewa, “Bari in faɗa maku wani abu. Kuma ina sane da cewa jami’an tsaro sun gayyace shi don amsa tambayoyi.

“Idan ka yi wani kalami musamman kan tsaron ƙasar mu, ya zama wajibi jami'an tsaron ƙasar mu su yi ƙarin tunani kan hakan kuma suna yin haka. Babu wanda ya fi ƙarfin doka.”

Obasanjo ya yi gaskiya!A daina bai wa tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fenshon fitar hankali
25/03/2024

Obasanjo ya yi gaskiya!
A daina bai wa tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fenshon fitar hankali

These are the headlines in today’s edition of The Guardian.

Get The Guardian on the newsstands for the latest in world news, sport and insightful analysis or click the link in Bio to subscribe to our e-paper

Ku cusa ɗabi'u nagari a zukatan 'ya'yan ku, kiran Ministan Yaɗa Labarai ga iyayeMinistan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, A...
24/03/2024

Ku cusa ɗabi'u nagari a zukatan 'ya'yan ku, kiran Ministan Yaɗa Labarai ga iyaye

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su jajirce wajen ganin sun cusa halaye masu kyau a zukatan ‘ya’yan su.

A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabiu Ibrahim, ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa ministan ya yi wannan kiran ne a Kaduna ranar Asabar, a wajen taron laccar watan Ramadan da NTA, FRCN, VON da NBC s**a shirya, mai taken “Sauye-sauyen Iyali: Haƙƙoki Da Wajibai a Mahangar Musulunci.”

A jawabin nasa, Idris ya ce iyali suna da wani aiki mai tsarki na sanya ƙa’idojin aminci, tausayawa, da gaskiya, tare da sauran ɗabi’u nagari a zukatan ‘ya’yan su domin su tsara halayen su da shiryar da ayyukan su a tsawon rayuwa.

Ya ce: “Dabi’un na ƙwarai su ne ke tafiyar da yaran mu ta cikin sarƙaƙiyar rayuwar duniya, suna taimaka musu su bambance abu mai kyau da mara kyau da kuma bibiyar matsalolin ɗabi’a cikin haske da imani.

“Ta hanyar koyar da waɗannan dabi'u a gidajen mu, muna ba yaran mu abubuwan da suke buƙata don zama masu riƙon amana da sanin ya-kamata a cikin al'umma."

Ministan ya ƙara da cewa iyali sun kasance ginshiƙin al’umma, wanda ke tattare da addini, ɗabi’u, da al’adu da kuma ginshikin al’umma, wanda ke raya zuri’a mai zuwa tare da inganta zumuncin da zai wuce lokaci da yanayi.

Ya ce ma’aikatar sa na gab da ƙaddamar da Kundin Tsarin Martabar Nijeriya, wanda ya ƙunshi yarjejeniyar zamantakewa tsakanin wannan ƙasar da ‘yan ƙasar, kuma za ta zama wani tsari da manufa ta tsarin ƙimar ƙasa.

Ya ce, “Sabon tsarin, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar a bana, ya ƙunshi Alƙawurran Nijeriya da kuma Ƙa’idojin ‘Yan Ƙasa, waɗanda ke da ginshiƙai bakwai kowanne.

“Gwamnati na da niyyar shigar da waɗannan ɗabi’u cikin tsare-tsare na hukuma, da wanda ba na hukuma ba, da kuma na koyar da sana’o’i don tabbatar da cewa an cusa su a zukatan ‘yan ƙasa.”

Idris ya ce gwamnatin Tinubu ta ba da fifiko wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shirye masu tallafawa da ƙarfafa iyali da kuma tabbatar da cewa kowane mutum ya samu damar yin rayuwa mai daɗi da kwanciyar hankali, tare da isassun damarmaki don cimma buƙatun sa da burin sa.

“Saboda haka ne gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen samar da yanayi mai kyau ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya ta hanyar aiwatar da sauye-sauyen kasafin kuɗi da na kuɗi da nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, rage talauci, da samar da cigaba mai ɗorewa.

“Sauye-sauyen da Mai Girma Shugaban Ƙasa ke aiwatarwa, ba wai martanin da ba a shirya masa ba ne ga matsalolin tattalin arzikin mu; tsare-tsare ne da aka yi tunani a kan su sosai don gudanar da su tare da cikakken Shirin Shiga Tsakani na Jama'a don rage raɗaɗin sauye-sauyen," inji shi.

Ministan ya ce tare da sake fasalin Shirin Zuba Jari na Ƙasa, an ɓullo da wasu ƙarin tsare-tsare don tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen raba kuɗaɗe ga talakawa da marasa galihu a cikin al’umma, yana mai jaddada cewa daga yanzu za a tantance waɗanda za su amfana da Lambar Shaidarsu ta ɗan Ƙasa (NIN) da BVN ko asusun waya da aka tantance.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu ana gudanar da sauyin yanayi a fannin noma, inda ya ce tawagar sa ta yi mamakin irin nasarorin da ake samu a noman rani a lokacin da s**a gudanar da rangadi a wasu al’ummomin manoma a jihohin Kano da Jigawa.

“A ranar Alhamis, na jagoranci Tawagar Sadarwa ta Ƙasa, wadda ta ƙunshi manyan mashawartan Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, da kuma manyan daraktoci na Hukumar Wayar Da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), NTA, VON, da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a rangadin aiki a jihohin Kano da Jigawa domin ganin yadda sauyin yanayi a fannin noma ke faruwa a sannu-sannu.

“Ziyarar da tawagar mu ta kai wa Shirin Noman Rani na Haɗeja mai samun goyon bayan Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya ya nuna yadda ake gagarumin noman shinkafa, zoɓo, da alkama, da dai sauran amfanin gona da manoman Jihar Jigawa suke nomawa, waɗanda duk shekara suke noma a bakin tekun kogin Haɗeja da Jama'are. Don Allah, dukkan mu mu rungumi noma da kiwo da fa’idar da suke da ita,” inji shi.

Hoto: Minista Idris tare da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Dakta Ahmed Nuhu Bamalli, a wurin taron

Ku yi amanna da Tinubu, matsaloli za su ƙare, inji Ministan Yaɗa LabaraiMINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mo...
22/03/2024

Ku yi amanna da Tinubu, matsaloli za su ƙare, inji Ministan Yaɗa Labarai

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri su yi imani da gwamnatin Tinubu.

Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin buɗa baki da ya yi tare da shugabanni da ma'aikatan kafafen yaɗa labarai wanda ma’aikatar ta shirya a ɗakin taro na Armani Events Centre da ke Kano.

Idris ya ce gwamnatin Tinubu tana aiki tuƙuru domin ganin ta shawo kan matsalar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya ce, "Ma'aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta himmatu wajen tabbatar da gyaran hukumomin da ke ƙarƙashin ma'aikatar da nufin inganta fannin."

Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin na ƙoƙarin farfaɗo da matatun man fetur na ƙasar nan, inda ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki.

Game da cire tallafin man fetur da aka yi, Idris ya ce Nijeriya ta fuskanci raguwar yawan man da ake amfani da shi a cikin gida na kimanin lita biliyan ɗaya bayan cire tallafin, wanda ya nuna kashi 53 cikin 100 na yawan man da ake amfani da shi da farko.

Ya ƙara da cewa, “Hakan ya bayyana yadda ake safarar man fetur ɗin mu ta kan iyakokin ƙasar nan domin amfanar waɗanda ba sa biyan ƙasar nan haraji”.

Ya jaddada cewa cire tallafin man fetur ya zama dole domin waɗanda ba sa biyan haraji sun fi ‘yan Nijeriya cin gajiyar tallafin.

A cewar sa, “Abin da ake amfani da shi na man fetur a cikin gida ya ragu da kusan kashi 53 cikin 100, ma’ana sama da lita biliyan ɗaya da muke amfani da ita a lokacin cire tallafin ta ƙare a yanzu. Kuma tambayar da za ku yi wa kan ku ita ce: Ina wannan man ya ke zuwa?

“Yaya ba zato ba tsammani amfanin cikin gida ya ragu da kashi 53 cikin 100? Wannan yana nufin cewa wannan man fetur ɗin ya samo hanyar fita daga kan iyakokin mu don amfanin waɗanda ba sa biyan haraji ga ƙasar nan.

“Ba shi da ma’ana a ci gaba da ba wa gidan wani tallafi lokacin da rufin ku ke ɗiga, taga ta karye, kuma yaron ku bai je makaranta ba. Dole ne ku tallafa wa kan ku kafin ku ba wa wani tallafi.”

A kan abin da gwamnati ke yi don rage wahalhalun da ke tattare da cire tallafin, sai ya ce, “Akwai ƙarin albashi na wucin gadi na naira 35,000 a kowane wata na wata shida – an riga an biya na watanni huɗu.

“Gwamnonin Legas, Osun, Oyo, Ogun, Jigawa, Adamawa, Ebonyi, Neja, Ondo da Ekiti su ma sun ɗauki wannan shiri na Gwamnatin Tarayya na biyan albashin ma’aikatan su. An buƙaci sauran gwamnatocin jihohi su aiwatar da irin wannan.

“An kafa Kwamiti Uku kan sabon mafi ƙarancin albashi kuma tuni ya fara aiki. Masu ruwa da tsaki a shiyyar siyasa guda shida su na gabatar da takardar da ke nuna sabon mafi ƙarancin albashi ga gwamnati, ana ci gaba da tattarawa.

“Shugaba Tinubu ya amince da kafa Asusun Tallafawa Ababen More Rayuwa ga Jihohi don su zuba jari a muhimman wurare da za su samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa kuma akwai shirin fitar da motoci masu amfani da gas na naira biliyan 100, don isar da motocin bas masu amfani da gas, da kayan aikin canza motocin.

"Tuni, Shirin Shugaban Ƙasa na Iskar Gas (CNG) ya fara tallafa wa abokan hulɗa masu zaman kan su da na gwamnati a wannan fanni.

“An fara bayar da kuɗi naira 25,000 a kowane wata ga miliyan 15 daga cikin gidaje mafiya talauci da marasa galihu a Nijeriya, wanda aka shirya na tsawon watanni uku. Magidanta 3,140,819 sun riga sun sami biyan kuɗi na farko kafin a dakatar da shirin don dubawa da gyarawa.

“Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a fitar da hatsi tan 42,000 daga Asusun Ajiya na Nijeriya, don raba wa marasa galihu kyauta da Jami'an Tsaron Farin Kaya (DSS) da Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) s**a himmatu wajen sa ido a kan rarrabawar.

“Shugaban ya kuma amince da naira biliyan 100 don tallafa wa Asusun Raya Aikin Noma na Ƙasa (NADF) a shekarar 2024 kuma Ma’aikatar ta fara aiwatar da ayyukan fitar da naira biliyan 200, wanda Shugaban Ƙasa ya amince da shi, ta hanyar sababbin kuɗaɗen shiga tsakani na musamman guda uku wanda aka kafa a matsayin wani ɓangare na matakan kawo sauƙin kawar da tallafin ga 'yan kasuwa, waɗanda su ne: Shirin Bayar da Tallafin Kuɗi na Shugaban Ƙasa (PCGS), Asusun Tallafawa na FGN MSME, da Asusun Fannin Masana'antu na Gwamnatin Tarayya."

Ministan ya ƙara da cewa a wani yunƙuri na sauƙaƙa shiga shirin lamuni na ɗalibai, da magance ƙalubalen da ake fuskanta da kuma inganta yadda ake aiwatar da shi, Shugaba Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattijai takarda inda ya buƙaci a soke da kuma sake kafa dokar lamuni ta ɗalibai.

Daga nan sai ya yi alƙawarin cewa Shirin Zuba Jari na Jama'a zai dawo da ƙwarin gwiwa bayan an yi nazari sosai kan yadda ake tafiyar da shi, inda ‘yan Nijeriya da s**a kammala karatun su a matakin gaba da Bautar Ƙasa (NYSC), da masu riƙe da OND za a riƙa biyan su alawus-alawus na wata-wata, ta hanyar Shirin Bayar da Lamuni na Jama'a har sai sun samu ayyukan yi.

Ya kuma ce shugabannin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da s**a shuɗe ba su tafiyar da babban bankin yadda ya dace ba, amma Tinubu ya dawo da martabar babban bankin da ya ɓata.

"Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa ta fara samar da sakamako mai kyau, saboda tattalin arziƙin ƙasar yana farfaɗowa sannu a hankali, kuma matsalolin za su ƙare," inji shi.

*TSAGE GASKIYA, TA YAU JUMA'A TA FITO!*Jaridar Al-Mizan bugu na 1626 ta fito!Babban labarinta shi ne: Kisan 'yan'uwa 4 a...
22/03/2024

*TSAGE GASKIYA, TA YAU JUMA'A TA FITO!*

Jaridar Al-Mizan bugu na 1626 ta fito!

Babban labarinta shi ne: Kisan 'yan'uwa 4 a Muzaharar Ashura a Sokkwato
*Kotu ta umarci 'yan sanda su biya diyyar Naira miliyan 80.

Akwai kuma labari mai kanu: Jamhuriyyar Niger ta yanke alakar Soji da Amurka.

Sai labarin: Indiya za ta kaddamar da wata doka mai nuna 'wariya' ga Musulmi.

Ku hanzarta neman Jaridar ta wannan mako a wuraren da kuka saba samun ta kan farashin nan na N250 kacal.
Kar kuma ku manta da ziyartar shafinmu na intanet a adireshi kamar haka https://www.almizan.ng
Muna jinjina gare ku masu karatun mu.

Himma ba ta ga raggo! Kai ma za ka iya zama Hafizin Kur'aniIbrahim Musa, Editan Almizan ne ya fassara makalar daga turak...
21/03/2024

Himma ba ta ga raggo! Kai ma za ka iya zama Hafizin Kur'ani

Ibrahim Musa, Editan Almizan ne ya fassara makalar daga turakar Farfesan a Facebook

Yadda Za ka Haddace Shafi Daya Na Al-Qur'ani A Rana A Duk Shekarun Da Kake

Daga Ibrahim Dooba

A shekarar da ta gabata, a ranar Litinin, 4 ga Satumba, na gayyaci membobin guruf din mu na WhatsApp na “One Ayah A Day” wato “Aya Daya A Rana,” da su yi tarayya da ni a sabon gwaji na haddar Al-Qur’ani.

TUSHEN BAYANIN

Wani abokina mai suna Saheed Kunle Ayegboka ya ba ni labarin wani malami wanda karatunsa daidaitacce ne. Da aka tambaye shi tsarin haddarsa, sai ya ce bai kirga shafi ya haddatu har sai ya karanta shi sau 300.

Sau 300 fa! Na tuna ya ba ni labarin ne a motarmu ta zuwa Gwagwalada, inda aka shirya zan yi jawabi kan dashen itatuwa. A cikin motar, kwakwalwata mai tunane-tunane ta fara yin kwarkwasa da ra'ayin aiwatar da tsarin, amma na yi sauri na gargadi kaina, kai sau 300 fa aka ce. "Wa ke da lokacin karanta shafi sau 300?" Na nuna rashin yarda da hakan.

FUSKANTAR TSORONA

Amma na jajirce cewa sai na yi; tunda dai, abin da bai kashe ka ba, ai sai dai ya kara maka karfi. Kuma wace hanya ce mafi kyau don magance manyan matsaloli? Rarraba su zuwa gungu-gungun da za su iya sarrafuwa.

“Ban sani ba ko shi (Sheikh) yakan yi haka ne a zama guda ko kuma yana rarraba maimaitawar ne. Misali, in zauna in karanta shafi sau 300 zai dauke ni kusan sa’o’i 8,” na rubuta wa ’yan guruf din namu a lokacin. Kodayake hakan yana ɗaukar ɗan gajeren lokaci a yanzu.

To maimakon in zaci Shehin na maimaita shafi sau 300 a zama guda ne, me ya sa ba zan tunkari matsalar ta hanyar rarraba zaman karatun ba?

SABANIN NAZARIYYATA

Ga wa]anda s**a karanta littafina "Sirri Daya na dalibai masu hazakar cinye jarabawa da ‘A’," wannan tsarin gaba daya ya saba wa abin da na yi amanna da shi, kuma ya saba wa kimiyyar da ta ce aikin dawo da abu a ka ya fi maimaitawa inganci. Wannan yana nufin cewa a cikin duk abin da na koya na koyar, na fi ba da ƙarfi a aikin dawowa fiye da maimaitawa.

KOYON WANI SABON ABU DA SAMAR DA SABON ILMI

Amma sai na yanke shawarar bincikar shaida. Ga rahotona ga membobin guruf din "Ayah Daya A Rana."

TSARIN

Daga yau, zan rika karanta shafi daya sau 10 bayan kowace sallar farilla. Da ma yana ɗauka ta kusan mintuna 2 da daƙiƙa 30 ne karanta shafi guda.

Don haka zaman mintuna 30 bayan kowace Sallah ba abu ne mai wahala sosai ba. Wannan yana nufin kowace rana zan karanta shafi guda sau 50 ke nan. A cikin kwanaki shida kuma, zai za ma na karanta shi sau 300. Insha Allahu.

SAKAMAKON DA AKE TSAMMANI

Zan gani idan tsarin haddar na aiki ko kuma idan bai yi min aiki ba. Ganin cewa ina da shekaru 44, muhimmancin binciken shi ne zai nuna cewa, kowa a kowane irin shekaru mutum yake zai iya haddace Al-Qur'ani.

A ranar Laraba, 6 ga Satumba, na wallafa sabon sako:

Sabunta bayani a kan maimaita shafi sau 300

Ranar farko (Litinin): Na maimaita shafin sau 40.
Rana ta biyu (Talata): Sau 13 kawai na iya maimaita shi saboda ina da baƙo, kuma muka je gona.
Rana ta uku: Na maimaita sau 50. Rana daya tilo da na cimma abin da na yi niyya. Ina jinjina ga kaina.
Jimla: Maimaitawa sau 103 ya zuwa yanzu.

SAKAMAKO NA FARKO:

Bayan maimaitawa sau100, ban haddace shafin ba. Amma na karu da sanin shafin, kuma karatuna ya kara kyau. Zan iya gama shafin yanzu cikin mintuna biyu. Don haka lokacin karatuna bayan kowace sallah ya koma minti 20 maimakon 30 a baya.

Ko akwai wani rahoto daga waɗanda s**a shiga gwajin? Na tambayi 'yan guruf din mu.

Abin sha'awa, mambobi biyu sun ba da rahoton abubuwan da s**a faru da su. Hajiya Zubaida, wadda ta riga ta haddace AlQur’ani gaba daya, ta gwada tsarin, kuma ta ga yana da amfani:

"Na gwada tsarin a kan ɗaya daga cikin shafukan da ke da wahalar riƙewa. Alhamdulillah tsarin ya yi aiki. Kodayake hakan ya kwace min mintunan bita masu daraja😃😀."

Mamba na biyu Dk. Nasir Mu’azu Kontagora ya ce:

“Na gode, Farfesa. Na yi sau 40 ran Litinin, sau 50 ran Talata, ran Laraba ma sau 50. Haka nan ya kasance gare ni. Har yanzu ban haddace shafin ba, amma karatun ya zama mai sauƙi. Yanzu cikin minti 1 da daƙiƙa 30 nake kammala kowane shafi, don haka, na kwashe mintuna 15 don karanta shafi sau 10. Shukran Wa Jazakallahu Khairan, Prof.”

A wani lokaci, na daina walllafa sabbin bayanai ga membobin guruf din, amma na ci gaba da tattara su a cikin manhajar app Notes na wayata.

Ran Alhamis: Maimaitawa 40 ne kawai na yi.

Juma’a 8 ga Satumba: Bayan sallar subahi na maimaita karatun sau 10 a ranar Juma’a, sai na kirga na maimaita karatun shafin sau 150 ke nan. Kuma na gano cewa, na haddace ayoyi uku (16-18) ba tare da niyya ba. Tun da ina kan tafiya ne ranar Juma'a, na maimaita karatun sau 30 ne kawai domin na yi salla sau uku ne (Wato na hada azahar da la’asar da kuma magariba da Isha).

Ƙarin sabunta bayani: A ranar Asabar na iya maimaita karatun sau 30 ne kawai. Don haka, ya zuwa wannan kwanan wata (9/9/2023), na riga na maimaita karatun shafin sau 203.

Sakamako: Na haddace ƙarin ayoyi biyu ba tare da wani ƙoƙari na haddace su ba - aya ta 19 da 20. Zan iya karanta shafin yanzu cikin minti guda da dakika 40 (1.40). Karatun inji ya shigo ciki ke nan. Wannan yana nufin cewa zan iya karanta duka shafin ko da ban kula ba, kuma ba zan yi tuntube ba. Kamar tuƙi ne, ka isa gida ba tare da tunawa da yadda ka isa gida ba.

Har ila yau, ina da yakinin cewa idan aka fara min kowace aya, zan iya gama karanta ta har zuwa karshe cikin 95% na lokaci. Wannan yana nufin cewa na haddace dukkan ayoyin da ke shafin, amma ban haddace tsarin zubin ayoyin ba.

Bayan maimaici 250, na gano cewa na haddace duk shafin. Yayin da na ci gaba da bin tsarin a wasu shafuka, ta bayyana cewa lambar haddata ita ce 150. Wato, ina tuna da duk shafi bayan na karanta shi sau 150. Wato ina haddace shafi a rana guda. Amma don tabbatar da shi, sai na ci gaba da maimaitawa har sai na karanta shi sau 300.

Da yake ina saurin karanta shafi a yanzu, sai na kara yawan maimaitawar bayan kowace Sallah zuwa 30, wanda ke dauka ta minti 30 ko kasa da haka, domin yanzu ina iya karanta shafi cikin kasa da minti daya.

KAMMAWALAWA:

Lokacin da na yi bidiyon wannan tsarin haddar, kuma na wallafa shi a shafukan sada zumunta, wani abokina mai suna Hashr Garba, ya ce: “Ka samu (formula) ingantaccen tsarin haddar AlQur’ani da kake nema tunda dadewa!” Ya san cewa na yi ta gwajin dabaru daban-daban don haddar Alkur’ani tsawon fiye da shekaru ashirin. Kuma ina ba da garantin cewa wannan shi ne tsari mafi sauki.

Har ila yau, ba shi da bukatar ƙwazo sosai kamar dabarar dawo da hadda. Kowa na ba wannan shawarar, da farko yakan koka game da yawan maimaitawar, amma yakan sami gamsuwa a gaskiyar cewa tsarin yana aiki.

Mafi mahimmanci, kana karantawa ne kawai ba tare da ƙoƙarin haddace wani abu ba. A gare ni, zan iya haddace shafi ɗaya a rana a cikin sa'o'i biyu da rabi. Amma da yake ba ni da horon zama mai tsayi haka, kawai ina yin minti 30 ne bayan kowace salloli biyar.

Ina ba da shawarar maimaita karanta shafi sau 300 ga kowane haziki da ma wanda ba haziki ba. Shin, wannan ba babbar nasara ba ce cewa yanzu dai ba ka da wani uzuri na kasa zama hafizin Qur’ani?

Address

Babban Dodo Zaria
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AlMizan posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AlMizan:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Zaria

Show All