23/09/2022
Ko ka san tusa ta gagari likitoci?
Tusa ba abar kunya ba ce kaɗai, za ta iya kasancewa wata alama ce mai muhimmanci ta yanayin lafiyar jikinka. Amma kuma har yanzu likitoci sun gagara fahimtar lamarinta.
Na tsani in fito fili in yi wannan magana amma ba shakka kam likitoci suna da matsala kan sanin al'amarin da ya danganci yadda tusa take faruwa. Domin a yanzu dai abin kunya ba wani abin a-zo-a-gani da s**a sani game da yadda iskar mai wari ke haduwa a cikinmu.
''Iskar da ke fitowa daga duburarmu, tana gaya mana abin da ya shafi dan taki ne (20cm) a cikinmu kawai,'' in ji Peter Gibson na jami'ar Monash a Victoria ta Australia. Gibson na son sanin abin da ke faruwa a can cikin cikinmu ( nisan 130cm), inda abinci ke narkewa, har a samu tusa a ƙarshe.
Sarrafa abincin da ciki ke yi, ya danganta ne ga mu'amullar da ake yi tsakanin kwayoyin halittarka da irin abincin da ka ci, da aikin samar da kuzari da kayan ciki ke yi, sannan kuma da irin ƙwayoyin halittar da ke jikinka, wanda duka wadannan abubuwa ne da kowanne za a iya samun wata alama tasa a cikin wannan iska (tusa). Samun wani fitaccen sauyi kan yadda warin tusarka yake ka iya kasancewa alamar wata mummunar cuta da ta shafi wani daga cikin dukkanin wadancan abubuwa da muka bayyana a baya wadanda suke haifar da tusar.
Gibson ya ce, '' Mun san dan wani abu kadan game da ita, amma ya kasance abu mai wuyar gaske a san ainahin abin da ke faruwa game da tusa. Saboda haka ne ayarin masanin s**a duƙufa kan wani bincike a cikin 'yan hanjinka, inda za su rika auna iskar tusarka daga wuri zuwa wuri a kowane mataki na narka abinci da kayan ciki ke yi.
Dan muhimmin abin da muka sani a kan tusa kawo yanzu ba shakka ya nuna mana cewa batun tusa muhimmin abu ne da ke buƙatar bincike. Idan ya kasance jikinka na samar da iskar hydrogen da methane da yawa, to hakan na nuna ga alama akwai matsala da yadda cikinka ke sarrafa kayan abinci mai ba wa mutum karfi (carbohydrates).
Misali hakan na sa wasu daga cikin sinadaran wannan kayan abinci mai ba mutum karfi (starche, sugar) su rube a cikin ciki.
Yawan iskar methane ka iya kawo cikas ga yadda hanjinka ke motsawa, abin da ke nufin zai iya haifar maka da matsalar kasa yin bayan gida akai akai, musamman ga mutanen da suke da wata matsala ta hanji. Sai dai kuma abin takaicin shi ne, tak**aimai ba mu san inda wannan iska ta methane take samuwa ba a cikin mutum. ''Abin dai da aka ɗauka kawai shi ne, tana samuwa ne daga can ƙasan babban hanji, amma dai ba mu sani ba,'' in ji Gibson.
Sinadarin hydrogen sulphide ne ke sa tusa ɗoyi ko wari k**ar na rubabben kwai. Bayan damuwa da wannan iska ko wari ke haifar wa mutane idan wani ya yi tusa a wuri, idan mutum yana fitar da iskar da yawa to hakan zai iya kasancewa wata alama ce ta wani ciwo a bangon 'yan hanji wanda zai iya bayar da wani muhimmin bayani,'' in ji Gibson.
Wani babban abin mamaki kuma shi ne, har ya zuwa yanzu fitacciyar hanyar da aka fi iya bincike a kan tusar mutum, ita ce ta numfashi, wato ba ta kai tsaye ba ta dubura. Tun da wata daga cikin iskar da kake fitarwa ta tusarka na shiga cikin jininka, kuma ka fitar da ita ta huhunka, zai iya kasancewa a samu ɓurɓushin tusarka ya biyo ta bakinka.
Sai dai kuma abin takaicin shi ne wannan ba zai nuna maka inda ainahi iskar ta samo asali ba. Sannan kuma wata iskar da jikinka ke fitarwa k**ar wadda kwayoyin bakteriya da ke tsakanin haƙoranka ke fitarwa na iya jirkita sak**akon da za a samu.
Wani zabin kuma shi ne, a ruɓar da kashin mutum, to daga nan iskar da za a samu ta ruɓewar kashin za ta iya zama daya da warin tusarka. Ko da yake a nan ma, ba za a gane matsalolin da ke samuwa ba a farkon narkewar abinci.
To a nan ayarin Gibson na ganin akwai hanyar da za su yi maganin wannan ƙalubale, inda s**a ƙirƙiro 'yar wata mitsitsiyar na'ura wadda mutum zai haɗiye, k**ar ƙwayar magani.
Yayin da take tafiya a cikin mutum daga nan zuwa can za ta rika aika wa wata kwamfuta bayanan irin iskar wurin da ta je, haka kuma za ta riƙa auna wasu abubuwan k**ar yanayin zafin wurin da take da kuma guba ko sinadaran da ke wurin.
Gibson ya ce daga karshe na'urar za ta biyo kashi ta fito.
Ta wannan hanya likita zai iya samun cikakken bayani na duk wurin da wannan na'ura take. Kawo yanzu wadannan masu bincike sun jarraba wannan dabara a kan wasu aladu kuma nan da 'yan watanni suke sa ran gwada ta a jikin mutum.
Idan aka ga cewa wannan 'yar na'ura ba ta da wata illa a cikin mutum, Gibson ya ce, zai samar da matattarar bayanai ta irin iskar da ke cikin mutum wadda ta shafi cutuka daban-daban da kuma yanayin irin rayuwar mutum. Daga nan za a iya sanin irin illa ko matsalar wani magani da ake yi wa mutum na irin wadannan cutuka.
To tun da an gano cewa iskar methane tana da alaƙa da matsalar rashin yin bayan-gida yadda ya k**ata, Gibson yana fatan gano inda wannan iska (tusa) take haduwa da kuma lokacin da take samuwa. A nan kuma, sai ya ce, ''Abin da kawai kake buƙata shi ne, abin da zai rage samar da wannan iska, wanda shi ne, sauyin abinci ko kuma wani magani da zai rage wannan matsala ta rashin yin kashi yadda ya k**ata.
Wanda wannan kuma wata babbar matsala ce a duniya a yau.'' Ya kara da cewa ''to amma ba za mu iya sani ba har sai mun auna mun gani.''
Ba shakka ba za a ga aibun Gibson na dagewa da ya yi a kan wannan lamari na tusa ba. Kamar yadda shi kansa ya ce, ''Abin sha'awa ne sosai, kana ƙara nitsawa a cikin binciken kana ƙara hangen irin hasken da ke tattare da shi.''
Fatanmu dai shi ne ya yi nasarar tabbatar da alƙawarin da ya yi, kada ɗokin ya ƙare da wata tarin iska(tusa) mai dumi kawai.
Daga: Dr Salahudeen Sicey